Abban Sojoji Takun Karshe Book 3 Chapter 104

Abban Sojoji Takun Karshe Book 3 Chapter 104

Abban Sojoji Takun Karshe Book 3 Chapter 104

Join this link to follow my tiktok acct👇

https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1

قصة حب رومانسية بين سحريش والجراح العام رفايت💋💘❤🤍❤💕💖*

*Father of soldiers*

*🔥TAKUN ƘARSHE🔥*

Am sorry,

"Is Enough!"tsit su kayi basu ƙara cewa uffan ba,

  "Kafin nan da 3 minutes inaso inga kowa asaman dining chairs yana cin abinci"

Miƙewa suka yi ba don sun so ba suka nufi dining area,kowa yaja kujera ya zauna,wuri ya samu shima ya zauna,tare da ƙwalawa Azmee kira,


Fitowa tayi daga cikin kitchen ɗin fuskarta duk alamun hawaye,Serving ɗinsu ta shiga yi,daƙyar suke Cusa abincin abakinsu, 

"Kunsan Allah!kaf sai kun cinye abincin nan,its better ku saki jikinku,"


Loma suka soma yi,Suna ci hawaye na zuba,kowa da abunda yake ayyanawa aransa,

  "Babban yaya,kaifa?ba zaka ci ba?" Fawan ne yayi maganar,

Ɗaga mashi kai kawai yayi batare da yace ƙala ba,


Takun takalmi suka jiyo kamar ana tunkarosu,ɗagowa sukayi da idanuwansu suna kallon mai shigowar,Mommy ce jikinta sanye da Sleeping dress,ƙarasowa tayi ta samu wuri gefen Sgr ta zauna,

  Hada baki su kayi wurin gaisar da ita Mommy barka da dare,

  "Yawwa Sons,"ataƙaice ta amsa masu tare da kallon Fuskar Sgr dake a gefenta,

  "My son,har Yanzu ba zaka daina sa damuwa aranka ba?ina fa sane da irin yarda kake rayuwa acikin gidan nan yanzu,Ba abinci ba bacci taya zaka samu natsuwar yin investigation akan Kidnappers ɗin da Suka ɗauke mun Romeo ɗina"idanuwanta cike tab da hawaye ta karasa maganar,

  Calmly ya furta"Mommy,don't worry about that,Addu'arki kawai nake buƙata,"

  "Kullum haka kake ce mun,why should i not worry?addu'a dama inayi maka,Ni so nake inga kana cin abinci kuma kana bacci",


  Bai amsa mata ba sai ma fawan da yayi ma magana"Fawan,Call Jahad for me,"miƙewa fawan yayi jiki ba ƙwari ya nufi bedroom ɗinsu Sehrish,

mayar da hankalinshi yayi kan Mommy

  "She needs ur caring,tana cikin wani hali na buƙatar uwa atare da ita,Fawan zai kira maki ita,pls ki bata kyakkyawar kulawa,"yana kai ƙarshen maganar ya miƙe da sauri yabar dining ɗin,sam baison anayi mashi magana akan halin da yake ciki,

Girgiza kai kawai tayi,ita kanta jurewa kawai takeyi,


A bakin ƙopar ɗakinsu Fawan ya tsaya tare da sanya hannu yana kwankwasawa,

 "Wanene,"muryar hosana ce yaji ta amsa mashi,

 "Ya fawan ne,jahad ake kira,"

  bude mashi ƙopar Hosana tayi tare da ɗan leƙo da kanta tana kallonshi,

  "where is she"?

Nuna mashi cikin ɗakin tayi da hannunta,Jahad ya hango kwance saman Darduma,

  "Kamar bacci take yi ko"?

Jinjina mashi kai tayi"Eh,"

  "Ta ci abinci"

"A'a,bata ci komai ba,"

."Okey taso mun ita,"

Juyawa tayi ta koma cikin ɗakin zuƙunnawa tayi agaban jahad tare da sanya hannu tana bubbuga bayanta

  "Jahad!jahad!"mutsu mutsu ta fara yi kafin ta yunkura ta tashi zaune,ta rame sosai tun daga kan fuskarta zaka lura da hakan,idanuwanta sun ƙanƙance saboda kukan da take sha,

  "Hosana bana ce kada ki tashe ni ba,"

  "Yaya fawan ne ke kiranki ae,"ta ƙarasa maganar tare da miƙewa ta koma saman gadonsu,

 jiki ba ƙwari ta miƙe ta nufi ƙopar ɗakin,Fawan na ganinta ya ɗan saki fuskarshi,

 "Ya fawan,"ta ambaci sunanshi,

"Babban yaya ne yace in kira mashi ke,"

Hannunta ya ruƙo ya jata suka nufi dining area,

 Lokacin da suka ƙarasa dining area ɗin,kiranta Alex tayi"jahad,"Amsa mata tayi"na'am mommy,"da hannu Alex tayi mata nuni da tazo kusa da ita ta zauna,zagayawa tayi 6angaren da Alexandra take,taja kujera ta zauna,tana sauke ajiyar zuciya,

   "Ya jikin naki,"? jahad tace"Alhamdulillah da sauƙi,"

   "Good haka nake son ji,"

 Da kanta tayi serving ɗin jahad,ta shiga bata abincin abaki,dole Jahad ta saki ciki taci Abinci sosai,



 *Boss Bature*


Ajiyar zuciya ta soma saukewa tare da Ambaton"ALHAMDULILLAH"mayar da idanuwanta tayi kan Sehrish dake sume a ƙasa,da Sauri ta ƙarasa wurinta zama tayi daga gefenta sannan ta sanya hannunta tare da janyo Sehrish ta ɗaurata asaman cinyoyinta,lumshe idanuwanta tayi tare da buɗe su akan fuskar Sehrish,Slowly ta ɗaura tafin hannunta asaman fuskar Sehrish tana shafata,kafin ta yarfar da Sumar kanta gefe guda,tayi hakan ne don taga rubutun dake a bayan wuyanta,Wanda tun suna yara Maman Sadeeq ta bata shawarar tayi masu shaida,Sehrish ta sanya mata SB ma'anarshi Sehrish buzuwa,Hosana ma akwai nata rubutun wuyan HB haka ma jahad,kowaccensu tana da shi abayan wuyanta,

