Daudar Gora (Chiki Ka Shata) Hausa Novel Page 7 - Novels Elite

Daudar Gora (Chiki Ka Shata) Hausa Novel Page 7 - Novels Elite

Daudar Gora (Chiki Ka Shata) Hausa Novel Page 7 - Novels Elite

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲      

  ✨𝕯𝕬𝖀Ɗ𝕬𝕽 𝕲𝕺𝕽𝕬✨

           (𝕮𝖎𝖐𝖎 𝖐𝖆 𝖘𝖍𝖆𝖙𝖆)

            𝓑𝓲𝓵𝔂𝓷 𝓐𝓫𝓭𝓾𝓵𝓵 𝓬𝓮🤙🏻

7

.........Haniniya da ƙarar takun sawayen wani farin ingarman doki ta saka Babiy sakin cokalin da yake shirin kaiwa bakinsa ya miƙe domin ceton kansa kamar yanda Dattijo nan da hadiman dake tare da su suma sukai nasu waje. Tuni tulunan zumar uku da Babiy ya kawo sukai nasu gefe suma, gaba ɗaya zumar ta kelaye a wajen. Cikin daka tsawa dattijon nan ke duban hadiman da suka biyo dokin domin kama shi...

     “Wane mara hankalinne yay sakacin daya kunce?”.

    Su dukansu jikunnansu rawa yake, cikin ƙarfin hali shugaban hadiman dake kula da barga ya zube ƙasa yana mai girgiza kansa. “ALLAH ya ƙara maka tsahon rai an gama masa wankane za'a maidashi na rantse maka”. Dattijon ya cije baki mai nuna alamar takaici, “Na baku mintuna goma kacal ku madashi shashashu kawai”. Miƙewa hadimin dattijon yayi cike da girmamwa dan dama sauran sunata ƙoƙarin ganin sun kama dokin ne, bama su kaɗai ba hadiman da yawa sun ƙaru saboda bahagon dokine da babu ma iya controling nashi sai Tajwar Eshaan. Horarran doki ne daga horonsa, da abinsa ya dawo ƙasar ruman, dokin yafi kowanne doki tsananin ƙarfi a masarautar. Shiyyasa idan har sukai sakaci ya ɓalle kowa sai ya jigata kafin a kamashi da ƙyar, kafinma kamashin sai an samu wanda sukaji raunika da yawa. Akwai randa irin haka ta taɓa faruwa baƙaramin jigata mutane yay ba harda masu karaya a hadimai, kuma duk iya wahala da jigata babu wanda ya iya kama dokin har duhun magriba yayi dan da yamma al'amarin ya faru. Kowa yayi laushi an rasa in za'a kama sai ga Tajwar Eshaan ya fito sallar magrib, abu mafi ban mamaki daya saka masarautar yin shiru na sakanni uku kiran sunan dokin kawai yay sai gashi gabansa, ya girgiza jikinsa tare da yin haniniya sannan ya koma kan ƙafafunsa ya tsaya cak tamkar bashiketa jigata mutane da hargitsa wajen ba. Wannan abun mamaki ya saka dukan hadiman da suka zube saman gwiyawunsu kawunansu a ƙasa a lokacin kasa haƙuri sai da suka saci kallon dokin dama Tajwar Eshan ɗin da hirami daya yafa a kansa ya rufe rabin fuskarsa.....

        ★★★★

  A ɓangaren Iffah gaba ɗaya idanunta sun kasa barin ƙofa, babban burinta kawai dawowar Babiy taji zuma ta isa hanun Shahanshan. Sai dai shiru kakeji har akai sallar juma'a bai shigoba. Ko abinci babu yanda Ummu batai da ita tai zaman ci ba amma taƙi, Hanash ma sai da ya mata maganar tazo suci kamar yanda sukanyi duk juma'a tunma su Fariha nada rai amma tace batajin yunwa. Ƙyaleta sukai dan sun kasa gane minene ya hanata nutsuwa waje ɗaya.

     Babiy bai shigo gida ba sai bayan sallar la'asar. Azabure Ummu ta miƙe tana kallonsa. “Innalillahi wa inna'ilaihirraji'un. Abu Hanash haɗari kayi?”.

        Kai Babiy ya girgiza mata yana kaiwa zaune da ƙyar. “Ke dai bani ruwa na fara sha”.

