*H U G U M A*
*Arewabooks:Huguma*
*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)
Part 02
Page 23
Wankin kai da qunshi akayi mata,haka suma yaran duka,sunata murna don ba'a taba musu gyara da lalle irin wannan ba,bata wuce awa biyun ba ta dawo,koda ya dawo gidam ya samesu da gyaran bai kawo komai ransa ba,tunda yasan dama already ita kullum cikin gyara take ta saba (qalubale gareki, keda bakya komai sai sallah ko idan zakuyi biki ko wani sha'ani na taro ya kama,mai gida har ya gane hakan,yara suyita tambayar umma unguwa zamu?,umma biki za'a yi,ba lalle ba gyaran kai babu kitso).
*******Karfe hudu na yammacin washegari tayi wata kyakkyawar shiga cikin wani tsadajjen crystal swarovski lace,duk inda ta motsa ko ta gifta daddadan qamshi ne yake fita daga jikinta da wani irin qyalqyali mai daukan hankali.
Ta nutsu ita daya daga can bakin gate,ta yadda abbas data kirashi gida urgently bazai gane abinda ke faruwa cikin gidan ba har sai ya shigo.
Daga waje ya kashe motar,ya bude ya fito ya kulle yana kallonta cikin mamaki,tace yazo gida yanzu yanzu,yazo kuna ya tarar da ita cikin ido me narkar da zuciya da idanunsa
"Wow......amma kin kyauta da kika kirani naga wannan kwalliyar kada nayi missing nata" ya fada yana murmushi,batace masa komai ba sai kama hannunsa da tayi suka shiga cikin gidan.
Mutuwar tsaye yayi sanda yaga yadda aka maida harabar gidan nasa kamar wani event center,har yaushe akayi hakan bayan fitarsa daga gidan duka duka bai wuce awa uku ba,ko ina ya daga kai manya banners ne masu dauke da hotonsa cikin full police uniform a tsaye,da wasu rubututtuka na nuna murnar tayashi qarin samun promotion da yayi,ga family saman kujeraru da shigowarsa ta saka kowa miqewa yana masa maraba,a lokacin wani irin sassanyan abu yaji yana tsarga masa akan widad din
"Ya rabbb,wacce irin yarinya Allah ya azurtashi da ita?"
"Surprise?" Ya fada yana sauke idanunsa a kanta yana lumshesu cike da wani irin shauqi,saita jinjina kai lallausan murmushi yana kubce mata,shima kan ya jinjina,ya kuma kama hannunta da kyau cikin nasa ya fara takawa zuwa ciki suna riqe da hannun juna ya nufi yan uwa dake dakon isowarsa don a gaggaisa kafin a fara ciye ciye na abinda aka tanada a wajen.
Cikin wani yanayi me kyau da qayatarwa aka kammala taron lafiya,abu yayi masifar qayatarwa,ya burge masoya, abokan adawa kuma da masu taya hafsat kishi kamar su mutu
"Yar qanqanuwar yarinya ta iya kidifiri da iyayi,ta kora sa'ar uwarta uwar gida cikin yaranta gida tazo tana shimfida abinda taga dama" ire iren abinda su gwaggwo hassana da gwaggwo fanteka suke fada kenan,saidai babu bakin cewa komai saidai gulma daga gefe,hakanan kuma sukaci suka sha suka watse.
Sai data tabbatar an sallami kowa harabar gidan ta barwa su shazali zasu qarasa gyarawa sannan ta dawo cikin gidan duba yaran,tasan bata da matsala don suna tare da aminatu,tare suka taho wannan karon.
Aminatun kam akwai hidima,ba qyuya sam,harta sake musu wanka,affan da nawwara sunyi bacci,ita da mimi ne kadai suna kallo a ipad din widad da abbas din yabar mata kwanan nan,don dama itace bata da ita,hafsat nada tata duk da ta bari yara sun tsoma tatan a ruwa.
Bayan ta tabbatar sunci abinci sai ta dauki affan tayi musu sai da safe,don ta gaji tubus,ta kuma ji shigowar abbas din tun kusan dazun ma tana waje tana sallama da mutane.
Tana tura qofar suna hada ido,waya yake amsawa,da alama kuma mai tsaho ce,don haka ta daga masa hannu kawai,ta ajjiye masa affan ta kitchen ta hado musu baqin shayi me kayan qamshi sosai,don ya koya mata itama,sanann ta wuce toilet ta hada ruwa mai zafi tayi wanka.