  "Ya Allah na gode maka,daka dawo dani cikin hayyacina,Adai dai lokacin da ƴata ke buƙatar taimako na,"tana magana hawaye ne shararowa akan fuskarta,waige waige ta soma yi tana kallon ɗakin da suke ciki,Allah sarki lokaci guda ta fashe da kuka Saboda ta gane ɗakinta ne na gidansu Abusufyan,Bazata ta6a mantawa da irin rayuwar farin cikin da tayi ba acikin gidan,Tunawa da mahaifinta Baba buzu mai gadi yasa ta ƙara sautin kukan nata,

  "Zainab!Zainabu abu,"haka yake ƙwala mata kira,idan yana nemanta,tayi matukar danasanin bijire mashi da tayi a lokacin da yake raye duk da ta auri za6inshi,bakowa tafi jin kunyar haɗuwa dashi ba,irin Abusufyan batasan da wani ido zata kalleshi ba,Ga kuma Hajiya Ameena,mutanen da suka yi mata halacci ta butulce masu,


Ruwan hawayen abu ne suka wanke mata fuskarta,wanda hakan yayi silar farfaɗowarta daga suman da tayi,Yunƙurin amai ta fara yi daga kwancen da take,da sauri abu ta ɗago da ita,nan take aman ya kwararo daga bakinta,tamkar ƴan hanjin cikinta zasu fito waje,hannu abu tasa tana ɗan bubbuga mata bayanta,Sosai ta dinga sharara aman anan ƙasa,ta galabaita sosai ga zazza6in da ya yi mata mugun kamu,

  Miƙewa abu tayi da sauri ta fito daga dakin ta shigo palour,fridge ta hango da sauri ta nufe shi,buɗewa tayi tare da zura hannu ta ɗaukko bottle water jiki na rawa ta koma cikin ɗakin,A gaban sehrish ta zuƙunna a lokacin ta kammala kwarara Aman,cire murfin robar tayi tare da tarba tafin hannunta ta debo ruwan tana zuba mata shi abakinta tana kuskurewa,bayan ta gama kuskure bakin Abu ta kafa mata robar ruwan abakinta,Sosai ta shiga kwankwadar ruwan tana sha,sai da ta ƙoshi sannan ta janye bakinta,Har lokacin Sehrish bata dawo hayyacinta ba,jikinta duk ya saki babu ƙwari,

    Ajiye robar ruwan abu tayi gefe tana kallon fuskarta,

  Gam ta runtse idanuwanta,tana faman ciccije la66anta,

  "RISHI"ta furta sunanta,

A hankali Sehrish ta ɗan ware idanuwanta akan fuskar abu,wani irin sanyi ne ya ratsa zuciyarta,ganin Oummansu agabanta,kuma da alama tadawo cikin Hayyacinta ne,

  "Oumma,"ta ambaci sunanta tare da fashewa da wani sabon kuka,

  Ita ma abun fashewa tayi da kuka,Cikin Shesshekar kuka take cewa"Laifina ne!komai ya faru arayuwarku ni ce sila,Ni naja maku...."

  "Oumma ba laifin ki bane,ki daina ɗaurawa kanki laifi,Allah ya rigada ya ƙaddara faruwar hakan"

  "Rishi bakisan irin raɗaɗin da nake ji acikin zuciyata ba,bansan tsawon lokacin dana ɗauka bana acikin hayyacina ba,bansan ya rayuwarku ta ƙare ba,Nasan dole kunsha Wahala"

  Sosai suke yin kukan babu mai lallashin wani acikinsu,

Sai da suka yi mai isarsu,Sannan suka tsagaita da yin kukan,

   "Ina Hosana take?ina Jahad?duk suna ina?meyasa kike zaune ke kadai acikin gidan nan?Babu kowa atare dake?

  ɗagowa Sehrish tayi daga kwancen da take saman ƙirjinta,cikin sanyin murya tace"Hosana da Jahad suna a Abuja wurin danginsu Daddy"

  Cike da Mamaki abu ta maimaita sunan Daddy,

  Sehrish tace"Eh,mahaifinmu nake nufi,Daddy Abusufyan atare muka zo kano,Tun da ya fita da marece bai dawo ba,kuma akwai security guards dake tsaron gidan,Amma bansan ya akai Ya sayyadi ya shigo ciki ba,"

  Tunda Sehrish ta ambaci sunan Abusufyan jikin abu ya kara yin sanyi lakwas,shiru tayi na wani lokaci kafin tace"Kina nufin Abusufyan yana atare daku"?

  ɗaga mata kai Sehrish tayi"Eh,"

Abun yayi matukar ɗaure mata kai,cike da mamaki tace"Taya akai kuka san cewa shi ne mahaifinku?Kuma ya akai kuka haɗu dashi"?har ya kai ku wurin danginshi"?daƙyar take magana saboda Ciwon kan da take ji yana ɗan takura mata,

  "Oumma,Labari ne mai dogon zango....,"kasa ƙarasa maganar tayi sakamakon tashin Zuciyar da take ji,

  "Sannu kinji,idan muka samu natsuwa sai ki sanar dani"

   ta ƙarasa maganar tare da ruƙo hannayen Sehrish Cikin nata,suka mike tsaye suna fuskantar junansu,haɗa ido sukayi lokaci guda suka sakarwa juna murmushi,

 "Kin girma sosai,komai naki ya canza mun,"duƙar da kai kasa sehrish tayi tana dariya,

  "Allah sarki hosana,Ashe da rabon zata rayu"?

