MAKAUNIYAR ƘADDARA_*💔
*Page 26*
___________________________
💫💥💫💥💫💥💫💥💫💥💫
*_ALBISHIRINKU MATAN AFRICA DA KEWAYE , SHAHARARRAR KUMA
KASAITACCIYAR MAI SAIDA KAYAN MATAN NAN WADDA KUKAFI SANI MAMAN YUSUF YAR
SOKOTO TANA YI MAKU ALBISHIR DA CEWA ZAKU IYA SAMUN KAYANTA ADUK INDA KUKE
CIKIN FADIN NIGERIA DA NIGER KARKU MANTA MACE MAI GYARA KANTA BATA BORANCI_* 💃💃💃💃💃💃💃 07069711327
_Akwai zafafan kayan Mata masu kyau da arha cikin sauki da
rahusa Kuma duk inda kike zamu aika maki kayanki cikin aminci da yardar Allah
ba cuta ba cutarwa don a Dade anayi sai gaskiya uwargida da amarya ku garzayo
Kar abaku labari_
Munada kalolin Kaya kamar haka💥💫💥💫💥💫👇🏻👇🏻
Maganin sanyi sahihi Mai fatattakar sanyi cikin kankanin
lokaci na maza Dana Mata
Maganin gyaran nono domin dawo da martaban nononki hadin
gargajiya da bashida illah ajiki
Maganin hips Mai tado da hips cikin kankanin lokaci
Maganin kiba Wanda zaisa ki ciko dai dai misali kiyi kyau
kema ki shigo cikin jerin Mata masu aji
Maganin rage kiba da tumbi Wanda zaisa ki sace ki koma Yar
dai dai abin alfaharin kowane namiji,
Akwai kalolin gumbuna masu kyau da saukar da ni'ima
Maganin matsi masu ciko da gaba da matseki Kamar Yar budurwa
uwa uba zasu Baki dandano Mai gamasar da maigida
Kalolin garrika masu bawa mace niima da jimawa ajiki
Kalolin tsumi Sha yanzu magani yanzu dasa Mai gida ihun Dadi
Zumar mallaka
Zumar goron Tula
Zumar ridi
Zumar Mai rubutu
Hadin mallaka
Turaren mallaka
Shu'umar humra
Turaren AL'AJABI
Matan gaske
Ak 49
Sirrin tafin k'afa
Turaren fuska
Hatsabibin turare
Kwallin mallaka
Zoben mallaka
Jigidar maida tsohuwa yarinya
Maltinar Mata
Karya gado
Yajin Mata (yajin Mai ciko da mace)
Yajin maza (domin Karin k'arfi)
Muna dahuwar Kaya kamar haka💫💥💫💥👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
Dahuwar zabo (mallaka)
Kazar Yar gata
Yan shila
Ciccibi
Dambu
Zuciya
Yan ciki
Kwai ukku
Tsoka Tara
Kifi
Da sauransu
Akwai sirrika sosai da muke hadawa ga wacce kishiya ta
addabeta ko wadda take fama da butsarin namiji ko mafadacin namiji ko namiji
Mai yawon dare ko Wanda yake bin Mata insha Allah duk zaku samesu Kuma da
yardar Allah za'asamu biyan bukata
Muna bada magani ga yarinyar da tsautsayi ya fad'a Mata ta
rasa budurcinta ta hanyar fyade ko yaudarar da namiji Kuma insha Allah zaadace
da yardar Allah
Abubuwan da yawa gsky Wanda in nace Zan lissafasu sai nakwashi
tsawon lokaci maiso tabini PC don ganin kalolin kayan da muke dasu ,
Karku manta mace Mai gyara kanta Bata boranci taku ce maman
yusuf Yar mutan sokoto 07069711327
.
Don Allah wadda Bata shirya ba tabari sai ta shirya sannan
tayimun magana🙌🏼🙌🏼🙌🏼🙌🏼🙌🏼ngd
07069711327
__________________________
*page 26*
...........Baki ya buɗe zai bama wanda suke maganar amsa
dai-dai da isowarsa gab dasu hakan ya gagara. Dan a take harshensa ya sarƙe
saboda sauka da idanunsa sukai akan fuskar Little dake ɗauke a kafaɗar
Zinneerah ya wani lafe jikinta hannunsa na wasa da jelar kitsonta ta bayanta.
Ita kanta sake shiga ruɗani zuciyarta tayi kasancewar kusancinsu sosai yau da
little ɗin ya ƙara fiddo mata da kamanninsu ainun.
Sannan ganin yanda yake kallon
little ɗin shima sai da hanjin cikinta suka motsa. Ba ita da shi bane kawai a
ruɗanin hatta da mmn sadiq sai da tayi kamar zata kifa daga bayansu. Ƙirjinta
kuwa yay wani mummunar bugawa tanabin AK ɗin da kallo. Duk da ƙarancin shekarun
Sadiq da Abdull suma dai su kalli little su kalli AK ɗin da ayanzu yay ƙarfin
halin ɗauke idanunsa yana maida hankalinsa ga wanda suke wayar duk da a baɗini
sam hankalin nasa baya tare da shi.
A haka suka wuce juna su Sadiq na
waiwayensa, hakama mmn sadiq sau kusan uku tana waiwayowa ta kallesa, kamar
yanda shima ɗin ya kasa daina binsu da kallo. Zinneerah kam da ƙar ta cigaba
dajan ƙafafunta ta ƙarasa dasu sashen hajiya iya. Inda acanma kallo ya koma
sama. Dan tun sallamar da sukayi kowa ya amsa su Meenal suka taso da gudu suka
rungume Mmn sadiq suna mata sannu. Sun juyo da nufin ma su Sadiq sannu da zuwa
idanunsu ya sauka akan little.
“What!”.
Jamal ya faɗa a hankali yana tsare little ɗin dake lafe a
kafaɗar Zinneerah har yanzu da ido. Sam hankalin Zinneerah baya tare dasu a
yanzu, dan yau tafi kowacce irin rana shiga ruɗani akan kamannin little da Yah
Adnan. Shiyyasa harta sauke little ɗin ƙasa bama tasan tayi ba. Hakan kuma
dataine ya bama duk sauran yaran gidan ganinsa sosai. A take sannu da zuwan da
suke Mmn sadiq ya shiga maƙalewa a maƙosansu. Dan yau harsu Momie suna a sashen
suma.
Cikin ƙarfin hali Khalipha
da yay mutuwar tsaye shima ya nuna musu hanyar ɗakin hajiya iya yana faɗin,
“Mama ku shiga tana ciki”.
Kai Mmn sadiq ta ɗaga masa tana
murmushin yaƙe dabin Khalipha ɗin da idanu itama dan ta ganesa duk da ya ƙara
buɗewa fiye da wancan sanin datai masa.
Duk wannan al'amari dake faruwa Farah na ɗaki
kwance dan taƙi sakewa a cikinsu kamar yanda takeyi dama idan tazo gidan. Saboda
karma Adnan ɗin ya zargeta catai masa bata da lafiya. Yarda yay tunda yasan
tana laulayin ƙaramin ciki kamar yanda Mammah ta sanar masa.
Hajiya iya na kwance suka shigo.
amma tunda idonta ya sauka akan little itama babu shiri sai gata zaune. Ta haɗiye
yawu da ƙyar tana miƙa masa hannu shi dasu Aliyun. Babu musu duk suka nufeta.
Sai da suka gaisheta da jiki sannan suka zazzauna inda ta nuna musu a kusa da
ita kan gadon. Little kuwa matsawa yay jikinta ya kwanta dan shi dama akwai son
jiki. Su Sadiq sun shagwaɓa shi, harma dasu Mmn Sadiq ɗin.
Hajiya iya takai hannu kan
little ta shafa zuciyarta na wani irin harbawa. A ranta ko rayawa take tamkar
Moddibo na ƙarami. A fili kuma saita maida hankalinta ga Mmn sadiq dake
gaisheta cike da kulawa.
Tunda suka shige aka shiga ƴar
kallon kallo a falon, dan bakin kowa ya kasa furta komai. Sai can kamar a fisge
Saffiya tace, “Wannan ai yaron dana ɗakko muku hotonsa ne. Amma kuma ba maman
bace wannan”.
Shigowar Baffah da AK ne ya hana kowa
amsa zancen Safiyya ɗin. Sai ma zubama Yayan nasu ido sukai zukatansu fal ruɗani.
Shima kansa a ruɗanin yake. Amma kasancewarsa gwanin kamewa yasa babu mai iya
fahimtar halin da yake a ciki akan fuskarsa. Sannu da zuwa duk suka shiga yima
Baffah. Ya amsa musu sama-sama yana nufar ɗakin mahaifiyarsa dan ba'a cikin
hayyacinsa ya dawo ba.
Da sallama ya shigo, AK biye dashi a
baya. Ganin Mmn sadiq ya saka Baffah nuna jin daɗinsa. Suka gaisa cikkn girmama
juna. Suma su Sadiq suka gaishesu ya amsa musu da kulawa. Sai da ya maida
hankalinsa ga Hajiya Iya data kafe AK da kallo sannan shima idanunsa suka sauka
akan little da barci ya fara ɗauka a jikin hajiya iya.
Wani irin muƙut, Baffah ya haɗiye yawu
da ƙyar yana kallon little da ƙyau. Kasa jurewa yay sai da ya juyo ya kalli AK
da gaba ɗaya hankalinsa ke akan little shima. Ya sake maidawa ya kalli little
again zuciyarsa na wani irin rawa. Dan ƙarara zakaga shi ruɗaninsama akan
fuska. Kasa jurewa yay sai da yace, “Ikon ALLAH innata kunga wani kamanni yau
dake neman hargitsa tunanina anan, ɗan wanene wannan?”.
“Bakai kaɗaiba Babangida. Ni
kaina bakaga na kasa daina kallon yaron da Moddibo ba. Ai wani hikima sai
UBANGIJI. Wlhy sai kace Moddibo na ƙarami. Hauwa'u wannan yaro nikam idan a
wani guri na gansa ai sai nace namune ma. Ina kika samosa?”.
Duk da faɗuwa da gaban mmn Sadiq yayi
cikin juriya tai murmushi zata bata amsa Aliyu yay saurin faɗin, “Mama ƙaninmu
ne”.
Shiru ɗakin yayi, Mmn Sadiq ta
sauke wani ɓoyayyar ajiyar zuciya. Dan a ganinta ba'a wannan halin da hajiya
iya ke a ciki yakamata tasan matsayin little ba. Amma insha ALLAHU tayi
alƙawarin tana samun lafiya zasuzo ita da Abba sumasu bayanin komai. Shiyyasa
taso tunma kan Zinneerah ta taho su faɗa musu. Amma batasan dalilin Abban na
hanawaba.
Baffah ne ya katse tunanin na
maman sadiq da faɗin, “Kai masha ALLAH, ALLAH ya albarkaceku, hikimar UBANGIJI
ai tafi ƙarfin mamaki. Hakan na ƙara nuna mana muhimmancin zuminci da ƙarfin
jini dake tsakaninmu Hauwa'u. ALLAH ya sake ƙara mana ƙarfi da kusanci, ya kuma
sa muci amfanin hakan duniya da lahira”.
Da amin duk suka amsa. Baffa ya shafa
kan yaran duka har little daya ɗan buɗe ido ya dubesa na kusan sakan goma
sannan ya maida ya rufe. Daga haka aka koma gaishe-gaishe duk da zuciyar kowa
dai ba adaidai takeba.
Bayan Baffah ya fita aka kawoma su mmn
sadiq abinci da ruwa. Ruwanma kawai suka sha dan a ƙoshe duk suke dama. Suna
nan zaune tare da hajiya iya har akai kiran sallar magriba Khalipha yaja su
Sadiq suka tafi massallaci. Bayan an idar ne sun dawo suka iske Little ya
tashi. Sai dai suna toilet Zinneerah ta kaisa zaiyi fitsari. Sannu suka sakema
Hajiya iya dake zaune ta idar da salla duk suka fita.
