Rumbun Qaya page 31

Rumbun Qaya page 31

Rumbun Qaya page 31

 *RQ*


    Page 31


***Cigaba da tsaiwa tayi a wajen shi kuma ya cigaba da abinda yake yi kamar babu mutum a wajen. Sosai ta shak'a ta cika ta hau ranta yayi mugun baci. Gaba daya ta gama lura da Aryan mugun dan rainin hankali ne. Abinda yayi niyya shi yake yi, kuma shi zaka yi masa magana ya share ka amma shi be yarda yayi maka kaki amsa masa ba. Cigaba da tsaiwar tayi har kusan goma da rabi ganin bashi da niyyar bata yasa ta bud'e baki tace


"Sir zan makara dan Allah."


"Hello." Ya daga waya ba tare da ya amsa mata ba. Wasu hawayen bakin ciki ne suka shiga sakko mata ta juyar da fuskarta ta goge su zuciyar ta na tafarfasa. Ya dan jima yana amsa wayar yana satar kallon ta kad'an kad'an har ya gama. Ya mike rike da wayar sa a hannu sai wallet din sa da I'd card din nata yake ciki.


"Idan kin gama tsaiwar muje." Yace sanda ya isa gaban kofar ya bud'e yayi waje. Wani takaici ne ya sake turnike ta, tabi bayan sa a sanyaye. A reception ya tsaya suna magana da Zainab tazo ta gota su kawai ta fice daga wajen. Tsayawa da maganar da yake yayi, sai ya sauke kansa ya karasa yi mata bayanin da yake mata sannan yabi bayan Raihanan. Har ta fita gate din yayi saurin kunna motar shi yabi bayan ta, ya tarar da ita tana tsaye gefen titin da alama napep take jira. A gabanta yayi parking ya sauke glass din sannan yace mata


"Shigo muje."


Dauke kanta tayi daga kallon bangaren sa, ta saka hannu ta tsaida napep. Da sauri ya balle murfin motar ya fito ya saka hannu ya tare


"Oga rabu da ita tare muke." Yace ma me napep din, dariya ya kwashe da yace


"Gaskiya ne oga, ai na gane yaren." 


"Hajjaju kar kiyi saki reshe fa, irin yallabai wahalar samu suke duk sai ire-iren mu ne suka rage."


Banzan kallo tayi masa, ya sake fashewa da dariya ya tada napep dinsa ya wuce yana dagawa Aryan din hannu


"Kina sake bata lokaci ne." Yace mata yana nuna mata hanyar motar, hawayen da ya zubo mata ta share ba tare da tayi magana ba, ta wuce ta bud'e motar ta shiga saboda makarar da tayi. Shigowa yayi ya daura seat belt ganin tana hawaye ya ciro tissue daga saman gaban motar ya dora mata akan cinyar ta sannan ya tada motar.

   Tafiya suke tamkar kurame babu wanda yayi magana da dan uwan sa, kanta na kallon window tunda suka soma tafiyar shi kuma nasa na kallon hanya. Hamma Hydar ne ya kirata ta d'aga.


"Kina ina? Gani a kofar wajen naku."


"Yanzu nake tahowa hamma."


"Yanzu? Ya akayi haka?"


"Eh nayi mantuwa ne shine abinda yasa."


"Ok, sai kun karaso ina jiranki."


"Ok tam." 


"Hydar ne?" Ya tambaya


"Umm."


"Ok." Ya cigaba da abinda yake yi. Sake juyar da kanta ta cigaba da yi har suka karaso garin na Kumbutso.


"Kinyi printing out schedule dinki?" Ya tambaya suna isowa daidai wani cafe


"Umm." Ta sake bashi amsa a takaice. Be sake magana ba ya shiga kwanar da zata kaisu wajen, tayi mamakin ganin yasan wajen tunda ba wai ya tambaye ta bane ba. Motar Hamman ta, ta hango a karkashin wata bishiya.


 "Ya isa nan." 


Tace dan bata so ya karasa wajen Hamman. Banza yayi mata ya cigaba da tafiya har sai da yaje daidai gefen motar da Haydar din ke ciki shi da wani abokin sa sannan yayi parking ya kashe motar. Ranta a bace ta kama kofar zata fita ya ciro I'd card din ya dora mata a kan kafarta sannan ya bud'e kofar ya fita. Fitowa Hydar yayi dan tun daga shigowar su harabar wajen har zuwa parking din da yayi a kusa dasu yana kallon su. Da sauri ta wuce dan taga irin kallon da Hamma Hydar din yake mata. Hannu Aryan ya bashi sukayi musabiha sannan yace


"Dama tare kuke?"


