A RUBUCE TAKE (K'addarata) book 2 page 12

A RUBUCE TAKE (K'addarata) book 2 page 12

 

A RUBUCE TAKE (K'addarata) book 2 page 12

*H U G U M A*

*Arewabooks:Huguma*

*_A RUBUCE TAKE_*

       (K'addarata)

          Part 02

Page 12

           Sam ya manta da batun dauko hafsat daga wajen saloon,yana biye da widad din suna gyara parlor zuwa kitchen wadanda sukayi mugun kewarta,don duk gyaran da hafsat din zatayi bayayin kamar na widad,ya rasa meye dalili.

           Tayi masa kira ya kusa guda bakwai,ta cika tayi fam,cikin ranta tanata fadin inda waccar sadakar yallan yakai ai bazai manta ba,tilas ta tare musu drop na keke napep ta kawosu gidan.

           Dai dai sanda suke kitchen shi da ita,yau jin kansa yake fes,bai gane nauyin yadda yayi rashinta ba sai yanzu data dawo da kulawarta a kansa,ko cikin kitchen dinma taso ya zauna falo ne,amma sai ya kalleta sosai yana saka qwayar idanunsa cikin nata

"Bazan iya ba.....kinsan yadda nayi missing kallon kyakkyawar fuskar nan?" Ya qarashe maganar yana shafar gefan fuskarta,inda wani kwnataccen baqin gashi mai sulbi ya mamaye wajen,sai murmushi ya subuce mata,ita da Allahnta ne kawai sukasan yadda ta dinga kokawa da zuciyarta a kansa,bata sake sanin yadda ya samu gurbi cikin rayuwarta ba sai a yanzu data sake riqeshi da muhimmanci......sai da su hajiya fanna suke ankarar da ita game da muhimmancin kula da mallakar hankalinsa ta kyakkyawar hanya irin wannan da take kai yanzu.

         Kusan tare suke aikin,yaqi ya zauna,saidai gaba daya a rikice yake,yayi yayi tabar aikin yau zaima kowa takeaway amma tace dashi cikin narkewa da karyar da wuya a shagwabe

"Dole nayi belin kaina na biya bashin abincin da ban ciyar da kai ba" sosai maganarta ta burgeshi,ta kuma samu kyakkyawan gurbi a zuciyarsa,ya sakar mata wani tattausan murmushi,yana jin kamar ya bude qirjinsa ya maidata ciki,bai taba tunani akwai so mai zafi irin wannan ba.

         Dan qaramin ihu ta saki tana yarfe hannu,ya watsar da lettuce din hannunsa da yake gyarawa ya nufota, hannun ya kama yana m

"Tai miki ciwo?" Saita zame hannun a hankali

"Ba sosai bane,na tsorata ne" ta fada a shagwabe,kai ya girgiza

"No,ban yarda ba gaskiya.....ajjiye muje,na yafe girkin yau" maqale kafada tayi

"Su mimi fa?"

"Kowa zai qoshi,baki da damuwa" kafin ta ankara ya sanya hannu ya dauketa cak da hannu biyu

"Wai wai wai......kilo dinki nawa baby?.....wait......waima......how many months baby na yake yanzu?" Ya tsaya cak yayi maganar cikin rada.

        Duk sanda zai mata maganar cikin sai kunya ta kamata,musamman idan ta tuna wautar data tafka,da irin wayon daya dinga mata a sannan na cewa sai ansha ruwa an qoshi ake samun ciki.

          Kanta ta boye a faffadan qirjinsa tana dariya qasa qasa

"Bazan gaya maka ba,nima saina rama" dariya suka saki gaba daya a tare sanda suke shigowa parlor din,hakan yayi dai dai da shigowar hafsat ita da yara gaba daya.

         Mutuwar tsaye tayi,ta tsaya cak tana kallonsu,sanda ya zaunar da ita saman kujera one sitter ya tsugunna gabanta kan gwiwoyinsa hadi da dora kansa saman cinyarta bayan ya kama hannunta yana sake dubawa......sai taji gaba daya kamar rufin sama ne zai rufto a kanta,jakar hannunta data saka pampers na nawwara da sauran tarkace ta silale daga hannunta ta fadi,ta bada dan sauti abinda yaja hankalinsu kenan.