  "Sai ma kin ganta Oumma,Zaki sha Mamaki Allah,saboda hosana duk tafi mu girman jiki,"

 wani irin farin ciki ne ya lullu6eta mara misaltuwa,


Sun jima suna tattaunawa atsakaninsu,kafin daga bisani Sehrish ta shiga toilet don tayi wanka,tunda ta rufo ƙopar toilet ɗin,ta sulale ƙasa jikin ƙofar tana kuka ƙasa ƙasa,Abunda ya sayyadi yayi mata ya tsaya mata aranta,yadda ya dinga goga mata Abunshi ajikinta,Da kuma harshenshi da ya sanya yana lasar mata bayanta Ba ƙaramin ƙona mata rai yayi ba,runtse idanuwanta tayi sosai,wani irin ɗaci ta dinga ji acikin zuciyarta,lokaci guda ta fara jin ƙyanƙyamin jikinta,hada ƙaiƙayi miƙewa tayi ta soma tu6e kayan baccin dake ajikinta,


Lokacin da ta kammala wankan ta fito jikinta ɗaure da towel,bata samu kowa a ɗakin ba,Amma taga an gyara shi,komai ya koma yadda yake,hatta aman da tayi an kwashe shi da tarkacen Ya sayyadi,tasan cewa aikin Oummansu ne,


Jiki ba ƙwari ta wuce saman gado ta haye,tare jan bargo ta lullu6e jikinta,bakowa take jiran dawowarshi ba,fa ce Daddynsu,Tayi mamakin jimawarshi awaje,har wuraren 12,Allah yasa dai yana lafiya,


Kitchen ta shiga ta ɗauko Ashana,da sauri ta fito ta dawo harabar gidan,inda ta tattara Tsummokaran Ya sayyadi da ya bar masu,ba tare da taji komae ba ta Ƙyasta ashanar ta jefa ta asaman kayan nan take wuta ta soma ci ajikinsu,har sai da ta cinyesu abu na tsaye tana kallonsu,


Ajiyar Zuciya ta sauke tare da bin gidan da kallo,mutane ta hango a bakin gate ɗin gidan Sanye da kakin Sojoji,kowannansu a yashe ƙasa sai bacci sukeyi,Abun ba ƙaramin ɗaure mata kai yayi ba,ranta ne ya bata cewar Securities ne,Da alama Ya sayyadi ne yasa su yin baccin Dole,don ya samu hanyar shigowa cikin gidan,


Girgiza kai kawai tayi tare da komawa cikin falon,Bedroom ɗin ta shiga,tsayawa tayi abakin ƙopar ɗakin tana kallon Sehrish dake ƙumshe cikin bargo,jikinta sae kerma yake yi,

 Idasa shiga cikin ɗakin tayi har zuwa gefen gadon ta zauna,tare da Ambaton Sunanta"Sehrish,"

  Muryata na kerma tace"Na'am Oumma,"

   "Taya zan iya samun Daddynku?inaso nayi magana dashi,"

   "Ina da waya,nabarta a ɗaya daga cikin ɗakunan dake a upstairs,"

  Da sauri abu ta mike ta fuce daga ɗakin,Upstairs ta wuce,tana neman ɗakin da sehrish ta faɗa mata,Ɗaki ɗaya ta samu a buɗe,tun kafin ta shiga tajiyo ringing ɗin wayar tura ƙopar tayi ta shiga cikinsa,A saman gado ta samu wayar,hannu takai ta ɗauki wayar tare da duba screen ɗin

  "My Boss Man,"shi ne sunan daya bayyana akan Screen ɗin wayar,picking call ɗin abu tayi tare da kara wayar a kunnanta,batasan wanene ba kawai ranta ya bata cewar Abusufyan ne,tayi tunanin zai yi mata sallama sai taji shiru,

  Batare da ta kawo komai aranta ba,ta soma magana,

  "Assalamu Alaikum,Oummansu Sehrish ce ke magana,dan Allah kadawo gida akwai matsala,Sehrish tana cikin wani hali,yanzu haka bata jin daɗin jikinta,duk ta tsorata saboda abunda Ya sayyadi yayi mata,

  Sgr dake kwance asaman gadonshi,baisan lokacin da ya mike daga zaune ba,a kiɗime yace"What?meya faru da ita ne?Waye ya shigo"?

   Abu bata wayi muryarshi ba,ita dai kawai koma wanene so take akawo masu ɗauki ko dan saboda halin da Sehrish take ciki,

  "Ya sayyadi ne ya shigo cikin gidan,bamu san taya akai ya shigo ba,Ya so ya cutar da rayuwarta....."gaba daya abu ta kwashe dukkan abunda ya faru ta sanar dashi a ƙarshe tace"dan Allah idan ka tashi dawowa,Ka biya koda chemist ne asamo mata maganin Zazza6i,ga tashin zuciya da take ji,Tunkan takai ƙarshen maganar,Yayi rejecting Call ɗin,

  Hankalinshi yayi mugun mugun tashi,har wani jiri ya soma gani acikin idanuwanshi,a zafafe ya tunkari ƙopar fita daga bedroom ɗinshi,sai ga Marshal ya faɗo cikin ɗakin har karo suka kusan yi,

  "Bro whats happening?Where are going?"

  Zuciya ce kawai ke fusgarshi,

  "Omar,Airport zani je,"

Damko damtsen hannunshi Omar yayi ganin yana ƙokarin wuce shi ya tafi,

  "Haba Rafayet!Airport kuma at this time?Me zakayi acan "

  "Pls omar,leave alone,ka bani hanya in wuce,Zuciyana tafarfasa take yi,idan har ban kama wancan fasiƙin mutumin ba,hankalina bazai kwanta ba,"

  A ruɗe Marshal yace"Wai wa kake magana akai?ko ka gano waɗanda suka kashe junaid ne"?

  Girgiza kai yayi'A'a,ina magana akan wancan Bastard ɗin dake a Kano,Yau ya taka har gidan da Abusufyan yake..wai har...'kasa ƙarasa maganar yayi saboda raɗaɗin da yake ji acikin zuciyarshi,

  Hankalin Omar ba karamin tashi yayi ba,tun kafin ma ya ƙarasa jin abunda ya faru ɗin,

  "Rafayet,pls Calm down ur mind,Kayi mun bayani yadda zan fahimta,'

  Mika mashi wayarshi yayi batare daya furta komai ba,

Kar6ar wayar Omar yayi, kaitsaye ya shiga call log nashi,

  Kiran da Sgr yayi ma sehrish ya fara gani,"Calling ɗin layin yayi,

A lokacin abu na acikin falo tana safa da marwa,jiran dawowar Abusufyan kawai takeyi,

  Kiran na shiga wayar,da sauri tayi picking tare da zabga sallama,

   "Am..sehrish,pls inason sanin meke faruwa anan ne,"?

