Daudar Gora book 2 page 56

Daudar Gora book 2 page 56

Daudar Gora book 2 page 56

 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲      

  ✨𝕯𝕬𝖀Ɗ𝕬𝕽 𝕲𝕺𝕽𝕬✨

           (𝕮𝖎𝖐𝖎 𝖐𝖆 𝖘𝖍𝖆𝖙𝖆)

            𝓑𝓲𝓵𝔂𝓷 𝓐𝓫𝓭𝓾𝓵𝓵 𝓬𝓮🤙🏻

𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 (56)

........“Haba Waheeda ina kika shiga kekuwa haka kinsa zuciyata na neman ƙarasa harbawa a tsaye”.

      Da ƴar raha-raha da ga can Daneen Waheeda ta ce, “Oh oh Kinga kwantar da hankalinki nabar wayar ne a ɗaki wlhy ina sashen surukinki. Halan wani masifar shegiyar can ta sake jangwalowa?”.

     “Uhhm ai wannan karon ba ita ta jangwalo ba ita aka jangwalowa. Ni Ashwaq naga abinda zai kasheni a wannan masarautar yau da raina. Wai kin san kuwa madarar da aka shayar da ɗakinki wai Miran Jasim ne ya samar da ita”.

     “What!”.

  Daneen Waheeda ta faɗa cikin zabura da ga fasa zaman da tai niyyar yi da ga can. “Wait! Wait wait Ashwaq wai nikam mi kike son faɗa minne haka. Jasim Akhi namu kike nufi yake shirin kashe Eshaan ɗin komi? Ni Wlhy gaba ɗaya ma kin rikitamin lissafi”.

          “Bake lissafinki ke a rikice ba, ai kowa ma yau a masarautar nan lissafinsa a rikice yake wallahi.......”

   Tiryan-tiryan ta kwashe komai na zaman kotu a yau ta faɗa mata kamar yanda ta saba kai mata gulmar duk wani motsin yan masarautar musamman Malikat Bushirat. Wani irin irin tashin hankali Daneen Waheeda ta shiga tana zungura manya-manyan zagi dan ita dama can mace ce masifaffiya mai zafin tsiya. A wani lokutan akance tafi kowa gado mahaifinsu a kaf ƴaƴan Tajwar Abdul-majeed. Daga can ta ce, “Gobe ki tsumayi zuwana RUMAN ƴar uwa wannan dambarwar ba'ayita babu ni kusa ba. Amma karki faɗama kosu Mammah. Shin yaya baƙar dagarki tayi ne za'a kashe mata tilon ɗan gwal ɗin ta da take hura muku hanci”.

      “Uhm-iuhm ai labarin kam dai babu daɗin ji, amma tunda kince kina tafe ke dai kwantar min da hankalinki sai kin iso kawai”.

     “Okay bara kiga naje na fara shiri ma tun yanzu. Amma da mutuniyarki zan taho dan wannan karon kam inaga sai na nunama Eshaan ƙwanji akan Iftihal dan ko yaƙi ko yaso sai ya aureta tunda dai matan sun daina mutuwar”.

          “Ina tare da ke ɗari bisa ɗari kuwa. ALLAH ya kawo ku lafiya”.

    Da ga haka sukai sallama Malikat Ashwaq na faman sakin murmushi, dan itafa ranta fari ƙal da abinda ya faru a yau ɗin.

      (Ina fatan kun gane matsayin Daneen Waheeda dai. Itace ƙanwa ga Daneen Ammarah da Tajwar Haysam mahaifin Tajwar Eshaan. Ɗiya ta uku ga Malikat Haseenat da mukace tana aure acan yankin larabawa. Ƙawace sosai ga Malikat Ashwaq, kuma ƴar uwa, dan kusan ma itace tai ruwa tai tsaki wajen ganin Malikat Ashwaq ɗin ta auri Tajwar Haysam duk da shima dai ya sota a karan kansa. Tare sukai karatu dan haka akwai shaƙuwa mai ƙarfi a tsakaninsu da har take tayata kishin Malikat Bushirat. A duk sanda ta sami wani sabon labari musamman akan koma bayan Malikat Bushirat sauri take taga ta sanar ma Daneen Waheeda. Shiyyasa a randa hadimanta sukazo mata da bayanin Malikat Bushirat taje wajen Malikat Haseenat akan ƙara auren Tajwar Eshaan tai azamar kiranta ta sanar mata dan tasan babban burin Daneen Waheeda ɗin shine haɗa auren babbar ɗiyarta da Tajwar Eshaan da suke kusan sa'anni. Ta matuƙar mutuwa a kansa amma shi ko kallo bata ishesa ba. Hakan yasa ita Daneen Waheeda ɗin taso a haɗa auren amma Malikat Bushirat taƙi bada haɗin kai. Dan ta fahimci so Daneen Waheeda keyi Tajwar Eshaan ya auri ƴarta su koma juya akalarsa data mulkin ƙasar ruman ɗin. Ga kuma sharaɗin da UWA ta gindaya mata na karta yarda Tajwar Eshaan ya auri wata da ga cikin zuri'ar masarautar sam. Yin hakan gagarumin abune da zai rusa komai da yake komai a hanunsu. 🥱 ALLAH yasa kun gane).