          Da sauri ya miqe yana nufarta hadi da fadin

"Subhanallahi" sai yasa hannunsa ya kama kunnuwansa ya riqe duka biyun yana kuma fadin

"Am so sorry......nayi laifi ko?,bansan za'a gama muku da wuri haka ba,me yasa baki kirani ba?" 

"Wanne irin nau'in kira kakeso nayi maka abbas?, miscall nawa kake buqata daga gareni kafin ka amsa wayata?" Ta jefa masa tambayar tana kallonsa da idanunta da suka fara zubar da ruwan hawaye,tanajin wani zafi a qirjinta kamar zuciyarta zatayi bindiga.

          Goshinsa ya dafe,shaf ya manta wayar na a silent

"Ya salam.....i forget to......."

"To what?!,kada kacemin komai,don babu abinda zaka gayamin da zai sakani yarda da kai,kawai ka shirya cimin mutunci ne,oho.....dama shi yasa ka turani gyaran gashi ni da yara don ka samu kebewa da matarka?,me yasa baka gayamin ba?,ai da ban dawo yanzu ba bare naga cin amanar da kuke aikatamin"

"Cin amana kuma?" Widad ta fada cike da zallar mamaki, saboda nauyi da kalmar tayi mata,me yasa hafsat din take abu kamar kwancan hauka?, uncle abbas din kwartonta ne ko kuwa?,ita bataga dukka abinda yake faruwa a gidan ba,oh.....hala ma dadi abun ya mata kenan?,shi yasa a jiya fanna keta mata fada kan matakin da ta dauka,tace sam baiyi ba,zata sake nesanta kanta da mijinta ne hadi da kawo kusanci tsakaninsa da hafsat din,ta gani,ta gani kam

"Ke ba dake nake ba,kiyimin shuru tun ban cimmaki na lallasaki ba" wani murmushi widad din ta sake,hankali kwance ta girgiza kai

"Wuce nan......wuce nan wallahi,me jiya ma tayi ballantana yau?" 

"Ya isa....ya isa" abbas ya tsaidasu yana daga hannunsa,hafsat dake kallon widad kamar wata sakarya cike da madaukakin mamaki yadda yarinyar ke kallonta kanta tsaye,ba alamun tsoro ko shayi a tattare da ita,ta dauke dubanta daga kan widad ta mayar kan abbas

"Kaga abinda ka jawomin ko a wajen diyar cikina?.....shikenan b......burinka......yac.....cika" tana kaiwa qarshe kuka ya kubce mata,sai tayi dakinta da gudu gudu ba tare data dauke jakarta a wajen ba.

              Kafin wani a cikinsu ya sake cewa komai mimi da nawwara suka shigo da gudunsu hannuwansu dauke da leda babba

"Daddy.....kaga abinda abban kaduna ya bamu,yanata sallama bakaji ba,yace zai dawo anjima" idanunsa dauke dauke da damuwa da bacin rai ya bude yana kallon yaran,abban kaduna amini ne ga mahaifinsa,kuma shine a yanzu ya bashi part daya cikin gidan suke zaune,saboda yana kallonsa tamkar dan cikinsa.

          "Me aka samo mana" widad ta fada cikin qoqarin kawo raha da kawar da bacin ran data fuskanci ya taba zuciyarsa,ta karba ledar ta bude tana biyewa yaran tare da sako abbas din a ciki.

         Cikin mintuna qalilan tayi nasarar kore masa bacin ransa,shima ya zauna cikinsu ana rabon kayan wasan yara fal leda da chocolates masu yawa daya kawo musu,sai da aka kusa kiran sallah sannan ya nufi daki yace zai daura alwala,su shirya idan ya dawo zasu fita yayi musu takeaway.

          Murna yaran suka hauyi,nawwara tace baei ta gayama mommy sai mimi ta jawota

"Kina gaya mata zata hanamu zuwa,don Allah kada ki gaya mata kawai kiyi Shuru"

            Tsaf ta shirya cikin gold laffaya data sake fiddata a jinin larabawa sosai,sanda ta fito parlor din narkewa abbas yayi a wajen yana binta da wani kallo mai nauyi,ko nawa ne.....kuma komai yawan kudi bayajin qyashin kashewa ya siya mata wasu kaya daya gani suka burgeshi ko kuma kayan gyara,saboda ya sani,komai ta saka yana dacewa da ita fiye da yadda ya gansu.