Zinneerah ta fito riƙe da
little dake mata maganar da ba wani fahimta takeba sosai saboda bawani ya iya
bane da ƙyau. Murmushin ƙarfin hali take masa itama tana magana ƙasa-ƙasa.
Hakan yayi dai-dai da shigowar AK ɗakin da sallama. Amsa masa duk sukayi
idanunsa na sauka akan Zinneerah da little ɗin. Ita dai bata yarda ta kalli
sashen da yakeba, sai da a bazata suka ji little yace, “Abbah ruwa zan ca”.
Gaba ɗaya suka kalli yaron
da mamaki dan AK yake kallo, kuma shine ya shigo hannunsa riƙe da goran ruwa.
Murmushi AK ɗin ya saki wanda ya
sake fidda kamanninsa da little ɗin ainun yana nufosu. Ƙirjin Zinneerah ya
harba da ƙarfi lokacin da yazo gab da su ya miƙama little ɗin hannu alamun yazo
gareshi yana faɗin, “Oh my Sweetheart zo, zo”.
Saurin sakar masa shi tayi tana ja
baya, shiko little cike da farin cikin daya bawa kowa mamaki musamman ma su su
Zinneerah da suka san miskilancin yaron ya wani maƙalƙale Yah AK ɗin yana sauke
ajiyar zuciya. Shi kansa AK ajiyar zuciyar ya sauke a ɓoye da sake manne yaron
a jikinsa jininsa na tsinkewa. A hankali ya sumbaci goshin yaron sannan ya
zauna a bakin gado ya saka masa ruwan a baki yana shafa kansa.
Baki little ya janye yana faɗin,
“Ƙoshi Abbah”.
A bazata sukaga AK ɗin yayi dariya da
jan hancin yaron yana faɗin, “Wannan hausan naka bai cikaba little Handsome”.
Ƙaramar dariya hajiya iya da zuciyarta
ke ƙara raunana da shiga ruɗanin wannan al'amari tayi. hakama Mmn sadiq tai
murmushin yaƙe kawai. Kallon Zinneerah hajiya iya tayi. “Inno na a bashi abinci
ko”.
Kai ta kaɗama Hajiya iyan da
nufar kulolin da aka kawoma su mmn sadiq ɗin basu ciba. Ta buɗe ta zubo abincin
kaɗan a filet. Kallo ɗaya tayima little ɗin dake jikin Yah AK yana masa firar
da baya fahimta dan maganar tasa ba nuna taiba ta ɗauke kai. “Malami sakko ga
abincin”. Tai magana tana dubansu.
Kafaɗa ya noƙe alamar bai zuwa. Hakan
yasa Zinneerah hararsa ta ɗauke kanta ta maida gasu Aliyu. “Kuma zakucine
Abdull na saka muku?”.
Kai suka girgiza mata alamar a'a.
Dan haka ta sake duban inda little yake ganin ko motsi baiyiba har yanzun. Zata
sake magana AK ya harareta kaɗan da miƙa mata hannu alamar ta bashi abincin.
Baki ta ɗan tura gaba da miƙewa takai masa. Harta juya little yace, “Aunty!”.
Juyowa tai ta kallesa, ganin ya maida kansa
kamar bashi ya kiraba yasata hararsa, sai ko a cikin idon AK daya ɗago. Da
sauri ta ɗauke kanta ta nufi hanyar ƙofa tana ƙunƙuni a cikin ranta.
Baya taɗan ja
saboda Khalipha da zai shigo. Ya dubeta da murmushi dan zuwa yanzu kam ya yarda
wannan Zinneerah ce daya sani a Shira hospital. Sai dai little ya saka
zuciyarsa a tsananin ruɗani da firgici, dan inhar zai auna da ma'aunin hankali
shekarun little zasu iya kaiwa dai-dai da hasashen haihuwar Zinneerah. Amma
yaƙi ya yarda da cewar shine ɗan data haifa ɗin.
“Kanwata sai ina kuma?”.
Murmushi tai masa daɗan shafar wuya. “Yah Khalipha zan
fitane kawai”.
Murmushin ya
sake sakar mata shima, da matsawa ya bata hanya ta fice shikuma ya ƙarasa
shigowa idanunsa na sauka akan Yayansu dake bama Little abinci a baki. Ji yay
sun wani bala'in birgesa. Har yana ayyanawa a ransa inama ace yaron nan jinin
yayan nasune da gaske.
Takawa Khalipha yay ya zauna kusa
da yayan nasu yana mai shafa kan little ɗin. Juyowa little yay ya kallesa sai
kuma ya juya ya cigaba da karɓar abincin. Kaɗan yaci abincin yace ya ƙoshi,
badan AK ya gaji da bashiba ya haƙura ya barsa. Haka ya cigaba da zama a
jikinsa har ya sake komawa barci.
Su Mmn Sadiq basubar gidanba sai wajen
tara saura na dare. Da ƙyar aka raba little da jikin Yayah Adnan, dan lokacin
da Khalipha dazai kaisu yazo amsarsa sai gashi ya farka a bazata. ya ƙanƙame AK
ɗin yaƙi zuwa wajen Khalipha. Murmushi AK yay da lumshe idanun yana sunbatar
little ɗin a goshi da shafar bayansa. Shi kansa ƙarfin hali kawai yakeyi, amma
ji yake kamar karya rabu da yaron dan yayi bala'in shiga ransa.
Daga ƙarshe dai da ƙyar ya yarda
Khalipha ya ɗaukesa dan sai da aka haɗa da masa wayo. Motar na ficewa ya sauke
wata nannauyar ajiyar zuciya hawayen da baisan kona minene ba suna ciko masa
idanu. Ƙoƙarin maidasu yay yana furzar da huci mai zafi da nufa garden ya zauna
dan babu abinda yafi buƙata a yanzu kamar kaɗaici.
Yanda AK ya kaɗaice kansa
Zinneerah ma harabar gidan ta fito can wajen motoci ta hau bayan ɗaya daga ciki
ta zauna tare da faɗawa duniyar tunani. Gaba ɗaya zuciyarta a ruɗani da ɗimuwar
kiɗima take. Shin a ina aka faɗi a ragaya ne? Wane darasi rayuwa keson karantar
da ita a wannan gaɓarne bayan darasissikan data baro a shekarun baya?. Ko
mahaukaci ya kalli little ya kalli Yah AK dolene ya danganta alaƙar jini a
tsakaninsu. Dan abinda zai matuƙar baka mamaki ba kammaninne kawaiba. Hatta da
wasu a cikin halayen Yah Adnan akwai alamunsu ga little. Kenan to.......
“Kai ina”. Ta faɗa a fili tana girgiza
kanta dake matuƙar sara mata. Kamar ance ta ɗaga kai can ta hango Baffah a
barandar sama yana kaikawo alamar shima akwai abinda ke damunsa, wanda bata
raba ɗayan biyu zancen kamanin little ne da Yayan nasu.
“Ya ALLAH kai ne gagara misali,
ka buɗemin tunani, ka yalwatamin fahimtata. Ka gafarta mini zunubaina”. Ta faɗa
hawaye na silalo mata akan kumatunta masu zafi. Zurfi sosai ta ƙarayi a tunani
har motar Khalipha daya kaisu mmn sadiq ta shigo gidan bata saniba. haskatan da
yayne shima ya sakashi ganinta. yana gama fakin ya nufo inda take. Sau biyu
yanayin sallama babu amsa, har dai ta kaisa ga ɗan bugar motar ta gefen
kunnenta sannan ta kawo nannauyan numfashi tana dubansa.
“Wane irin tafiya tunanine haka
da zurfi ƙanwata?”.
Murmushin yaƙe tai masa tana duƙar da
kanta ƙasa. Hakan datai sai ya ƙara fiddo masa da kamanninta na baya sosai. Yay
murmushi yana gyara tsaiwarsa da faɗin, “Zinneerah na tambayeki mana?.”
Gabantane ya faɗi, amma
sai cikin dauriya tace, “Ina jinka Yah Khalipha”.
Kansa ya kaɗa mata yana ajiye keys ɗin
hannunsa da wayarsa alamar maganar mai muhimmanci ce. “Dan ALLAH ki faɗamin
gaskiya kin manta dani ko?”.
Duk da tambayar tasa tazo mata a
bazata dan ba ita tai zaton jiba sai da taji dumm. Ganin ya kafeta da idanu ya
sata yin murmushin yaƙe tace, “Ban gane mi kake nufi ba Yah Khalipha”.
“Nasan kin gane Zinneerah,
amma tunda hakane bara na miki dallah-dallah”.
“Tun randa na ganki a
gidan nan nasan nasan fuskarki, amma na rasa ina na sanki dan kin banbanta da
waccan ɗin dana sani a yanzu. Nasha gwadaki naga ko zaki nuna ke kin sani amma
baki nunaba, sai yau da naga mama na tabbatar da cewa kece. Shiyyasa mamaki ya
kamani na rashin nuna kin sanni da kikai kafin yau”.
Tabbas taji kunya. amma sai ta
dake, ta buɗe baki da zummar bashi amsa sukaji ƙamshin turarensa da takun
tahowarsa. Duk kallon waje. sukai Zinneerah na haɗiye maganar da tai niyyar yi.
Ganin yanda yake kallonsu ya sata jin wani iri, babu shiri ta diro akan motar
tai cikin gida sum-sum duk da alamar ta zauna da Khalipha ke mata da hannunsa.
Khalipha da shi
kansa kallon da Yayan nasu ke musu ya bashi mamaki, cikin dauriya yace,
“Yayanmu na zata ka kwanta ma ai”.
“Shiyyasa kazo nan kake taɗi?”.
Ya faɗa yana wucesa. Saurin waro idanu Khalipha yay waje da
biyo bayansa. “Ni Abdul-Mutallab, jikan Abdul-Mutallab, ƙanin Abdul-Mutallab
wane ni Yayanmu”.
Ɗan juyowa yay ya dubesa. Hakan yasa kunya
kama Khalipha yakai hannu yana shafa wuya da risinar da nasa idanunsa ƙasa.
Wani irin juya idanunsa da
suka ɗan fara sauya kala yayi yay gaba batare da ya sake cema Khalipha ɗin
komaiba, dan harga ALLAH baya cikin hankalinshi da nutsuwar. Binsa da kallo
Khalipha yay harya shige sashen Hajiya Iya. Kasa binsa yayi, sai kawai shima ya
nufi sashensu zuciyarsa na ƙoƙarin karkato masa wani abu daban.
★★★★
Washe gari da safe suka tashi da tashin
hankalin ruɗewar jikin Hajiya Iya. Dan tunanin data kwana yi jiya game da
kamanin little da AK ya ja jininta sake hawa sama matuƙa. Ita Zinneerah bata
fahimtaba dan duk zatonta Hajiya Iya barci takeyi, dan itama kanta barcin nata
rabi da rabi ya kasance. Sai da ta farka da asuba taji hajiya iya na wani irin
wahallen nishine hankalinta ya tashi. Ruɗani ya sata fita da gudu zuwa ɗakin AK
ta hau bugawa tana kiran sunansa.
Zaune yake saman sallaya yana karatun
Al-Qur'ani dan shi ko sau ɗayama bai rintsa ɗinba. Yanda yaga rana haka yaga
dare, a daren na jiya. Tunda yaji bugun ƙofar yasan ba lafiyaba. Ya ajiye
Qur'anin tare da miƙewa a nutse ya nufi ƙofar ya buɗe ko sauraren Farah data
farka da jan tsaki baiyiba.
A rikice Zinneerah ta damƙo hannunsa
jikinta na rawa ga hawaye na kwarara. “Yayanmu Granny, Granny Yayanmu, dan
ALLAH kazo Granny karta mutu”.
A take shima ya rikice. Ya shiga binta
a baya tana riƙe da hannunsa har sannan tana jansa. Tunda suka shigo yaga halin
da Hajiya Iyan ke a ciki sai hankalinsa yafi nata tashi, a take yay kanta yana
kiran sunanta da ƙarfi.