Daga mishi kai yayi


"Yes, ko nayi laifi ne?"


"Kayi, ba hurumin ka bane kawo kanwata wajen nan, akan me ma zata shiga motar ka?"


"Point of correction, kanwar mu dai."


"Ko?"


"Yes, kai ma ka sani ai, yadda take kanwarka nima tawa ce."


"Da kenan banda yanzu, dan Allah Aryan don't drag Raihana into this, she's innocent shiyasa duk abinda yake faruwa ma bata sani ba, bama son duk abinda zai bata mata rai please dan Allah ka fita daga rayuwar ta."


"Me kake tsoro?"


"Komai ma, duk abinda zai faru ya tsaya iya tsakanin mu, amma banda ita."


"Don't be selfish mana Hydar, menene laifi na dan Allah?"


"Kai ma ka sani, mu bar wannan maganar tunda ba shine ya kawo mu ba, maganar kanwata ne kuma ina fatan zaka ja baya daga gareta."


Murmushi yayi me taushi sannan yace


"Hydar kenan, kana kara zugani ne wallahi, ina kuma wani tunani akan hakan, kuma zanyi trying luck dina, kaga karshe sai na zama sirikin ka kenan."


"Allah ya kiyaye, kamar bamu da tunani ko hankali?"


"Ya zakayi da innocent heart din ta toh? Idan tayi falling mun?"


"Ba ma zai taba yiwuwa ba, never mu sake wata alaka tsakanin mu, ba ni ba, ko Abby ba zai yarda ba wallahi, bare Lamido da Sadeeq, it's over kawai tunda ka samu abinda kake so daga wajen Abby shikenan, babu sauran wata alaka tsakanin mu."


Murmushi kawai yayi, duk kuwa da maganar ta dake shi sosai, amma sai ya nuna be ji komai ba.


"Hamma yace wai na makara ba zai min clearance din ba sai anjima."


Ta karaso wajen nasu tana fada, abinda ya hana Aryan fadar abinda yayi niyya sai ya juya akalar maganar zuwa wajen ta


"Muje zai barki."


 Yace yana kallon ta, kallon Hamma Hydar tayi taga shima ita yake kallo, sai kawai ta juya Aryan din yabi bayanta. A kofar shiga wajen ta tsaya yazo ya wuce ta, tabi bayan sa. 


"Wa nake gani?"


"Ni ne Oga."


"Lallai yau nayi babban kamo, oga kai ne a tsangayar tamu haka da tsakar rana?"


 LGI Tanko yace yana mikewa, ya bashi kujera ya zauna sannan suka gaisa


"Kwana biyu oga, Ka buya."


"Wallahi abubuwan ne suka yi yawa Oga T, ya aiki ya fama da students."


"Alhamdulillah wallahi, gamu nan muna lallabawa, tunda kunki saka mu a harkar mai."


"Haba Oga ai ku manya ne."


"A ah ina fa, yara dai."


"My wife to be na kawo clearance Oga."


"Are you serious, tana ina? Kace dai bana oga zai motsa, dama inaga kaf class din mu kaine kadai ka rage."


Murmushi Aryan yayi kawai, ya waigo wajen da Raihana take tsaye kamar munafuka yace ta matso


"Madam sannu da zuwa, bismillah zauna mana.". 


Yace yana nuna mata kujerar da take kallon ta Aryan din. Kalmar Madam din ce tayi mugun daure mata kai, yanzu yanzu fa ta shigo ya kora ta, shine yanzu har da bata seat da kiran ta madam, me Aryan din yace masa hala?


"Ina takardun naki."


"Gasu sir." Ta mika masa kanta a k'asa. Karba yayi ya ajiye yace tasa hannun ta tayi thumbprint, tasa yayi yace shikenan. 


"An gama?"


"Eh shikenan oga, har an gama."


"Ok, godiya nake oga, sai mun shigo wani watan in sha Allah." Ya mike tsaye


"Allah ya kaimu, idan an saka bikin saura ka manta kaki sanar min, ko da yake nine me baka auren ma tunda dai amaryar tamu ce."


"In sha Allah. Thank you so much sir, a huta lafiya.'


"Yawwa, ku gaida gida."


