🔥🔥 *_KUFAN WUTA_* 🔥🔥
Free page 01
*TAFIYA DA GWANI ME DADI*
*ZAFAFANKU BIYAR sune suka sake dawo muku da wasu sababbin tsararru kuma zafafan labaransu guda biyar kamar yadda aka saba*
RAYUWAR MACE
rano
NOOR ALB
Mamuhghee
MASARAUTA
miss xoxo
BAK'AR INUWA
Billyn Abdul
KUFAN WUTA
Huguma
Zaku samu gaba daya labaran akan naira
1k kacal
2_400
3_500
4_700
*Zaku saka kudin ta wannan account din*
1487616276
BILKISU IBRAHIM MUSA
ACCESS BANK
*SAI KU TURAWA WANNAN NUMBER SHAIDAR BIYANKU*
09032345899
*KATIN MTN KUMA*
09166221261
*_TEAM ZAFAFABIYAR_*
_MUJE ZUWA_🏃🏾♀️🏃🏾♀️🏃🏾♀️🏃🏾♀️🏃🏾♀️🏃🏾♀️
Dogon layi ne sosai kamar irin na kowacce unguwa ta masu matsakaicin qarfi,hagu da dama na layin gida jene a jere na masu matsakaiciyar rayuwa,wadanda basu cika mugun kyau ba,kamar yadda kuma basuyi lalacewa da rashin kyan gani ba,duk da cewa wani gidan yafi wani kyau,kamar yadda kowa da irin yadda ubangiji S W T ya tsara masa matakin rayuwar da zai wanzu a kai.
Yawancin gidajen plate ne masu soraye,masu ginin benen daga cikinsu 'yan qalilan ne,haka nan gaban gidajen akwai kwata wadda tabi ta kowanne qofar gida,saidai kuma a rufe take da slap,duk da cewa zakaga daya biyu na wani gurbi da babu slap din,gurbin dake nuni da cewa cirewa yayi ko karyewa,ko kuma an tsigeshi ne bisa qarfi da da yaji,da kuma qiriniya irin ta yara,wanda bisa dukkan alamu ma slap din an hada taro da sisi ne daga mazauna layin an ginashi.
Daga can tsakiyar qarshen layin,wanda zaka iya karya kwana ta shiga dakai wani layin daban,dandazon yarane a tsaye carko carko sunata hargowa,idan daga nesa ka taho,zaka iya hangen yadda qura take tashi a wajen,alamu dake nuna cewa fada ake sosai a wajen.
Idan ka duba tsakiyar wajen sosai,yara ne guda biyu,wadanda gaba dayansu ba zasu zarta shekara goma ba gaba dayansu,'yar baqar dirarriyar yarinyar nata qoqarin kada abokiyar fadan nata,wadda idan kayi mata kallon farko ba zaka zaci zata iya dambe haka da abokiyar fadan nata ba,kasancewar bata kai wancar garin jiki ba,fara ce ba sol ba,kana iya hangen doguwar sumar kanta me santsi yadda ta debi qasa da yashi na wajen,sakamakon cirewar danwakalin kanta,baya ga hijabinta data ci damar dashi tun daga sanda za'a fara fadan.
"Iman.....iman.....ga malam nan" wata yarinya ta qaraso wajen bayan taja birki tana haki,da alama daga wani sashen ta kwaso gudunta ta kuma tuqe a nan.
Sarai iman din ta jita,saita qara himma da hanzarin ganin ta yar da rahama kafin malam din ya qaraso,ta tabbatar matuqar bata gama ba ya qaraso fadan yazo qarshe,hakanan kuma babu makawa itace me laifi a wajen malam din,koda kuwa ta fisu gaskiya.
Saidai bata kai ga cimma burin nata ba taji tsawar malam din a kanta
Dattijon mutum,wanda a qalla shekarunsa sun tasamma hamsin,sanye da fararen kaya qal,riga 'yar ciki da wando,sai babbar riga malum malum,kansa sanye da farin rawani,hannunsa dauke da buzu daya nade wani abu a ciki,daya hannun nasa kuma yana riqene da baqar leda
"Ke hajaru,kinci gidanku!,saketa nace" Ya fada cikin kaushin murya idanunsa duka bisa yarinyar.
Tunkude rahama hajar iman tayi,ta duqa tana kwasar takalmanta da dankwalinta da suka turbude cikin qasa,ranta a bace na rashin samun damar tumurmusa rahama da batayi ba,dai dai lokacin malam ya waiwaya ga yaran yana musu fada,tare da kora kowa zuwa gida,bayan ya bude ledar hannunsa ya fidda alewa ya rarraba musu.
"Muje gida ke kuma,'yar qaniya" ya fada yana tasa qeyar iman zuwa gida,suna tafe yana mata sababi har suka isa qofar daya daga cikin gidajen dake jere a layin.
Tun daga qofar gidan zaka karanci cewa gida ne na makaranta,ma'ana gidan da ake karantar da almajirai,saboda babbar rumfar kwanon da tabarmi dake malale saman simintin dake qasan rumfar kwanon,tun daga malalen simintin,tabarmin dake shimfide din zuwa qasar dake gaban gidan a share wajen yake fesss,kai kace lomar tuwo zata fadi ka duqa ka dauka abarka kaci saboda tsabar tsabta.
Da hanzari almajiran dake zaune a wajen,wadanda basufi biyar ba suka miqe
"Sannu da zuwa malam" duka suka furta,daya daga cikinsu ya matso yana niyyar karbar ledar hannun malam din,sai ya dakatar dashi
"Yi zamanka habu....inasu haladu?" Ya jefa tambayar ga daya daga cikin mazauna wajen,wanda ya fisu girma da wayo....
File name: KUFAN-WUTA-1.txt
File type: text/plain
Author: Huguma
File size: 259 KB
Domin saukewa a waya latsa