Taken Taro: Himma Ba Ta Ga Rago
ABUBUWAN DA ZA A GABATAR A LOKACIN TARON
1- Gabatar da Lakca daga masana daga fannoni daban-daban don ilmantar da masu bai wa fasahar ƙirƙira da ƙere-ƙere da ƙanana da
matsakaitan Sana'o'i.
2- Ƙaddamar da Littafin Sana'o'i
a) Sana'o'i Hamsin a aikace
b) 43 Practical skills for Economic Empowerment.
3- Bajekolin kayayyaki da ake sarrafawa a gida domin ƙarfafa guiwar masu ƙanana da matsakaitan Sana'o'i da fasaha ƙirƙira da ƙere-ƙere, wajen nuna fasahohin mu da muka gada don tafiya daidai da zamani.
4- Ƙaddamar da Manhajar kasuwar Yanar Gizo ta Taskar Nasaba (Kasuwar Baje-koli),
wadda za ta taimaka wajen bunƙasa ƙanana da matsakaitan Sana'o'i da fasaha ƙirƙira da ƙere-ƙere.
5- Karrama fitattun mutane da Sarakuna da masu fasaha da ƙirƙira
domin gudunmowar da suke bayar wa wajen samar da ayyukan yi da
ɓunƙasa Al'adu da Tarihi da Tattalin arziki wadda hakan yake samar da zaman lafiya da ƙaunar juna a cikin al'umma. Daga jihohi Goma Sha Tara na Arewa da Abuja (19 Northern State +Abuja).
Dama ce a gareku domin haɗin guiwa ko bada tallafi ko ɗaukar nauyi ko kuma bada tallace-tallace don ganin an samu nasara, sai ku Tuntuɓe mu a 09131227413, 07063387335, 08030977378, 08139135902
Taskarnasaba001@gmail.com
Rana: Wuni uku a, Janairu 2023
Wuri: Jihar Kaduna
Lokaci:- 09:00 na Hantsi zuwa 04:00 na Yamma