Daudar Gora book 2 page 89

Daudar Gora book 2 page 89

 

Daudar Gora book 2 page 89

DAUDAR GORA 

Book 2

Page 89

...... Suna shiga bedroom din sa ya wani irin rungumeta tsam-tsam a jikinta tamkar zai maidasu su zama abu guda. Yanda Iffah kejin gudun zuciyarsa da bugawarta hankalinta ya tashi matuka. Tayi yunkurin dagowa ta kallesa amma yaki bata koda kankanuwar dama. 

Sosai numfashinsa ya fara fisga, gashi ya ki sakinta balle ta bashi wani taimako, mutsu-mutsun kwatar kanta take amma ta kasa. Sai kawai ta fashe masa da kuka. Sakinta yay da sauri, sai dai bai yarda sun hada ido ba ya rabata ya wuce. Gaban window yaje ya tsaya kawai ya tsirama harabar masarautar ido. A gurin Iffah ta durkushe ta cigaba da kukanta. Tsahon mintuna goma suna a haka sautin kukanta kawai ke ratsa dakin, shiko yana a inda yake tsayen kamar gunkin da aka dasa domin tarihi. Mikewa tai itama jin jiri ya fara dibar idanunta, dan akwai yunwa tare da ita, rabonta da abinci tun jiya. A bakin gadon ta zauna jagwaf, ta dafe kanta tsahon minti daya kafin ta janye.

 Ciwo hannayenta ke mata sosai saboda matsar da suka sha a wajensa, har sun dan kumbura dan matsar bata wasa bace. Jin sun mata tsami babu dadi ta shiga murzasu a hankali ko zataji sassauci. Bata san sanda ya baro wajen window din ba, ganinsa kawai tai durkushe gabanta ya kamo hannun nata a cikin nashi. Kallo daya taima fuskarsa tai saurin dukar da kanta, dan idanunsa sun yi masifar firgitata. Sun yi wani irin kadawa jazur irin wanda bata taba gani ba,hakama fuskarsa gaba daya tayi jazur kuma babu alamar yayi kuka, kawai tsabar tashin hankaline ta sauya masa kamanni. Hannayen ya shiga murza mata a hankali, kafin tsahon lokaci kamar wanda aka fisgo furucin da ga halshensa ya ce, "I am sorry".

   Da sauri ya dago ta dubesa, ganin yanda ya tsurama tafin hanunta idanunsa masu ban tsoro yasata jin hawaye sun sake cika mata ido. Dayan hanunta ta daura akan habarsa mai cike da lallausan bakin gashi ta dago, cikin dauriya da dakiya ta saka idanunta cikin nasa, muryarta na karkarwa ta furta, "Dan ALLAH kayi kuka koda kadanne Zakina. Kayi kuka! kayi kuka!! kayi kuka!! Zan shanye hawayen a cikina na adanasu cikin manyan SIRRIKANKA da ka bani ajiy....."

   Kafin tama kai karshe sai ga hawaye sharrrrr da ga idanunsa kamar an bude fanfo, wani irin murmushi mai tsananin ciwo da kuna ya sakar mata hawayen na kara gudu. Da sauri ta tara hannayenta suka sauka a ciki, kallon tafin hannun nata da hawayen nasa ke sauka yayi, sai ya sake fashewa da kukan, hawayen na cigaba da sauka a cikin tafin hannun nata. Sai da suka taru sosai sannan tasa harshenta ta shiga lashe hawayen tana hadiye tare da fashewa da sabon kukan itama. Kansa ya daura a saman cinyarta yana zaune da ga kasan lallausan carpet din gaban gadon itako tana daga zaune a kan gadon, itama sai ta daura kan nata a kan nasa suka cigaba da kukan a haka zabban tausayi…

    Bayan sallar azhar da ya kasa fita saboda zazzabin da ya rufesa mai zafin gaske itama ciwon ciki ya takurama Iffah na jin yunwa, abinka da ba ita kadai ba.

