Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe page 41 Complete by Boss Bature

Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe page 41 Complete by Boss Bature

Sponsored Link

Takun Ƙarshe

Shigowa dakin hajjaty yayi bakin shi dauke da sallama, tsayawa yayi ganin bata a cikin ɗakin har ya juya zai fita ya jiyo saukar ruwa a toilet, ajiyar zuciya ya ɗan sauke ya nufi gefen gadon ta har ya yunkura zai zauna idanunsa suka hango mashi plastic bottles dake ajiye kan mirror drawer, miƙewa yayi tare da nifar mirror din ya tsaya yana kallon robobin kamar na ruwa haka suke, rubutun larabci ya gani a jikin su baisan me aka rubuta ba saboda baya jin harshen, zuciyar shi bata kwanta da su ba, ɗaya ya ɗauka ya buɗe murfin ta yakai hancin shi zai shinshina da sauri ya kawar da shi gefe ya yamutsa fuska haɗi da ta6e baki yana ɗan jan numfashi.. 


Motsin buɗe kofar toilet ne yaja hankalin shi ga kallon ta, fitowa tayi daga ciki, tayi ɗaurin gaba da towel, ta naɗe black hair din ta da wani towel ɗin

Suna haɗa ido da juna ta sakar mashi murmushi.


"mere pyaar, sai yanzu zan sanyaka a idanuna? Ina ka shiga ne ka barni da kewarka"?


Lumshe idanun shi yayi a hankali ya buɗe su yana bin ta da kallo mai cike da jin shaukin ta.


Ta baya tayi hugging din shi ta kwantar da kanta saman shoulder dinsa, ta ɗaura hannayenta kan chest din shi.


"Wifey, i'm sorry wani kira akai min mai mahimmanci shiyasa ban samu damar zuwa gurin ki ba, amma kina araina" kwanto da kanta tayi kan shoulder din shi, nuna mata robar hannun shi yayi"menene wannan?


Fuskarta dauke da murmushi tace"maganin da sheikh imam Ya bada ne don adinga ba marwa tana sha, yace in sha Allah zataji sauƙi nan bada jimawa ba..." ta fada tare da manna mashi kiss kan cheek dinsa, gogan ya haɗe fuska sam bata kula da yanayin shi ba, taci gaba da cewa"  


"Nayi ma sheikh imam alkawarin zancigaba da kula da ita, har zuwa lokacin da zata ji sauƙi"


ajiye robar yayi tare da janyota ta dawo ta gaban shi

Saurari Littafin Kurkukun Ƙaddara Takun farko  Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora.


"Meye alakarki da marwa ne"? Fuskar shi adaure yayi mata maganar

"Yar uwata ce musulma, kuma tana bukatar taimakonmu saboda mune danginta  ayanzu..." bata ƙare maganar ba ya rufe mata baki da yatsan shi


Calmy yace "Kingane ni bazan hanaki yin aikin lada ba, kawai bana so kina shisshige mata ne, ke ko kyamarta ba ki ji? kuma baki gudun ta goga maki lalurarta"? Zame hannun shi tayi daga kan bakinta



"Haba pravin, meya kawo wannan maganar? Ita ma fa ba ita ta daura ma kanta ba, bayan haka sheikah imam ya fada mana hanyoyin da zamu kare kanmu daga sharrin aljanu...." bata ƙare maganar ba yai saurin janyota kan kirjinshi yakai bakin shi saitin kunnanta, in a low voice ya furta"ni dai hankalina bai kwanta ba, kinsan bana son duk wani abu da zai cutar min dake, pls ki taimaka min ki aje aikin kula da marwa..."  yanayin yadda yakeyi mata magana ba karamin kashe mata jiki yayi ba.


cike da shagwa6a tace"dan Allah kabarni inyi aikin nan, indai kayi imani da cewa Allah shi yake tsare bawansa, nayi maka alkawarin zan kula da kaina, amincewarka kadai nake bukata..."

Badan yaso ba ya amsa mata da toh.


ƙara matseta yayi a jikin shi, a hankali ya fara manna mata hot kisses kan wuyanta har ya zuwa kan kirjin ta..tuni ta fara jan numfashi tana lumshe idanunta, daukarta yai gaba ɗaya ya kwantar kan mattress ya zame kayan jikin shi ya rage daga shi sai short, ya fada kanta yaja bargo ya lullu6e su...romancing dinta ya cigaba da yi, gaba ɗaya ya rikitata, tsawon mintuna shabiyar kacal, wani irin kasalallan bacci ya yi awon gaba da hajjaty.