  Abu tace"ba Sehrish bace,Oummansu ce,"

  Abun ya ɗan ɗaure mashi kai,jin tace Oummansu ce,a iya saninshi tana da ta6in Hankali,gaisar da ita ya fara yi cike da girmamawa tare da gabatar mata da kanshi a matsayin yayansu sehrish,abu ba ƙaramin daɗi taji ba,

  Bata 6oye mashi komai ba,kaf ta kwashe abunda tasan ya faru ta sanar dashi,"

  Jinjina kai Omar yayi,jikinshi har tsuma yake yi,daƙyar ya iya furta"Zan yi magana da Abusufyan ɗin,Ki kula da Sehrish ɗin kafin ya dawo gidan,"

  amsa mashi tayi da toh,daga bisani su kayi sallama,

  Zuba ma juna ido sukayi shi da Sgr,

"Bansan wani irin dabban mutun bane wannan,wai ma ina security ɗin dake tsaron gidan ne?aikin me sukeyi ne da har suka barshi Ya samu damar shiga gidan?shi kuma Uncle bansan ya akayi har yayi dare haka ba awaje,"Omar ne yayi maganar ranshi a matukar 6ace,

  "Last time ma,Ya ta6a yin irin hakan,Ya tafi ya barta ita kaɗai acikin gidan,"Acewar Sgr,

Omar yace"ba don Oummansu na a kusa ba,da bansan mezai biyo baya ba,Amma naji daɗin jarumtar da tayi wurin ceton sehrish ɗin,"

  Kar6ar wayar Sgr yayi daga hannunshi,Layin Abusufyan ya kira,

  Almost 3 times tana ringing ba'a ɗagawa,

  Sauke wayar yayi daga kan kunnanshi,

 Omar yace "Allah yasa dai lafiya,hankalina fa duk ya tashi,abunda za'ayi yanzu Kawai gobe da asussuba su dawo gida kawai,nasan kafin lokacin may be Abusufyan ɗin ya dawo,Zan cigaba da trying layinsa,"

  Dakyar ya samu ya lalla6a Sgr ya fasa zuwa airport ɗin,Amma fa abun ya tsaya Mashi aranshi,gefen gadonshi ya zauna,Omar ma ya zauna akusa dashi,

  "Omar,kodai mun aikata wani zunubi ne da yasa waɗannan abubuwan ke faruwa damu ne?daga wannan sai wannan!

  "Rafayet,ba laifin mu bane Laifin wasu ne aka ɗaura mana,ni tunda nake arayuwata ban ta6a fuskantar tashin hankali irin na waɗannan ranakun ba,kuma ban ta6a tunanin cewa rana irin Wannan zata zo mana ba,"

  "What's the solution now?time fa yana ƙure mana,Daddy ma harya fara karaya da dawowar junaid,ɗazu da safe da yazo bedroom ɗina,Tsare ni yayi akan in faɗa mashi gaskiya,Junaid zai dawo yaci gaba da sa rai,ko kuwa bazai dawo bane,A lokacin saina kasa buɗe baki inyi mashi magana,"Sgr ne yayi maganar 

  Omar yace"Wlh nayi regretting ɗin 6oye mashi ainihin abunda ya faru,Duk da munyi hakan ne don mu ceto rayuwarshi,Amma kuma fa mun tabka kuskure babba,Don kuwa duk ranar daya gano cewa Junaid ya mutu,wlh ya gama yarda damu har abada,zuciyarshi zata karaya ne,Inajin tsoron wannan ranar,Rafayet,kodai mu sanar dashi gaskiyar lamarin ne"?

  Shiru Sgr ya ɗan yi yana nazarin maganar tashi,girgiza kanshi ya ɗan yi tare da cewa"That's not the solution Omar,koda ace zai sani,yakasance time ɗin da muka kama waɗanda su kayi silar mutuwarshi,Mu gurfanar dasu agabanshi,before mu yanke masu hukunci akan idonshi,ina ganin kamar zaifi jin sauki acikin zuciyarshi,"

  Sun jima suna tattaunawa a tsakaninsu kafin daga bisani,Kowannansu ya ɗauro alwala,Suka daidai ta sahu tare da kabbara Sallah,


Ataƙaice 


Abusufyan bai tashi dawowa cikin gidan nan ba sai wuraren sallar asuba,Bawan Allah ashe Bayan ya baro gidan su Maman Sadeeq akan hanyar dawowarshi gida aka turo mashi da saƙo cikin wayarshi cewa za'a kashe Ƴarshi da ya bari acikin gidan,Hankalin shi yayi mugun tashi,Ya kure gudun motarshi,idonshi ya rufe saboda tashin hankalin dayake ciki,Baisan sa'adda ya buge wani Tsoho ba dake ƙoƙarin tsallaka titi,Tsohon yaji mummunan rauni dole ya tsaya don yaji bazai iya daukar alhakin guduwa yabarshi cikin mawuyacin halin da zai iya rasa ransa,mutane suka kama mashi tsohon yasa shi a motarshi suka wuce dashi asibiti,babu yadda ya iya,kamar ya fasa ihu haka yaji saboda tsabar baƙin ciki,duk da wani bangare na zuciyarshi na tunasar dashi akwae security guards a gidan,Bashi ya baro asibitin ba sai wuraren Sallar Asuba Ya dawo cikin gidan,Yayi mamakin ganin komai lafiya,Lokacin daya shiga ɗakin abu kwance ya samesu rungume Saman gadon ita da Sehrish suna ta sharar baccinsu,Hankalinshi ya kwanta sosai ganin babu abunda ya faru dasu,


Falo ya koma ya zauna saman sofa,jikinshi duk amace,Ringing ɗin wayarshi dayaji yasa shi zura hannu cikin aljihu ya ɗauko wayar tare da duba sunan mai kiran nashi,Marshal Omar ne,

  Picking call ɗin yayi tare da kara wayar a kunnanshi,

  "Omar me kake yi har yanzu bakayi bacci ba"?

