π™π™π™π˜Όπ™ π˜Ώπ˜Όπ™‰π™†'π™Š.....!! π‘©π’Šπ’π’šπ’ 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 π’„π’†πŸ€™πŸ» π‘ͺ𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 1

π™π™π™π˜Όπ™ π˜Ώπ˜Όπ™‰π™†'π™Š.....!! π‘©π’Šπ’π’šπ’ 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 π’„π’†πŸ€™πŸ» π‘ͺ𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 1

 

π™π™π™π˜Όπ™ π˜Ώπ˜Όπ™‰π™†'π™Š.....!! π‘©π’Šπ’π’šπ’ 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 π’„π’†πŸ€™πŸ» π‘ͺ𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 1

π“π²π©π’π§π πŸ“²

  πŸ«— π™π™π™π˜Όπ™ π˜Ώπ˜Όπ™‰π™†'π™Š.....!!πŸ«—

           π‘©π’Šπ’π’šπ’ 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 π’„π’†πŸ€™πŸ»

π‘ͺ𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 1

*Ψ¨ِΨ³ْΩ…ِ Ψ§Ω„Ω„َّΩ‡ِ Ψ§Ω„Ψ±َّΨ­ْΩ…َٰΩ†ِ Ψ§Ω„Ψ±َّΨ­ِΩŠΩ…

_Da sΕ©nan ALLAH, Mai rahama, Mai jin Ζ™ai._

........Ƙarfe uku da mintuna ashirin da biyar jirgin daya taso daga birnin tarayyar Nigeria Abuja ya sauka a *_AMINU KANO INTERNATIONAL AIRPORT_* da ke a Kanon dabo. Cikin nutsuwa duk wani passenger dake a cikinsa suka fara fitowa. Vvip section Ζ™yaΖ™Ζ΄Ζ™yawar budurwa dake cikin ado mai tsananin Ι—aukar idanun duk wanda ya kalleta ta miΖ™e a hankali tana Ι—an wani Ι“ata fuska tamkar mai jin warin mutane. Sanye take cikin wasu shegun wando da riga da sukai tsananin fidda cikakkiyar surarta musanman ma wandon jeans Ι—in da ya kasance fari tas, an Ι—an faffasashi daga cinyarta da gwiwa har ana iya ganin kalar fatarta. Siririn veil kalar pink mai haske da yay dai-dai da kalar rigar jikinta shima data Ι—an yana a saman kanta ya matuΖ™ar Ζ™awata adon nata da fidda zagayayyar fuskarta, sai bag fara tas da adon stones pick and blue daga gani kasan mai tsada ce. Ga wani shegen takalmin mai tsananin tsini sai dai ya matuΖ™ar Ι—auki Ζ™afar tata musamman da wandon ya kasance baije Ζ™asa can sosai ba kuma yabi jikinta ya lafe luf sai ya bama siririyar sarΖ™ar Ζ™afarta da taji adon stones pink and blue damar fitowa Ι—ar. Yanda ta rufe idanunta da eyeglasses blue ya Ζ™ara saka fuskarta kwarjini da bayyana Ζ™yawunta mai sanyi, sam fuskarta babu alamar wata fara'a, sannan babu kwalliya ko Ι—igo idan ka cire Ι—an lipstick kalar pink mai shining data zizara ma laΙ“Ι“anta. A kallo Ι—aya zaka Ι—auka bata san minene ko murmushi ba, sannan zaka iya kiranta da Ζ™abilar kudancin Ζ™asar, dan babu ta inda tai kammani da Hausawa ko yankin arewacin Ζ™asar musamman inda addinin Muslunci keda Ζ™arfi irin su kano. 

          A hankali taja Ζ™aramin tsaki dai-dai tana miΖ™ewa da tura wayarta cikin aljihun wandonta, headphones Ι—in kunnenta kalar pink ta gyarama zama, tare da gilashin idonta sannan ta ciro ledar chewing gum ta Ι“are ta jefa a baki tana ballama saurayin dake ta bayanta kaΙ—an harara, tun Ι—azun ya dameta da kallo dan jaraba har zuge labulen da ya rabasu yayi. Bag Ι—inta ta fisga ta Ι—ora a kafaΙ—a Ι—aya sannan ta Ι—auka Apple laptop Ι—in ta tana sake jan siririn tsaki ganin shima ya miΖ™e tai ficewarta cikin takunta na Ζ΄ammata marasa jin magana..