Fitowa pravin yayi daga cikin bargon ya sauko daga kan gadon Ya haɗa uban gumi a jikin shi, shu'umin murmushin gefen fuska ya saki tare da kallon hajjaty dake bacci...A hankali Ya furta"I'm sorry, zan yi maki laifi, saboda bazan bari kiyi silar tona min asirina ba," ya faɗa tare da juyawa ya nufi robobin maganin ya kwashe su, Ya shige toilet da su, Allah kadai Yasan meya yi masu, jim kaɗan Ya fito da robobin a hannun shi yana faman sakin shu'umun murmushi ya ɗaura su kan mirror.


Kafin ya fita daga dakin saida ya fara hawa gadon Ya sumbaci la66anta  kafin ya sauko shaf shaf ya maida kayan jikin shi ya juya cikin takun tantirai Ya fuce daga dakin.


Fitar shi keda wuya hajjaty ta fara mutsu mutsun farkawa daga bacci, wata irin kasalace ta mamaye jikinta dakyar ta lalla6a ta miƙe ganin babu sutura ajikinta yasa tayi saurin kai hannu ta janyo towel dinta ta lullu6e jikinta, muryarta adisashe ta fara ambaton sunan shi shiru taji bai amsa mata ba alamar baya adakin, lumshe idanu tayi tare da jingina kanta jikin headboard, A hankali take tariyo abunda ya shiga tsakaninta da pravin wani irin shaukin son shi take ji, dai dai da minti ɗaya bata ta6a gajiya da shi ba, saboda soyayyar gaskiyace a tsakaninsu, bata ta6a haɗa son shi da wani ba.


Tunawa da marwa yasa tay saurin saukowa daga kan gadon ta shiga toilet, donta tsarkake jikin ta, bayan ta fito ta shirya cikin riga da skirt na atamfa ta feshe jikinta da turare, ta yafa mayafi akanta, da sauri ta dauki robobin maganin ta tura su cikin ledar da aka kawo su, ta fito ta nufi dakin marwa, da sallama ta shiga dakin fuskarta dauke da murmushi take kallon marwa dake akwance kan mattress ta rufe idanunta.


Zama hajjaty tay gefen katifar ta ajiye jakar agaban marwa.


"Sannu marwa ya jikin naki? a hankali ta buɗe idanunta waɗanda suka kaɗa jawur ta dubi hajjaty, dakyar ta kakaro murmushi tana kallon ta

tayi kyau abunta, ɗazu da safe hajjaty ta taimaka mata tay wanka har kaya ta canza yar doguwar rigace a jikin ta,  jikinta sai kamshin turaren da hajjaty ta fesa mata yakeyi.


"Sheikh imam ya aiko da maganin ki,"


ta fada tare da ruƙo kafadun marwa ta taimaka mata ta zauna tare da jingina bayanta jikin pillow


"Kina jin yunwa" girgiza mata kai tay alamar a'a, 


"Dama nasan ba lallai kiji yunwa ba, saboda dazu kin cika cikin ki da abinci" ta fada yayin da take bude murfin robar farko mai ɗauke da sunan zam zam..


"Kiyi bismilla ki sha, kur6a ɗaya zakiyi" ɗaga mata kai tay alamar toh


Lokacin data kurbi maganin kiris ya rage ta amayar da shi saboda zaurin da ya buso hancin ta.


Lura da yanayin ta yasa hajjaty cewa"am sorry halan maganin bai da dadi? Ɗaga mata kai tay alamar eh

Saurari Littafin Kurkukun Ƙaddara Takun farko  Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora.

"Eyyah sai kin daure,kinsan yadda magungunan gargajiya suke akwai ɗaci, wani zakiji shi da bauri wani kuma tsami" ta faɗa tana yamutsa fuska, bayan ta kammala bata magungunan, tace"wannan ɗayan daya rage, a cikin ruwan wanka za'a ɗiga maki shi, zuwa anjima in sha Allah zan sake dawowa, sannan pls kada ki manta kiyi evening azhkar"


tun da ta fara magana marwa keta kallonta so take ta faɗa mata wani abu tarasa taya zatai mata magana daga ta yunkuro zatai magana sai ta kasa saboda muryarta babu dadin ji



Hajjaty sam bata lura da hakan ba, bayan ta maida robobin maganin a cikin ledar, ta ajiye gefen katifar marwa"ni zan tafi, da anjima zan shigo kawo maki dinner" ta fada tare da sakar mata murmushi ta mike ta tafara tafiya har ta kusa fita kunnuwanta suka jiyo mata marwa dake ta kokarin yi mata magana.


