Daudar Gora Book 2 page 86

Daudar Gora Book 2 page 86

Daudar Gora Book 2 page 86

 DAUDAR GORA 

Book 2 

Page 86

-."Anan ma dai tayi dariya da fadin (Ke ta dabance ta-kurya, sannan kanki na kawo wuta fiye da yanda nake bukata). Naji dadin yabonta harda godiya ta.

 Wasu magungunan ta sake bani, ta tabbatar min nai duk kokarin da ya dace na shayar da Ashwaq da Danish-Ara. Na mata godiya nan ma ta sake bace mun. Na shayar dasu maganin su duka uku nima kuma na sha wanda ta umarceni, sai dai kuma washe garin da Ashwaq tasha nata akawayi gari tayi barin cikin da ni ban taba sanin da shi ba. Ranar nayi farin ciki sosai, a wani gefen kuma ina mamakin toda miye na boyewar da tayi? A nufinta da karmu taba sani sai ranar haihuwa kenan? Lallai kasancewata da uwa alkairine. Abu mafi kara sakankancewa da uwa shine bayyanar ciki a jikina kafin cikar wata gudan data fada. 

Nayi farin ciki nayi farin ciki, duk wani masoyina ma yayi farin ciki. Itama kanta uwa tazo ta tayani farin ciki tare da sake kawo min wasu magungunan dazan na amfani da su har na haihu. Tace kariyane ga abun cikina dani kaina. Dan suma su Ashwaq zasu iya kawoma cikin nawa hari. Na yarda da ita fiye da kowa da komai a duniya zuwa yanzu, dan haka babu wani dar a tare dani na amsa. Haka na cigaba da rainon ciki, tare da soyayyar da ban taba zato da tsammani da ga Haysam ba. Ashe haka yake tsananin so da kaunar haihuwa. 

Hakama mahaifiyarsa da yan uwansa su Ammarah kowa tattalin rayuwata yake yi, Masarautar ma gaba daya wani irin girmamawa akemun data kara sakamun kaina fadì da jin babu kamar uwa a tare dani a wannan duniyar. A haka watan haihuwa ya kama mun, kowa fatansa ALLAH ya saukeni lafiya, ni kuma babban fatana na haifi da namiji, dan inata fargabar tambayar uwa hakan, kar tacemun bata da tabbaci. 

A haka dai na wayi gari wata safiyar laraba ina nakuda a tsaitsaye, uwa ta gargadeni fadama kowa, dan haka naita dauriya sai Jasrah dake nane dani, idan taga ina murkususu taita kuka, idan ya lafamun ta sani gaba da tambaya naita dai lallabata. Har safiyar Alhamis babu haihuwa babu alamarta, ranar mana cinye wannan yinin a wannan wahalar babu wanda ya farga har dare, dan ko Ammarah dake tare dani naki barin ta sani. Sai zuwa dare da ya ke tafiya daren juma'a kenan ina tsaka da shan murkususu na sai ga uwa. Naji dadin zuwanta, dan koba komai ina saka ran taimakonta. 

Tako zomin da taimakon sai dai ta hanani, acewarta yau ne ranar da zata sanarmin sharudanta, idan na amince zata bani maganin da zan haihu lafiya kuma da namiji da zai zama magajin kujerar Shahan-shan, idan kuma na bijire zata barni tai tafiyarta babu kuma tabbacin zan rayu balle dan, idan kuma na rayu na haifi mace ta warware abinda taima su Ashwaq su sami ciki wata a cikinsu ta sami da namiji, dan dama dai tun farko ita ta hana Haysam haihuwa saboda abinda Mammah take mata. Cikin riko da magiya nace mata dan ALLAH ta bani, indai nice na amince, koma mi tazo da shi zan amsa. Sai da ta jadadada min sau uku nima na

amsa mata sau uku. Maganin ta bani nasha kadan ta karbe abunta sai ko na samu lafawar ciwon, harna samu damar zaman saurarenta. Ta ce da ni (Bushirat ke ce kika kawo kanki gareni ban gayyatoki ba, kika kuma zo min da bukatarki ta magance miki ita?) Kai na daga mata alamar hakane, taci gaba da fadin (Gadai abinda kike nema nan kin samu, da ga yau zuwa gobe sunanki ya koma *_MALIKAT BUSHIRAT ne, zaki samu girmamawa da ga kowa. Ada nayi alkawarin hana Haysam gadar sarautar kujerar Shahan-shan, dan in har bashi da magaji ko ubansu mutuwa yay bai isa hawa ba. 