      

         ★★..... ★.....


    Abune da bata sabayi ba, wato kiranyen uwa da rana. Sai dai yau abubuwa sunma kanta yawa, ciki har dajin zafin miyasa uwa zata ɓoye mata ƙulle-ƙullen Jasim akan tilon ɗanta. Yanda fa take nuna mata biye take da duk wani mai son ganin bayanta ko ɗanta, yaya akai anan aka faɗi a ragaya kuma?, dole ta nemota domin samun warwarewarsu. Cikin sa'a kuwa tana fara hayaƙin sai gata. Kamar yanda ta saba takai gurfane gareta. Shiru uwa batace komai ba, ta dai zuba mata idanun nan nata jajaye marasa ƙyan gani. Malikat Bushirat ko nace ta-ƙurya taita ƙoƙarin danne ɓacin rai da zafin dake taji ta ɗago kaɗan ta ɗan dubeta, sai kuma ta maida kanta tana furzar da huci mai zafi. “Abubuwa da yawa sun faru a yau, mafi ɗaure kai daɗewar maƙiyi a gefen hanun damar Saiful-malik ɗina batare da kin taɓa fargar dani hakan ba ko sau ɗaya ba uwa. Keface Uwa mai share kukan mai kuka, ke face uwa da tai min alƙawarin bama Saiful-malik ɗina kariya tunkan samuwarsa. Keface Uwa da ta sanar min zama ido akan motsin duk wani da zai iya yunƙurin cutar da koda bangon ɗakina ne balle gudan jini na. Amma sai gashi a yau naci karo da abinda ban taɓa cin karo a bakinki ba. Yanzu nan har daɗewar Jasim ta kai haka cikin son ganin bayan jinina amma ban sani ba?”.

         Ɗan daburcewa uwa taso yi, dan bata so akazo wannan gaɓar da wuri haka batare data kammala shirinta ba. Anya kuwa batayi babban sakaci akan ta-ƙurya ba. Itama fa itace tsanin cikar nata burin data ɗauki tsawon shekaru tana bi matakala-matalaka domin maida murtani ga ahalin wannan masarauta baki ɗaya.... Ganin irin kallon da ta-ƙurya ke mata ne ya sata haɗiye komai ta dai-daita yanayinta. Fuskarta ta sake tsukewa da gyara zaman ƙasaitarta. “Ta-ƙurya ban ɓoye miki domin wani dalili ba, sai dan kareki da ga shagala kan al'amarin sa, amma ki sani na jima biye da Jasim da hana makircinsa tasiri kan Ajlaan. Shin bakiyi mamaki ba ne yau? Bakiyi mamakin faruwar abinda ya faru ɗin ba ne? To bari na kaiki inda baki sani ba. Nice nan da kaina na buɗewa Jasim aiki yau, kuma na fara ne tun a randa ya kai kayan asiri fadar Ajlaan. Ban miki maganar bane ba dan ina son sai an kai ƙarshe. Kuma duk abinda ya farun yau a kotu nima ina tare da ku”.

         Wata irin wawuyar ajiyar zuciya Malikat Bushirat ta sauke. Gaba ɗaya sai taji abinda ya tsaya matan a maƙoshi ya faɗa a cikin cikinta. Ɗari bisa ɗari ta yarda da zancen uwa, dan bata taɓa mata ƙarya ba (hummmm). Fuskarta ɗauke da murmushi ta sake gurfana a gabanta. “Yanzu kam na fahimta, na fahimci komai uwa. Dama ni nasan bazaki bari na faɗi ba. Amma naso ace kin sanar min tuni, da sai na ɗaiɗaita rayuwar Jasim, sai na kafa tarihi akansa irin wanda ko harara wani bazai sake kwatantawa ga Saiful-malik ɗina ba a wannan masarautar”.

      Wani irin shegen dariya uwa ta kwashe da shi. “K ƴar halak ce ta-ƙurya, shiyyasa nake sonki fiye da duk wanda ya kasance a ƙarƙashin baiwata. Na miki alƙawarin bazaki sake yin kuka ba, zan cigaba da tsaya miki fiye da tsayawar da nai miki a baya. Zan cigaba da kare Ajlaan fiye da kariyar da kike tunanin yana da (Wa'iyazubillah . Ya rabba ka tsaremu da aikata shirka koda a cikin duhun jahilci ne😭🙏). Zan baki mamaki, tabbas zan baki mamaki ta-ƙurya”.

        “A kullum cikin bani mamaki kike ai uwa, shiyyasa bazan gaji da faɗa ba, bazan gaji da maimaitawa ba ke ta dabance a cikin daban”.

