ππ²π©π’π§π π²
π« ππππΌπ πΏπΌππ'π....!!π«
π©ππππ π¨ππ πππ πππ€π»
πͺππππππ 2️⃣
........Ζyakykyawan saurayi ne chocolate color mai cikar kamala da nutsuwa. Baida hayaniya a yanayinsa na zahiri bai kuma da fara'a sam akan fuska. A halittar jiki da cikar kamalar fuska mai nuna barazana ko maΖiyinsa dole ne ya yarda yaci wannan suna na *_Smart_*. Maimakon kallon wadda yaron yay nuni da kira Aunty Lulu sai ya Ιaga shi cak ya sauke Ζasa kawai tamkar ma baiji ba. Da gudu kuwa yaron ya nufeta cikin farin ciki da ihun kwakwazo yana mata oyoyo Aunty Lu.
A hankali ta saki murmushi daya Ζara Ζawata Ζyawun fuskarta a karo na farko tana mai tsayawa cak har yaron ya Ζaraso gareta. Yana dab da zuwa gareta ta ajiye laptop Ιinta a saman akwatin dake Ιayan hanunta ta tarbi yaron. Dai-dai nan MM Atik Kumo da ya biyota ya Ζaraso wajen. A hankali murmushin dake a saman fuskarta ya fara Ιacewa, cikin ΖanΖanin lokaci fuskarta ta koma asalin yanda take. Cikin fushi da tsananin Ιacin rai ta watsa masa kallon nan nata na raini da wulaΖanci. A fusace ta furta, “Halan kai babu zuciya a Ζirjinka? Nifa a duniya na tsani wasu *_MAYUN MAZA_* wlhy”.
_(Mayun Maza!!!)_ Kalmar tai wani irin amsa kuwwar maimaita kanta a cikin kunnensa duk da bashi aka faΙawa ba. A hankali ya Ιago fararen idanunsa masu girma karan farko ya saukesu a kanta. Dai-dai nan itama cikin tsiwa ta nuna MM Atik Kumo da yatsanta mai Ιauke da farce data Ζara a duk farautan hannuwan nata biyu da Ζafafu. Ζauke idanun nasa yay da sauri wani irin sukar baΖin ciki na tokare Ζirjinsa, a duniya ya tsani mace irinta da zata iya saka kowane irin kaya ta fita kamar yanda take, tun daga samanta har Ζasa babu suffar mace musilma bahaushiya a tare da ita. Siririn tsaki yaja yana sake tamke fuska sai dai kunnensa na garesu.
Itako da bata san yanayi ba yi take kamar zata tsole ma MM Atik Kumo ido da yatsanta data nunashi da shi. A cikin kaushin murya take faΙin, “Wlhy! wlhy! idan ka sake gigin zuwa gabana a karo na uku saina wulaΖantaka a wajen nan, mafi munin wulaΖanci, na yaga maka rigar mutunci kuma, danni *_FURAR DANΖO CE, A SHEKARA ANA DAMU BA FARAU-FARAU!!._* Mtsowww ban san damuwa ok”. Fuuuu ta figi hannun yaron da ya tsaya kawai yana kallonsu tare da lap-top Ιin ta tai gaba batare data ja akwatin ba.
Babu alamar gargaΙin nata ya zafi MM Atik Kumo, dan wani murmushin ma ya saki da bin Ζugunta da kallo a ransa yana maimaita kalmar _(Furar danΖo a shekara ana damaki baki farau-farau)._ Wani shegen yawu ya haΙiye yana lumshe idanunsa da suka wani ΖanΖance tare da lashe lips Ιinsa.
A gaban motar da Uncle Smart ya ke tsaye taja birki, cikin hucin takaici tai masa kallon sama da Ζasa fuska a yatsine. “Kai kuma malam haka ake aiki a garinku? Kana kallon mutane da kaya bazakaje ka amsa ba!!?”.
Idan motar nan ta motsa to shima da ke jingine a jikinta ya motsa. Wani irin baΖin cikine ya sake turniΖe mata zuciya, “Kai sakarai kai waye da har ina maka magana zaka Ιauke mun kai? kan bala'i.....!”
Da sauri yaron ya katseta da faΙin, “Aunty Lu! Uncle Smart ne fa! Shi bai san ihu, muma idan zai kaimu school ca yake muyi shiru a mota, kuma Daddy ma baya masa ihu ki bari kem.....”
“Kai dalla yimun shiru. Shi Ιin waye da baza'a masa ihu ba. Shashasha da shi driver mai jiran wata tayi a bashi dubu goma”.