  On the other hand Omar yace"Uncle,Ina ka shiga ne anata nemanka,"?

  Nan Abusufyan yake sanar dashi abunda ya faru dashi akan hanyar dawowarshi gidan,

   "Yanzu na dawo gidanma,Na same su cikin koshin lafiya suna ta bacci,"

  A nan Omar ya kwashe duk abunda Abu ta sanar dasu ya faɗa ma Abusufyan,A zabure ya miƙe tsaye jikinshi na rawa,

  "Pls Uncle,ka kwantar da hankalin ka,Tunda ba abunda ya faru dasu,Abunda ya kamata kawai ku dawo gida yau yau ɗin nan zamanku anan baida amfani,dama saboda ciwon Mahaifiyarsu ne Kuma ta samu lafiya,Yakamata ku dawo gida,Hankalinmu sai ya fi kwanciya,"

..jinjina kai kawai Abusufyan keyi sam ya kasa buɗe baki yayi magana,Allah kaɗai yasan raɗaɗin da yake ji acikin Zuciyarshi,dakyar ya iya buɗe baki yace"Shikenan Omar,yanzun nan zamu shirya,'

  "Allah ya dawo daku Lafiya,"

"Ameen"daga haka su kayi Sallama,

Komawa Bedroom ɗinsu yayi wuraren karfe 6 na asuba,da alama ko sallar asuba basu yi ba,sai sharar bacci sukeyi,

  Zagayawa yayi gefen da Sehrish take a kwance ya zauna tare da zuba mata ido yana kallonta,Yayin da hawaye ke sharara akan fuskarshi,tsananin tausayinta ne ya kamashi,baiji daɗin abunda ya faru ba,ta wani 6angaren kuma yaji sanyi aranshi da Allah ya tsare mashi ita,ga kuma Mahaifiyarsu da ta dawo cikin hayyacinta ta silar abunda ya faru,

  Shessheƙar kukan da Abusufyan keyi ne ya farkar da Sehrish,buɗe idanuwanta tayi masu ɗauke da bacci,Suna haɗa ido dashi tayi hanzarin mikewa daga zaune tana ambaton sunanshi"Daddy!yaushe ka dawo?meya faru kake kuka,"

  "Daughter,Am sorry!am really sorry,duk laifina ne dana tafi nabarki ke kaɗai acikin gidan,"

  "Daddy,bangane akan me kake magana ba?nifa babu abunda ya faru dani,"tayi hakan ne don ta 6oye mashi gudun karya sanya damuwa aranshi,batasan cewa ya riga daya ji ba,

  "Omar ya sanar dani duk abunda ya faru dangane da zuwan sayyadi cikin gidan nan,"

   Mamaki ta shiga yi taya akai Ya Omar yasan abunda ya faru  dasu?can kuma ta tuna da lokacin da Oummansu ta nemi yin magana da Abusufyan may be a wurinta yaji komai,

  "Dan Allah Daddy,kada kasa damuwa aran ka tunda ba abunda ya faru dani lafiyata kalau,Sai ma wani abun farin ciki da ya faru,Oummanmu ta dawo cikin hayyacinta,Sanadin zuwan ya sayyadi,Kuma ta lalata mashi idanuwanshi,karkaso kaga yarda ya dinga kururuwa yana ihu," Tayi maganar tana kwatanta mashi irin yarda Ya sayyadi yayi ihun,

  Hakan ba ƙaramin kwantar mashi da hankali yayi ba,dama tayi hakan ne don ta sanyaya mashi ranshi,

  ɗaure fuskarta ta ɗan yi ashagwa6e tace"Daddy banga kana farin ciki da abunda na sanar dakai ba"?

  Daƙyar ya ƙaƙaro murmushi akan fuskarshi yace"Ina farin ciki mana,Naji daɗi sosai,kawai dai  nadamu ne akan Halin da kika tsinci kanki a lokacin da bana nan,"

  ɗaure fuskarta tayi"Why Daddy,bana ce ka kwantar da hankalin ka ba?komai ya wuce,Yanzu lokacin farin ciki ne,Ga ka, Ga Ni,ga Oummanmu kuma,Bari na tashe ta daga bacci kuyi magana,"ta ƙarasa maganar tare da sanya hannu tana ɗan bubbuga kafadar Oummansu,

  Murmushi kawai Abusufyan ke saki yana kallonta,

  "Oumma!oumma!ki tashi ga Daddynmu nan ya dawo,"

  Kasa tashi abu tayi saboda kunyar Abusufyan da take ji,Ashe tun shigowarshi dakin ta farka,tana jinsu suna magana amma tayi likimo,


"Nasan cewa idonki biyu abu,bakison gani na ko"?Abusufyan ne yayi maganar ayayin da yake leƙen fuskarta,pillow ta sanya tare da rufe fuskarta dashi,

  Murmushi suka saki atare shi da Sehrish,

  "Inason magana dake,ki tashi daga zaune,"cike da jin kunyarshi ta cire pillow ɗin tare da tashi daga zaune suna fuskantar juna,Ta kasa ɗagowa su haɗa ido da Abusufyan,kunyarshi ta rufe ta,kamar tayi rami ta binne kanta,

      

   "ZAINAB"ya ambaci sunanta da wata irin kasalalliyar murya,

   daƙyar ta iya motsa lips ɗinta wurin amsa mashi,

   "Na'am,"

Murmushi ya saki tare da ɗaga hannunshi sama yana furta"Alhamdulillah!Alhamdulillah,Almost 3 times yana ambaton hakan,Cike da tsantsar farin ciki,

   Sai faman sauke ajiyar Zuciya take yi,matsawa yayi kusa da ita tare da sanya hannayenshi biyu ya tallabo fuskarta yana ƙare mata kallo,

  Siraran hawaye ne suka soma Zarya akan fuskarta masu ɗumin gaske,

   "Hawayen menene wannan"?