Amma a yanzu saboda ke na janye komai, Zan hukunta Abdul-majeed da Haseena akan laifukansu su da zuri'arsu, amma ke kam kin tsira keda danki, zan baku gata zan maidaku yan lele) godiya na mata cike da jin dadi. Cigaba tai da fadin, (Sharadina na farko bayan kin haihu zan dauke mahaifarki gaba daya, dan wanna dan kwara daya ya isheki yakar kowa a masarautar nan, sannan haihuwarsa shi kadai a nufin shine kawai magajin wanna masarauta) na amince Uwa. Na bata amsa babu wani tunani ko kyakykyawan nazari. Murmushi

tayi tamun jin jina. Ta cigaba da fadin, (Sharadi na biyu bayan haihuwarsa zakiyi yankan bakaken shanu guda goma, rakuma mata da basu wuce shekara uku da haihuwa ba suma goma zaki soke. Sai bakaken karnuka) anan ne na dani diri-diri da jin karnuka, amma sai tai saurin fadin (Karki damu su wannan karnuna zaki yankasu domin kariyar duk wani cutarwa da wani zai kawoma danki ne, dan kina haihuwar magaji tofa babu mai zama haka kuma bayanki za'aita yunkurin gani ke da dan) hakane kuma uwa. 

Na gane mi kike nufi na amince. Na bata amsa cike da gamsuwa da bayanin ta. Nan ma tayi murmushi da cigaba da fadin (Zaki cigaba da wannan yanka ne duk bayan watanni shida, sannan zaki sadaukar da jinin macen hadima mai dauke da ciki karami bayan ya cika wata uku, idan ya kara wata wata ukun zaki sadaukar da hadimi mai sabon aure da basu wuce wata daya ba shima) nan ma nadan shiga rudani amma ta nunamin idan bana bukata zatai gaba, ai duniya babu abinda ake iya samu cikin sauki. Sannan kuma bawai tace na kashesu bane da kaina, nawa kawai shine bata sunansu, sauran aikin nata ne) nifa matsalata kawai shine a haifi magaji, na zama abar kwatance akan karfin iko fiye dana Malikat Haseenat dan haka na amince. 

Ta cigaba da fadin (Saradi na biyu lokacin da yake cika shekaru goma sha biyu a duniya zakiyi kokarin a hada aure tsakanin wani makaskancin talaka da wadda kukafi shakuwa a kannen Haysam idan an samu ciki aka samu kuma mai tambarin zuri'arsu a gado bayan kwana uku zamu amshe yarinyar, inma babu tambarin ma dai ahakan zamuyi, za kuma mu kauda Abdul-majeed a doron duniya Haysam ya gajesa. Haysam zaiyi mulki na tsahon shekarun girman danki, yana cika shekarun gadar mulki zaiyi murabus ya daurasa. 

A ranar nadin zamowarsa Shahan-shan za'a aura masa mata hudu, matan nan dukansu zasu zama sadaukarwarmu tare da Haysam, dan in har yana raye tofa zaki cigaba da zama yar kallo ne sai abinda Haseenat tace danki ma yayi zai yi.…..) Da sauri nace na amince, dan bazan taba iya cigaba da zama karkashin ikon wata ba bayan kuma dana ke mulki. Tayi murmushi a lokacin da fadin (Shiyyasa nake jinki kamar yar dana haifa a cikina ta-kurya. 

Zan saki ki zama mai nasara kuwa bisa nasarar kowa. Wannan yaro da zaki haifa zai cigaba da aure muna kauda matan har sai sun cika adadin da zasu zama ginshikin rike karagar mulkinsa. Da ga karshe zamu kawo masa matar aurensa da zata zama duk wani motsinta sai da umarninki ne, koda ta haifa masa magaji kece zaki cigaba da amsa suna MALIKAT.