Daure da towel ta fito,fatarta sai sheqi takeyi,ya ajjiye wayar gefe ya miqa mata hannunsa,batayi qasa a gwiwa ba ta miqo masa nata hannun,yayi mata mazauni saman cinyarsa yana sansanarta,yana bala'in son qamshinta,ba qaramin burgeshi yakeyi ba
"Sannu da hidima madam" murmushi tayi tana saqalo wuyansa da hannunta
"Kaine da sannu yallabai,don dukka aikinka ne wannan" da mamaki ya daga kai ya dubeta,don dai shi yasan sisinsa babu a ciki,hasalima baisan zata shirya ba sai daya shigo gidan.
"Aikina kuma?" Gira ta daga tana murmushi
"Sosai,mun samu kyakkyawar kulawa daga gareka,ka sauke dukkan wani haqqi naka dake wuyanmu,wanann yasa har a cikin zuciyata naji ka cancanci fiye da haka ma,donma ni din ba wata bace,da fin haka naso ya kasance" cikin jikinsa ya qanqameta yana cusa kansa tsakanin qirjinta,abinda ya sanya tsigar jikinta tashi,ya sauke mata zazzafan numfashin da dole ta riqe kansa da hannunta tana 'yar dariya
"Ji nakeyi kamar na maidaki cikina na boyeki,zuciyata har wani irin zafi takemin saboda sonki" yana kaiwa nan saiji tayi ya watsata saman gadon ya kuma maye gurbin towel din jikinta.
Washegari ta tsinci alert a wayarta da sunan mijin nata har na naira million daya,ta sameshi a bayan gidan shi daya da wasu takardu data tabbatar ayyukansa yake,da alama za'a baza komar kama wani mai laifi ne
"Yallabai kudinka sunyi batan kan shigowa account dina fa,da saninka?" Takardun ya aje gefe,ita daya duk duniya yakema haka idan yana aiki irin wannan
"Zonan" yace tana bata hannunsa,saita qaraso din ta zauna
"Ba batan kai sukayi ba,sun shiga inda ya dace ne,nawa kika kashe jiya." Fararen idanunta tadan juya kadan
"Bazance ba,amma dai bazai wuce three hundred thousand ba" kai ya jinjina
"Kice duka tattalin arziqinki kika kwashe" saita saki dariya,kome zata bawa abbas din batajin zatajishi a matsayin asara
"To yayi,kudin dana tura duka naki ne,inason ki zauna kiyi tunani ko kiyi shawarar sana'ar da kike sha'awa,inason ki fara kasuwanci cikin gida" sosai ya bata mamaki kamar yadda itama ta bashi mamaki jiya,ta sauko saman gwiwoyinta ta fara masa godiya,ya kamata ya tayar da ita
"Ban miki komai ba,saboda ke din kin bani komai"
*H A F S A T*
Kai kawo taci gaba da yi,wayar hajiya habiba tana hannunta,duk hoto daya da zata bude tashin hankali ne yake sauko mata mara adadi,kamar ta hadiyi zuciya ta mutu,abbas dinta mijinta da kuma yaranta,duka under control na widad,wacce irin asara take shirin tafkawa?.
"Nidai gaskiya kin bani mamaki,am totally disappointed wallahi,ni duk sai kunya ta kamani ma da naga irin abinda akeyi a wajen,sai lawal ne ya bani address na gidan nan,shima yana daga gefe takaici ya isheshi,don dai bashi da yadda zaiyi ne".
Kananun qwalla ce suka kubcewa hafsat,tana jin tata ta qare,duk wani abu da zatayi akan widad tayi amma jiya iyau
"Aah,ai kuka bai ganki ba,mafita ya kamata ki nema" komawa tayi ta zauna,don gaba daya jikinta babu sauran qwari ko karsashi
"Meye ma banyi ba,kissar nayi babu ci,malaman nabi amma sai abun yayi kamar zaiyi tasiri saiya wargaje" murmushi haj habiba ta saki
"Malamai kika bi ko muna malamai?,hajiyata kiqi kudinki kizo na kaiki inda zaki mori kudinki,kissa kuma iri iri ce hakanan iyawa ce,ki fita batun yarinyar koda an miki aiki yayi,ko agabansa ki dinga nuna bata gabanki shine kawai"
"Wallahi na shirya,ko nawa zan kashe a shirye nake,ai ranar biyan buqata rai ba'a bakin komai yake ba" murmushi ta saki
"Gwara da Allah ya ganar dake ai" (hmmm,kodai shaidan ya batar da ita,Allah yasa mufi qarfin zukatanmu,muje dai zuwa masu karatu,aci gaba da haquri,so nake mu sauke dukkan darasin dake ciki,saboda labarina yafi rinjaye da true life story)