Cikin Shessheƙar kuka tace"Kayi haƙuri,ka yafe mun,Na gane kuskuren dana yi,Naji jiki Abusufyan,nayi dana sanin butulce maka da nayi,Haƙƙinka ne yake ta bibiyar rayuwata,Ni ce silar duk wani abu daya faru a rayuwarmu nida ƴa'ƴana...."ta ƙarasa maganar tare da fashewa da kuka,Hannu tasa ta zame hannayenshi daga saman fuskarta,kafin ta Sauko daga saman gadon ta zuƙunna saman guiwowinta agabanshi,tana ci gaba da yin kukan....

   "Tun da nake arayuwata,ban ta6a ganin mutun mai kyakkyawar Zuciya irin taka ba,duk irin girman laifin dana aikata maka,hakan baisa ka guje ni ba,Sai ma bibiyar rayuwata daka ci gaba dayi duk don kaga Ka taimake ni,Amma na kasa gane hakan,saboda tsabar baƙin kishin da nake dashi na yanke maka hukunci batare dana tsananta bincike ba......"

     Ruƙo hannunta Abusufyan yayi tare da ɗago da fuskarta yace"pls bana son muna tuna abunda ya wuce,Ni komai ya wuce a wurina Abu,tabbas naji zafin abunda kika yi mun Amma wlh banta6a ruƙe ki araina ba,kullum burina inga na taimaki rayuwarki saboda baki da kowa abu,Allah kaɗai gare ki,Sai kuma Ni dana haɗa zuri'a dake,Ba zanso rayuwarki ta wulaƙanta ba,ko ba don haka ba Ke amana ce agare Ni,"


Zuba masu ido Sehrish tayi tana kallonsu fuskarta ɗauke da Murmushi,tsabar farin ciki kamar ta zuba ruwa a ƙasa tasha,

  "Bansan da wasu kalmomi zanyi amfani ba wurin bayyana maka irin farin cikin da nake ciki ba,Abusufyan Allah kadai ne zai iya biyanka,",addu'oi ta shiga yi mashi yana amsa mata da ameen,Kafin daga bisani Ya nuna mata gefenshi ta miƙe ta zauna,

   "nasan kinyi kewar ƴa'ƴanki sosai,In sha Allah Yau ɗinnan zamu wuce Abuja,Zaki ga Hosana da Jahad,da kuma sauran Family ɗinmu,"


Fira sosai suka shiga yi,Anan ta samu labarin irin wuyar dasu sehrish suka sha bayan 6acewarta,da kuma yadda akai suka haɗu da dangin mahaifinsu da shi kanshi Abusufyan din har kawo yanzu da suke bata labarin,Abu tasha kuka sosai tsananin tausayinsu ne yakamata,ta wani 6angaren kuma tayi farin ciki sosai Da Allah ya nuna mata wannan ranar da ranta kuma da Lafiyarta,


Batare da 6ata lokaci ba Suka kammala shirinsu na komawa Abuja,A jere Motocinsu suka fita daga cikin gidan,Motar Abusufyan na atsakiyan motocin security ɗin gidan,Kaitsaye hotoro suka wuce domin yin sallama dasu Maman Sadeeq,

  Sunsha kuka sosai,musamman Maman sadeeq da Abu,rungume juna suka yi kamar karsu rabu,babu wanda bai zubda ƙwalla ba acikinsu,kafin su tafi sai da Abusufyan ya damƙa ma Malam Nura key din gidansu dake a nasarawa G.r.a,Ya mallaka masu shi duk da haka sai da ya ƙara masu da zunzurutun kuɗi har miliyan 10,yace ya dauki miliyan bakwai yaba Baban Umari cikon miliyan ukkun,don bai manta da gudunmawar da akace ya bada ba wurin neman abu,anan take ya rubuta ma Malam Nura cheque,Duk da haka bai ƙyalesu ba,Bayan haka kuma yayi masu albishir ɗin cewa tare dasu Za'ayi aikin hajjin bana,Wayyo Allah saboda tsabar farin ciki,kasa bude baki su kayi don suyi mashi godiya,Kuka kawai sukeyi,abun da basu ta6a tsammanin zasu samu a rayuwarsu ba,Yau gashi silar taimakon da sukayi Allah ya ɗaukaka rayuwarsu,

  Sehrish kuwa Dama tayi alƙawarin zata taimaka ma Sadeeq ya gyara keken shi,maimakon kuɗin gyaran keken sai Gashi ya samu kyautar danƙareriyar Motar Abusufyan gaba daya ya mallaka mashi ita,kusan zaucewa Sadeeq yayi saboda tsabar farin ciki,sun jima a wurinsu suna bankwana,kafin daga bisani Sukayi masu Sallama,Anyi rabuwar mutunci sai kuma in Allah ya haɗasu wurin shagalin bikin Ƴa'ƴan abu,


Ɗaya daga cikin motocin security ɗinsu suka shiga Gidan baya Abu da Sehrish,Abusufyan yana agaban motar,A jere Motocin suka kama hanyar fita daga unguwar,


Su Maman Sadeeq na tsaye a kopar gida ita da Mlm nura,tare da sadeeq sai bye bye suke yi masu da hannu,yayin da hawaye ke zuba a fuskar kowannansu,


Sehrish sai lekensu takeyi ta glass ɗin motar dake a zuge,har sai da suka 6ace ma ganinta tukunna ta hakuri da leken,Rayuwa kenan in akayi hakuri Komai mai wuce ne,


Hannu abu tasa tare da janyo Sehrish ta rungumota ajikinta,a lokacin har motocin sun haura saman titi,Sun miƙi hanyar barin garin da matsakaicin gudu,

   Da zarar ta ɗago da idonta ta kalli madubin motar,Fuskar Abusufyan take gani yana sakar mata murmushi,Sunnar da kanta ƙasa tayi tana ƴar dariya,

  Sehrish batasan wainar da suke toyawa ba,domin kuwa ta lumshe idanuwanta da alama bacci ya fara ɗaukarta,

