A Rubuce Take (K'addarata) page 54 Hausa Novel - Novels Elite

A Rubuce Take (K'addarata) page 54 Hausa Novel - Novels Elite

A Rubuce Take (K'addarata) page 55 Hausa Novel - Novels Elite

*H U G U M A*


*_A RUBUCE TAKE_*

      (K'addarata)


*Arewabooks: Huguma*


Page 54



       Tana tsaka da game din taji mararta ta murda,ta dakata tana zare idanu jin wani abu mai danshi ya fara fitowa ta jikinta,gabanta ya fadi,kada dai ace wannan jinin ne da bataso yazo mata?,yanzu ya zatayi?,yi na qarshe da tayi suna tare da latifa,hankalinta a kwance yake,ta dinga kula da ita da ciwon mararta.


          A tsorace tadan miqe don duba jikinta,sai tayi sauri ta koma ta zauna saboda mararta data murda mata,ta dafe marar tana jin yadda danshin ke biyo jikinta,hankalinta ya tashi sosai,kawai sai kuka yazo mata,tana ganin kamar ba zata iya ba. gumi ya fara yanko mata ya gauraye da hawaye,ta soma jan majina tana raba ido.


        Sallamar da yayi cikin falon ya sanyata sake tsorata,sai taji kamar ta tashi ta zura da gudu,idanunshi a kanta,cikin mamakin yanayin da ya ganta a ciki,itama shi take kallo kamar wacce ta aikata wani mummunan abu.


           A nutse ya qaraso,hannayensa zube a aljihun wandonsa


"What's happening?,lafiya?" Tsareshi taci gaba dayi da idanu,saidai qwalla ta cika idanunta fal,har bata iya ganinsa sosai,kallonsa take kai tsaye,kamar mai tsoron wani abu dake a jikinsa,maimakon ta amsa masa sai hawayen ya fara saukowa,ta sake dora hannunta saman mararta dake qara murda mata.


"Me ya faru ne?" Ya sake maimaita tambayar yana sake qoqarin karantar fuskarta,hawayen dai taci gaba da fitarwa,a hankali idanunsa ya sauka saman hannunta,yadan kalli wajen na tsahon wasu mintuna,sai ya matsa gaba a hankali yana qoqarin miqa hannunsa,sai kuma ya janye yana duban qwayar idanunta


"Ciwo cikin yake miki?" Kai ta gyada masa,Hawaye na sake saukar mata,sai ya sake matsowa yana cire hannunsa guda daya daga aljihunsa


"Oh sorry....sannu,tun yaushe?"


"Yanzu" ta fada a narke, zuciyarta tana karyewa,saboda komai yayi mata tana kallonsa banbarakwai,don ba haka ummu ta saba mata ba,indai tace bata da lafiya gaba daya komawa take kamar jinjinniya a wajen ummu,ta yita tattarota tana langabe mata a jiki,takanyi kamar ta maido ciwon a jikinta


"Muje kici abinci,sai mu fita na kaiki kiga likita ko?" Kai ta girgiza da sauri,don ita bata qaunar ma abinda zai sanya ayi mata zancan asibiti,bata qaunar magani sam sam sam,babban abinda yake saka a gansu a rana ita da ummu kenan


"Why.....zaki zauna ne a gida cikin yana miki ciwo?"


"Ai zai daina" ta fada muryarta na rawa,saboda yadda ciwon ya fara mata azaba da gaske,wannan shine karo na biyu daya taba mata haka,duk da cewa duka duka period din nata ma wannan shine yinta na hudu.


"it is not possible ki zauna da ciwo,oya......taso kici wani abun ko kadanne idan ma ba zaki asibitin ba" ya furta yana miqa mata lallausan hannunsa mai dumi,wanda ya wadatu da sassanyan qamshinsa.


          Hannun ta kalla sannan ta rintse idanunta da gaske tana jin yadda ake kartar mararta,yadda tayin sai ya tuna masa koda wasa ba zata taba yarda intentionally su hada hannu ba,don haka kansa tsaye ya miqa hannu ya kamo.hannunta guda daya,ya kuma dagota gaba daya.


          Luuuuu ta tafi jikinsa ba tare data shirya ba saboda wani azabar murdewa da marar ta sakeyi fiye da dazun,kamar numfashin ta zai bar gangar jikinta,take ta zabi bin gangar jikinsa ta yiwa kanta madogara,tana gama samun kyakkyawan masauki saita saki kuka tana kiran sunan ummu,hannayensa ya saka gaba daya ya rufeta da kyau cikin jikinsa.


          A yadda ta samu masauki me kyau cikin jikinsa ya sanya hatta da bugun zuciyarta da kai kawon numfashinta tana jinsa sosai cikin jikinsa,kamar jininsa suke bi cikin kowacce bugawa da zaiyi.