 Dan hatta shi a karan kansa ko hukunci bazai iya zartarwa ga wani ba sai da umarninki. Ki kula ki nutsu kisa hankali a jikinki a duk aure-auren sa kada ya auri wata mai alaka da zuri'arsa, idan kuma har kikai hakan to komai ya lalace kenan, duk wahalarki ta tashi a banza, mu kuma bazamu taba amsar kuskure ba, in har kika

gagara cika wadan nan sharucidan namu zaki bamu

madadinsu ne da jinin abinda zaki haifa, dan shine diyyar kuskurenki. Kuma shine hukuncinki) hankalina ya matukar tashi dan duk duniya a yanzu babu abinda nafi so kamar abinda ke cikina din, a shiga rokonta da magagiya. 

Ta tabbatar min itafa saina kuskure mata ne zata aikata hakan, dan bijirewar Abdul- majeed ga ayyukanta bisa shishshigin matarsa yasa zatai masa hukunci da mutuwa da mutuwar dansa (Haysam) da ya fi so, zakuma ta tabbatarma Mammah ita ba komai bace a wanna masarautar shiyyasa ta hanyar yayan da take takama da su, dan haka Ammarah ce zata zama wadda za' "aima auren sati biyu ta haifi yar da muke bukata, dama ta kashe Miran Nayyar a cikin ruwan swimming pool na gidan, Waheeda kuwa dama bawani tanada zuciya mai kyau bane kanta kawal ta sani dan haka bata gabanta, Jin wanna kashe-kashen hukunci da zatai ga zuri'ar Mammah saboda abinda Sukai mata a bijirewa yasa na karajin tsoronta, dan haka na amince ga dukkanin shardanta. Ta bani magani nasha, tare da tabbatar min zata kaworin hadimar da zata kasance amintacciyata wajen gudanar da ayyukana. Dan dolene zan boye kaina tsahon rai batare da kowa yama taba kawowa kansa nice ta-kurya ba. Koda kuwa a cikin hadiran da zasu dingamun aiki ne matsayin ta-kurya, Bayan tafiyarta haihuwa ta tashi gadan-gadan, Alhamdullah na haifo yarona namiji mai kamanina dana Haysam.

 A hankali, abinda duk ta fada ya cigaba da tabbata, babu wata matar Haysam da ta kara koda kwatanta samun ciki, dan haka na kara sakankancewa da ita, duk kan umarninta na fara cikasu kamar yanda ta bada, kuma komai na tafiyamun babu wata damuwa har zuwa lokacin da aka dauke Eshaan daga gabana. Ta nuna bacin ranta, kamar yanda na nuna damuwata, sai dai duk wani kokarin mu babu wanda ya saurareni, da Mammah ce ma, itama daga baya ta bada goyon bayan dauke san. Duk da tafiyace ta wani shekaru naji zafinta, sai dai bana iya cika wata guda banje na dubeshi ba. Yawan zuwana yasa Abbu (Tajwar Abdul-majeed) yayi magana a lokacin, aka kuma sakamun dokar sai bayan shekara-shekara. 

Naci kuka a ranar amma uwa ta kwantar min da hankali akan daukar mataki da tabbatar min ba sai yana raye dokar zatai aiki ba.Lokaci yayi da Ammarah zatai aure. Da taimakon su Miran Jasim aka cika wanna aikin, bayan wucewar su Mammah Umrah. Anyi auren Ammarah an kuma samu cikar burin samun ciki. Bayan dawowarsu an kwashi rikicin da har yay sanadin kai Jasim kurkuku. 

Da ga baya dai komai ya lafa Ammarah ta haihu. Bayan haihuwarta abubuwa suka nema cabewa dalilin samo wani hatsabibin mutumn, sai dai duk da haka muni nasarar mallakar abinda ta haifa da kuma kauda Abbi (Shahan-shan Abdul-majeed) nafi kowa jin ciwo da shiga tashin hankalin abinda akaima Uwa a masarautar nan dan ranar ni nasan irin kukan da naci na tashin hankali. Kwatsam bayan na gama fidda rai da rasa uwa a wata raar da Haysam ke cika shekara uku da hawa karagar mulki sai ga uwa ta bayyana.Farin cikine ma da bazan iya musaltashi ba, itama har taitamun dariya, ta kuma nuna jin dadinta da yanda na damu da rashin ta, ashe tanada y an leken asiri da ke kai mata rahoton komai a shekarun nan da bata nan…✍️

2 Comments

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post