    Kafinma ya rufe baki Iffah da itama jikinta ke rawa ta kawo masa ruwan, dai-dai nan Hanash ya fito daga ɗakinsa cikin shirin fita ƙwallo. Shima a ruɗe yay kan Babiy ɗin yana jera masa tambaya. Babiy ya ajiye kofin ruwan yana mai kallonsu gaba ɗaya. “Kunga ku kwantar da hankalinku babu abinda ya faru daga masarauta ne. Wani bahagon dokine fa ya kunce al'amarin tamkar yaƙi, hatta da zumar dana kai ba'a mora komai a cikinta ba ma”.

    Ummu da Hanash suka shiga jera salati, yayinda Iffah taji wani ƙududun baƙin ciki ya tokare mata maƙoshi, hakan na nufin bataci nasara ba sai ma Babiy daya dawo da raunika. Jitake kamar taga Tajwar Eshaan gabanta ta shaƙesa da hannayenta har sai ya bar duniya saboda tsabar tsanarsa. Har Hanash ya gama yima Babiy dressing ciwukan batace komai ba, daga ƙarshe ma ɗaki ta shige ta shiga faman kaikawo na tunanin abu na gaba. Dan tayi alƙawarin bazata taɓ haƙuraba sai ta kai *_Tajwar Eshaan ibn Haysam Abdull-majeed_* ƙasa zata samu salama game da rasa ƴan uwanta. 


         Sam a wannan dare Iffah bata wani isashen barci ba saboda ƙullawa da kwancewa aka shiri na gaba. Abinda ta gama ƙullama zuciyarta yasata shirin fita a gidan da hantsi da dalilin cewar zataje wajen Ikram duba mamanta bata da lafiya bazata jima ba. Ummu tayi kamar bazata barta ba amma taita mata magiya harta amince da sharaɗin karta jima, kuma dolene ta rufe duk jikinta. Ta yarda da hakan saboda tana son fitar. A gurguje tai shirin fitar, tare da lalubo wayar Arfa a cikin kayansu. Koda ta haɗa batteryn ta kunna tayi sa'a tanada caji, dan haka ta loda number da take buƙatar kira tana mai addu'ar ALLAH yasa akwai kuɗi ma. Addu'ar tata bata amsu ba, dan haka ta tura wayar cikin jikinta bayan ta kashe sannan ta fito tai sallama da Ummu ta fita bayan ta amsa kuɗin taxi. Sai da ta fito daga cikin anguwarsu gaba ɗaya sannan ta tsaya ta sai kati, koda ta loda sai ta sake gwada kiran lambar ɗazun. Cikin sa'a kuwa aka ɗauka, jimm sukai su duka kafin ta katse shirun da sallama. Daga can aka amsa a noƙe alamar rashin sanin dawa ake tare. Fahimtar hakan ta saka Iffah bashi amsa tunkan yay tambayar.

     “Sir! Kana magana da Fareedah bint Zayy......”

      “Serious?”.

Ya faɗa cikin katseta da alamar zabura tun kan ta ƙarasa faɗa. Baki ta ƙyaɓe a ƙasan zuciya tana jan tsuka, a zahiri kam sai ta saki murmushin da har sautinsa ya kai cikin kunnensa. Cike da sake ƙanƙan da kai tace “Tabbaci Sir. Ina buƙatar muhaɗune yanzu yaya za'ayi?”.

      “Kai! Iffah! Ke ɗin dai?...”

“Bazan samu damarba ko......?”

Cikin sauri ya katseta. “No ba nufina kenan ba, kawai na shiga al'ajab ne. Amma bara na ajiye tantamar tawa gefe dai. Inaga zanzo na sameki gida kawai...”

     “A'a sir”.

“Miyasa?”.

  “Ba buƙatar hakan, mu haɗu kawai”.

Jimm yayi na tunani, sai kuma ya sauke numfashi. “Okay! okay inaga bara na tura miki adireshin inda nake a yanzu haka sai mu haɗu nan in ba damuwa ko”.

        “Ya dai kasance babu abinda zai shafi mutuncina a wajen sir”.

     “Wannan shike ƙara samun naji ke ta daban ce Iffah”.

    Baki ta sake ƙyabewa. Amsa garesa kuma tace “humm” kawai.


