Feenart Hausa Novel Page 9 | Novels Elite

Feenart Hausa Novel Page 9 | Novels Elite

Feenart Hausa Novel Page 9 | Novels Elite

✨✨ FEENEART ✨

      BY NUSAIBA ALKAMAWA

🅿️9️⃣

_Kira ne yashigo wayata,da gawa nayi,muhd yace min yana kan hanya,aikuwa cikin xumudi nakashe wayar ina mai xumudin jin labarin daxai bani ,,,,,,,,,bayan yan sakanni yabugo min waya yacemin ya iso to nace masa nafita nasauke shi adakin baki,,muka xauna akan royal  chair fuskar shi  dauke da farin glass saii shaining glass din yake.

"barrister muhd?nafada bakina dauke da murmushi. 

shima amsamin yayi yace "na'am matar barrister ,,,murmushi nayi nabude fridge nadauko masa SWAN WATER na mika masa ''''karba yayi tare da cemin ya gode , nace masa habibi bani labarin da kace xaka bani ,,murmushi yayi Wanda yasaka dimples dinsa suka lotsa ,yace Fenart kin fiya xumudi ,,fadan labarin nan xaii iya kara jefani cikin wani hali Amman tunda rayuwata tace na bata ,,toh yaxama dole nabata,yafada yana dan murmusawa"nikuwa kara gyara xama nayi,ina sauraren sa.

yafara magana kamar haka !!!!!  Muhammad SA'ED shine cikakken sunana ,dane ga marigayi saed da marigayiya saudatu ,iyayena sun dade da rasuwa ,,mahaifi nane yafara  rasuwa sannan mahaifiyata ,ni suka fara Haifa sai kanwata fateema xahra sai auta seeyahma   ---------iyayenmu ba wasu masu karfi bane ba saidai rufin asiri na Allah ,,,sun rasu sunbar mana gida kwalli daya   ,,,bamu san dangin iyayen namu ba har Allah yakarbi rayuwarsu, da yake agidan marayu suka taso har akayi musu aure. 

------ninake ciyar da gidanmu ina Dan buga bugata ahakan nake biyawa kannena kudin makaranta na arabi Dana boko  ,,,,,haka yau idan munsamu muci idan bamu samuba haka xamu xauna da yunwa. 

SBD hakane xahra tadaina xuwa makaranta ganin nauyin xaimin yawa ,nake biyawa kaina da seeyahma kadai ,,dayake seeyahma tana son karatu sosai ,babban burinta shine taxama babbar likita saboda ta taimakawa jama'a musammanma dataji labarin mahaifiyar mu agurin haihuwarta ta rasu  ,,,,,,seeyahma tana da haxaka Dan tunda nasaka ta amakaranta bata taba xuwa 2 position ba saidai 1 SBD hakane ma malaman ta sukayi mata jumping ,,,,kyaututtuka kuwa seeyahma tarikeshi babu adadi da hakane muke kara bata kwarin gwiwa har Allah yasa fateema tasamu aiki agidan wasu masu kudi da hakane muke rufawa kanmu asiri. 

     Inason kannena fiye da yacce nakeson rayuwata sune kadai xan kalla naji farin ciki ,,bani da kowa saisu muntaso da kaunar junanmu ,,siyama  tana jss three ,,kyanta sai kara fitowa take  kamar yar larabawa duk tafimu kyau duk da muma munada kyau amman nata nadabanne, gata da farinjinin jama'a 

  Ana hakane akaita 

shirye -shiryen dawowar waleed wato Dan gidan alhaji usman (Inda fateema take aiki )

Daga america ,shi daya tilo agurin iyayensa duk wani gata na duniya anbashi ,sun dauki son duniya sundaura mishi ,,,,shiyasa bayajin maganar kowa ciki kuwa harda na iyayensa ,,,da suka turashi America karatu baya xuwa makarantar ,,yawanshi yake xuwa da 'yammata  ,,,,daga club saii hotel ,,haka yacewa iyayen nasa ya kammala karatun xaidawo gida ,,murna wajan iyayen ba a magana dan ra bonshi da gida shekara uku kenan,,, har party aka shirya masa ,,haka akayi shagali ,,,yaudai kusan satinsa biyu da dawowa . 

  ,,,,,baifiya xama agida ba saidai yawo ,,,Amman dai yau anci sa'a yana gida sakamakon tilastawar mahaifiyarshi yanxuma haka yana xaune kan kujerar da mahaifiyar yake ,yadora kafa kan daya ,,,zahra xahra momy ta kwallawa fateema kira ,na'am hajiya ,,,Fatima tatawo da saurinta ,,,walid yadago Kai domin yaga wacece wannan me irin sunan Beb dinshi. 

Wow shine Kalmar da yafada axuciyarshi  to a ina momy tasamu wannan xaxxafar me kyau haka ,,???gaskiya na kwadaitu da ita xanje wurinta da bukatata ,,,,momy tace am ,,,Fatima ,talatu tagama abincin kije kikarba kitafi gida saikuma gobe. 

da wannan maganar momyn tasa takatse masa tunanin dayake akan xahra. 

durkusawa tayi tace to hajiya ngd ,jitayi kamar ana kallonta dagowa tayi suka hada ido da walid ,,harararshi tayi naganin irin kallon kurillan da yake mata ,,(,domin xahra badai tsiwa ba)

Wucewa tayi sai asannan yadaina kallonta yace momy a INA kika samu wannan babyn ???momy tace anan bayan gidan nan take ai marainiyace kuma talakawa ,yanxu tana min aiki ne anan gidan ,,,shikuwa walid dadi yaji yayi murmushin mugunta domin hakan yayi masa musamman da yaji marainiya ce. 