Zinneerah daketa yarfe hannu kukanta na
ƙara tsananta ya duba cikin sarƙewar harshe yace, “Ɗakkomin waya a ɗakina,
m....”
Batama bari yakai ƙarsheba ta kwasa da gudu ta
fice. A guje ta shigo ɗakin har tana bangaje Farah data sakko daga gadon tana
mitar an tasheta tana barcinta. Wanwar Farah ta zube a ƙasan tiles ɗin amma ko
kallonta Zinneerah bataiba ta nufi wayar data hango a drawer gefen gado duk da
bata da tabbacin nasane. Sai dai tana kaiwa garesu ƙamshinsa dake manne dasu
suma ya tabbatar mata nasanne. Duka ukun ta kwasa ta sake tsallake Farah dake
nishi a ƙasa ta fito.
Da ƙyar ya iya saita kansa
ya lalubo Number Baffah, shima Baffah da yake ba wani barcin kirki yayiba akan
idanunsa kiran ya shigo. Mamaki da tsoro ya sakashi ɗagawa ganin sunan Adnan.
Cikin ƙanƙanin lokaci dukkan ƴan gidan
suka gama taruwa sashen hajiya Iya dake cikin mawuyacin hali. Khalipha ne keta
ƙoƙarin bata taimakon gaggawa kasancewar ɗalibin likitanci dake gab da
kammalawa insha ALLAH. Da ƙyar ya samu yaɗan saita wasu abubuwa. sai dai ya
basu tabbacin dolene a wuce asibiti da ita tunda nan gida ba kayan aikine da
shi ba.
Suna idar da sallar asubahi ko Shira
Hospital suka wuce. A canne likitocin da sukai duty ɗin dare suka rufu kanta.
Yayinda AK kuma ya shiga bige-bigen waya na shirin wucewa da Hajiya Iya London
kamar yanda dama yaci buri tun da, sai dai tace bata zuwa Nigeria ma akwai
likitoci ƙwararru. A yanzun kam tunda bata a hayyacinta yaci alwashin sai ya
kaita insha ALLAH an duba wannan ciwon ƙafartata mai kama dana gado. Dan mafi
yawan ƴan family ɗinsu na ɓangaren mahaifiyarta duk sanadin ciwon ƙafa suke
barin duniya kamar dai Inno. Ga su duk ALLAH ya basu jikin ƙiba dama masha ALLAH............✍
*_Kuyi haƙuri naji kunata cewa bana bana yayinku naƙi muku
surprise. Wannan karon abin ya haɗa da wasu uzurorine wlhy. Amma insha ALLAH
zan baku mamaki indai pages ne, ina kuma sake baku haƙuri wannan karon akan
tafiyar hawainiyarmu ta Typing gaba ɗaya. Ku ɗauki hakan matsayin yau da gobe
sai ALLAH. Sannan wasunmu sunada lalurorin yau da kullum tattare da su, da kuma
uzirorin rayuwa da duk sukazo mana tamkar an saita. Mukammu bama jin daɗin
hakan, dan babban burinmu shine muga mun taru gaba ɗayanmu mun faranta muku
tamkar yanda kuka faranta mana kuma kuke zuwa kuna sayen buks ɗinmu a koda
yaushe. ZAFAFA TEAM na godiya gaba ɗayansu tare da fatan alkairi a gareku da
ban haƙuri. da babban albishirɗin ganin gyara daga garemu baki ɗaya insha
ALLAH_*
*_Masu karantawa a waje kuma dan ALLAH ku daure kuzo ku saya
naku copy ɗin da halalinku kuma ALLAH zai sakama kasuwancinku albarka ta inda
bakuyi zato ko tsammaniba insha ALLAHU. Dan duk wanda ya kare mutuncin wani da
fita haƙƙinsa kaima ALLAH zai fita naka ya kuma kare mutuncinka da izininsa._*
*Muna godiya da zaɓin zafafa a koda yaushe😍😍😘😍😋🤗🙏🏻*.
*_ZAFAFA BIYAR NEXT LEVEL sunzo da sabon salon da duk
ya zarta na baya_*
Dan haka masoya karku bari ayi tafiyar bana babu ku a ciki💃🏻💃🏻.
*_★ AL-ƘIBLA_*💘
_Na Safiyya Huguma_
*_★ MABUƊIN
ZUCIYA_*💖
_Hafsat Rano_
*_★ DALAAL_*💝
_Na Miss xoxo_
*_★ UBAYD MALEEK_*💓
_Na Mamu gee_
*_★ MAKAUNIYAR ƘADDARA_*💔
_Na Bilyn Abdull_
Lalai daga ji babu tambaya bana ma ZAFAFAN ku da turirinsu
suke tafe. Dan dagani kasan za'a ragargaza cakwakiya, soyayya. Tare da nishaɗi💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻.
Gasu duka akan farashi mai rahusar gaske.
Kamar haka👇🏻💃🏻
Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇
0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of
payment)👇👇
*_08085405215_*
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN
NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇
0903 234 5899
💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍
*_ALLAH ka gafartama Iyayenmu🙏🏻😭_*
*_TYPING📲_*
*_LIttafin nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH karki karanta
sai kin biya. Idan kuma kin saya, muna haɗaki da ALLAH karki fitar mana. Dan ALLAH
ku zama masu riƙon amana da adalci a garemu🙏🏻😢_*
*Page 27*
_______________________
*_WANI KAYA SAI AMALE💃🏻💃🏻💃🏻._*
*_INA MATA ƳAN
ƘWALISA MA'ABOTA SON KALOLIN GIRKE-GIRKEN ZAMANI. KU GARZAYO GA DAMA TA
SAMU A TAFIN HANNUNKU CIKIN SAUƘI💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻😋😋😋😋_*
Nigeria @ 61
COOKING COMPETITION!!!
from lavender
Catering ina masu son koyon girki ga dama zaku shiga gasarmu ta girki bayan
kunyi register damu akan 10k,wanda yazo
na 1zai shiga ajin mu free hade da wasu prize din na 2 da na 3 kuma zasu
bayar da rabin kudine da wasu prize suma
saura kuwa zasu ayi musu ragin 5% da
wasu prize wannan gasa zamu yita ranar lahadi ne 3/10/21 zamu rufe registration
na gasar ranar asabar.
Lavender catering school zamuyi practical class. zamuyi 30
dishes continental, snack & desserts, traditional dishes, drink. Fee din
40k phone number WhatsApp and call
09080299283 akwai discount na 5% ga
mutum uku farko wadanda sukai register aranakun independence 1/10/2021 to 3/10/2021 Nigeria @ 61
Shi class zamu fara on 14/10/21.
*_KU GARZAYO KAR ACI KASUWAR SAMA BABUKU, DAN NAMU BA IRIN
NASU BANE💃🏻💃🏻💃🏻😋😋_*
________________________
*Page 27*
...........Alhmdllh an samu daidaituwar jikin hajiya iya,
amma bawai tana a cikin hayyacinta yanda ya kamata baneba. Shiyyasa shima AK ya
kammala dukan shirinsa akan tafiyar da ita. A wannan karon Baffah baiyi
yunƙurin hanashiba. Sai ma taimaka masa da yay da wasu abubuwan kasancewar
tafiyar ta zama ta gaggawa.
Duk wanda ya kalla shirawa a
yinin yau yasan lallai an taɓa musu wani babban jigonsu, dan kowa idanu jajur.
Daga masu kukan zuci har masuyin na zahiri irinsu Zinneerah. Dan ita dasu
Bahijja haɗe kawuna sukai sukaita rusar uban kuka sai da Yah Haneef yayta
lallashinsu da ƙyar da nuna musu sumata addu'a sannan suka ɗan nutsu.
Haka suka kasance yau yini guda
a asibiti likitoci nata ƙoƙarin su, yayinda AK keta shigi da fici na ganin
sunbar Nigeria a yau insha ALLAH. Yau ko ƙwaƙwaran abinci babu wanda ya samu
yaci a cikinsu, sai ruwa da ƴan kame-kame. Salla kawai ke tashinsu.
Yah Adnan bai farga da babu matarsa a
asibitinba sai da zasu koma gida domin shiryawa. Ransa ya ɓaci matuƙa amma ya
daure ya shanye har suka isa gidan. Kamar yanda yay hasashe kuwa a gidan ya
isketa wai taji ciwo a ƙafa saboda turewar da Zinneerah tai mata da asuba, ga
kuma zazzaɓi tanaji. Duk da ya lura da yanda take alamar kuka ta zauna tasha
baibi takantaba ya hau shirya musu kaya da kansa batare daya mata bayaniba.
Yana gamawa kuma fiwowa yay zuwa ɗakin hajiya iya. Inda ya iske Zinneerah zaune
tanashan sabon kuka.
Tsaye yay kawai shiru yana kallonta
batare dayayi maganaba tsahon lokaci. ita kuma batasan da shigowar tasaba kanta
na a cikin ƙafafunta ne. Yaɗan furzar da huci da cije lip ɗinsa yana ƙarasa
takawa cikin ɗakin da ƙyau. Gyaran muryar daya saka Zinneerah ɗagowa yayi.
Kallon cikin ido sukaima juna sai kawai ta fashe masa da kuka. Idanunsa ya
lumshe yana ɗan kauda kansa gefe.
“Dan ALLAH Yayanmu kaje
dani duk inda zaku kaita”. Ta faɗa kukanta na kuma tsananta. Baice mata komaiba
ya nufi bathroom ɗin ɗakin dake gyare tsaf duk da yau babu wanda yabi takansa.
Ruwa mai ɗumi ya tara a botiki ya fito, inda ya barta anan ya isketa tana
cigaba da kukan nata. “Tashi kije kiyi wanka”. Ya faɗa yana nufar inda
littatafan hajiya iya suke na addini batare daya sake kallontaba.
Jin abinda yacene ya saka Zinneerah
miƙewa da saurinta duk zatonta ƙorafinta ya karɓune. Littatafan ya gama ɗauka
da wasu ƴan abubuwa na Hajiya Iyan yasa a ƙaramar jikka. a saman gado ya barta
ya fice domin zuwa shima yayi wankan.
Sauri-sauri Zinneerah tahau shiri bayan
fitowarta wanka kasancewar ba salla takeba. Tana gamawa ganin jikkar daya ajiye
akan gado itama ta jawo akwati tahau haɗa nata kayan. Tana tsaka da neman
wayarta da tun jiya bayan ta kira mmn sadiq bata sake ganin wayarba, har so tai
ta kirata yau ma ta sanar mata halin da ake ciki amma sai bataga wayarba.
Shigowar AK ɗakin da sallama ciki-ciki,
Baba Rahi biye da bayansa ɗauke da tire ya sata dakatawa da leƙe-leƙen neman
wayar da takeyi. Juyowa tai tana kallonsu, yanzu kam shima yayi wankan
dan yana sanyane cikin ƙananun kaya sai uban ƙamshinsa ke tashi dan yama danne
nata turaren data saka. Shiko kallo ɗaya yay mata ya ɗauke yana maidawa kan
akwatin data haɗa kaya. Baiyi maganaba sai zama da yay cikin sofa ya ɗora
ƙafa ɗaya kan ɗaya yana sauraren Baba Rahi dake lallaɓata ta zauna taci abinci.
“Baba Rahi na ƙoshi, ALLAH bana jin
yunwa”.
Manyan idanunsa da launinsu ya
canja gaba ɗaya a yunin yau ya ɗago ya zuba mata cike da gargaɗi, babu shiri ta
amshi kofin shayin da Baba Rahi ke miƙo mata tai ƙasa da kanta tana kaiwa baki
badan yana mata daɗi ba, dan bakintama ji take yana wani ɗaci-ɗaci. Ɗauke
idanun nasa yay ya jingina da kujerar yana mai lumshe su. Sai dai kuma yana
kallonta ta ƙasan idon.