          Yanda take taku tsinin takalmin nata na bada wani irin sautin jan magana, ga sautin madaidaicin akwatinta da take gungurawa tamkar a gajiye ya jawo hankalin mutane da yawa gareta. Caaaa idanu da yawa a kanta, wanda basu iya gani suyi shiru tuni sun fara tankawa, wasu Ζ΄ammatan kuwa kishine ya lulluΙ“esu, yayinda samari da yawa sukai mutuwar tsaye da ganin wannan Ζ™yaΖ™yΖ™yawar halitta. Ita dai daka ganta kaga cikakkiyar baΖ™ar fata haihuwar Africa sai dai Ι—abi'u da shiga duka ba namu bane. Ga wani shegen Ζ™amshi da duk wanda ke a kusa da ita kaΙ—an dolene ya jisa saboda yanda ta bulbulashi kamar ba mace ba. A yanda take juya madaidaita lips Ι—inta a taunar chewing gum Ι—in bakinta kawai dole ya tada hankalin mai kallonta. Dan duk namiji mai tsantseni ya dubeta sau Ι—aya bazai sake yarda yay na biyu ba kodan tsoron ALLAH... 

       *_Mawaddat Isma'il Ibrahim JiΖ™amshi_* kenan da akafi kira da suna _Lulu Ζ™amshi_ Ζ™yaΖ™yΖ™yawar budurwa mai kimanin shekaru ashirin da huΙ—u a duniya. Itace Ι—iya ta uku a gidansu. Mahaifinta sananne ne da kowa yafi sani da Engineer Isma'il l. JiΖ™amshi. Babban Ι—an kasuwa ne kuma mamallakin *_JiΖ™amshi Motors_*. Mawaddat yarinya ce da batajin magana, gata masifaffiyar gaske ta bugawa a jarida. Ζ³ar gata ce shalele kuma Ζ΄ar shagwaΙ“a a gidansu musamman wajen mahaifinsu Engineer Isma'il Ibrahim JiΖ™amshi da Kawunta Yousuf Ibrahim JiΖ™amshi. Gatan data samu da rayuwar turai data tashi a ciki ya sata zama fanΙ—ararriyar gaske. Ga rashin kunyar tsiya. Dan kowace irin shiga Lulu Ζ™amshi zata iya fita da ita waje ko zama a cikin gida in har ba Uncle Ι—in su Yusuf yana kusa ya tsawatar mata ba. Mawaddat ta samu wadataccen ilimin boko, dan a yanzu haka ita Ι—in lawyer ce mai zaman kanta, duk da dai karatun ma da Ζ™yar ta iya kammalashi saboda rashin jinta, gaba Ι—aya karatunta a Ζ™asar Ζ™etare ta yisa idan ka cire Nursery school datai a Nigeria. Sai dai a Ι“angaren ilimin addini kam fanko ce, dan ko faatiha Lulu Ζ™amshi ba lallai ta kawo maka ita dai-dai ba. Sam bata son harkar talauci, ba kuma ta son talaka. Abu Ι—aya ne ALLAH ya taimaketa da nisantata da shi duk da rayuwar turai data tashi a ciki, shine kasancewa da namiji. Ko kai Ι—an uban waye a kuΙ—i ko nasabar zuri'a baka ishi Lulu Ζ™amshi kallo ba, dan ko turawan sun buga sun barta kam, hannunka ma yace zai yi gigin zuwa jikinta komai shigar rashin mutuncin da tai zata sauke maka kwando-kwandon masifarta. Ta dai yarda ta shiga club aci uban rawa ayi nishaΙ—i tai gaba. Sai sirrintaccen harkar da takeyi da har yanzu babu wanda ya sani a gidansu, dan tana aikatawa ne cikin taka tsantsan da kula, shiyyasa har yanzu babu wanda ya ganota duk da an Ι—an taΙ“a samun akasi tsakaninta da Uncle Yousuf dai ya kusa harbota ta kuΙ“uta da Ζ™yar.