Juyowa tay tare da kallonta da alamun rudani akan fuskarta, da hannu take yi mata alama, hajjaty ta kasa gane me taje nufi, ita dai taga marwa sai nuna mata dunkulallun yatsun hannunta takeyi


"Marwa akwai wani abu da kike bukata ne"? Ɗaga mata kai tay alamar eh, komawa tayi gaban katifar ta zukunna tana kallonta, ruwan hawaye tagani kwance akan fuskarta"pls ki daina zubda hawayenki dan Allah, ki fadamun abunda kike so zanyi maki" da hannu marwa ta dinga goga floor tana kokarin kwatanta mata abunda take so ta dauko mata sai dai takasa fahimtarta

Saurari Littafin Kurkukun Ƙaddara Takun farko  Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora.

"Marwa kiyi hakuri, wallahi bansan me kike nufi ba" buɗe baki marwa tayi  ta fara mata gura gura.. tsoron maganarta hajjaty take ji nan take ta tuna da maganar pravin dayace mata ita bata tsoron marwa ta goga mata lalurarta, tuna wannan yasa tay saurin mikewa gabanta na faduwa ta fara ambaton sunan Allah acikin zuciyarta.


Cikin rawar murya tace"marwa sai anjima zan dawo in sha Allah" da sauri ta fuce daga dakin, marwa ta kifa kanta cikin pillow ta fashe da kuka mai tsuma zuciya tamkar ranta zai fita 💔

________________________________✍️



*(AFTER 3 DAYS BAYAN KWANA UKU)*


A kalla yau kwana uku kenan da zuwansu Anila gidan hajiya adama, har ila yau ba su ƙara jin duriyar Ana ba, babu ita babu labarin ta, abun ya ɗaga hankulan mutanan gidan sun damu da rashin ta, kusan kullum sai anila da mahboob sun kira layinta a switched off suke samun shi, Lamarin ya ɗaure masu kai, basu da wata hanya da zasu Iya tuntu6ar wani nata, saboda ba su ta6a kar6ar layin yan uwanta dake a joss ba, abu biyu ya haɗe ma Aneelerh ga damuwar halin da junaid yake a ciki, kwata kwata baya sakin jiki da kowa ga ƙiwuya bai yarda da kowa na gidan ita kadai yake manne mawa, kuma har yau yaƙi buɗe baki ya tanka mata ya zama kamar kurma sai dai yabi ta da ido ko in yana jin yunwa sometimes yana bude baki ya furta kalmar yunwa, wani abu daya fi daure mata kai idan dare yayi zasuyi bacci ta rungume shi a jikin ta, sai ya dinga firgita yana sambatu kwata kwata bata gane me yake cewa.


Har su mami ta sanar ma abunda yakeyi suka ce taci gaba dayi mashi addu'a in sha Allah zaiji sauki, ita dai hankalinta bai kwanta da yanayin shi ba, ranta yana bata wani abu ba dai dai ba agidan dole akwai wani abu daya faru wanda yayi silar guduwar Anah da kuma rikicewar baby junaid! Kwana biyu da baije school ba sai ga kira daga class master din su junaid, bayan sun gaisa da anila ta ta tambayeta meyasa kwana biyu junaid baizo school ba, tace mata baida lafiya ne amma idan yaji sauki zai cigaba da zuwa


Saurari Littafin Kurkukun Ƙaddara Takun farko  Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora.

Cikin kwana uku anila duk ta fita hayyacinta har faɗawa tayi saboda damuwar rashin Ana da kuma halin da baby junaid yake a ciki, abie har kiranta yayi shi da uncle dan iya da su ummu suka taru akanta suka yi mata nasiha cikin lallami da lallashi donta kwantar da hankali saboda kowa ya fahimci bata acikin nutsuwarta, ko abinci sai zahra tayi dakyar take samu ta ci ta zama abun ban tausayi daga ita har junaid din harma kwara ita akan shi saboda ya takura kan shi ya kuma takura mata ya hanata sukuni ko toilet zata shiga sai ya sanya rigima zai bita, dakyar take samu ta lalla6a shi da wayarta don yayi game kafin ta samu ya kyale ta, idan salla zatayi sai dai ta goya shi abayanta, har yau babu abunda ya canza, yanzu girkin gidan ya dawo hannun mami da ummi saboda rashin Ana, zahra kuma ba azaune take ba, tana zuwa aiki, ita kuma anila kota nemi su bata ta tayasu aiki sai suce taje taji da junaid zasu kula da komai...💔


