Mataimakin Shugaban Ƙungiyar Arewa Youths for Asiwaju masu goyon bayan ɗantakarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu, Dakta. Maina Isma'il Abdullahi Gimba ya kai ziyara ga shugaban hukumar Tsimi da Tanadi na jihar Kaduna Muhammad Jalal domin tattaunawa a kan yadda za su yi aiki tare don tunkarar babban zaɓen 2023.
Ziyarar dai, an yi ta ne a ranar Alhamis a ofishinsa da ke Kaduna.
Maina, ya bayyana cewa, a shirye suke su yi aiki tare da kowa, kuma su na aiki ba dare ba rana domin samun nasarar APC a dukkan matakai.
A mako mai zuwa ne ɗantakarar shugaban ƙasa na Jam'iyyar APC, Bola Ahmad Tinubu zai kawo ziyara jihar Kaduna.
Sun yi ganawar tattaunar ne kan yadda za a tarbe shi da kulawa ta musamman ga tawagar na
Muhammad Jalal shi ne Darakta na ƙungiyoyi na shiryar Arewa maso yamma mamba a Kwammiti yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na APC (PCC). Muhammad Jalal ya nuna godiyar sa a gare shi bisa wannan ziyarar don ƙarafafa juna.