Tun daga nan yake bibiyar fateema da bukatar shi akanta  haka yake shiga dakin da akabata,,akwai lokacin daya shiga aikuwa tayi masa wulakanci kuma tace Indai wannan ce bukatarshi akanta to yasani baxa tataba amincewa ba. 

"haka dai yafita cikin bacin raiii yace kuma baxai hakuraba xataxo hannunsa ne . 

Ana haka watarana seeyahma tagaji da xama ita kadai agidan ,ya yayan nasu bayanan sai ita kadai ,,shiryawa tayi da xummar xuwa gidan da xahra take aiki ko tayata aikin tayi ,,,shiga tayi cikin gidan inda masu gadi basu tsare ta SBD sun santa tana xuwa daman 

Waige_ waige tafara tana Neman yar uwarta ,,,,karo suka kusanyi da waleed yadago da niyar shararamata mari ,,enahhh saiyaci karo da wata kyakkyawar yarinya ai da saurinsa yawayence da cewa hy (lol) sannan yasauke hannayensa. 

Ita kuwa ko kallo bai ishe taba  ,,,tafara tafiya binta yayi yana cewa beby gurinwa kikaxo? harda seeyamah baxa tayi magana ba saikuma tayi tace gurin yaya ta Fatima naxo,,yace wacece yayartaki ?cike da kosawa tace Fatima xahra ,yace u means yayarkice ???tace eh tareda shigewa ciki tabarshi cike da mamaki ,yace plan dina xaifi tafiya daidai da ga ke har ita xakuyi bayani ne . 

Tun daga sannan yake bibiyar siyahma  ita kuwa Fatima baikara bibiyarta ba acewarshi siyahma tafita kyau suk sanda siyahma xataje makaranta saiya tsareta ita kuwa bata tsayawa ,,tun abin baya damunta harya dawo yana damunta , shiyasa ta fadawa Fatima halin da take ciki ,itama xahran tafada mata natan domin ba abinda suke boyewa junansu ,xahran tace mata karta kuskura ta kulashi domin ba mutumin kirki bane ba 

Yauma tana hanya yabiyota aikuwa tayi masa rashin mutumci Amman gogon ko ajikinshi acewarshi saiya cimma burinshi akanta 

Yaudai Fatima tana aikin ta walid yafito yace sannunki da aiki Dan Allah idan kingama kishiga dakina kigyaramin ,nixan fita ,toh kawai nace masa tana me mamakin sauyawar walid domin da idan xai sakata aiki da tsawa da kuma gadara yake sata. 

"nace Allah yasa shiriyace taxo masa. 

Ni kuwa ina gida nadawo daga skul dayake exam muke yi  ta final years dinmu  ,naci abinci wadda masoyiya seeyahma ta girkamin muna hira tacemin sweetbros idan na kammala karatuna naxama cikakkiyar doctor mai taimako ga al 'umma ,,kasan menake so nayi ??yace aa *masoyiya* ,tace min tana son tagina mana gida kato kuma takaimu makka da madina yafada yana  me *kallon Fenart* bakinshi dauke da murmushi ita kuwa fenart girgixa kaii take alamar yacigaba ,,aikuwa cigaba wa yayi yace :tana son taje gidan marayu irinmu ta dunga taimaka musu takare da cewa Allah yarayu mu sweetbro bana son na mutu bancika burikar naba ,murmushi yayi mata yace insha Allah xaki cika burinki masoyiya "insha Allah yaya ,,,uhmmn bara natashi natafi gurin aiki duk kin cikani da surutu gashi har xan makara ,tace yaya Dan Allah ka xauna kuyita hira bansan meyasaba nakejin kirjina yana bugawa ba plx yaya. 

"Siyahma rigima nidai baxan xauna ba gwara naje na nema mana abincin da xamuci Amman daii bara nakira miki xahra idan tagama aikin nata tadawo gida ,,daily number xahra nayi tana dagawa tacemin sweetbros kadawo gidane ?nace mata eh Amman yanxu xan fita ga yar rigimarki nan tace lalle_ lalle saina kiraki kidawo gida yanxu ,,dariya Fatima tayi tace " masoyiya akwai ta da rigima kamar bayau ne kadai take xama ita kadai ba agidan ba.

,to kace mata ganinan bara nadan karasa aikina saura kiris ,,to shikkenan saikin karasa ,,,nafada INA me katse wayar na kalli siyahma nace to kinji dadi gatanan xuwa.

"tace eh to saika dawo toh nace ,harna kai bakin kofa ta kwalla min kira waiwayo wa nayi na kalleta ta sakar min  murmushi .

Nima namayar mata. 

"tace yayana Allah yatsaremin kai ,,ameen siyahma ,nafada INA mai karasa fita. 

Share it fisabilillah❤️

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post