Baba Rahi ce ta cigaba da
lallashinta har taɗanci abincin shima kaɗan ta ture idanunta cike da kwalla
tace ta ƙoshi, Batare da Baba Rahi tace komaiba tahau tattare kwanikan zata
fita da su ya dakatar da ita. “Baba barsu anan jeki abinki”.
Amsa masa Baba Rahi tai tana
maido tiren ta ajiye, Zinneerah kuwa kallon inda yake ta ɗanyi kamar zatai
magana sai kuma ta maida kanta ta duƙar. Shi kuma batare daya tashi koya buɗe
idanunba yace, “Tashi ki ɗauka maganinki da abincin kizo nan”.
Ita tama manta wai bata da
lafiyane. Shakkarsa yasata miƙewa ta ɗakko din tayi yanda yace batare data musa
bin umarninsa ba. Ɗagowa yay daga yanda yake a zaune ya buɗe abincin da kansa
ya sake tura mata gabanta. “Na baki 10minutes kawai ki cinyesa”. Daga haka ya
koma a yanda yake kamar ɗazun. Cika idanun Zinneerah sukai da ƙwalla. Taja
abincin gabanta tana ƙoƙarin haɗiye ƙwallar tata dan bataga wajen yin wargi ba.
ALLAH ma ya sota abincin ba wani mai yawan tsiya bane dan baba Rahi dama ta
santa bawani cin abincin take sosai ba. Sai da ta gama tasha maganin sannan ya
sauke ƙafarsa da gyara zamansa yana faɗin, “Zonan”.
Babu musu ta miƙe zuwa garesa. Sai dai
inda ya nuna matan ta zauna ne yasata jin shakku tatsaya tana duban gefen nasa.
Harar daya balla mata ce ta sata zaman babu shiri daga can ƙarshen kujerar duk
da tazarar ba wata mai tsaho bace a tsakaninsu.
Ƙasa tai da kanta tana wasa da
yatsun hannunta, ji take ba'a taɓa saka rayuwarta a takuraba irin ta yau ba,
dan kwarjininsa da ƙamshinsa gaba ɗaya sun sakata jin ɗakin ya musu kaɗan.
Shiko ko a jikainsa kallon hanunta da taketa faman cuɗawa a juna kawai yakeyi
cike da nazari. Mikuma ya tuna oho masa sai yay saurin kauda kansa. Kusan
mintuna uku suna a haka shiru kafin ya sake dubanta.
“Kikace zaki bimu?”.
Ya faɗa ciki-ciki idanunsa ƙyam akan fuskarta.
“Eh Yayanmu dan ALLAH”.
Ta bashi amsa itama murya na rawa. Kwarjininsa na
sake tsumata dan ta kasa ɗagowa ta dubesa. Tamkar bazai sake cewa komaiba sai
kuma yaɗan girgiza kansa. “Idan kin bimu karatunki fa? Ko kin jinginesa
kenan?”.
Idanunta da suka ciko da ruwan hawaye ta
ɗago a karo na farko ta kallesa, sai gasu a cikin nasa dan shima ita ɗin yake
kallo. Yanda ya tsatstsareta dasu ne ya tilastata maida nata ƙasa hawayen
cikinsu da batasan na miyeba na gangarowa. Sai dai tana danganta zubar tasu da
takurar da tayi na kasancewar su zaune a waje ɗaya yanda mafalkinta bai taɓa
kaiwaba.
Ya sake maimaita mata cewar, “Nace karatunki
fa idan kin bimu?”.
Muryarta na rawar kuka tace, “Yayanmu
nidai kaje dani dan ALLAH, idan na dawo naje makarantar, inason na kasance da
Granny kawai”.
“Saboda karatun baida muhimmanci
a wajenki ko?”.
Kasa cewa komai tayi a wannan gaɓar,
hakan ne ya sakashi sauke murya ƙasa da alamun lallashi a ciki yace, “Bazaki
bimu yanzuba, dan shi ilimi abune mai muhimmanci ga mai nemansa, adalci ɗaya
zan miki shine idan kunyi hutu zakizo ki ganta ok”.
Sharrr hawaye suka sake ɓalle mata. Ta ɗago
zatai magana ya miƙe abinsa yana faɗin, “Na gama magana ki tashi ki saka mata
kaya kala biyu a wancan jikkan dana ajiye, sai abubuwan da kika sani masu
muhimmanci da take amfani dasu yau da kullum. Wannan kayan naki da kika haɗa
kuma ki kaisu sashen Momie dan zaki koma da zama can wajenta”.
Daga haka ya fice abinsa ko
waiwayenta baiyiba duk da yaji kukan data fashe dashi. Kansa kawai ya girgiza
yana ƙara jinjina ƙuruciyarta da shagwaɓa a ransa.
Karo ya kusanci da Farah wadda ke
ƙoƙarin shigowa ɗakin alamar biyosa tayi, ya ɗan bita da kallon mamaki kamar
zaiyi magana sai kuma ya ɗauke kansa da raɓata ya wuce abinsa. Har tayi kamar
ta shiga ɗakin Hajiya iyar taga mi yayo a ciki tun ɗazun sai kuma ta fasa tabi
bayansa da sauri. Yana shiga ɗakin itama tana shigowa. Zama yay cikin kujera ya
hau haɗa shayin daya saka Baba Rahi dafa masa shima. Sai da ya kammala zai fara
sha sannan ya kalli Farah data zauna kusa da shi ta wani tsatstsaresa da
idanunta manya.
“K kina ganin abinda kikayi yau shine
dai-dai? Kowa yana asibiti ke kina gida kwance?”.
Cike da isarta tace, “Amma dai
kasan nima banda lafiya ne ai. Sannan wannan shegiyar yarinyar sanda ta shigo ɗakinan
ta ɗauka wayoyinka turenifa tayi a ƙasa amma ko waiwayena batayiba. Jiba kaga
yanda ƙafata ta kumbura”. Tai maganar tana nuna masa ƙafar da cigaba da faɗin,
“Wlhy yanda ta sani jin azabarnan itama sai na sakata taji wadda ta fita dan
saina karyata kafin nabar gidan nan”.
Ɗauke idanunsa yayi daga kan
ƙafar kamar baiji mita faɗaba. Duk da masifar data cigaba dayi akan Zinneerah ɗin
bai tanka mataba harya gama shan tea ɗinsa sannan ya miƙe. Hakan da yay ya ƙona
ran Farah, sai dai ganin ya ɗakko man zafi ya dawo ya zauna da kama ƙafar tata
ya ɗora a jikinsa ya sakata sauke ajiyar zuciya.
Duk da ya jita baice uffanba ya hau
shafa mata maganin a wajen yana ɗan dannawa kaɗan-kaɗan itako tana zuba shagwaɓa.
Sai da ya tabbatar maganin ya shigeta sannan ya ajiye ƙafar yana dubanta cikin
ido. “Yau zamu wuce”.
Mamaki ƙarara a fuskarta tace, “Ina?”.
Kansa tsaye yace, “London, Granny
zataga Doctor acan”.
Jitai kamar an daɓa mata mashi a ƙirji.
ta tattaro yawun takaici ta haɗiye muƙut tana dubansa, “Amma my Hero duk
likitocin ƙasarnan har sai an kwashi kamar Granny dake fama da jikin tsufa an
wahal da ita zuwa wani waje”.
“Ke kika kallesa a fuskar wahala.
mu neman sauƙi zamu insha ALLAH ”.
Harara ta zuba masa a kaikaice
zuciyarta nayi mata zafi, cikin ɗan rawan murya tace, “To sai dai kuje ni kasan
dai babu inda naje. Bazai yuwu na shigo ƙasarnan ba kuma ban ziyarci kowaba”.
Juyiwa yay ya kalleta cikin ido
fuska a tsuke ainun, cike da gargaɗi da barazanarsa yace, “Da zaki taho ai nan
aka turoki, dan haka iya nan ɗin zaki tsaya. Nan da awanni shida jirginmu zai
tashi”.
Yanda ya tsareta da idanun ya
hanata iya cewa ƙala, dan tasan mi wannan kallon nasa ke nufi a gareta. Dole ta
tsuke bakinta hawaye na rige-rigen sakko mata. Batare dayabi takantaba ya miƙe
ya fice dan yanason yin magana da Baffah.
Miƙewa tai a harmutse itama ganin ya
fice tana masifar bazata yarda hajiya iya ta bisuba. Dan babu yanda za'ai a
jajubar musu gayya a takurawa rayuwarsu. Khalipha ɗinma ta ɗauki alwashin
wannan karon bazai koma mata da zama a gidaba. Sai dai ya koma hostel kamar
yanda Mammah ta faɗa. Haka taita masifa tana kuka da neman wayar Mammah amma
taƙi shiga. daga ƙarshe sai auntynta ta samu ta kira sukaita masifar tare,
Auntyn ta ta katse wayar ta kirashi. Yana ganin kiran sanda yake tare da Baffah
yaƙi ya ɗaga dan yasan zancen dai bai wuce mai hali tayi halin nataba...........✍
★★★
*_ZAFAFA BIYAR NEXT LEVEL sunzo da sabon salon da duk
ya zarta na baya_*
Dan haka masoya karku bari ayi tafiyar bana babu ku a ciki💃🏻💃🏻.
*_★ AL-ƘIBLA_*💘
_Na Safiyya Huguma_
*_★ MABUƊIN
ZUCIYA_*💖
_Hafsat Rano_
*_★ DALAAL_*💝
_Na Miss xoxo_
*_★ UBAYD MALEEK_*💓
_Na Mamu gee_
*_★ MAKAUNIYAR ƘADDARA_*💔
_Na Bilyn Abdull_
Lalai daga ji babu tambaya bana ma ZAFAFAN ku da turirinsu
suke tafe. Dan dagani kasan za'a ragargaza cakwakiya, soyayya. Tare da nishaɗi💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻.
Gasu duka akan farashi mai rahusar gaske.
Kamar haka👇🏻💃🏻
Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇
0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of
payment)👇👇
*_08085405215_*
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN
NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇
0903 234 5899
💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍
*_ALLAH ka gafartama Iyayenmu🙏🏻😭_*
*_TYPING📲_*
*_LIttafin nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH karki karanta
sai kin biya. Idan kuma kin saya, muna haɗaki da ALLAH karki fitar mana. Dan
ALLAH ku zama masu riƙon amana da adalci a garemu🙏🏻😢_*
*Page 28*
___________________________
*MG’s SKIN CARE*
(With us, your skin is elegant..)
Are you guys looking for where to buy ur skincare
product @ mg's skincare is the best plug for you🤗
Do you wish to have that flawless skin that's free of all
skin prblm
Do you wnt to achieve that milky skin that turn heads
wherever you go😉
Try mg's product nd I assure you you'll never use any other
product except mg's product✅
Mg's will gv you the best out of all
With mg's product ur skin is 💯 clear,fresh,smooth nd
ur skin will absolutely glow all day💃
We have herbal whitening black soap now nd beauty set
available
Nd both the soap nd the beauty set is for all skin type
everyone can use it🤗
Just gv it a try now nd see wonders✅
Chat:08062991549
Call:08064532391
Soap price:3k
set:11k
Follow us on
Instagram@glow_with_mgs
Facebook:mg's skincare
Nd guess wht🦻
Duk Wanda zesiya Kaya daga yau Alhamis 30-9-21 zuwa
Nanda 5days that is ranar talata there will be 20% off discount a soap nd the
set😍so what are you guys waiting for hurry nd
grab urs💃 now is the time to glow🧖♀️
Pamper ur skin🦵
Shine like a bride 👰
be part of the glow team karkubari abaku lbr
Just chat 08062991549 to plc ur orders😘
Do not forget to follow us👆
Like nd comment pls dearies😘
Patronize us🙏
mg's always serve you the best✅❤️
KAYAN MG’s SKIN CARE, GANGARIYA NE, SAI AN GWADA AKAN SAN NA
KWARAI, KU GARZAYA KU SAYI NAKU KAYAN A KULI KALILAN DOMIN DAGA YAU TAFARA
BONANZA. IDAN ANJE ACE DAGA ZAFAFA NE, AKWAI RANGWAMEN KUDI SOSAI, KYAU,
INGANCI, RAHUSA.. SAI KAYAN MG’s SKIN CARE.
