A RUBUCE TAKE (K'addarata) book 2 page 24

A RUBUCE TAKE (K'addarata) book 2 page 24

 

A RUBUCE TAKE (K'addarata) book 2 page 24

*H U G U M A*

*Arewabooks:Huguma*


*_A RUBUCE TAKE_*

       (K'addarata)

            Part 02


Page 24


         Kafin su gama hutunsu a bauchi ta tattauna da mutanen da suka zame mata tamkar fitila a rayuwarta,su anty deena hajiya sha'awa dasu hajiya fanna,anty deena tace


"Kina 'yar kano cibiyar kasuwanci ai baki da matsala,kaya kawai za'a yita kawo miki kina saidawa kina maido kudin ana sake miki sari" su hajiya fanna dake 'yan kasuwa ne suma sukace ba matsala zasu dinga karba,ta zauna tayi shawara da tunani ta zabi kayan da zata dinga saidawa,bata bar bauchi ba saida kayan suka iso,ta raba wasu suka wuce kaduna da wasu.


           Abu kamar wasa saiga kaya sunata shiga ana hada mata kudinta,hakan yayi mata dadi sosai,a cikin lokaci qalilan ta fara gane amfanin sana'a ga mace.


           Ta maida kanta sosai ga kulawa da mijinta da yaronta dake shiga watanni takwas,gasu mimi da takejinsu kamar yaran cikinta,bata da sauran matsala sai godiya ga Allah.


          Watansu daya da dawowa ya dauki su mimi ya maidasu bauchi kan mamarsu ta dawo,bata wani damu ba tunda zuciyarta babu wani mummunan nufi a ciki,saidai bataji dadin tafiyar yaran ba,don hatta mimi taso a barta amma hakan bai yiwu ba.



*R U B U T A C C I Y A R  K' A D D A R A*



        K'arfe hudu na yammaci,tana kitchen tana aikin abincin dare,affan yana goye a bayanta,don aminatu bata nan tana islamiyya,yau din ta dauko aiki me dan wahala,favourite foods na abbas din takeyi har guda biyu,don ma aminatu ta rage mata wasu ayyukan kafin ta wuce islamiyya.


        Knocking taji anatayi sosai,kamar za'a balla qofar,mamaki ya kamata,sam bata qaunar bugu me qarfi haka,taha tsaki ta share bugun ta qarasa juya miyarta sannan ta ajjiye ludayin ta nufi qofar tana tambayar waye da dan qarfi,saidai ba'a amsa mata ba har ta bude qofar.


         Tsananin mamaki ya kamata ganin abbas a tsaye,ya kafeta da ido kafin ya sanyo kai ciki,saita rabe gefe tana bashi hanya hadi da binsa da kallon mamaki,a hankali kuma ta taka ta bishi a baya jikinta na wani irin mutuwa.


          Sai da ya gama qarewa falon kallo tsaf sannan ya kalli wayarsa dake hannunsa ya maida dubansa gareta da murtukekkiyar fuskarsa


"Ina kika je?"


"Ni kuma?,ina zan fita ba tare da saninka ko izininka ba?,ina kitchen ina girki"


"kina kitchen kuma?" Ya sake tambayarta cikin yanayi na rashin yarda sosai kwance a fuskarsa,abinda ya bawa widad mamaki sosai


"Eh mana,uncle na taba yi maka qarya?" 


"Amma naketa kiranki baki dauka ba?,kamar kin fita ko kin tafi Wani wajen?" Idanu tadan zuba masa sannan ta sauke ajiyar zuciya mai qarfi,sai kawai ta kama hannunsa suka wuce zuwa bedroom dinta inda tabar wayar a ajjiye.


          Cak ta dauko wayar ta danqa masa a hannunsa,ya dubeta ya dubi wayar sannan ya bude


"A silent take,ni na sakata saboda inason affan yayi bacci,kada kira ya shigo ya tadashi" wayar yadan juya a hannunsa kadan yana sauke ajiyar zuciya a jejjere,sai ya koma da baya ya zauna a bakin gadonta.


         A matuqar sanyaye ta fice,ta shiga kitchen ta bude fridge ta fiddo zobo me sanyi data hada masa da yaji kayan hadinsu abarba,daya daga cikin nau'ikan zobon data koya a class dinsu da deeja Berver (the best online class da na taba shiga da ya burgeni qwarai qwarai 0907 927 4454).


           Tason yana matuqar sonshi saboda taste dinsa na dabanne da ba ko wanne gida zaka shiga ka samu irinsa ba,shi yasa bata rabo da yi masa.