           Yatsunta ta murza saman fuskarsa tana murmushi

"Yallabai" murmushin shima ya saki yana gyara tsaiwarsa

"Wudd(so,qauna,soyayya mai zafi)" kai ta langabe gefe,tana jin dadin sunan sosai

"Ka yima mommyn mimi magana sai mu wuce gaba daya,kada a dauko mata abinda batajin cinsa" 

"Saidai ke ki kirata" ya amsa mata yana shafa gefan sumar fuskarsa zuwa habarsa,gaba daya ta gana tsumashi,bai taba ganin mutumin da ciki ya boye sosai a jikinsa,ya kuma yi masa mugu mugun kyau ba kamarta.

          Kafada ta daga,ta kuma taka a hankali ta nufi dakin.

       A nutse tare da sallama ta tura qofar ta shiga,da sauri hafsat ta daga kanta tana mamakin jin muryar yarinyar cikin dakin,sai data shiga sosai yadda zata ganta da kyau sannan tace

"Maman mimi..... uncle yace ki shirya ki samemu a mota,zamu dan fita shan iska" widad tayi maganar cikin wani salo me aji da gayu.

          Ashar hafsat din ta saki sannan ta miqe tsaye kamar kububuwa

"Ga hanya nan ki ficemin daga daki tun baki raina kanki ba,ke har kin isa na shiga rigar alfarmarki don zan fita da mijina,idan kunje kada ku dawo" fuska tadan yamutsa cikin nuna yanayin alhini

"Ayyah....me yayi zafi?,Allah ya baki haquri" widad ta fada qaramin murmushi yana qwace mata,wanda hakan ya sake tunzura hafsat, saita tako kamar zata yo kanta,widad din ta juya ta fice abinta.

            Ta samu duk sun fice daga parlor din babu kowa,don haka ta tsaya taci dariyar da taketa dannewa

"Inda ta kamaki da kinci qaniyarki" ta gayawa kanta da kanta tana ganin tsaurin ido da qoqarin da itama tayi dariya na sake qwace mata.

        Ta jima tsaye tana duban bakin qofar bayan fitar widad din,ta hango soma wanzuwar raini qarara a tsakaninta da yarinyar,banda haka a baya yaushe ma ta isa ta isko falonta indai ba ita tayi kiranta ba sanda ta maisheta ma'aikaciyarta?,balle har ta samu sararin da zata shigo har daki ta gaya mata magana mai kama da jirwaye,saita koma ta zauna tana huci,ta sake tashi tana laluben su mimi,daga bisani ta fahimci dasu akayi tafiyar,domin kuwa ga kayansu nan tun na safe zube a falon,kenan har canjin kaya tayi musu,ta lailayo ashar ita daya ta dura

"Zasu ci ubansu ne,gobe ko dakinta akace su kalla ba zasu sake ba" saita koma daki kwanyarta cike fal da tunani, itakam dai banda uwa uwace,da tace anya ummanta tana mata abinda ya dace da dukka iyayen kudaden da take turawa da sunan za'a yi mata aiki irin wanda takeso?.

          Widad da kanta ta zaba musu wani eatery suka sauka a can,kowa yayi order din abinda ransu yakeso,yau kam mimi kamar tayi me saboda dadi,don sam a gidansu bata saba ganin wannan rayuwar ba,shi kansa abbas din ba qaramin dadi yakeji ba duk sanda ya debo familyn nasa sukayi fita irin wannan,suna cin abincin suna raha a tsakaninsu,bayan sun kammala yayi musu takeaway suka tafi dashi,ya tsaya wani supermarket ya hado musu da sauran kayan qwalam.

           Tayi zarya daga dakinta zuwa falon bayan fitarsu sau babu adadi,jiran dawowarsu kawai takeyi,suna sallama tana fitowa daga dakin,sanye da wata riga ruwan madara mai dan qaramin hannu daga can saman kafada,a saman rigar ta daura fallen zani.