      “Hhahahahahaha!!!!!!!”.

Uwa ta ƙyalƙyale da wata irin mahaukaciyar dariya har ta-ƙuryar najin sautinta cikin iska, kai kace gaba ɗaya masarautar koma ƙasar ruman ɗinne baki ɗaya zasu jita...


     (Uhm uhm da alamafa akwai wani ƙulli tare da Uwa, ko minene shi🤔? Muje dai zuwa sannu sannu ai bata hana zuwan sai dai a daɗe ba'a je ba🏃🥱)


      ★★.... ★....


   A wani bala'in firgice ta farka da ga barcin da ya figeta bayan idar da sallar azhar. Kanta dake wani irin sara mata ta dafe tana ambaton sunan ALLAH. Ta kai tsahon minti uku a haka kafin ta miƙe daga saman sallayar da anan barcin ya kwasheta. Gaba ɗaya jikinta tsuma yake, yayinda zuciyarta ke mata tariyar mafarkin nata dalla-dalla. Jin jiri na neman zubdata ƙasa tai saurin zubewa bakin gado tana sake dafe kai. A hankali ta furta, “Uwa!! Wacece ita? Ta ina zan fara bincike saninta”. Kantane ya sake sara mata, tunda take mafarke-mafarkenta bata taɓa mai nauyi irin wannan ba. Duk da bataga fuskar wadda ke zaune a kujerar ƙarfen nan ba zagaye da wasu irin munanan halittu taji a ranta dole ta kasance abar tsoro. Sai kuma ganin Malikat Bushirat da tai a gabanta dirƙushe, shin minene haɗin Malikat ɗin da waɗan nan munanan hallitun? Tajwar Eshaan a gefe ɗaɗɗaure da wasu irin igiyoyi wuta, sai dai shima bata ganin fuskarsa amma tana iya jin yanda yake ambaton sunayen ALLAH raɗam....

        “What's wrong.....?”

   Ɗagowa tai da sauri dan sam bata san da shigowarsa cikin ɗakin ba, hasalima bata san ya dawo ba. Idanunta data kafeshi da su ta ɗan janye tana ƙara tsarkake sunan UBANGIJI mahaliccin wannan bawa. Komai nasa mai ƙyau ne da birgewa. Hatta kayan zaman gida idan ya saka badan kwalliya ba sai su fidda cikar kamalarsa da zati.

          “Kaina ke ciwo”.

     Ta faɗa kanta a ƙasa dan kallon nan nasa na ƙasa-ƙasa da ke daburta mata lissafi bata son shi. (Aljanun sunzo kenan) ya faɗa a zuciyarsa yana wani ɗan yamutsa fuska. A zahiri kam baice komai ba ya dai cigaba da kallonta. Kusan minti ɗaya sannan ya motsa da cigaba da takawa a hankali cike da ƙasaitar nan tasa. A gabanta yaja ya tsaya, tare da zare hannunsa dake cikin aljihun wandon jeans ɗinsa ya miƙa mata. Idanunta ta ɗago ta kalli hannun da ke fari tas da shi, ga jini nata kaikawo a tafin kamar ba namiji ba. Idanunsa ya ɗan lumshe da buɗewa a lokaci guda yana gyaɗa mata kai alamar ta ɗaura nata. Kamar mai jin tsoron hakan ta ɗago natan ta ɗora a cikin nasan. Sake lumshe idanun yayi kamar wani wanda maganaɗisu ya taɓa, batare da ya buɗe ba ya ɗagota ta miƙe tsaye itama. Matsota yay kawai jikinsa ya rungumeta tsam-tsam. Sassanyar ajiyar zuciya ta saki nutsuwa na ratsata, sai kawai ta ƙanƙamesa itama tare da kwanciya luff a faffaɗan ƙirjinsa tana shaƙar daddaɗan kamshin turarensa mai saka zuciyar mai shaƙa nutsuwa.........✍️

        



_Oh oh su Iffah an waye an manta da mu dangi🥱_



   

*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*


*DAUDAR GORA Billyn abdul*


*KI KULANI hafsat xoxo*


*A RUBUCE TAKE Huguma*


*RUMBUN K'AYA Hafsat rano*


*IDON NERA Mamuh ghee*



_LITTAFI DAYA: 400_

_LITTAFI BIYU: 600_

_LITTAFI UKU: 800_

_LITTAFI HUDU :1000_

_LITTAFI BIYAR: 1200_


_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_


_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_


_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_


_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_


_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_


_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_


ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN


MARYAM SANI

ACCESS BANK

0022419171


SAI A TURA SHAIDAR BIYAN 


09033181070


IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA


09166221261


*ƳAN ƘASAR NIGER🇮🇳. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*


+227 96 09 67 63


Books biyar  1250CFA

Books hudu  1050CFA

Books uku  850CFA

Books biyu  650CFA

Bookk daya  450CFA


KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.

MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏽_*

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post