 Haka ya tashi cikin kakkarwar sanyi ya bata madara ta sha, tana sha ta amayar da ita, a hakan dai ya taimaka mata cikin karfin hali ta gyara jikinta, sake bata madarar yay tasha kadan, shima sai ta takura masa wai sai ya sha dan rabonsa da abincin kirki tun jiya. Kin sha yay ta sanya masa kuka, dole yasha rabin kofi ya kauda kansa, da ga haka suka dunkule waje daya kwance zafin jikinsa na matukar ratsata. Ganin zazzabin baida alamar sauka sai ma karuwar da yake yi yasa Iffah kiran Sayeed Fayzul-haq. Babu bata lokaci suka iso da Doctor Afif da ke matsayin amintaccen likitansa. 

Doctor Afif din kansa sai da hankalinsa ya tashi gain yanda jinin Shahan-shan din yay wata irin kololuwar hawa, ga bugun zuciyarsa har ya canja. Cikin sauri ya danna masa allurar barci mai matukar karfi dan in har aka cigaba da zama a hakan akwai babbar matsala kam. 

Da farko kin yarda ma yay ayi allurar sai da Iffah ta sanya masa kuka sannan ya kauda kansa kawai baice komai ba. Sai Sayeed Fayzul-haq ne yay ma Doctor din nuni da yayi aikinsa dan kauda kan nasa a nufin amincewa, Iffah dai na zaune ne kansa a saman cinyarta tanata faman sharar hawaye. Duk da karfin allurar ya jima baiyi barcin ba, dan sai da Iffahr ta hada da tofa masa addu'oi sannan aka dace barcin ya daukesa.

    Haka ta cigaba da zama kansa a saman cinyarta har aka kira sallar magrib, kafafunta duk sunyi tsami,da kyar ta gyara masa kansa ya koma kan fillo, sannan ta mike ta gabatar da sallar magrib din. Alkur'ani ta dauka ta shiga raira karatu a nutse tana hawaye, bata ajiye ba har aka kira sallar isha'i nan ma ta gabatar. 

Ta jima tana addu'oi akan wadan nan al'amura da suka cure musu, tashinta babu jimawa Malikat Haseenat da Daneen Ammarah da Daneen Waheeda da Iftihal sukazo dubashi. Basu shigo ciki ba iyakarsu falo, Iftihal nata yan kalle-kalle dan wanna shine karo a farko a rayuwarta ma data shigo sashen nasa. Iffah na fitowa ta wani dukar da kai dan ita kam tsoranta takeji matuka yanzu. 

Cike da kauna da tausayi Malikat Haseenat ta rungumeta, kafin ta dagota da fadin, "Hafida-ti kema ai ba lafiyarce da ke ba ma, dan zazzabin ne a jikinki. Kin ma ci abinci. Idanun Iffah cike da hawaye ta girgiza kai da fadin, "Na koshi Jaddah".

    "Bazai yiwu ba dan bake kadai bace. K Iftihal hadomin abinci mai sauki acan. Cikin rawar jiki Iftihal ta nufi dining room, har yanda tai din ya bama Daneen Waheeda haushi sai dai babu damar magana. Babu jimawa ta kawo abinci, Malikat Haseenat ta amsa da kanta ta na bama Iffah'r. 

Da kyar take amsa da taunawa kamar magani, batafi cokali hudu ba tace ta koshi. Lallabata Malikat Haseenat da Daneen Ammarah suka shiga yi, da kyar ta kara biyu, daga haka suka shiga lallashinta da nasihar ta kwantar da hankalinta, dan saita kwantar da hankalin natane shima zata taimaka masa ya kwantar da nasa. 

Ta gamsu da nasihar tasu, anan ma takejin Ummu sun wuce, Malikat Bushirat ma jikin nata ya sake rikicewa yanzu haka ga likitoci can sun kasa shiga su dubata dan kurajen jikinta nata cigaba da fashewa warin na kara karuwa. Batace komai ba illa hawaye da suka zubo mata sharr. 