___________________________
*Page 28*
............Ƙarfe takwas da kwata dai-dai jirginsu ya tashi
zuwa ƙasar London. Farah nata ƙunci akan ita batai shirin komawaba yau. Sai dai
shi uban gayyar yasan haushinta bai wuce na tafiya da Hajiya iya ban. Har cikin
ransa mamakinta ke ƙara faɗaɗa a ransa. Yanaji kuma lokaci yayi dazai maidota
cikin hayyacinta akan danginsa.
Ita kanta Mammah wannan karon ya shirya
mata tsaf, dan yasan ba ƙaramin rikici zadu kwasaba akan wannan tahowa da
Hajiya iyan da yay, shiyyasama ko faɗa matai biyiba sai sun isa ta gansu. Ita
kanta Farah sai da suka isa airport hankalinta ya ƙara tashi.
Tun bayar wucewarsu zazzaɓi
mai zafi ya rufe Zinneerah. Ta kuma maƙale a sashen hajiya iya taƙi tafiya
wajen Momie da yace mata. Sai da su Meenal da suma suka gama shan nasu kukan
suka biyota sannan. Ganin halin da take ciki suka koma suka sanarma Momie. Da
kanta tazo har sashen hajiya iya ta lallaɓata da lallashinta sannan suka kashe
komai na sashen ta ɗauki duk abinda take buƙata na amfaninta da kuɗin da Yah
Adnan ya bata, dana Khalipha suka wuce. Sai dai fa wayarta ce sunsha nema
yanzun ma amma basu ganiba. Ta rasa inda ta jefata tun jiya da rana bayan tayi
waya da Mmn sadiq. Momie ce tace subar wayar da safe azo a sake dubawa tunda an
kira ma a kashe take. Haka ta haƙura suka tafi can sashen duk da dama ta saba
kwana wani lokacin.
Tun daga wannan ranar rayuwar Zinneerah ta koma
sashensu Jamal, tanajin daɗin zama da kowa dan babu mai tsangwamarta ko nuna
mata banbanci, sai ma wani al'amari mai ƙarfi dake neman saƙuwa tsakaninta da
Yah Moos'ab duk da har yanzu bai firta mata cewar yana sonta ba. Yabarma ransa
har sai ta kammala secondary kamar yanda yaci buri.
Amma sai kaf-kaf yake da
ita musamman da yaga tafiyar Granny ta sakata shiga wani hali. Itako tsaf ta
fahimci inda ya dosa amma take nuna masa bata gane komai, ɗaukarsa take kamar
sauran samarin gidan kawai, dan ita bata saka soyayya a lissafin rayuwarta duk
da tanajin Yah Khalipha a ranta shikam. Amma sai take ɗaukar hakan matsayin
ganin girmansa akan taimakon da yay mata wancan karon da bata da gata.
Kullum takanyi waya da Khaliphan
a wayar su Jamal, anan ne takejin cigaban da ake samu game da jikin hajiya iya
da Yayansu keta kashe kuɗi akan ganin ta samu lafiya. Bata taɓa waya da shi ba.
Sai dai duk santa ta buɗe akwati zata ɗauka abu takanci karo da kuɗin da ya
bata bandir guda na ɗari biyar, sai turarensa shima daya bata tare duk a ranar
da zasu tafin, duk da ko sau ɗaya bata taɓa shafashiba ya gauraye mata kayan
cikin akwatin da ƙamshinsa.
Sai da suka cika
sati uku cif da tafiya Zinneerah taji muryar Hajiya iya. ALLAH sarki zokaga
murna da farin ciki ita dasu Bahijja. Bama suba duk wanda yake a gidan ranar
saika fahimci yana a cikin farin ciki, dan duk sai da ta gaisa dasu. Kwana biyu
dayin haka kuma Baffah ya dawo daga can ya ƙara sanar musu da cigaban da aka
samu.
Hajiya iya na cikin sati na
bakwai a london su Zinneerah suka sami hutun makaranta. Kai tsaye ta sanarma
Momie tanason taje gida hutu, duk da tana waya dasu kullum ta wayar su Bahijja
dan ita dai tata wayar an rasa inda ta faɗa har yanzun, harma ta haƙura dan
tasu Meenal ma ta wadatar da ita tunda dama daga amsa waya da kiran su mama sai
games suke da wayoyin, sauko abinda ya shafi karatu idan ta kama. Yah Khalipha
kuma ya mata alƙawarin zuwa mata da wata idan zaizo.
Shiri Momie tai mata na zuwa gida
ita da Baffah duk da kuwa anan cikin garine. Ranar da suka cika kwana biyu da
samun hutu Moos'ab da kansa ya kaita gida tare dasu Jamal. Ganin little ɗinta
daya ƙara girma da ƙannenta da mama ya mantar da ita kewar su Bahijja da suka
wuce. Tuni suka shiga hira tana ƙara bama mama labarin yanda jikin hajiya iya
keta ƙara ƙyau. Amma Yayansu yace bazata dawoba sai bikin su Aunty Safiyya.
Mmn sadiq taji daɗi sosai, dan tana
ƙaunar hajiya iya da zuri'arta kodan karamcinta garesu. Sai dai kuma a wannan
karon ta shirya binciken Zinneerah akan samuwar little. Dan tun ganin AK datai
hankalinta bai sake kwanciya ba. Ita harma zargi take itama Hajiya Iya dalilin
little ɗinne ciwonta ya motsa.
Ba ƙaramin girgiza zukatansu Sakina
wannan zuwan ma Zinneerah tayiba. Dan su kansu sunsan ta wuce da ajinsu yanzun,
samarin anguwar kuwa da suka nuna suna sonta a baya suka dingi ɓata Zinneerah a
wajensu ganinta ya sake dawo dasu gareta. Sai dai taƙi bama kowa fiska dan
burinta bana aure bane yanzu karatu ne.
Tana kwana huɗu da zuwa sai ga Yah
Haneef da Yah Mas'ood sunzo wai zasu kaita ai mata passport inji yayansu. Bata
fahimci inda zancen ya dosaba amma saita shirya suka tafi harda Little da tun
zuwansu gidan suka janyesa. Shiko duk da rashin son mutanensa sai gashi ya saki
jiki dasu kamar yanda yayi randa su Jamal sukazo.
Wajaje sukaje kusan uku kuma duk
sun jima. basu dawoba sai yamma lis tare da siyayyar kayan ciye-ciye fal leda
da suka yima little. Bayan wucewarsu ne Mmn Sadiq dakema little shirin barci ta
duba Zinneerah ɗin.
“Niko nace dama tunkan kizo nan
kinsan wannan Yayan naku ne Zinneerah?”.
Zinneerah dake cin gyaɗa ta ɗago tana
kallon mama. “Mama wane Yayan a ciki?”.
Kai tsaye Mama tace “Adnan”.
Shiru Zinneerah tai tana kallon Mama na wani ƴan sakkani, a ranta tambayar na
bata mamaki. “Wai badake nake maganaba ne kika tsaya kallona?”.
Numfashi Zinneerah ta sauke dan
itama ta tafi wani tunani ne kuma daban. “Yi haƙuri Mama, tambayarce wlhy ban
ganeba”.
“Basai kin fahimceniba dama ai. Amsa
zaki bani”.
Da ƴar dariyarta tace, “A'a wlhy mama
ban sanshiba sai a wannan karon da yazo gidan, bamma taɓa ganinsa ba nikam. To
shi dama akace baya zuwa ma ƙasar a ina zan sanshi Mama?”.
Idanu Mmn sadiq ta zuba mata cike da
nazari, kamar zatayi magana sai kuma tai shiru ta barta kawai. “Tashi ki kai
Wannan ɗaki tunda barcin nasa yayi nisa”. Miƙewa tai ta ɗauka little da yay
barci tunkan su dawo, sai da maman zatai masa wanka ya farka. Ana gamawa kuma
ya sake komawa dan ya gaji matuƙa sunsha yawo.
Da kallo kawai mmn sadiq ta bita harta shige ɗauke
da little ɗin. Harga ALLAH ranta cike yake fal da fargabar abinda zuciyarta ke
ayyana mata a koda yaushe tun ganinta da Adnan ɗin. Shi kansa Abba data bashi
labari zancen ya girgizashi, har yau kuma sun kasa daina tattauna maganar a duk
sanda take tare da shi. Sai dai sun kasa fahimtar komai akan al'amarin sam. To
gashi wadda ma suke da hope ɗin samun wani bakin zare a gareta tace bama
tasanshiba itama. Duk da ta fahimci Zinneerah bata iya ƙarya ba wannan karon ta
gagara gaskatata akan batun rashin sanin Adnan.
Washe gari da taci burin sake zaunar da ita
akan batun sai ga Moos'ab wai yazo ɗaukarta dan zasu wuce da sassafe gobe idan
ALLAH ya kaimu wajen hajiya iya. A take farin ciki ya bayyana ga Zinneerah
tahau shiri, mmn sadiq kuma suka hau gaisuwa da Hajiya iya ta wayar Moos'ab ɗin
itama. Sai da suka gama wayarne ta miƙe ta shiga haɗama hajiya iya ƴar tsarabar
data san zataji daɗinta idan an kai mata. Cikin ƙan ƙanin lokaci Zinneerah ta
gama shirinta tsaf suka wuce bayan sunyi sallama da Abba ta waya duk da dama
jiya mama ta sanar masa fitar su Zinneerah ɗin, shine ya ɗanyi zargin ko wajen
hajiya iya zasuje dama. To amma baiyi tunanin tafiyar haka gab ba.
Tunda suka iso gidan suka
haɗu dasu Jamal suketa murnar tafiyar musamman ma ita da ko jirgin ƙasa bata taɓa
ganiba😹, dan su huɗu kawai zasuje ashe. Ita, Jamal,
Meenal, Bahijja. Anan ma koda ta dawo ba zaman sukaiba, fita suka sakeyi ita da
Moos'ab ta ƙarasa abinda ya rage mata tunda wannan ne karon farko da zata
ƙetare 9ja. Abinka da maganar kuɗi kuwa sai gashi a tsakanin fitarsu ta jiya
data yau ɗin komai ya kammala, tunda dama ƙasar tamu waka sani ya sanka akeyi.
Suna dawowa sashen hajiya iya taje ta ɗakko
abinda zata buƙata suka shirya kayansu tsaf duk da bawasu uban kaya suka ɗauka
ba. Gara itama ta haɗama Hajiya iya da saƙonta na wajen mama da kuma abinda
tace ta ɗakko mata.
________________★★
Abin mamaki yau sai ga Zinne ta
danya mai tallar riɗi da gyaɗa a airport za'a ƙasar burtaniya. Babu wani ɓoye-ɓoye
murnarta take nunawa a fili musamman da suka iso airport ɗin. Aiko su Jamal
suka tasata gaba da tsokana suna dariya. Ko'a jikinta dan iya gaskiyarta ta faɗa.
Bayan kammala tsarabe-tsaraben airport jirginsu ya ɗaga zuwa ƙasar burtaniya
zuciyar Zinneerah cike taf da tsoro lokacin da jirgi zai tashi. Dan sai da ta
ƙanƙame hannun Bahijja dake kusa da ita hanjin cikinta na wulƙitawa tamkar zata
amayosa ta baki. Sai da jirgin ya gama dai-daita a gajimare ta buɗe idanunta
tana sauke tagwayen ajiyar zuciya.
Tun Zinneerah na marmarin tafiyar
da ɗoki harta fara ƙosawa, dan bata da jimirin dogon zama dama ita. Lokacin da
jirgin ya samu kaiwa ga ƙasa jitai kamar tamafi kowa farin ciki tsabar gajiyar
datai da ƙaguwar son ganin Hajiya Iya. A wannan gaɓar ba itace kaɗai baƙauya ba
hatta dasu Jamal ɗin ƙauyawa suka koma. Dan shine karonsu na farko zuwa ƙasar
london.