       ★     


    Kallon baki da hankali mai haɗi da tsoro tun daga ƙarƙashin zuciya yake mata tun bayan gama masa dogon jawabin da tayi. Tasan zataga fiye da hakan ga kowa bama shi kawai ba, dan haka bataji komai ba sai ma murmushi data sakar masa. Bata san mi yake tattaunawa da zuciyarsa ba, amma tanaji a ranta yana auna shekarunta da maganganun da kowa zai auna da wautarta ne kawai. Ilai kuwa sai ta tsinkayi muryarsa da irin amsar datai tunanin samu. 

       “Nikam Iffah shekarunki nawa?”. 

   “Ashirin a kwashe biyu sir”.

Ta faɗa tamkar bata fahimci alaƙar tambayar tasa ba. Kansa ya jinjina da cije lips nashi, kansa tsaye yace “Nama tunaninki mai kama da mafarki uziri. Amma zan baki shawara data dace da waɗanan shekarun naki na ƙuruciya. Ƙoƙarin ya kamata kiyi wajen cinye jarabawar share fagen shiga jami'a da ke  tunkaroki kamar yanda nasan burinki. Tunaninki kuma ya zam tamkar baki taɓa yinsa ba, sannan na kasance na farko kuma na ƙarshe da kika faɗawa. Hakanne zai baki damar cigaba da ƙyaƙyƙyawar rayuwar da kika fara da ke da ahalinki har nima na cigaba da saka rasan samunki matsayin uwar ƴaƴana wata rana dan ALLAH Iffah”. Ya ƙare maganar da haɗe hannaye alamar roƙo.🙏🏻

     “Ƙyaƙyƙyawar rayuwa ta daɗe da yankewa a cikin rayuwata data ahalina. kuma irinta nake hangowa da son daƙilewa ga ƴan baya ciki harda ƴaƴan da kaima a karan kanka zaka iya haifa wataran Sir. Sannan wannan tsoron da nake gani yanzu a cikin idanunka shine zai tabbatar da hakan, koda ni bana raye kai zaka rayu ka tuna. Nagode da saurarena da kayi sir”.

     Da sauri yasha gabanta kasancewar ta riga ta miƙe. Tai takwaf-takwaf da fuska tana mai tsaresa da manyan idanunta da tuni hasken cikinsu ya koma launin ja. “Ki fahimceni Fareedah, koba komai na fiki shekaru, na fiki ilimin sanin rayuwa dama sirrikan dake zagaye da lungu da saƙo na ƙasar Ruman....”

      “Na sani sir, tabbas na sani shiyyasa ma na fara nemanka. Sai dai nima kayi haƙuri, dan babu shawararka ɗaya data shiga cikin wannan kan nawa, saboda abinda ke cikinsa tamkar kundin littafin da aka rubuta labari daki-daki ne, kaga dole zaizo feji bayan feji. Kuma duk abinda ya shiga ciki bazai taɓa goguwa ba sai ta hanya ɗaya tak! Mutuwa!. Mutuwa ce kawai zata goge wannan yunƙurin insha ALLAH. Na barka lafiya”.       

        Sororo ya bita da kallo harta tare mototaxi ta shiga, ji yay ta ƙara masa girma a ido, girma bana shekaru kawai ba na wata ilhamar kwarjini da cikar mutuntaka. In har yara irinta da ayanzu suka fara rayuwa zasuyi irin wannan tunani akan al'ummarsu mi manya kakaninsa, iyayensa, yayunsa dama sa'aninsa sukeyi ne su? Shin basa ganin abinda take gani ne? Ko kuwa da gaske tsoron data ambata ta gani a cikin idanun nasane a idon kowa?. Kenan hatta da sauran sarakunan ƙasar da mafi yawan cikinsu sun rasa ƴaƴansu suma cikin tsoron suke? Anya maganar mutane ba tabbatacciya bace akan danganta Shahanshan na daular ruman da magajin fir'auna daya shuɗe batare da labarinsa ya gushe ba?. Iffah! Iffah!! Da gasken gaske ke tadabance kamar yanda nasha faɗa a aji aduk sanda kika bada amsar data danganci darasi......


