FEENERT
By
NUSAIBA ALKAMAWA
Facebook: Alkamawa's Glow
🅿️5️⃣
Haka kwanaki sukai ta wucewa, inda ni tun lokacin DA akayi min maganar aure nake dan rashin lafiya atsattsaye ,inda nayi kokarin kada Momy tagane SBD bana son hankalinta yatashi,,saina KOma zaman daki bana fitowa ,hakan bai damu Momy ba dayake tasan halina naxama, adaki kuma ba wata me kulawa bace ba.
Kullum sai naji sauyi na rashin lpy ta yau dai abun yafi na kullum jikina ya Kara karfi kirjina bala'in ciwo yake min kamar zai faso yafito, ga wani irin ciwon ciki DA nakeji wanda yasaka nadurkushe akasa.
kasa jurewa nayi.
na Dan rarrafa nashigo parlour inajan bombom har Allah yasa naxo tsakiya
Ina wani irin layi kamar wacce xata suma kasa karasawa dakin Momy nayi SBD kaina daya saramin kamar xai rabe gida biyu gashi nakasa koda ihu ne,bakina ya mutu murus nakasa magana ,,karar bude kofa naji Amman nakasa waiwayawa muryar ya ansar DA ya nasib naji, Ansar ne yariga Nasib karasowa ya kalleni " yace afili ita kuma wannan sabon salone nakwanta wa akasa tana rike ciki oho Mata?
xai huce irin KO ajikinsa .
ya Nasib ne yakara so inda yaga Fenart adurkushe hannunta rike DA ciki yace,subanallah Fenart me ya same ki baki DA lpy ne ?
Yadago DA fuskata nikuwa nakasa magana saboda axababben ciwon DA yadame ni luuuu tatafi asume salati ya Nasib yasaka, ya na kiran sunan Momy Aida gudu Momy DA ya ansar suka fito suka ga Fenart ahannun ya Nasib innalillahi nasib meya same ta yana ganta a sume ??,,Momy yanxu ba lokacin magana bane ba dauko hijab mutafi hospital Allah yasa dai ba ciwontane yatashi ba yafada SBD sunsan irin wahalar data kesha idan za ayimata wankin koda.
Daukarta yayi ya nufi mota DA ita ya na kwalawa idi driver Kira DA saurinsa idi yaxo suka shiga mota yaja sai Alkaly pravet hospital.
"Inda su Momy DA Ansar suka biyo bayan su.
domin Bai tsaya jiran suba naganin tilon kanwarsa raii ahannun Allah, ita kuwa Momy data shiga daki tsabar rikicewa rasa mexata dauko tayi sai xagaye dakin take,
har saida Ansar yashigo yadauko Mata yajawo hannunta suka shiga motar ,,,,suna isa aka karbeta ,,Momy takira daddy tasanar masa, aikuwa yace gashinan domin wajan aikinsu babu nisa DA asibitin
Aikuwa sai gashi nan akace tana tareda doctor Amman haryanxu doctor baifito ba ,,,zama sukayi shikuwa ya Naseeb yakasa zama sai xirga _xirga yakeyi kamar yana Neman Abu ,,fitowar doctor ne yasa su Momy ta shi suna tambayarsa lafiyar diyar tasu.
Doctor yacire glass din dake face dinshi yagyara yamayar yace ,,yarku ansamu ta farfado Amman tana matsanainci wani halin narai KO mutuwa SBD ciwon yagama bin jikinta baku kawota asiibiti da wuriba kuma DA alama ta kwana biyu tana ciwon don yanxu ma babu maganar wanke kodar SBD talalace saidai asakamata wata idan kunshirya yanxuma xa a iya yin aikin,.
Hannu Momy tasaka akai ta na diskar kuka
Shikuwa ya Ansar baxa kataba gane wani hali yake ciki ba .
daddy yace yanxu doctor baxa ayimata wankin kodar ba kamar da abaya ?girgixa kaii doctor yayi yace baxaiyuyiba kasan anmata wankin kodar so go ma shabiyu yanxu idan kunshirya afara yi muku aikin Nasib yace eh doctor ashirye muke yanxu muje aciri tawa asaka mata kallonshi su dady sukayi cike DA tausayin Dan nasu na irin soyayyar DA yakewa kanwartashi.
Dady yace a'a Nasib niya kamata nabayar muje doctor nabada nawa ,saurin tareshi nasib yayi yace wllh daddy idan kabada taka baxan taba yafewa kaina ba tunda inada halin bayarwa kuma kaima kaga ba ishashshiyar lapiya gareka ba
Tofa shin acikin su waxai Bada tasa kodar?
Saikun biyoni xakuji yacce xata kaya.
Daga taskar Nusaiba Alkamawa