A yayin sakkowar tasu Jamal ne
gaba. Ita a bayansa sai Bahijja da Meenal biye dasu. Kowanne yana jaye da
trolly ɗinsa ƙarami a hannu. A kallo guda dolene su birge ka musamman da suka
kasance a ganiyar shekarunsu na ƙuruciya..............✍
*_Masha ALLAH. Guys asha hutun weekend lfy ko😋😉😘😍😘😍🤗._*
*_ZAFAFA BIYAR NEXT LEVEL sunzo da sabon salon da duk
ya zarta na baya_*
Dan haka masoya karku bari ayi tafiyar bana babu ku a ciki💃🏻💃🏻.
*_★ AL-ƘIBLA_*💘
_Na Safiyya Huguma_
*_★ MABUƊIN
ZUCIYA_*💖
_Hafsat Rano_
*_★ DALAAL_*💝
_Na Miss xoxo_
*_★ UBAYD MALEEK_*💓
_Na Mamu gee_
*_★ MAKAUNIYAR ƘADDARA_*💔
_Na Bilyn Abdull_
Lalai daga ji babu tambaya bana ma ZAFAFAN ku da turirinsu
suke tafe. Dan dagani kasan za'a ragargaza cakwakiya, soyayya. Tare da nishaɗi💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻.
Gasu duka akan farashi mai rahusar gaske.
Kamar haka👇🏻💃🏻
Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇
0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of
payment)👇👇
*_08085405215_*
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN
NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇
0903 234 5899
💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍
*_ALLAH ka gafartama Iyayenmu🙏🏻😭_*
*_TYPING📲_*
*_LIttafin nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH karki karanta
sai kin biya. Idan kuma kin saya, muna haɗaki da ALLAH karki fitar mana. Dan
ALLAH ku zama masu riƙon amana da adalci a garemu🙏🏻😢_*
*Page 29*
_________________________
*MG’s SKIN CARE*
(With us, your skin is elegant..)
Are you guys looking for where to buy ur skincare
product @ mg's skincare is the best plug for you🤗
Do you wish to have that flawless skin that's free of all
skin prblm
Do you wnt to achieve that milky skin that turn heads
wherever you go😉
Try mg's product nd I assure you you'll never use any other
product except mg's product✅
Mg's will gv you the best out of all
With mg's product ur skin is 💯 clear,fresh,smooth nd
ur skin will absolutely glow all day💃
We have herbal whitening black soap now nd beauty set
available
Nd both the soap nd the beauty set is for all skin type
everyone can use it🤗
Just gv it a try now nd see wonders✅
Chat:08062991549
Call:08064532391
Soap price:3k
set:11k
Follow us on
Instagram@glow_with_mgs
Facebook:mg's skincare
Nd guess wht🦻
Duk Wanda zesiya Kaya daga yau Alhamis 30-9-21 zuwa
Nanda 5days that is ranar talata there will be 20% off discount a soap nd the
set😍so what are you guys waiting for hurry nd
grab urs💃 now is the time to glow🧖♀️
Pamper ur skin🦵
Shine like a bride 👰
be part of the glow team karkubari abaku lbr
Just chat 08062991549 to plc ur orders😘
Do not forget to follow us👆
Like nd comment pls dearies😘
Patronize us🙏
mg's always serve you the best✅❤️
KAYAN MG’s SKIN CARE, GANGARIYA NE, SAI AN GWADA AKAN SAN NA
KWARAI, KU GARZAYA KU SAYI NAKU KAYAN A KULI KALILAN DOMIN DAGA YAU TAFARA
BONANZA. IDAN ANJE ACE DAGA ZAFAFA NE, AKWAI RANGWAMEN KUDI SOSAI, KYAU,
INGANCI, RAHUSA.. SAI KAYAN MG’s SKIN CARE.
_________________________
*Page 29*
.............Meenal da ke ƙarshensu ce ALLAH ya bata ikon
hango Yah Khalipha. Cike da jin daɗi da zumuɗi tace, “Guys ga Yah Khalipha
can”.
Kusan duk a tare suka kalli inda ta nuna
ɗin, hakan yayi dai-dai da ɗagowar Khalipha ɗin kuwa shima idanunsa suka hango
masa su. A tare suka nufi juna cike da zumuɗi da farin ciki. Jamal ya shige jikinsa
suma su Bahijja haka. Hannu ya miƙama Zinneerah alamar tazo itama sai ta noƙe
kafaɗa tana murmushi. Sosai hakan da tai yay bala'in birgesa. Ya saki ƙannensa
yana nufowa inda take fuska ɗauke da murmushi.
“Uhm Gimbiyar mata ke ta dabance fa”.
A bazata kalmar tazoma Zinneerah daga
bakin nasa. Kamar yanda shima tazo masa a suɓutar baki. Ta ɗago manyan idanunta
cikin nasa tana wani warosu irin alamar dai mamaki. Kansa ya girgiza mata shima
yana waro nasa idanun dariyarsa na ƙara faɗaɗa. Babu shiri Zinneerah tai dariya
da saka tafin hannunta ta rufe fuskarta dan taji kunya kuma.
Su Jamal dake musu dariya suma
suka shiga gaishesa. Da kulawa ya amsa musu har ita Zinneerah data samu ta
gaishesa a ƙarshe. Daga haka suka nufi taxi suka shiga yana faɗin, “Kuyi haƙuri
fa nan kunsan ajiye mota ga talaka sai yayi nishi, motar gidan Yayanmu ya fita
wajen aiki da ita”.
Cikin rashin damuwa da
wannan suka shiga dariyar maganarsa. Sai ma suka koma tambayarsa Hajiya iya. A
take ya fara basu labarin tana nan suna zuba tsiya da Aunty Farah. Yana basu
labarin rikicin da akeyi a gidan suna kwasar dariya. Sai dai ko sau ɗaya
Zinneerah bata saka baki a hirar tasuba. Murmushi kawai takeyi tana dai
saurarensu da kallon hanya, zuciyarta na yaba ƙyawun ƙasar burtaniya da
tsarinta. Tare da godiya ga UBANGIJI da ya bata damar ƙetare ƙasarta zuwa wata
ƙasa batare da ko a mafarkinta hakan ya taɓa zuwa mata a cikin ranta ba.
Sai da suka iso inda ya dace ta
kawo numfashi, waje ne daya samu tsararrun gine-gine da burgewa ga mai kallo.
Babu wani hayaniya a wajen dan saima ka ɗauka ba gidaje baneba wata
ma'aikatace. Su kansu sai bayan shigarsu ainahin cikin estate ɗin suka fahimci
nannefa inda gidan Yayan nasu yake kenan. Sun haɗu da mutane ɗai-ɗai dake kai kawo,
kamar masu fita da masu shigowa. Duk da kasancewar ginin estate ɗin a dunƙule
yake waje ɗaya idan ka shiga baka da alaƙa dana kowanne, abinda kawai zakai
nufar hanyar da zata kaika ainahin number naka building ɗin. Abinda kuma zai
birgeka a rayuwar wajen babu ruwan wani da wani. Iyakarka da kowa hello hii
idan an gamu.
Zinneerah daketa tunani a ranta
taketa ayyana dolene turawannan su dinga ganinmu a banza. Dan duk wani jin daɗin
duniya tamkar an tattarashine garesu. Basusan wani tashin hankalin rayuwaba
sukam sam. A African kashe-kashen nan kawai ya ishi bawa da yunwa. Mu baga
neman lahirarba duniyar da mukeso kuma kullum cikin wahal damu take. Gamu nan
dai babu fasali ko wasu abubuwan birgewa duk mun fita a hayyacinmu.....
Nannauyan numfashi ta sauke saboda taɓatan da
Bahijja tayi, “Haba Baby ina kika tafi haka ne?”.
Ɗan murmushi Zinneerah tayi da duƙar da
kanta saboda kallon da Khalipha ya kafeta da shi. A hankali tajawo trolly ɗinta
ta fito a cikin taxi ɗin tana gyara bag ɗinta. Jamal sarkin tsokana yace, “Ashe
ni ƙauyancina ma kaɗanne ga wadda ta fini”.
Harara ta zuba masa da kai masa duka ya
goce yana dariya. Khalipha ya girgiza kansa yana nufar ƙofar da zata sadasu da
gidan na yayansu yana faɗin, “Uhm kudai tuna a ina kuke yanzun, kokuma ku koma
Nigeria ba'a yanda kuka zo Burtaniya ba”.
Dukansu sun fahimci inda zancen
nasa ya dosa. Dan haka duk sukai ƙaramar dariya kowa na faɗin albarkacin
bakinsa.
Tunda suka shigo man kan
kowa ya tsiyaye tas suka koma santin zuciya, sunaji a ransu dolene Aunty Farah
da take hura musu hanci ashe tasan abinda ta taka. A ɗan corridor ɗin kafin ka
shiga ainahin falon duk suka cire takalmansu suka saka cikin drawer dake a
wajen alamar ba'a buƙatar ganinsu a waje. Sabbin Slippers na zaman gida
Khalipha ya ciro daga cikin drawer ɗin ya miƙa musu. Kowa cira yay ya saka
sannan suka shigo ainahin falon daya tsaru harya gaji. Sai ka rantse ma ba'a
amfani dashi tsabar yanda yake fes. Tozali da Hajiya iya dake hakimce zaune ta
ƙara ƙyau ya mantar dasu a ina suke da kuma santin. Tuni suka yadda bags suka
nufeda da gudu cike da ihun farin ciki duk suka ɗaneta.
Itama dai cike da farin cikin ta tarbesu tana
dariya dajin ƙaunar ƴan jikokin nata da kewarsu.
Cikin ɓacin rai Farah ta fito
daga wani lungu danjin hayaniya na neman halaka mata kunnuwa, sanye take cikin
wando dogo da riga da sukai mata ƙyau ainun, taku take cike da isa da ƙasaita
fuska a yatsine. Taja ta tsaya turus tana dubansu alamar batama san da
zuwansuba, dan sosai mamakin ganin nasu ke bayyana mata kan fuska ƙuru-ƙuru.
Gashi kuma babu damar magana saboda hajiya iya. Sai dai wani kallon tsantsar
takaici takema Khalipha da shima kai tsaye ita ɗin yake duba.
Kamar zatayi magana sai kuma ta fasa ta
janye idanunta daga kansa ta maida kansu Meenal da sai a yanzu nasu idanun suka
ganta. Duk da sunsan halinta na wulaƙanci sai sukai ƙoƙarin nuna murnar ganinta
suna gaisheta cike da girmamawa kodan darajar wanda ya ajiyeta a gidan. A
yatsine ta amsa musu ɓacin ranta na kasa ɓoyuwa, ta kafe Zinneerah da ko kallon
inda take bataiba balle gaisheta da ido.
Zinneerah da
batasan tanaiba gaba ɗayama hankalinta nakan Hajiya iya batasan da zuwanta
wajenba. Lura da kallon da Farah kema Zinneerah ɗinne yasa Khalipha kiran sunanta.
Ta juyo fuskarta ɗauke da murmushin da takema
Hajiya iya ta dubesa. batare da yayi maganaba ya nuna mata Farah.
Da iya gaskiyarta tace, “Ayyah Aunty
kiyi haƙuri bansan kin fito bane. Mun sameku lafiya? Yaya jikin Granny”.
(Buhun bura uban nan kayyasa) Farah ta
ambata a zuciyarta tana kafe Zinneerah da wani shegen kallo, dan babu abinda ta
hango a zancenta sai tsantsar rainin wayo a gareta. Batare data amsama
Zinneerah ɗimba tabar wajen cike da takunta na ƙasaita da izza kai kace wata
sarauniya ce.
Gaba ɗayansu da kallo suka bita. Hajiya
iya ta girgiza kanta kawai tana mai nema mata shiriyar UBANGIJI a ranta.