      ★★★

   

     Kwanaki uku kenan da Iffah ta tunkari malaminta batare da nasara ko ƙwarin gwiwa daga garesa ba. Sai dai hakan baisa taji ta sare ba ko haƙura da ƙudirinta. Koda ace nata ajalin take tunkara tayi alƙawarin sai tabi kadin jinin ƴan uwanta guda biyu. Koda ace bata da ƙarfin ikon ruguza mulkin sarkin dake kama da mulki irin na fir'auna zata tabbatar sai kuwwar gunjin kukanta ta fita a duniya, koba komai tanada yaƙinin a bayanta zata samu masu share mata hawaye insha ALLAHU.

     Hanyar da tabi a farko ita kaɗaice hanyar da tasan tanada ita wajen bi ta samu nasara cikin sauƙi. Sai gashi kuma ba'a dace ba. Gashi tabi ta biyu itama, sai dai anƙi buɗemata ƙofar saboda tsoro da ƙarfin tasirin mulkin azzalumin, a yanzu haka tunaninta hanya ta uku koda itama bazata samu nasarar ba. Zata kuma cigaba da bin hanyoyin koda zasu ninka dubu sau dubu har sai ta dace. Nannauyan numfashin data zuƙa ta fesar, tare da gyara kwanciyata ta jawo wayar Arfa da har yanzu bata bari wani a gidansu yasan da tana amfani da ita ba. Ido sosai ta tsurama wayar, tabbas ba gizo bane tarin missed call ne daga malaminta. Taruwarsu da rashin jin sanda suka shigo wayar kuma nada nasaba da kasancewarta a silent. Tayi kamar zata share amma sai ta kasa hakan. Dan a yanzu shine kawai madubin da take kallo matsayin damar dake a hanunta ta isa ga abinda take so da wurwuri. Cikin sa'a tana kokarin kiransa sai ga kiran nasa ya sake shigowa. A dakile ta amsa tare da masa sallama murya a cuɗe. 

       “Kiyi haƙuri”.

Kalmar farko data fara fita a bakinsa. Iffah taja numfashi mai nauyi tare da haɗiyewa muƙut. “Sir bakamun laifin komaiba nikam”. Ta faɗa tamkar komai baima faruba. “Humm” ya faɗa shima, sai kuma ya ɗora da faɗin “Ina son mu haɗu”.

    “Babu dalilin hakan sir”.

  “Akwai Fareedah, kar kiyi taurin kai”.

    “Koba komai kai ɗin malamina ne ai, mi zaisa na maka taurin kai?. Iya gaskiyata nake faɗa maka”.

       “A cikin gaskiyar taki harda haƙura da samun abokina”.

Zumbur ta miƙe zaune tamkar wadda aka kwantsamawa a radu a tsakkiyar kunne. “Sirrrrr!.....”

     “Na amince zan haɗaki da shi”.

Ya katseta da sauri. Jitai tamkar ta sandara ihu ko zaifi fahimtar farin cikin dake a tare da ita, amma sai tai ƙoƙarin gimtsewa. “Sir ba dole sai shi kawai bane zaiyi aikin, harma na samu wan....”

   “Fareedahhh!”.

Ya faɗa da wani yanayi a muryarsa. Ajiyar zuciya ta sauke a ƙasan maƙoshi. Sai kuma ta lumshe idanu tamkar tana a gabansa tace, “Shikenan ka turamun adireshi. Sai dai inda bazai taɓa mutuncina ba”.

    Murmushi yayi mai sauti, tare da faɗa kamar yanda ya saba tun acan baya. “Fareedah ke ta dabance ƙwarai da gaskeeee”.

    Baki taɗan laɓe batare da tace komai ba ta yanke wayar..........✍



*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*


*DAUDAR GORA Billyn abdul*


*KI KULANI hafsat xoxo*


*A RUBUCE TAKE Huguma*


*RUMBUN K'AYA Hafsat rano*


*IDON NERA Mamuh ghee*



_LITTAFI DAYA: 400_

_LITTAFI BIYU: 600_

_LITTAFI UKU: 800_

_LITTAFI HUDU :1000_

_LITTAFI BIYAR: 1200_


_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_


_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_


_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_


_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_


_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_


_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_


ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN


MARYAM SANI

ACCESS BANK

0022419171


SAI A TURA SHAIDAR BIYAN 


09033181070


IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA


09166221261


*ƳAN ƘASAR NIGER🇮🇳. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*


+2290165991


Books biyar  1250CFA

Books hudu  1050CFA

Books uku  850CFA

Books biyu  650CFA

Bookk daya  450CFA


KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.


MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏽_*

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post