         Sunkuyo da tasa fuskarsa yayi ta gefen fuskarta dake kwance kan qirjinsa da yake ya fita tsayi sosai ya cusa tasa fuskar yana leqata,wani irin kuka take a hankali hade da sheshsheqa,hucin numfashin ta ya daki fuskarsa,sai ya lumshe idanunsa tsigar jikinsa na tashi,ya sake riqeta sosai zai motsa,saita kuma qanqameshi tana sake sakin kukan,abinda ya sanyashi kusan daskarewa a wajen,gaba daya ta manna masa jikinta da kyau,lallausar fatarta takai ko ina a jikinsa ba tare data sani ba,ita din kuma tayi hakane saboda batason su motsa daga wajen,ta tabbatar ta bata wajen da jini,bataso kuma ya gani,kunya takeji,da wanne ido zata kalleshi?.


         "Let's move from here,mu koma daki ki kwanta na fidda mota kiga likita,jikinki shacking yakeyi" yana fada ya sunkuya kawai ya dauketa cak,bata da sauran zanbi sai kawai ta boye kanta cikin jikinsa,bayan ta saka hannu ta riqeshi da kyau.


         Bai lura da komai ba sai daya shimfide ta saman gadonsa sannan yaga hannunsa ya baci,ya daga kai ya kalleta,sake saka masa kuka tayi,abinda taketa gudu kenan,ta rintse idanu tana jiran jin fada ko duka daga wajensa,kamar yadda yaa ma'aruf ya taba mata saboda kawai ta kawo abinci ya bata flask din ya riqe hannunsa ya baci.


           Maimakon taji abinda ta zata saima jiyo sautin ruwa da tayi a toilet,ba jimawa ya fito da alama wankewa yayi,suna hada ido ta dauke kanta hawayen naci gaba da sauka,ciwo da kunya duka suka hadar mata,ya qaraso gabanta a hankali ya tsugunna


"Dama kina period ne?" Wayyo Allah,ji tayi kaman zata nutse a wajen,ta jawo filo ta cusa kanta tana sake sakin kuka,wannan abun sam bai kyauta mata ba,inda ta san zaizo gida zata dage sai ya kaita.


           Sake maimaita mata tambayar yayi amma shuru, ganin da gaske ba zata amsa mishi da komai ba,taqi daga kai ma ta fuskanceshi,sai kawai ya miqe yana murmushi ya fita a dakin.


           Da kansa ya gyara wajen data bata din a falo,wajen bashi da wani yawa sosai,ya dauki waya ya kira na 'yan mintuna ya kashe.


          Da pad ya dawo mata,ya ajjiye mata yace ta shirya zai fiddo mota suje asibiti,yana zaune a falo ya dora qafa daya kan daya yana amsa waya ta fito tana rab'e rab'e,kunya kamar qasa ta tsage ta shige,wayar na a kunnensa ya waiwaya ya dubeta,can qasan ransa fal dariya,duk da babu ko alamun hakan a saman fuskarsa,ya jima baiga yarinya mara wayo mai tsananin tsoro da kunya irinta ba,iya period kawai data fara ya gani?,inda ace ya karba budurcinta ne fa gaba daya?, Shi kansa daya raya zancan a ransa sai daya sake maimaitawa,sai kawai qaramin murmushi ya kubce masa,ya cije lips nasa na qasa kadan saboda yadda yaji jikinsa ya amsa gaba daya,baisan lokacin da hakan zai faru ba,amma tabbas duk sanda ya kasance qila saita kusa mace masa saboda tsoro. 


           Wayar ya kashe ya mayar aljihu sannan ya miqe,ya tako kadan gabanta


"Zaki iya tafiya?" Kai ta jinjina masa ba tare da ta iya kallonsa ba


"Muje to na gani idan zaki iya din" ya matsa gefe yana kallonta,ta rabashi a hankali ta fara takawa tana hada hanya,taku uku ya cimmata,ya riqo kafadunta suka ci gaba tafiya,tanason zare kanta,amma hakan da yayi mata saita dinga jin kamar relief yake bawa ciwonta,a haka suka qarasa,ya buda gaban mota ya sanyata ya kwantar mata da kujerar,sannan ya shiga ya tayar da motar suka fice daga gidan.