Yayinda su Jamal duk jikinsu yayi sanyi. Zinneerah kam ko'a jikinta, dan itako
a masu mugun hali taga waɗanda suka taka Farah suka shanye mizaisa na Farah ya
dameta. A bazata dariya ta siɓicema Khalipha ya kauda kansa gefe yanayi. Dan
haka kawai ta bashi dariyar. Ita dake takaicin zamansa shi kaɗai ga wasu huɗun
nan an kuma kwaso mata bayan Hajiya Iya. Sai dai kuma shi duk zatonsa tasan da
zuwan nasune tun farko, amma a yanda tayi yanzu kam ya tabbatar Yayansu ya ɓallo
ruwa yau.
Hajiya iya ce tai masa daƙƙuwa,
ya ɗauke kansa yana haɗiye dariyar badan yaso ba. Itama maida hankalinta ta
sakeyi gasu Bahijja dake gaisheta da tambayar lafiyarta, itama tana tambayarsu
mutanen gida da hanya.
Sai da Khalipha yace, “Ashe
ƙaryar gajiya kukeyi daman”.
“Yah Khalipha ganin Granny yasa
gajiyarma ta gudu ALLAH”. Bahijja ta faɗa tana dariya. Murmushi yayi da kallon
Granny dake magana da Zinneerah fuskarta a washe itama alamar tana cikin farin
ciki yau fiye da kullum, sai yaji daɗi a ransa. Koba komai sa huta da mitarta
na a maidata gida ita ta gaji da zaman kurkuku.
“Assalamu alaikum”.
Suka tsinkayi muryar Yayansu dake ƙoƙarin
shigowa a bazata. A take duk sukai tsit da maida dubansu ga ƙofar. Khalipha ya
miƙe ya nufesa ganinsa ɗauke da ledoji a hannu. Suma ɗin duk tsaye suka miƙe
domin bashi girmamawa. Ledojin ya miƙama Khaliphan yana faɗin, “Thanks besty”
ba tare dasu sunji miya faɗa ɗinba. Sai motsawar laɓɓansa kawai suka hanga.
Cikin haɗa baki sukace “Barka da dawowa
yayanmu;
Sai yanzune ya kallesu fuskarsa da ɗan
sakewa amma ba murmushi yakeba. Ya zame rigar sanyin saman suit ɗinsa yana
hanging ɗinta a hanger ɗin dake gefensa, sannan ya ƙaraso cikin falon. Gaba ɗayansu
gani sukai ya ƙara musu ƙyau da cikar haiba a idanu, kamar yanda Hajiya Iya da
Yah Khalipha suka ƙara musu. Sai da yakai zaune ya harɗe ƙafa ɗaya kan ɗaya
sannan yay magana.
“Kun iso kenan?”.
Nanma a tare sukace, “Eh Yayanmu”.
Batare daya
kalli kowansuba ya jinjina kansa yana musu nuni dasu zauna. Babu musu suka
zauna suna gaisheshi da tambayar jikin Granny.
“Ta warke ai, tunda gashi tana
mana boren sai kunzo”.
Duk da ba cikin raha yay maganarba sai
da sukai ƴan ƙananun dariya suna gumtse bakuna. banda Zinneerah da tun
shigowarsa kanta ke a ƙasa murmushi yanzunma kawai tayi.
Granny dake hararsa tace, “Ai ni ba irin wasu
bane da basa son mutane. Na saba jina cikin hayaniya da karaɗin ƴan jikokina
ina jin daɗi”.
Karan farko ya saki lallausan murmushi
yana miƙewa da ɗan taɓe baki, duban Khalipha daya kai ledojin abincin kitchen
ya dawo yayi. “Besty ina zuwa”. Ya faɗa yana nufar hanyar da Farah ta fito ɗazun.
“A fito lafiya Yayanmu” Khalipha
ya faɗa yana wata shaƙiyyar dariyar tsokana ƙasa-ƙasa da kaiwa zaune. Hajiya
Iya data fahimci mi yakema dariyar tace, “Halan zargina ya zama gaskiya akan
ƴar tutsun tasa? Tunda yanzu dai ba lokacin dawowarsa gida bane ba”.
“Ai da alama itace tai
kiransa a waya ko kuma ta kira Mammah ita kuma ta kirashi, dan a yanda ta nuna
mamakin ganin su Jamal na tabbata bai sanar mata zuwan nasuba. Kinsan wannan
jikan naki shine dai-dai dasu ai, ya manna musu rashin m ya noƙe da barinsu
suyita masifa”. Khalipha ya bata amsa magana ƙasa-ƙasa kamar wani munafiki yana
ɗan dariyar ƙeta.
Dariya Hajiya iya tayi itama, “Kaɗanma
ta gani indai nice Amina, ita Hindatun idan ta isa tazo gidan mana ta sameni
ja'ira kawai. Nima nan saina saitasu a layi da ƙyau ai kafin nabar wannan garin
da ba daɗin zamane da shiba”.
Sudai su Zinneerah da ba sanin ina
zancen ya dosaba saurarensu kawai sukeyi, ita babban burintama azo a basu
masauki ta kwanta dan kanta ciwo yake mata.
Shiko Khalipha dariyarsa ya
cigaba da sha dan show ɗin na Granny na birgesa. Sosai a zaman nan nata take
ƙara cusama Yayansu son ƴan uwansa a ransa da sanin muhimmancin su da girman
zuminci. Shiko da alama yana haddace karatunta tsaf kuma yana aiki dashi. Dan
rana ɗaya babu zato ya sanar masa ya kira cikinsu Haneef akan tahowarsu Meenal
nan ɗin. Bashi ba hatta Granny tayi mamaki dan duk tsogumin da take masa nason
zuwan su Zinneerah ɗin batai zaton zai saka suzo ɗinba. Aiko ranar yasha addu'a
a wajenta da albarka.
To yanzu dai gasu sunzo, shi dai yasan akwai
ƙura akan wannan zuwa nasu gidan, musamman daya kasance uwargida gimbiya Farah
batasan da maganar zuwan ba, amma bara su zuba ido suga yanda wasan zai kasance
dai, tunda shima yayan nasu ba kanwar lasa baneba.............✍
*_Masha ALLAH Guys, ina fatan asha hutun weekend lfy ko😋😉😘😍😘😍🤗._*
*_ZAFAFA BIYAR NEXT LEVEL sunzo da sabon salon da duk
ya zarta na baya_*
Dan haka masoya karku bari ayi tafiyar bana babu ku a ciki💃🏻💃🏻.
*_★ AL-ƘIBLA_*💘
_Na Safiyya Huguma_
*_★ MABUƊIN
ZUCIYA_*💖
_Hafsat Rano_
*_★ DALAAL_*💝
_Na Miss xoxo_
*_★ UBAYD MALEEK_*💓
_Na Mamu gee_
*_★ MAKAUNIYAR ƘADDARA_*💔
_Na Bilyn Abdull_
Lalai daga ji babu tambaya bana ma ZAFAFAN ku da turirinsu
suke tafe. Dan dagani kasan za'a ragargaza cakwakiya, soyayya. Tare da nishaɗi💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻.
Gasu duka akan farashi mai rahusar gaske.
Kamar haka👇🏻💃🏻
Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇
0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of
payment)👇👇
*_08085405215_*
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN
NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇
0903 234 5899
💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍
*_ALLAH ka gafartama Iyayenmu🙏🏻😭_*
*_TYPING📲_*
*_LIttafin nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH karki karanta
sai kin biya. Idan kuma kin saya, muna haɗaki da ALLAH karki fitar mana. Dan
ALLAH ku zama masu riƙon amana da adalci a garemu🙏🏻😢_*
*Page 30*
________________________
*MG’s SKIN CARE*
(With us, your skin is elegant..)
Are you guys looking for where to buy ur skincare
product @ mg's skincare is the best plug for you🤗
Do you wish to have that flawless skin that's free of all
skin prblm
Do you wnt to achieve that milky skin that turn heads
wherever you go😉
Try mg's product nd I assure you you'll never use any other
product except mg's product✅
Mg's will gv you the best out of all
With mg's product ur skin is 💯 clear,fresh,smooth nd
ur skin will absolutely glow all day💃
We have herbal whitening black soap now nd beauty set
available
Nd both the soap nd the beauty set is for all skin type
everyone can use it🤗
Just gv it a try now nd see wonders✅
Chat:08062991549
Call:08064532391
Soap price:3k
set:11k
Follow us on
Instagram@glow_with_mgs
Facebook:mg's skincare
Nd guess wht🦻
Duk Wanda zesiya Kaya daga yau Alhamis 30-9-21 zuwa
Nanda 5days that is ranar talata there will be 20% off discount a soap nd the
set😍so what are you guys waiting for hurry nd
grab urs💃 now is the time to glow🧖♀️
Pamper ur skin🦵
Shine like a bride 👰
be part of the glow team karkubari abaku lbr
Just chat 08062991549 to plc ur orders😘
Do not forget to follow us👆
Like nd comment pls dearies😘
Patronize us🙏
mg's always serve you the best✅❤️
KAYAN MG’s SKIN CARE, GANGARIYA NE, SAI AN GWADA AKAN SAN NA
KWARAI, KU GARZAYA KU SAYI NAKU KAYAN A KULI KALILAN DOMIN DAGA YAU TAFARA
BONANZA. IDAN ANJE ACE DAGA ZAFAFA NE, AKWAI RANGWAMEN KUDI SOSAI, KYAU,
INGANCI, RAHUSA.. SAI KAYAN MG’s SKIN CARE.
__________________________
*Page 30*
............Tunda ya turo ƙofar tsararren bedroom ɗin ya
shigo da shashshekar kukanta ya faracin karo cikin kunnuwansa. Batare da damuwa
da rashin amsa sallamarsa ba ya ƙaraso cikin ɗakin yana kallonta.
Zama yay a kujerar dake ɗakin tamkar
bai damu da kukan nataba, a dakile yace, “Kinsa an tasoni daga office, gani to,
mike faruwa?”.
A fusace Farah da ke a kwance tana kukan
ta tashi duk da tun farko tasan da shigowar tasa dama. Hawayenta ta share tana
kallonsa, sai dai yanda ya tsatstsare ta da idanunsa dake rikitata yasa ta
janye nata danta samu damar faɗar abinda ke a bakinta.
“Babu abindama bai faruba. Ni wlhy bazan
iyaba, tayaya wannan gidan zai ɗauki wannan gayyar dan ALLAH? Hidimar nawa
zasuci ta kuɗaɗe tun daga kan abinci, ruwa da wasu wahalhalunsu?. Kawai sai dai
muga yara batare da an sanar mana ba daga ni har kai. Ita bata tunani zamanta
ma a takure muke bare tasa an ƙaro mana wannan yaran harda mara kunyar
yarinyarnan data kusa min sanadin karayar ƙugu. Ko an faɗa musu rayuwar Nigeria
da babu tsari da tanan iri ɗaya ce? Nasan duk Khalipha ne munafukin nan dan dashi
zata haɗa bak......”
“K ya isa haka malama!!”.
Ya faɗa a kausashe cike da nutsuwarsa. Dan inma baka saniba
sai kace ba shine yay maganarba. Babu shiri Farah tai baya dan firgita tana
kallonsa dan ya fito mata a zakinsa. Ya tsatstsare ta da birkitattun idanunsa
yana nunata da ɗan yatsa. “Farah! Farah! Wlhy daga yau, daga yanzu, bakinki ya
ƙara kuskure akan Granny saina zubar miki da haƙora a wannan gidan. Da kike
cewa ta takura miki, mizai hana bazaki tafi inda zaki shaƙata ɗinba ke?. Ki
kiyayeni Farah, ina ɗaga miki ƙafane kawai saboda ra'ayina badan kai ƙarata da
kikeyi wajen mahaifiyata ba. Yara kuma nine na kawosu, idan kin isa dan ALLAH
ki maidasu Nigeria yau ɗin nan stupid kawai”. Ya ƙare maganar yana karkaɗa mata
yatsansa alamar gargaɗi na ƙarshe ya mike ya shiga toilet.