"Aure zaiyi kenan?" Ta raya a ranta. Tabe baki tayi suke fito daga wajen. A wajen motar suka samu su Hydar a tsaye suna jiransu


"Har anyi?" Hydar yace mata


QTace tayi saurin bud'e motar su ta fada baya dan ma kar Aryan din yace ta shiga motar sa 


"Zan wuce Hydar, sai yaushe?"


"Ba rana." Ya fada yayi saurin shiga mota


"Sai gani na uku, watakila a kano watakila kuma idan na zo har gidan wajen Abby."


"Muje khalifa."  Kawai yace dan sarai ya lura Aryan din so yake ya rama abinda yayi masa ranar nan.


Matsawa gefe Aryan yayi suka tada motar suka bar wajen yana kallon su. A nutse ya karasa wajen tasa motar ya shiga shima ya bar wajen. Suna gaban sa yana bayan su har suka shigo Kano, hanyar bypass suka dauka shi kuma yayi naibawa saboda yana so ya shiga asibitin Malam. Yana gate din asibitin Ya Nabeela ta kirashi tace masa Daddy ya farka ya kara sauri ya isa, ya same shi idon sa a bud'e sai dai baya magana. Tunda Aryan ya shigo yake hawaye, yana ta kokarin yin magana amma ya kasa. Ganin ya matsa sosai yasa Aryan kiran Dr ya fito waje ya bar su a ciki. Ya hangi tsantsar nadama da dana sanin a idon Daddyn wanda dama abinda yayi ta gudar masa kenan, abin takaici hatta yan uwansa sai da Hajiya Zeenat ta raba shi dasu, su kuma dangin Mommy sukayi fushi dasu babu ruwansu da yaran tsakanin su sai ta kure tun wani zuwa da sukayi ganin su Aryan din Daddyn yayi musu cin mutunci tas sai suka bar masa yaransa shiyasa suka zama basu da kowa sai kansu su suke komai da kansu. Abinda Hydar ya kasa fuskanta kenan, da su da sukayi rayuwa tare da mahaifin su dasu da sukayi rayuwa babu, basu da wani banbanci domin babu wani amfani da zasu iya nunawa da ya amfanar musu sai ma rayuwar kunci da ya sanya su duk ta dalilin biyewa mace da kaidin ta.


***Fada sosai Hydar ya rufe Raihana dashi tunda suka dauki hanya yake ta banbamin masifa, ta in da yake shiga ba ta nan yake fita ba, tun farko ma akan me yasa zata je office din har kuma ta yarda ta shigo motar Aryan din tun daga cikin gari har kumbotso.


"Abinda kike aikatawa kenan da babu idon mu kenan."


Ya karkare yana juyowa bayan. Kuka take dan zata iya rantsewa irin wannan fadan be taba hada ta da Hamman ta ba, duk da zafin zuciyar da yake da ita amma baya mata, basa taba mata fada duk abinda zatayi sai dai idan batayi daidai ba suyi mata ta sigar lallami amma sai gashi yau Hamman ta har buga dashboard yake saboda tsabar masifa.


"Abinda kike aikatawa kenan ko? Ina tambayar ki."


"Haba Hydar, yi mata a hankali mana,."


"Ba zaka gane ba Khalifa, bana son alakar ta da Aryan ko kadan, ba ta yadda za'a yi mu zura ido tarihi ya maimaita kansa, ina ba zai yiwu ba gaskiya."


"Na sani, amma menene amfanin fadan haka? Na tabbata a ba yadda zatayi ta shiga motar sa, ina ganin duk abinda zatayi kawai ku dinga tsayawa kuna shige mata gaba saboda gudun faruwar irin haka."


"Munayi ai, me ya kawo ni Kano a wannan lokacin idan ba dalilin ta ba, sai da fa nace ta jirani zan zo na kaita da safe tace zata iya zuwa da kanta, mukayi da ita zamu hadu a chan sai mu taho tare saboda wannan fitar da mukayi da sasassafe, amma kana gani har mukaje bata zo ba."


"Kayi hakuri dan Allah Hamma, wallahi I'd card dina na manta a office din shine naje karba be bani ba yace muje, wallahi har gate muka zo dashi na tsaida me napep ya hana shi daukata."


"Ahaap, ai na fada maka ba lallai idan laifin ta bane ba, kazo kana ta fada haka."


"Toh naji, wannan ya zama na karshe da hakan zata faru."


"In sha Allah ba zan sake ba."


