Feenart Hausa Novel Page 10 | Novels Elite

Feenart Hausa Novel Page 10 | Novels Elite

Feenart Hausa Novel Page 10 | Novels Elite

✨✨ FEENART ✨✨

  *BY NUSAIBA* *ALKAMAWA* 

 *PROFICIENT WRITER'S* ASSOCIATION 

🅿️ 1️⃣0️⃣

Bayan na fita siyahma takoma daki taxauna cike da fargaba, don batasan meyasa yau takejin tsoron gidan ba.

"littafinta ta dauko na boko tafara karantawa ta ajjiye tadauko na islamiyya. 

,,sauti tafaraji sama -sama tashi tayi atsorace ,,fado mata daki sukayi ,,,,innalillahi shine Kalmar da siyahma tafada, ganin wannan jahilin mutumin wato walid ,,to meye ya kawoshi ???

katse mata tunani yayi yace siyahma siyahma kenan ,yau gani gaki adaki daya ,,,kuma agida daya yau baxaki tseremin ba.

katse shi tayi tace meya kawo ka gidanmu ??

abinda yakawoni gidan nan shine abinda nake bibiyarki dashi kike wulakantani akanshi . 

"hasbunallahu waniimal wakil. 

Allah yayi min tsari da aikata ba daidai ba. 

Fara taku yayi yana tunkaro ni. 

Kara nasaki nace,wayyo yaya ,,,,dariya yayi irinta mugunta yace kee wawiya ki adana ihun naki domin yayan naki yayi nisa Dan saida mukaga fitar nashi tukunna muka shigo  gidannan. 

Nace Allah yayi min tsari da kai kuma abinda kaxo nema baxaka samuba aniyarka tabika ,,katse ta yayi ta hanyar cewa maxga, goma Ku rikemin ita aikuwa sai gasu sun shigo dayake suna waje siyahma batason dasuba ,,,,ihuu nasaka tana cewa wayyo yaya aunty xahra ,,,tsawa yasakar mata wadda yasakata yin shuru SBD taraxana yace" au lusarin yayan naki kike kira dake barinki kekadai agida ?????

 Kuka siyahma tafashe dashi gwanin ban tausayi 

Maxga da goma

 Ne suka to she mata baki bayan sun riketa duk da kuwa tana kokarin kwace kanta Amman karfin mace da namiji ba daya baneba. 

 (Nidai writer na rufo 

musu kofa idanuna cike da hawayen tausayin seeyahma )

Bayan nakoma domin naje nadauko muku rahoto. 

Ina shiga me xan gani ?????

Innalillahi,siyahma Nagani akwance ko motsi bata iyayi ,sukuwa su walid da masga da goma, Saii mata dariya sukeyi, suka fita domin jin sallama da akayi ,,ido biyu sukayi da Fatima Wanda tashigo gidan mamakine ya cikata ganin su waleed ,tace meya kawo Ku gidan nan ??

banxa sukayi mata suna kokarin tafiya ,,shangabansu tayi takara cewa tambayarku nakeyi marasa tarbiya,,karfen dake hannun goma ,,walid yakarba ,yama kawa fatima

Akai . 

Wani raxananniyar kara tasaka tareda faduwa akasa SBD karfen yashigeta Dan bibbiyu tadunga ganinsu

          Dariya sukasa na mugunta masga yace :mu ba aja damu idan kikace xakija damu to ke xakisha wahala,goma yace kyaleta ma taji da xafin ciwon da mukaji mata ga kuma  kanwarta cen tana ji itama ,,,suka saka dariya irin ta basawa,sannan suka fita    ,,,,,duk da xafin buguwar hakan baihanata jin abinda suka fada ba daga karshe ba ,,najin  maganar dasu kayi akan kanwartata.

kokarin tashi take Amman inahhh takasa haka tayita Jan kafa domin ta isa gurin seeyahma ,,,,dakatawa tayi .

tayi saurin daukar wayarta dake jikinta ,,daily number yayan ta tayi Amman harta gama ringing bai daukaba ,,muhd yace 

Nikuwa anawa bangaren. 

INA kallon kiran Amman bandaga ba acewata haka xasuce nadawo gida nikuwa yanxu inakan aikina ,da xahra tadameni ma saina kashe wayar  to da taga haka saita hakura tanufi dakin da siyahma take da kyar ,,,,,,tana isa me xatagani ???siyahma tagani cikin jini innalillahi ,ai da saurinta  tadaga siyahma ta dorata kan cinyarta tana kuka ganin halin da yar uwarta take ciki . 

 ----------aunty xahra su walid ne da abokansa sukayi min haka tana fada da kyer alamar ta wahala  tacigaba da Cewa aunty baxan taba  yafe musu ba ,aunty INA kaunarki kifadawa yaya muhd shima INA kaunarsa aunty mutuwa xanyi ,sai asannan xahra tayi magana SBD rera kukan da take tace,,aa siyahma kidaina fadan haka baxaki mutu kibarmu ba tafada cikin kuka ,aunty xahra babu rabon cika burikana. 

Allah baiyi xamu kasance tare dani daku ba ,   saurin rufe mata baki fateema tayi tace siyahma xamu rayu dake, "Kalmar shahada siyahma takeyi  naji harshenta yana karyewa ahakan takarasa fada sannan ta cika .

me Fatima xataji ?jitayi siyahma ta kara nauyi kuma tadaina motsi kiran sunanta Fatima takeyi tana siyahma ?masoyiya ? Amman shiru. 

,innalillahi siyahma kitashi Dan Allah ,,wayarta tadauka tadanna min kira

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post