          Gabansa ta dawo ta durqusa ta soma zuba masa sannan ta miqa masa idanuwanta a kansa,bai musa ba ya karba ya kuma shanye tas ya miqa mata cup din,saita koma gefan gadon ta kwantar da affan sannan ta dawo gabansa ta zauna tana tattara nutsuwarta a kansa


"Uncle,me yake faruwa?,kwanakin nan gaba daya idan ka kira wayata baka sameni ba sai hankalinka yayita tashi,sannan duka ka gaza nutsuwa a wajen aikinka,me yake faruwa?" Idanunsa ya lumshe yana kada kansa da yakejin ya masa wani nauyi,zuciyarsa kuma tana rabuwa gida biyu


"I don't know,kawai dai.......ina tsananin kishinki" shuru tayi tana nazarin maganarsa,a baya yana kishin nata amma ba ta irin hanyar da yanzu yakeyi ba,ya canza kwata kwata,wasu irin halaye yake mata da suke sakata shakku,kamar zargi zargi,to amma tunda ya bata wannan hanzarin bata da hurumin masa hukunci kai tsaye


"Ka kwantar da hankalinka uncle,ni taka ce har abada" qaramin murmushi ya subuce masa wanda baikai har zuciya ba,ya waiwaya yana kallon affan dake bacci abinsa hankali kwance cikin cikakkiyar tsafta da kulawa.


            Bayan wasu kwanaki da yammacin wata litinin,a yau din ba ita keda girki ba,don haka tun bayan kammala sallar la'asar ta gama komai.nata tana zaune,sai kiran ummu ya shigo mata,suka shiga hirarsu sosai tana wasa da hannun affan dake zaune saman cinyarta yana wasa da teether.


            A qalla sun kusa awa guda,suna gamawa kuma kiran anty fanna ya shigo,suka hau hirar kasuwanci da lissafin kudaden kayan widad din da aka saida wadanda suke hannunta.


           Daga qofar falonta taji ana knocking,ta dauki excuse tace zata kirata ta aje wayar ta miqe tana bude qofar,aminatu ce sanye da kayan islamiyya,hannunta riqe da waya


"Aah,har an taso?" Widad ta tambayeta


"Aah anty,yau korar school fees akeyi" dan bata rai tayi kadan


"Amma sau nawa zan gaya miki,duk sanda wata ya qare ki dinga tunamin ina baki?"


"Mamace tace na qyaleki hakanan,wancan watan kin kawo kayan abinci,yanzu kuma......" Sai maganarta ta katse saboda ringing da wayar hannunta ta fara,duka suka kalli wayar a tare


"Wayar waye wannan?"


"Wani ne,da uniform irin nasu abban affan,yace sunanshi samuel,oga ne yace wai a kawo miki wayar zakuyi magana" ta gane komai a dan bayanin aminatun,amma sai mamaki ya kamata,tasa hannu ta karbi wayar,kafin takai ga dagawa ta yanke,saita saki qofar ta juya cikin falon jikinta a matuqar sanyaye,abun na abbas har ya fara kaiwa haka?,meye haka mai qarfi ya shiga zuciyarsa dangane da ita?.


           Tana shirin zama amintu ta sunkuya ta dauki affan tana masa wasa sai gashi ya sake kira,batayi qasa a gwiwa ba ta daga wayar ta sakata a kunne tare da yin sallama.


           Maimakon ya amsa sai ya fadata da fada,ta runtse idanunta tana jin kakkausar muryarsa har cikin zuciyarta,sai ta miqe tsam ta wuce daki riqe da wayar tabar aminatu da affan a nan.


"Ke dawa kuke waya?" Ya tambayeta bayan ya gama fadan rashin daga wayar da wuri


"Nida ummu,sai kuma anty fanna"


"Shine har kusan awa daya da rabi?" Mamaki ya sake cikata,to meye a ciki?,yasansu kuma dukkaninsu dama idan tana waya dasu tana dadewa


"Eh lissafin kaya mukeyi da ita,ummu kuma dama kasan hirarmu ai" Shuru ya danyi sannan yaja tsaki ya kashe wayar.


            Duk yadda taso danne zuciyarta amma ta gaza saida hawaye ya silalo mata,wai meye hakan?,me yake faruwa?.


              Sai data dan koka kadan zuciyarta tayi sanyi sannan ta shiga toilet ta wanke fuskarta ta shafa farar powder sannan ta fito.


            Har yanzu suna falo ita da yaron,ta bata wayar tace ta maida masa,sannan ta zauna ta dauki tata wayar tana dubawa.


           Tex ta rubuta masa na ban haquri,duk da abun naci mata zuciya sannan ta tura masa,saita koma ta zauna jikinta gaba daya babu qwari.


              Falon shuru saboda aminatu ta fita da affan,zuzzurfan tunani ta shiga tanason gano ainihin abinda ya kawo wannan lamarin tsakaninta da abbas din amma ta gaza gano komai,cikin haka ta kwashe awa kusa biyu,ta daga idanunta tana kallon qofa sanda taji ansa key ana qoqarin bude qofar.


             Tasan waye,don shi kadai keda key din gidan,miqewa tayi cak da nufin shigewa bedroom dinta,motsinsa da taji kadai ya karya mata zuciya,bata kuma so tayi kuka a gabansa,saidai ta makara,bata kai ga isa dakin ba ya shigo,kuma ya ganta,yana dauke da affan,da alama ya tsaya ya karboshi ne.


           Daga nan inda yake ya tsaya bayan yayi sallama yana kallonta,ta amsa amma bata juyo ba,sai ya tako a hankali ya iso bayanta ya rungume ta ta baya,saita sake masa kuka kawai.

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post