  Sake ɗagowa abu tayi tare da kallon Mirror ɗin,suka ƙara haɗa ido dashi,

  Kashe mata ido ɗaya Abusufyan yayi,batasan lokacin da ta fashe da dariya ba cike da tsantsar farin ciki,

   Shima dariyar yayi,kusan minti 30 bata ƙara dagowa sun haɗa ido ba,saboda baccin da yayi awon gaba da ita,

  Wasa wasa shima bacci ya ɗauke shi,dama duk basu samu isasshen Bacci ba a adaren Jiya,


Wuraren ƙarfe 2 na rana suka ƙaraso Abuja,Slowly motocinsu suka shararo izuwa cikin gidan,tun da Hosana tajiyo sautin shigowar motoci da gudun gaske ta fito daga cikin falon don taga su wanene,


Bayan sunyi parking ɗin motocin,Abusufyan ya fito daga cikin motar,hosana na ganinshi ta ƙwala mashi kira"Daddy"!wani irin farin ciki ne ya lullu6eta,da gudun gaske ta nufe shi tare da faɗawa jikinshi ta ƙankameshi sosai,tana dariya,

  "Hosana,"ya Ambaci sunanta tare da ɗago da ita daga jikinshi yana kallonta,fuskarshi ɗauke da murmushi,

  Ɗaure fuskarta ta ɗan yi ashagwa6e tace"Munyi fushi daddy,Sai yau zaku dawo"?

  Yana ƙokarin buɗe baki ya bata amsa,karaf idanuwanshi suka sauka akan Jahad wadda ta fito daga cikin falon tana tunkaro su,

Gabanshi ne ya faɗi rass!Ganin yadda kamanninta suka sauya tamkar ba ita ba,ta rame sosai ,tafiyar kanta ma daƙyar take yinta,

   Ƙarasawa tayi gabansu ta tsaya batare da tace komai ba,idanuwanta na kallon ƙasa,

  "Jahad!kinyi rashin lafiya ne"?ɗaga mashi kai tayi alamar eh,

   "Zazza6i nayi sosae amma naji sauƙi yanzu,"

 Hannu yasa tare da janyota ya rungumeta ajikinshi,Kasa jurewa tayi aikuwa ta fashe mashi da kuka sosai,

  Hankalinshi ya ƙara tashi,

  "Jahad kukan menene"?

 Cikin shessheƙar kuka tace"bakomai Daddy,nayi kewarka sosai,"

  hannu yasa yana ɗan bubbuga bayanta yace"Am Sorry Daughter,pls ki daina kuka kada kisa nima na fara zubar da hawayen nawa,"

  Dakyar ta tsagaita da yin kuka ta ɗago da kanta daga jikinshi tace"Daddy,ina rishi take?ina kuma Oumman mu?Hosana ta sanar dani cewa an ganta,"

  Murmushi ya saki tare da sanya hannunshi ya ɗan kwankwasa glass ɗin motar,

  Buɗe murfin motar Abu tayi tare da fitowa daga cikin Motar,Zuba mata ido su kayi suna kallonta kamar yadda itama take kallonsu,

  Atare suka haɗa baki wurin ambaton sunanta"Oumma!"

  Murmushi ta ɗan sakar masu,tare da buɗe masu hannunwanta don su zo ta rungumesu,Matsawa suka yi tare da faɗawa saman jikinta,ta haɗasu duka ta rungume sosai,fashewa sukayi da matsanancin kuka kamar ransu zai fita,musamman jahad da take cikin wani hali na buƙatar kulawarsu,

  Itama abun kukan takeyi sosai,babu mai lallashin wani acikinsu,Fitowa Sehrish tayi daga cikin motar ta other side ɗin,jikinta a sanyaye ta zagayo ta wurin da suke,bayansu jahad ta fada ta rungumesu,abu ta haɗa da ita duka ta ƙanƙame abunta,


Tuni hawaye sun wanke fuskar Abusufyan,Yau burinshi Ya cika na ganin ya haɗa kan family ɗinshi,wannan rana ce da bazai ta6a mantawa ba arayuwarshi,,


Suna cikin wannan yanayin sai ga Abbansu junaid tare da Alexandra sun fito daga cikin gidan,tsayawa su kayi suna kallonsu fuskar kowannansu ɗauke da murmushi,

  "Bismilla,Ku ƙaraso daga ciki mana,"Abba ne yayi maganar tare da yi masu nuni da hannunshi,

  Kallonsu Abu yayi tare da yi masu gyaran murya yace"Koke koken sun isa haka,mu shiga daga ciki mana,"

  Raba jikinsu sukayi dana Oummansu,ta ruƙo hannun jahad da hosana acikin nata,Abusufyan kuma ya ruko hannun Sehrish wurinsu Abba dake atsaye,

  tunkan su ƙaraso Abba yace" masha Allah,Yau family ɗin Abusufyan ya haɗu wuri guda,Ga Uwar Ga uban Ga kuma ƴa'ƴansu,"ya ƙarasa maganar yana dariya,

Alex tace "U'r Highly welcome, Abusufyan's Family,Am glad to see guys "ta yi maganar tare da ƙarasawa ta rungumo Abu ajikinta,hakan ba ƙaramin daɗi yayi masu ba,


Sun jima a waje suna gaisawa kafin daga bisani suka koma babban falon gidan,Kowa dake acikin gidan sai da ya hallara A falon,Abusufyan ya shiga gabatar ma abu kowa,Sun yi farin ciki sosai,duk da tashin hankalin da suke ciki hakan bai hanasu yin Murnar dawowar Uncle ɗinsu ba tare da Oummansu rishi,Abusufyan ya lura da yanayin fuskokinsu,abun ya ɗaure mashi kai,mutanen gidan duk sun rame sunyi duhu,bashi kaɗai ba hatta Sehrish ta ankara da canzawar da mutanen gidan su kayi,Sai faman wurga ido takeyi taga ko junaid zai fito amma shiru babu shi,Ranta ne ya bata cewar ko sun fita tare dasu Babban yaya ne tunda bata gansu ba acikin gidan,