________________________✍️


Shin Ya labarin Benazir? Ay tun ranar da suka dawo gida ta kasa ta tsare tana jiran taj da Angel su dawo daga kasuwa, shiru shiru taji basu dawo ba har marece ya nutsa hankali atashe tace ma hajiya layla ta kira mata layin taj awaya taji meya hana su dawo! Hajiya layla tana yan kame kame tace mata ta manta bata da layin taj, kuma dayazo asibitin daukar Angel bata kar6a ba, sai dai ko dr shureim watakil shi yana da layin shi, ko da ta yi ma dr shureim magana akan ya kira mata taj cikin rashin kwanciyar hankali ya kira wrong number da gangan saboda ta tsare shi da ido tana jiran shi ya kira mata mijin ta, a dole yayi pretending ya ci gaba da magana yana fadin pls taj marece yayi ga benazir tana jiran ku, dan Allah ku dawo hakanan okey toh sai anijima Allah ya dawo daku lafiya, bayan ya katse kiran yace mata tayi hakuri ta kara jira suna akan hanya, baiwar Allah jiki asanyaye ta zauna kan sofa tana jiran dawowarsu, hankalinta kwata kwata ba a kwance yake ba, gani take kamar bazata sake ganin angel din ta ba...


Abu kamar wasa har dare yayi babu taj ba angel, hankalinta ba karamin tashi yayi ba, lokacin da zasu yi dinner bayan su tani sun kammala shirya masu abinci a dining hajiya layla tace tazo su ci abinci, tace mata bazata iya ci ba, in har taj bai kawomata Angel din ta ba


hankulansu ba karamin tashi yayi ba, gaba ɗaya suka taru akanta suka fara lallashinta suna bata baki duk don su samu su taci abincin amma taƙiya, babu wanda baiji tausayinta ba musamman da karfe goma sha ɗaya ta buga na dare, a lokacin ta gama gane karya sukeyi mata, zuciyarta ta karaya a karshe ta fashe da kuka  tace su daina boye mata gaskiya, kawai su fada mata ina yarta Angel? Saboda tana ji aranta ba taj bane ya dauke ta, babu wani siyayyar da suka je yi mata duk plan ne .." gaba daya aka rasa wanda zai faɗa mata gaskiya saboda fargaban halin da zata shiga, ranta yayi mugun 6aci zuciyarta ta hasala ganin sun zuba mata ido an rasa me magana a cikin su, idanunta suka kaɗa jawur, zafafan hawaye suka wanke fuskarta, tsabar fusata jikinta har kerma yakeyi tana faman jan numfashi tace"mami! Ya shureim, aunty sarah ku fadamin gaskiya ina babyna take? Wanene Yake son rabani da ita? Yarinyar nan ƴata ce fa halak malak, akan me zaku yi min karyar taj ya dauke ta sunje shopping mall? Meyasa har yanzu basu dawo ba? Kusan karfe goma sha ɗaya na dare, wlh idan har baku dawo min da babyna ba, komai zai iya faruwa..." dakyar ta kare maganar tare da sanya tafukan hannayenta ta dafe kanta kamar yadda take yi idan zatay pretending ta fara yi masu kuka na fitar hayyaci kamar zata rotsa dodon kunnuwansu, gaba ɗaya tabi ta furgita su, zeenatu tsabar tsoro daki ta shige ta kulle dama tunda Benazir din ta dawo ko gaisuwa bata hada su ba, bayan ta shiga dakinne ta fara tariyo fuskar Unaisah yarinyar data kira sunanta da Unaizah, har cikin aranta tana son ta kara haduwa da ita kuma tana son tasan wacece Unaizar su data mutu? ya akai komai nasu yazo iri ɗaya? Tabbas tana son tasan komai dangane da ita bayan haka tana son su kulla kawance da Unaisah saboda ta kwanta mata aranta tun a kallo na farko da idanunsu suka shiga cikin na juna.