         Da yake private hospital ne basu samu wani layi ba suka samu ganin likita,duk tambayoyin da yayi mata kusan shuru tayi,tanajin kamar ta narke,maza biyu a daki guda suna mata tamba game da period dinta,abinda ko acikin gidansu boyewa take ba kowa yasan ta fara ba, murmushi likitan yayi ganin lokaci lokaci tana satar kallon abbas


"Yallabai,da alama kai din ba yayanta bane na hannun dama,ko zaka bamu waje qilan tafiyin bayani" haka kawai cikin ransa yaji bazai iya barinsu su kebe ita dashi ba,don yaga baima fahimci matar aure bace,yayi yunqurin miqewa da nufin matsawa daga koda zuwa bakin window ne,saiji yayi caraf an kamo hannunsa,ya waiwaya a hankali,itace ke kallonsa tana qwalla


"Kada ka tafi please" hada ido sukayi da likitan,sai ya saki dariya sannan ya miqe


"Ta gaya maka abinda takeji,sai kayimin bayani,ina zuwa bari na samo nurse,za'a yi mata scanning,tunda kace ciwon mara ne" sai likitan ya cire abinda ya saqala a wuyansa ya ajjiye ya fice daga office din.


            Cikin kunya ta soma qoqarin zame hannunta daga nasa,amma saiya qara matsowa yana sanya dukka tafukan hannunsa a ciki da saman nata,ya rahe gap din dake tsakaninsu sosai yana dubanta


"Uhnnnn.... tell me,kinga idan ya dawo baki fada ba zan tafi na barku tare" qoqarin tsaida kukan nata take tayi,taja majina sannan tace cikin muryar kuka


"Marata ce take ciwo sosai" ta fadi cikin mugun jin kunya 


"dai dai ina?" Ya tambayeta yana kallon qwayar idanunta,sai ta motsa hannunta dake mararta kadan,kamar mai tsoron kada ya taba hannun nata.


         Idanunsa ya mayar kan hannun nata,sai yasa yatsansa ya nuna wajen


"Wajen nan kenan?' ta gyada kanta a hankali,sai ya dauke dubansa daga wajen yana fidda numfashi,ya miqe a hankali,yayi taku biyu kenan saiga likitan ya dawo,bayansa wata nurse ce,zata kusa shekaru talatin,ba yarinya bace.


        Yana dariya ya tambayi abbas me tace?,ya zube hannayensa a aljihun wandonsa yana duban likitan


"Ciwon maranne dai"


"Ba damuwa,da Allah ki mana scanning,bari naje mota na dawo" ya sake fada yana diban wasu takardu ya fice.


           Sanda taga an gama saitan scanning machine din tace kuma tahau sai ta fara zare idanu,ganin alamun tana jin tsoro sai nurse din ta dubi abbas


"Yallabai ko zaka taimaka mata" a nutse ya maida dubansa ga widad din,itama shi take kallo,idanun nan har yanzu qwalla ce kwance a ciki,ya cire hannayensa da tun dazun ke aljihunsa,ya tako a nutse ya iso gabanta.


         Sosai ua tsugunna a gaban nata,cikin murya qasa qasa, yadda ba wanda zai iya jinsu ya fara magana


"Kije ta dubaki,few minutes ne ta gama miki,ba ciwo ba zafi,just relax...." Baki ta kwabe tana dubansa


"Tsoro nakeji" 


"I promise you ba abinda zakiji,muje na rakaki" yadda take a tsorace yasa bata damu da kama hannunta da yayi ba,ya kaita har kan gadon sannan ta kwanta.


       "Dage rigar taki" nurse din ta fada tana dauko cream din da zata shafa mata saman cikinta,sai ido ya sake raina fata,matsawa yayi dab da gadon,yasa hannunsa a hankali ya fara janye rigar jikin nata,da hanzari ta riqe tsintsiyar hannunsa,sai suka hada idanu,ya tsareta sosai da manyan idanunsa masu wani irin kaifi da tasiri,ya girgiza mata kai murya kuma can qasa yace


"Nooo,i said just relax" sosai taji idanun nasa sun mata nauyi,saita kauda kanta gefe,hawayen da suka cika idanun nata suna gangarawa ta gefe.


          Kamar wanda aka zarewa laka haka ya dage mata rigar har zuwa saman cikinta, kyakkyawar farar fatarta mai sulbi ta bayyana,ya koma a hankali da baya yana jin kamar iska na yawo dashi,ya jingina da wani qaramin locker dake wajen idanunsa nakan saman fatar cikin nata.


*Arewabooks:Huguma*


KI KULANI miss xoxo


DAUDAR GORA Billynabdul


RUMBUN K'AYA hafsat rano


IDON NERA Mamuhghee


A RUBUCE TAKE huguma


_sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau'ikan salo da kuke so_


_masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_


0022419171

Maryam sani

Access bank


Saiku tura shaidar biya ga

+234 903 318 1070


*Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan*

09166221261


*Al'ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number*

+227 96 09 67 63



*Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post