Basu tashi sanin halin da Family ɗin suke ciki ba,Sai da suka huce gajiyarsu,tukunna Abba ya sanar da Abusufyan shima ɗin don ya matsa mashi ne akan son ganin junaid,Hankalin shi ba ƙaramin tashi yayi ba,jin anyi garkuwa dasu Junaid,baima son lokacin da ya rufe Abba da faɗa ba saboda ƙin sanar dashi da sukayi,Don me zasu 6oye mashi abunda ke faruwa acikin gidan,abun ya ƙona mashi rai,Har cikin ranshi baiji daɗin hakan ba,har ƙwalla saida ya zubar,


Yinin ranar Abu na tare da ƴan ukunta a bedroom ɗinsu,Sun sha firar yaushe rabo,har bacci ya ɗaukesu atare saman gadon,basu suka farka ba sai wuraren Sallar Magriba,


Bayan kowannansu yayo alwala Jahad ta shimfiɗa masu darduma suka jera atare da Oummansu,a tsanake sukayi sallar har suka kammala,basu tashi daga saman dardumar ba,ɗaga hannayensu suka yi sama suka shiga karanto addu'o'a abakunansu suna masu kara mika godiyar su ga Allah(S.W.A),


Allah Allah Sehrish take yi su kammala Sallar taja jahad gefe saboda ta tambayeta ina junaid yake sannan kuma ta bata Labarin Artabun da suka yi tsakaninsu da ya sayyadi,ita ma jahad ɗin a ƙagare take dasu ke6e ita da Sehrish,Don ta bata labarin mutuwar junaid,kota samu ta rage raɗaɗin dake acikin zuciyarta,bazata iya 6oyema Sehrish ba,duk da An gargaɗeta akan karta fadama kowa,


Basu suka samu lokacin kebewa da junansu ba,Sai bayan sallar Isha'e,kowa ya hallara a dining area,Suna cin abincin darensu,


Su biyu suka rage acikin bedroom ɗinsu,Zaune daga gefen gadonsu,kowa yayi tsit,na wani lokaci kafin Sehrish tace"Jahad,tun ɗazu nakeso na tambayeki game da canzawar dana ga mutanen gidan nan sunyi,kowa ya rame yayi duhu,musamman ke kamar kin yi ciwo,"

  Cikin sanyin murya Jahad tace"Labari ne mara daɗin ji Sehrish,Zan faɗa maki amma ina gudun na jefa ki cikin tashin hankali,"

  "Kada ki damu jahad,ki faɗamun koma menene,in sha Allah zan jure bazan tashi hankali na ba,"

    "Shikenan zan faɗa maki Amma kafin nan inaso ki yi mun alƙawarin cewa bazaki faɗa ma kowa ba"

..Sehrish tace"I promised you jahad,babu wanda zaiji abunda muka tattauna dake,"

  Shiru jahad ta ɗan yi yayin da take yin wasa da yatsun hannunta,

   "Ina sauraronki jahad,"ta faɗi hakan ne don a ƙagare take da ta ji abunda jahad zata sanar da ita,

  "Sehrish!munyi babban rashi,wanda ya raunata zukatanmu,"

..tunkan ta ƙarasa maganar sehrish taji gabanta ya faɗi rasss,

  Aruɗe tace"Jahad kada ki ce mun junaid ya mutu......!"

  Hawaye ne suka fara saukowa daga cikin idanun Jahad,bata 6oye mata komai ba game da mutuwar Junaid,Abun mamaki sai taga Sehrish na Zabga murmushi kamar wata zautacciya,

  Bata karaya ba,cigaba da magana tayi"Babu wanda yasan ainihin abunda ya faru,daga ni sai su ya Omar sai kuma Jami'an ƴan sandan da suke je wurin da kuma Sojojin dasu ya Omar suka je dasu,"

  Dakatawa tayi da yin maganar tare da kallon Sehrish,wadda ke ta sakin murmushi,

  Fashewa da kuka Jahad tayi tare da cewa"Sehrish meyasa kike yin murmushi?na faɗa maki ne don in rage raɗaɗin da nake ji acikin zuciyata,wlh da kinsan halin da muka shiga ni dasu Ya Omar da baki yi mana dariya ba,"tana kai ƙarshen maganar ta ƙara sautin kukan nata,

 Sai lokacin Sehrish ta tsagaita da yin dariyar,Sannan ta soma magana"Haba Jahad,taya zaki ce mun Junaid ya mutu farat ɗaya in yarda?bazan ƙaryata ki ba,mutuwa na akan kowa babu wanda yafi ƙarfinta,Amma ni dai ban yarda cewa junaid ya mutu ba,tunda banga gawarshi ba,"tuni hawaye sun cicciko acikin idanuwanta,

  Cikin Shesshekar kuka jahad tace"Taya za'ae kiga gawarshi!nace maki ko ƙashi ba'a samu ba daga sassan jikinshi,Saboda ya ruga da ya ƙone ƙurmus ya zama toka,"

  "Jahad ni ban yarda ba,Allah Junaid ɗinmu bai mutu ba,ki daina wahalar da kanki wurin faɗa mun,"

  Rai a6ace Jahad tace"Wlh dole ki yarda Sehrish!meyasa zakiyi mun haka!Maimakon ki tayani jimamin rashin shi amma shine kike ƙara jefa ni cikin damuwa,"

   Girgiza kai sehrish ta shiga yi tana faɗin'wlh bazan yarda ba,"tashin hankaline yasa Sehrish ta burkice mata,

  "Ko kin ƙi ko kin so dole ki yarda Sehrish,Junaid has gone forever,"

  Miƙewa Sehrish tayi jiki ba ƙwari ta nufi toilet,Shigewa ciki tayi tare da jan ƙopar ta rufe,

  Zuƙunnawa tayi ajikin ƙopar,sai lokacin ta fashe da matsanancin kuka kamar ranta zai fita,

  "Allah sarki Junaid,Allah ya jiƙanka,bazan ta6a mantawa da halarcin da kayi mun ba,

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post