Wanna ranar ita take guje mata, gashi tun kan aje ko' ina kuwa har tazo din. Basu wani jima a sashen ba suka tafi, haka ta koma dakin ta zauna ta saka Tajwar Eshaan gaba tana tofa masa addu'oi da fatan ALLAH ya sanya masa nutsuwa da Karfin zuciya akan al'amarin. 

Haka dai ta kasance bata wani samu isasshen barci ba, koda ya farka cikin dare da taimakonta ya samu yay salloli, ta debo masa abinci amma yaki ya ci, sai da ta fara masa kuka ya danci spoon biyu shima dole ta hakura ta kyalesa dan barcine bai gama sakinsa ba.Dan haka ya koma ya sake kwanciya……

   Gabanin asuba wan irin ihuface-iface na tashin hankali ya farkar da ita, zumbur ta mike kamar wadda aka tsungula. hun yayi yawa matuka dan haka ta fita a razane, ALLAH ma yaso doguwar riga ce ta abaya a jikinta. 

Hadiman sashen Shahan-shan din duk wasu sunyi barci ma, sai jami'an tsaro dake kai kawo a ta waje da Ghazi. Sai dai duk an firgitasu ashe sune keta hun, Wani irin sarawa kan Iffah yayi, a take ta birkice alamar mutanen sun zo. Wani irin jan takobin dake a hannun masu tsaron kofar shiga falon farko na kasa Iffah tai da ga cikin kubenta ji kake wani zuuuuuu!! 

Sharbebiyar takobi ce mai tsananin walkiya da tada tsigar jiki, tuni tayi tsakkiyar masarautar ta wani irin karta takobin bisa kasa. Kamar yanda mafi yawan mutanen masarautar sukaji wanna tashin hankali haka sukaji karta takobin da Iffah tayi akan kasa da yin wani irin kara ji ta ce. Duk wanda ya shirya idan ya isa yazo gabanta. 

Saiko ga kusan mutum hudu sun bayyana gaban nata tsirara sai dan ganye a gaba suna wani irin huci da bulbulo da wutar tsafi ta baki, Juyi ta sake. yI, da wulwula takobin ta cake akan kasa, kafin tai wani irin zarota tai juyi bakinta na ambaton sunan ALLAH tamkar kyattawar ido sai ga kawunan shegun a kasa hudu reras. Zo kaga ihu, ga hadiman da duk suka farka saboda tsabar tashin hankalin firgitasu da wadan nan mutane sukayi, wanda sune a

daren jiya suka shigo sukai musu kisan gilla dama. Ba kowa bane kuwa face a cikin zuri 'ar su uwa. Tuni fa masarautar ta kara rikicewa, wanda ma bai farka ba sunata farkawa. Can sai ga Jasrah ta fito cikin kuka da kururuwar an dauke Malikat Bushirat.

 Ba kowa yasan mike faruwa akan Malikat Bushirat din ba sai su shakikanta, duk da dai dazun anga duk ahalinta sunzo gidan, sannan Malikat Haseenat ta fito ranta a bace da sashen ita da Daneen Ammarah. 

Dama Daneen Waheeda bataje ba dazun din dan haka maganar dai har yanzu bata fita akan tsiyatakun da Malikat Bushirat din ta fada ta aikata da bakinta ba. Kowa dai nata hasashe da son bin kwakwkwafin al'amarin.

 Masarautar ta rude gaba daya, ALLAH dai yasa itama Daneen Ammarah da nata kwankwaman a ka da kyar ta rike Iffah. Barci dai a wannan dare yara kanana ne da basu san komai ba a wannan masarauta suka yisa. Dan tuni shima Tajwar Eshaan ya farka. Tun a daren Iffah tai kiran kaka a waya, asubar fari kam a cikin masarautar ta masa. Ana idar da sallar asuba aka shiga meeting na gaggawa. Kaka, Iffah, sai manyan masu fada ajin masarautar irin su Sayeed Fayzul-haq da sauransu........✍️

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post