            A yadda taga abbas da widad din sun shigo a tare suna dariya ya sake hassalata,tana isa tsakar falon tasa hannu ta janyo mimi ta zuba mata mari

"Gidan ubanwa kika tafi?, daga yau idan akace ki sake binta ba zakiyi marmari ba,saikin gayan uban wa ya baki umarnin fita....." Tayi maganar tana sake cakumo yarinyar kamar ta samu babba,ta kuma ware yatsunta zata sake zuba mata masu,abbas ya dakatar da ita a tsawace

"Kina dukanta ba zaki sauke hannunki ba zan rama mata,kuma da izinin ubanta mahaifi ta fita" ya amsa mata cikin tsananin fushi shima.

        Idanunta dake cakude da bacin rai ta daga ta kalleshi

"Me ka shawo a waje?,'yata zan hukunta kakemin shamaki?,to wallahi ba wanda a isa ya hanani hukuntata,tunda ba wanda ya haifa min ita" tayi maganar tana sauke kallonta akan widad da takejin inda za'a bata bindiga yanzu,a kuma bata damar kashe mutum guda daya tak a duniya ita zata harbe,bata sauke dubanta ba abbas ya zare yarinyar daga hannunta yana cewa

"Idan kina haukarki kiyi ke daya,karki sake kice zaki huce kishin haukarki akan yarinyata,don abun bazaiyi miki kyau ba" sai ya miqata ga widad dake tsaye tana kallon zallar hauka daga wajen mummy hafsat din.

          Ganin ya miqata ga widad saita zabura

"Karki sake ki tabamin 'ya don baki da iko da ita,idan kinji haushi kema ki haifi taki" waiwaya abbas yayi yayi mata alamar su wuce daki abinsu,kwnataccen murmushi ta sake masa a shagwabe

"Take it easy sir.....banason ka qare da ciwon kai please" kai ya gyada yana lumshe ido

"I Will handle it in sha Allah" saita kama hannun mimi suka wuce dakinta,suna tafiya tana shafa mata wajen tare da lallashinta,akwai qauna sosai tsakaninta da yarinyar,tana son widad din sosai,wannan yasa itama widad din duk cikin 'yan uwanta tafi sonta,uwa uba ma kama da takeyi da uncle abbas dinta.

        Shihewarsu daki da mimi ya sake hargitsa hafsat din,ta fashe masa da kuka tana masa hauka sosai,widad dake daki batasan ainihin abinda ke faruwa ba,don bata tantance abinda hafsat din ke fada,amma tashin muryarta da hayaniyarta ta tabbatar har harabar gidan ta isa.

          Batasna ya suka qarke ba,wajen goma da rabi ya shigo dakin,sosai kansa yake sarawa,qasan zuciyarsa yana ambaton sunan Allah,mutum ne da baya qaunar hayaniya ko kadan,ga hafsat kuma wannan din ba komai bane,ya duqa yasa hannu ya dauki mimin

"Ka barta uncle ta kwana a nan" kai ya girgiza kadan

"No.....i need space,i want to be with you..... only you" jin abinda yace sai bata qara magana ba,bashi ba,ita kanta tasan tayi tsananin kewarsa,tana kuma buqatarsa,ba zata bari kuma haukar hafsat ya bata musu wannan daren ba kamar yadda hajiya sha'awa tasha gaya mata

"Akwai hanyoyi da yawa da kishiya zata iya sace miki kwana,bawai saita hanyar dauke miki miji ya kwana a dakinta ba".

           Ko inda take zaune tana gursheqen kuka bai kalla ba ya kwantar da mimi daketa baccinta saman gadon,ya gyara mata kwanciyar gami da tofeta da addu'a,ya tsaya sosai bisa qafafunsa yana duban qofa

"Ko qwarzane na gani da safe a jikinta,wallahi wallahi ki kuka da kanki" daga haka ya fara nufar qofa

"Ai da saika barta wajen uwar daka sake mata" Ta amsa masa tana sakin wani kukan baqinciki daga zuciya zuwa maqoshinta.

          Kamar yadda ta saba bata barshi ya kwana da wani bacin rai ko tunanin hafsat ba gaba daya,ta dauke dukka wani tunani da hankalinsa zuwa wata duniya ta daban,ta sakar masa ragamarta gaba daya,ya fanshe dukka wata gajiya bacin rai da kuma bashin daya dauka a kanta,shi kansa yasan ya bata aiki da yawa,bashi da wani sauran aiki sai lallabarta da tattalata da ya shiga yi tamkar wani sabon qwai.

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post