     Wannan itace Mawaddat Isma'il JiΖ™amshi (Lulu Ζ™amshi) a taΖ™aice.


         Saurayin nan da suke tare tun daga cikin jirgin sauri yake na son cin mata, duk da yanda take takun nata cike da yauΖ™i da yanga. Wannan ita kaΙ—ai ce damar data rage masa, gashi kuma tana neman kufce masa. Tunanin hakan babbar asarace a garesa ya sashi Ι—aga murya wajen faΙ—in, 

       _“K! Sarauniyar mata. Son kowa ki dakata mana!!”._

    ƁuΙ—aΙ—Ι—iyar muryarsa da tsarin adon dake nuna shima Ι—in wani shege ne ya saka mata da yawa tsayawa cak, sai kuma suka shiga juyawa suna kallonsa. Sai dai abin mamaki ita ko nuna lamar ma tasan yanai batai ba tafiyarta take. Ganin ya cigaba da Ζ™oΖ™arin cimmata Ζ΄ammatan da duk suka juya garesa suka shiga taΙ“e baki da yatsine fuska. Ko kallo basu ishesa ba sai Ζ™oΖ™arin cimmata da yake yi dai-dai tana Ζ™oΖ™arin isa ga inda motocin Ι—aukar mutane keda hurumin tsayawa. Wani shegen kallo ta watsa masa fuskarta na sake tsukewa.

      Fuska ya marairaice yana mai haΙ—e hannayensa waje guda alamar roΖ™o gareta, amma saita ja masa tsaki zata cigaba da tafiyarta. Sake shan gabanta yayi da faΙ—in, “Haba mana Babie ki saurareni koda akan abu Ι—aya ne Please. Address ko phone number abeg you”.

           Cike da yauΖ™i da yanga ta furta, “A matsayinka na wa?”.

Duk da yay mamakin jin hausa a bakinta sai ya shanye, cikin murmushi ya ce, “Neighbour naki a jirgi mana beauty!. Sunana MM Atik Kumo. Mahaifina M Atik Kumo sunane da duk wanda ya kwana ya tashi a Nigeria dama Ζ™asashen Africa ya sansh.....”

     “Kai dalla can ka isheni da zance yannn-yannn!! kamar tsohuwar akorukura. Bani hanya kona wanke banzan face Ι—in nan naka zubin alakoro da mari stupid”. Ta faΙ—a cikin katsesa da yarfi ta bi gefensa ta wuce. Tamkar gunkin da aka sassaΖ™a domin tarihi haka yay tsaye Ζ™iΖ™am yana kallonta, hakama duk wanda ke kusa da su sai da yay mutuwar tsaye akan abinda tayi. Dan kowa dai yasan wanene sunan MM Atik Kumo, amma yarinyar nan mai zubin yahudawa tai masa wannan yarfin. Kuma ko'a jikinta kamar yanda shima babu alamar zai Ι—auki wani mataki.....


       “Laahhh *_Uncle Smart_* ga Aunty Lulu Ι—in nan”.

   Wani Ι—an Ζ™yaΖ™yΖ™yawan yaro dake saman jibgegiyar mota baΖ™a siΙ—ik ya faΙ—a yana nunata. Wanda ya kira Uncle Smart dake gefensa tsaye kansa a Ζ™asa da keypad waya Ζ™irar Nokia a hanunsa ya Ι—ago a hankali tamkar mai ciwon wuya.........✍️



_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_


*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*


FURAR DANKO

Billyn Abdul


-ZAFIN KAI

Mamuhgee


-TABARMAR ‘KASHI

Safiyya Huguma


-BAKON MUNAFIKI

Miss xoxo


Duka hudu 1k

Uku 800

Biyu 600

Daya 400


Pay atπŸ‘‡


1487616276 

Access Bank

Bilkisa Ibrahim

Sai katura shedar biyanka ananπŸ‘‡


09032345899


Idan katin waya ne kuma saika tura ananπŸ‘‡

09033181070


VIPπŸ”₯πŸ’―

Zafin kai 3k

Furar danko 3k

Tabarmar kashi 3k

Bakon munafuki 3k

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*πŸ₯°

Zafafa🫢πŸ”₯

*_ALLAH ya gafartama iyayenkuπŸ˜­πŸ™_*

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post