Jikin sa ne kuma yayi sanyi, duk sai yaji babu dadi fadan da yayi mata


"Ya isa toh kukan haka, ya isa."


Share hawayen take kokarin yi amma yaki tsayawa, babu abinda yafi ciwo ace wanda be saba maka fada ba yayi maka rana daya, yafi komai kona rai.


    Kwana biyu tsakani suka koma Adamawa sai kuma wani karshen watan. Suna zuwa Hydar ya kwashe komai ya sanarwa Abby abinda yake faruwa tun farkon haduwar sa da Aryan har zuwa wannan karon, ran Abby ne ya baci ya kirawo Raihanan tana daki a kwance ta samu sakon kiran nasa, ta dauka ma wani abun ne sai dai tana zuwa Abbyn ya hau fada, ya dinga mata fada musamman akan shiga motar Aryan din da tayi. Sosai jikin ta ya dinga rawa tana durkushe yana fadan


"Ya kyautu yau kiyi alaka da mutanen da suka tura mahaifin ki prison tun kina yar karama uhm? Ya dace kuwa?"


Girgiza kai tayi da sauri dan ko ta bud'e bakin ta ma ba zata iya magana ba sai dai kuka ya biyo


"Toh bana so, abinda ya faru ya riga ya faru kuma ko a yanzu sun girbi abinda suka shuka, duk da shi Muhd bashi da laifi ko kad'an amma babu wata alaka tsakanin iyalinsa da nawa, kowa yaji da kansa bana so."


"In sha Allah ba zan sake ba."


"Yawwa, Allah yayi miki albarka."


"Amin."


 Tace ta tashi fuskar ta a dukunkune ta fice. Tana shiga falo Daadah ta rikota, kawai ta sake fashewa da kuka da karfi.


"Na shiga uku ni salamaatu, me ya faru?"


"Laifi tayi Dadah, ta shiga motar Aryan har ya kaita clearance."


"Duk akan wannan maganar ce bata mutu ba ni Hajara? Akan me zaku matsa wa yarinya ne wai? Menene laifin ta, soyayya suke yi? Yau ace ma idan soyayya suke yi menene a ciki? Baku yarda da kaddara bane ko me? Eh? Ko zaku ja da hukuncin Allah? Idan ma haka ba, wai Aliyu idan Raihana bata samu saurayi me sonta ba, shin kune zaku aure ta ne wai? Ko zama zatayi tayi a gida kuna kallon ta eh?"


"Baki fuskanta bane Daadah, bafa hanata kula kowa akayi ba, Aryan din ne dai, tayaya Abby zai dauki Raihana ya kaita gidan nan tayi rayuwa?"


"Sai me toh? Dan tayi."


"Kayya, Dadah karki manta fa abinda ya faru, karki manta."


"Ban manta ba sarai, kuma bana daga cikin marasa yarda da kaddara, dan haka ba zan hana abinda Allah ya yi ba, kuma na tambaye ta ko Yaron nan yace yana son ta, tace a ah be ce ba, menene abun tada jijiyoyin wuya fisabillillah?"


"Haka tace? Wallahi ni dashi yace min yana sonta, ido da ido kuma ba wai a waya ba."


Saurin zabura Raihana tayi, ta kalli Hydar da sauri shima kuma ita yake kallo


"Kwarai da gaske, kuma ko da be furta ba ai action dinsa ya fada, ni namiji ne duk nasan irin wannan abubuwan."


"Na shiga uku." 


Tace da sauri ta ruga ta shiga dakin ta, hannun ta a saman kirjinta saboda yadda ya buga da karfi.


"Yanzu dai sai ku bar yarinya ta sarara dan Allah, tunda da alamu duk ma abinda kuke tunani da zato ita bata ma sani ba, amma kunzo kuna mata fada akan me?"


"Daadah please ki gane mana."


"Naki na gane din, kai ba kwanan nan aka je aka tambayo maka aure ba, duk ba auren zakuyi ba kuma ma rana daya? A bar min yarinya ya shaki iskar yanci dan Allah, idan ba haka ba wallahi zamu saka kafar wando daya da duk wanda zai takura mata. Ba ku kuka tura ta Kanon ba, da kunsan da haka?"


"Allah ya huci zuciyar ki toh."


"Amin, ka gayawa Abban naku nace bana so, atoh."


Dakin tabi Raihanan shi kuma ya kada kansa kawai ya fice.

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post