Daga cikin falo ta dinga jiyo sautin muryoyinsu Hajiya layla suna ta kokarin lallashin Benazir, hada alhaji ubaid a lokaci baijima da shigowa gidan ba, gaba daya mutanan gidan suka taru akanta, in ka cire Alhaji musa saboda baya nan baisan budurin da sukeyi ba 

Adaren ranar dakyar suka samu bacci ya ɗauketa, jikinta hada zazza6i.


har ila yau tana akwance ba lafiya, saboda rashin Angel dinta, tayi kukan harta gaji, kowa na gidan tausayinta yake ji, yau kwana uku kacal da rabuwarsu da unaisah tana jinyar zuciyarta bata son cin abinci ko wanka ta dainayi ta zama kamar mahaukaciya, kusan kullum sai hajiya layla ta matsa ma shureim akan ya kira anila yayi mata magana ta fada masu ina ne gidan iyayen yarinyar, dr shureim yace tayi su yi hakuri bazai iya ba, bayaso ya takura ma anila bayan haka babu amfanin suje gidan iyayen yarinyar tun da ko sunje yarinyar fa ba yar benazir bace ganinta bazai amfani benazir da komai ba saima ya ƙara ɗaga mata hankali tunda ba basu ita za'ae ba, adole hajiya layla ta hakura da yi mashi maganar Azeezaty


 _________________________✍️


Idan muka koma bangaren Marwa, jikinta ya ƙara tsauri babu wani cigaba a lafiyarta, yatsun hannunta sai ƙara matsewa sukeyi ga wasu kananun kuraje da suka fara feso mata akan fuskarta, baiwar Allah ita kadai tasan halin da take a ciki, wani lokaci idan hannunta suka fara mata radadi kamar zata zauce, duk da halin da take aciki kokari take ta fallasa asirin wanda yai silar ɗaura mata ciwon, sau uku hajjaty ke xuwa dubata kuma tana kokarin kiyaye duk wasu sharudda nayin amfani da maganin da sheikh imam ya bata sai dai takasa gane an canza ruwan maganin rashin sani ya fi dare duhu batasan tana ƙara wa marwa ciwon ta ba takasa lura da yanayin ta, gashi duk in ta shigo daki sai marwa tayi mata alama da hannu har yau takasa fahintar me take nufi, idan tayi yunkuri takura kanta akan tay magana wani irin radadi take ji a makoshin badan taso ba ta hakura, wani lokaci idan tayi ma hajjaty alama da hannu ta kasa ganewa saita buga kanta jikin pillow tayi ta kuka kamar ranta zai fita, dakyar hajjaty take samu ta lallasheta har ta shawo kanta.


Saurari Littafin Kurkukun Ƙaddara Takun farko  Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora.

A cikin yan kwanakin nan hajiya saratu bata bari hanya ta haɗata da hajjaty saboda tsoranta da take ji, hajjaty harta fara lura da ita, ranar da ta shiga kaima baba obie abinci hajiya saratu tana adakin, tun da taji sallamar hajjaty da sauri ta mike ko sallama batayi mashi ba ta fuce daga dakin, tun daga nan hajjaty ta fara lura da ita, abun ya ɗaga hankalin ta, tarasa gane laifin me tayi mata? Duk da dama tasan ba sonta take yi ba akwai tsanarta a zuciyarta amma yanzu abun ya karu fiye da lokacin baya


Idan muka koma bangarensu twins tun ranar da suka ga iftila'in daya faɗawa marwa basu ƙara marmarin komawa gidan ba, saboda kyankyami da kyama suke ji, a hotel suka koma da kwana, daga bisani da hajiya saratu takira zayn awaya ta fara zazzaga mashi masifa akan rashin dawowarsu gida yace mata su fa bazasu dawo ba in har ba an fidda mai aikin nan daga gidan su ba, bata musa masu ba, saima cewa tayi su bata lokaci zatayi magana da baba obie akan a maida marwa garin su indai hakan zai kwantar masu da hankali, sunji dadin maganarta hada yi mata godiya


✊Boss Bature💋: ________________________✍️


A kishingiɗe yake saman lallausan rug din dakin baba obie ya ɗaura head dinsa kan pillow, jikinshi na sanye da jallabiya fara kyal, fragrance dinsa ya haɗe da sanyin A.c din dakin, ba su jima da dawowa daga sallar asuba ba yabiyo baba obie dakin shi...A hankali yake danna phone dinsa Kira ne ya shigo ganin sunan commender james yasa shi picking call din tare da kara wayar a kunne, cikin girmamawa suka gaishe da junansu kafin daga bisani commender james ya sanar da shi sun samu izni daga manyan su, za su shigo Nigeria da shi da sauran sojojin da suka tsinci su Angel a dajin evil forest

Chief yace"I'm very happy to hear that, I can't wait to see you"

Commender james yace"I'm also very happy, this is the first time I'll be coming to Nigeria because of the children we found in the forest. 

Sponsored Post

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post