Da wani banzan kallo ta bisa, ji
take tamkar ƙirjinta zai buɗe dan tsananin zafin da takeji na cika mata gida da
akayi. Ta tsani takura a rayuwarta. Dama Mammah ta faɗa, zuwan Khalipha tamkar
buɗe hanyar banbarowar danginsa ne garesa, dan sun sami ƙofar da suka kasa samu
tuni. To ita kam sai dai ayi duk ma abinda za'ai waɗanan yaran bazasu zauna a
gidan nanba, kai itama makirar tsohuwarnan mai ƙulla komai saita tafi.........
Fitowarsa ta katse
tunaninta. Tasa hannu ta share hawayenta tana dubansa duk da kallon fuskar tasa
kawai tsoro take bata ma. Zatai magana ya katseta dan yasanta da shegen naci da
mita akan abu, “Ki kwaso duk kayanki na ɗakincan tunda ba amfani kike da
shi ba su zauna. Jamal ya zauna wajen Khalipha”.
A zabure ta miƙe tsaye tana dubansa
hawaye na rige-rigen sakko mata. “Haba Yah Abdul-Mutallab, ɗakin nawa zan
basu?”.
“Zama ɗakin kikeyi ne?”.
“To amma dan ALLAH kodai bana zama a ciki ai dai sunansa ɗakina.
Suje ɗakin Granny su zauna mana”.
Wani banzan kallo ya mata idanunsa na
sake canja kala. “Wlhy Farah idan kikace zaki bani ciwon kai akan zuwan
yarannan tabbas zan baki ciwon zuciya ni kuma. Garama tun muna mu biyu kije ki
kwaso abinda yake naki a can ki basu ɗakin, idan kuma kinƙi zakisha mamakina
dan ina nan Abdul-Mutallab ɗin ɗin da kika sani”. Yana gama faɗa ya fice
abinsa.
Khalipha kawai ya samu a
falon, Granny taja su Zinneerah zuwa ɗakinta. Jamal kuma Khalipha ya kaisa nasa
ɗakin. Duk ƙoƙarin ɓoye fushinsa da yake sai da Khalipha ya gane. Har cikin
ransa baiji daɗiba. Shiyyasa yaso Yayan nasu ya haƙura da batun zuwan yaran
tunda ba dole bane. Dan yasan Farah ba zataso suzo ɗinba. Tunda shima a yaya
yake zaune gidan ma. Ita kanta Granny ɗan hali Farah ke nuna mata duk da
tsufanta.....
“Ina suke?”.
Ya katse Khalipha muryarsa cike da ɗaci. Cike da son kauda
masa damuwarsa Khalipha ya miƙe yana dariya. “Ai Yayanmu kasan waɗanan yaran
ƴan gatan Granny ne. Ta jasu ɗaki wai suyi wanka da barci. Shima Jamal yana wajena”.
Goshinsa yaɗan murza da furzar da huci
yana lumshe ido. Batare da ya samu yanda yake so na daidaiton muryar tasaba ya
nufi ɗakin yana cewa, “Taya zasu zauna a wannan ɗakin harsu huɗu zasu takura
mata ai”.
Bin bayansa Khalipha yay yana
magana cike da lallashi. “Yayanmu daka barsu isarsu zaiyi ALLAH, kaga munma
huta da mitar Granny akan kaɗaici ko”.
“Bazai yuwuba Khalipha ɗakin
Farah zasu koma”.
Dama abinda Khalipha kema gudun kenan.
Ya ƙara buɗe baki zaiyi magana a dai-dai isowarsu ƙofar ɗakin AK ya ɗaga masa
hannu alamar ya isa. Kai Khalipha ya dafe dan harga ALLAH baya buƙatar wata
fitina akan zuwan yaran nan tsakanin yayan nasu da matarsa. Idan ta gaskiya
za'abi sune da laifi, gashi kuma dama ba'a sanar mata ba tun farko. To amma
yasan halin Yayan nasu tunda yace haka za'ayi dole a yarda ayi hakan”.
Daga can Granny
tace, “Khalipha shigo mana”. Dan batai zaton AK ɗin baneba. Batare daya nuna
shi ɗin baneba kuma ya murɗa ƙofar ya shiga da sallama ciki-ciki. Akan
Zinneerah data fara wanka harta kwanta ya fara sauke idanunsa. Ya janye yana
maidawa ga Granny dake gyarama Meenal kwalar riga. Bahijja kuma na toilet tana
wanka.
“A'a wai dama baka komaba?”.
Hajiya iya ta faɗa idanunta akan AK. Kansa kawai ya kaɗa
mata yana kaiwa zaune. “Yanzu zan koma Granny, akan waɗannan dama na shigo, su
koma can ɗakin ba'anan zasu zauna ba”.
Shiru tai tana kallonsa cike da
nazari, sai kuma ta saki murmushi tana girgiza kanta. “Moddibo bazai yuwuba. Ka
barsu anan muyi zamanmu zai ishemu”.
A karon farko ya kalleta shima.
Ta kaɗa masa kanta da iya gaskiyarta tace, “Idan akai hakan ba'a ƙyautaba
Moddibo. Inda itace taso su zauna mata a ɗaki dan kanta hakan ba damuwa bane.
Amma ko nice miji yayma ƙarfa-ƙarfa akan danginsa su zauna min ɗaki zanga kamar
an ƙasƙantar da nine. Ka barsu kawai suyi zamansu nan zai ishemu duka zaman
kwana nawane ma”.
Bai iya yace mata komaiba, sai idanunsa
dake ƙara canja launi ɓacin ransa na bayyana a fili, miƙewa yay a hankali
batare da ya sake kallon kowansuba yace, “Saina dawo”. Daga haka ya fice yabar ɗakin..
Da ga hajiya iya har Khalipha da su
Meenal da kallo suka bisa suma damuwa fal ransu. Suna son Yayansu dan shima
yana son su. Ko rashin sakewarsa a garesu kowa yasan wannan halinsane da kuma
yanayin rayuwar daya tashi a hannun Mahaifiyarsa. Amma sunsan badan ƙuntatawa a
garesu yake musu hakaba.
Afusace Meenal tace, “Wlhy na
tsani matarnan, danma taga ta samu Yayanmu mai haƙuri dajin maganar iyayensa shiyyasa
takema mutane wani iskancin”.
“Barta hankali zamu koyama shegiya ai a
wannan karon, tunda ta yarda mukazo gidan nan wlhy tayi gamo da gamonta kuwa”.
Cewar Bahijja itama muryarta har zuga take.
Rai ɓace Hajiya iya ta kallesu tana musu
daƙƙuwa. “Duk kunci iyayenku, ina ruwanku a cikin wannan zancen? Kunsan ALLAH
duk wanda ya aikata wani abu a gidannan saina ɓata masa rai kuma ya koma gida.
Ina kuma sake gargaɗinku shiga abinda ba'a sakakuba. Wannan ma ai rainine.
Koyaya take ai matar Yayankuce taci albarkacinsa a wajenku marasa kunya”.
Duk ƙasa sukai da kawunansu alamar
nadama. Dan dama sunsan wannan ba tarbiyyarsu bace. Hasalima Hajiya iya bata
yarda da irin wannan maganar a gabansu, yau ma dai akasi aka samu. Haƙuri suka
bata. Shima Khalipha ya ƙara musu faɗa sannan yace suzo suci abinci shima zai
wuce school ne.
Duk wannan abin da sukeyi Zinneerah
najinsu sarai, amma tai shiru kamar barci takeyi. da Khalipha ma yace a tadata
taje cin abincin Hajiya iya hanawa tai. Catai su barta idan ta tashi sai taci
nata tunda ta riga tayi barci.
A ɓangaren AK kuwa koda ya fito daga ɗakin
hajiya iya ɗakinsa ya sake komawa. Zaune ya tarar da Farah da waya a hannu
kamar ba ita ta gama kukaba yanzun. Ko'a jikinsa dan ya shirya mata tsaf, ya
kuma san Mammah bazatazo gidanba dan yunda Hajiya Iya ta dawo daga asibiti taƙi
zuwa, dama kuma ko asibitin bataje ta dubataba. Yanzu hakama tana China batare
da sanin Farah ɗin ba, dan shekaran jiya ta wuce da daddare.
“Ki tashi ki tattara komanki
dake a ɗakin nan ki maidashi ɗakinki. Karna dawo na taddaki anan ko wani abu
naki”. Daga haka ya juya ya fice abinsa bai jira cewartaba.
Fuskarta bayyane da tsantsar
mamakinsa ta bisa da kallo. Yana fita ta miƙe a fusace dayin wurgi da wayar
hannunta. ‘Ni zaka wulaƙanta akan waɗanan banzayen ƴan uwan naka
Abdul-Mutallab? Saboda nace bazasu zaunamin ɗakiba kaima zakace na bar maka ɗakinka
bayan kasan nafi son zama a cikinsa. Na rantse da ALLAH sai yaran nan da
tsohuwarnan sunbar gidannan zan baka mamaki kai dasu. Bazan sake zubar da
hawayena akansu a banzaba mu zuba mu gani’.
Yanda take surutai ita kaɗai a kuma
matuƙar fusace sai ta baka dariya. Ta koma tamkar wata zararriya. Sanin halinsa
yasa bata ƙetare maganarsaba ta shiga tattare duk wani abu nata tana saka mai
aikinta tana kaiwa ɗakinta. Sai dai kuma alwashin ƙuntata su Hajiya iya a gidan
tacisa yafi sau shurin masaƙi.
Bayan ta gama tattare
komai nata tsaf ta saka mai aikin nata sake gyara masa sannan ta jawo masa ɗakin
ta rufo harda saka key.
Su dai duk
wannan abu dake faruwa su Hajiya iya basu saniba suna ɗaki abinsu tana hira da
jikokinta. Abincin ma anan sukaci kusa da ita har Jamal da yana gama kimtsawa
ya tafi can. Shiko Khalipha ya wuce school kamar yanda ya faɗa.
________________★
*_DANYA_*
Su inna sun kai Karima asibitin kusada.
Likitocin nata faɗa ganin yanda jikinta ko ina sayin duka ga tsohon ciki da a
yau ma yaketa nuna alamun zai fito duniya. Dan tunkan su wuce ashe naƙuda take
shiyyasa jikin nata ya nema rikicewa.
Ɗakin haihuwa suka kaita dan
shine yafi cancanta da ita a wannan halin. Daga haka suka shiga bata taimakon
gaggawa. Suka bar su Inna a waje da zaman jigum-jigum. Tun suna zuba idanun
jiran kukan jariri da wuri har al'amarin ya fara fin ƙarfinsu. Dan ihun Karima
kawai suke jiyowa babu na jariri. A haka suka cinye wannan yinin suka shiga
marece. mahaifiyar Babawo sai kiransa take a waya yaƙi ɗauka. dan tunda ta
sanar masa abinda ke faruwa kafin su baro Danya bai sake yarda ya ɗaga mata
wayaba. Dole sai ƙaninsa keta kaiwa da kawo akan komai har ALLAH ya sauki
Karima wajen ƙarfe goma na dare.
Tsabar wahalar data sha daga ita har
jaririyar sun fita hayyacinsu ko kukan kirki batayiba. Koda aka buƙaci kayan
haihuwa babu abinda sukazo dashi asibitin. Aiko Nurse ta balbalesu da masifa
dan haushi. Inna ta miƙe itama a fusace tana danƙarama Nurse zagi abu ya nema
zame musu faɗa sai da aka lallashi Nurse ɗin da ƙyar. Dan sun fahimci Inna ma
ba kanwar lasa baceba.
Wannan abin daya faru yasa gari na
wayewa aka basu sallama suka dawo gida duk da Karima na buƙatar zama ƙarƙashin
kulawar likita. To amma jarabar Inna bazaisa su iya cigaba da kulawa da Karima ɗin
cikin kwanciyar hankaliba dan haka suka sallamesu..........✍