Ζwal-Ζwal yaron yay da idanu kamar zai yi kuka. Ya kalleta ya kalli Uncle Smart Ιin da ya Ιauke kansa kamar ma bada shi take ba. Itako idanu rufe ta cigaba da zazzaga masa masifa kamar mai jiransa dama. Da yawan mutane hankalinsu ya fara dawowa kansu. A hankali ya raba jikinsa da jikin motar, batare da ya sake mata kallo na biyu ba bayan wanda ya mata sanda take gaban MM Atik ya buΙe motar ya shige abinsa, da wani irin Ζarfi ya fisgeta yay reverse Ιin daya saka taron fashewa ganin zai takasu, fuuuu ya Ιace da ga wajen yay hanyar fita airport Ιin baki Ιaya..
Tuni wasu da abin ya birgesu suka shiga ΖyalΖyala dariya da faΙin hakan da yay ya musu dai-dai. Wasu ko mamakin Ζarfin halinsa sukeyi. Duk da dai tabbas guy Ιin ya haΙu iya haΙuwa, sai dai duk wanda ya kalli uniform Ιin dake jikinsa ya san kalmar driver data kirashi da shi kam gaskiya ne. Wasu ko dariya suka shiga kwasa da yaΙa mata baΖar magana musamman ganin wulaΖancin da taima MM Atik Kumo da har yanzu yana tsaye a wajen duk da body guard Ιinsa da sukazo suka zagayesa shima yana kallon komai.
Lulu da gaba Ιaya ta koma butum butumi da wulaΖancin driver Ιin nata tuni jikinta ya fara tsuma. Numfashinta har wani irin fisga yake dan Ιacin rai, da sauri MM Atik ya matso gareta, yayinda security Ιinsa suka fara yima mutane nunin su tafi dan ALLAH. So yake yace wani abu amma wlhy shi tsoronta ma yake ji, bai taΙa ganin masifaffiyar yarinya irinta ba, ga azabar kwarjinin tsiya kamar wata babbar mace mai shekarun dattijantaka. Da Ζyar ya iya furta, “Please calm down Babie...”
“AnΖi ai Calming down Ιin kai kuma!. Har ni sakarai irin wancan guy Ιin mai aikin tuΖi a gidanmu ΖarΖashin ikona zaima wannan walaΖancin? Mi yake taΖama da shi....?” Da sauri yaron nan yace, “To Aunty Lu bana faΙa miki Uncle Smart baya son ihu ba ki daina masa...” Hannu ta Ιaga zata fallama yaron mari MM Atik ya janyesa da faΙin, “Please Babie karki aikata haka”. Idanu ta rumtse da masifar Ζarfi dan kuka ma take jin yana taso mata tsabar baΖin ciki da tuΖuΖin da zuciyarta ke mata duk da kasancewarta mutum mai shegen taurin kai akan abu.. Duk yanda MM Atik Kumo yay ΖoΖarin ganin ta shiga motarsa hakan ya gagara. Dole ya haΖura cikin bodyguard Ιin sa yay mata kiran Ιaya daga cikin taxi Ιin dake wajen da dama su aikinsu Ιaukar manyan mutanen. Nanma Ζin shiga taso yi, sai da ya dinga magiya da roΖonta sannan. KuΙin dake a aljihunsa ya ciro batare daya irga ba ya ajiye masa kusan dubu goma. Godiya sosai mai taxi ya dingayi tare da tambayar ina zai kaita. Cikin Ιar-Ιar ya dubeta, sai ma yaji ya kasa cewa komai ganin yanda take uban huci.. mai taxi da ya fahimci shima bai sani ba ya dubeta ta mirror. “Hajiya ina zamuje...?”
“Gidan ubanka!! Dilla malam kaja mota ban san shiga sharo ba shanu”.
“ALLAH ya baki haΖuri”.
Mai taxi ya faΙa yana kunna mota........✍️
*_Kai kai wannan yarinya ta cika jaraba. Anya zan iya kuwaπ²π? Bara dai muga ko zamu iya cigaba da bin al'amarintaππ€. Nasan dai Uncle Smart ya higa uku yauπ₯±._*
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay atπ
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim
Sai katura shedar biyanka ananπ
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura ananπ
09033181070
Ζ³an Niger kuma ga naku. Kuyi magana ta wannan number Ιinπ
+22799643131
VIPπ₯π―
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*π₯°
Zafafaπ«Άπ₯
*_ALLAH ya gafartama iyayenkuππ_*