Kungiyar kwadago ta yi watsi da shirin Tinubu na biyan 'yan Najeriya N8,000

Kungiyar kwadago ta yi watsi da shirin Tinubu na biyan 'yan Najeriya N8,000

Kungiyar kwadago ta yi watsi da shirin Tinubu na biyan 'yan Najeriya N8,000

Babbar ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya ta yi Allah-wadai da matakin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na neman amincewar majalisar dokoki don karbar rancen naira biliyan 500 daga Bankin Duniya da nufin aiwatar da shirin da ta kira na bogi don rage raɗaɗin ƙarin farashin man fetur da aka yi babu lissafi.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban NLC, Kwamared Joe Ajaero ya fitar ranar Talata.

Sanarwar ta ce, "Shawarar biyan naira 8,000 ga magidanta miliyan 12 mafiya talauci a Najeriya tsawon wata shida cin mutunci ne da kuma ba'a ga haƙuri da imani da muke da shi a kan tattaunawa da gwamnati."

"Rashin tunani ne gwamnatin da ta haddasa tsananin wahala a kan mutane cikin ƙasa da wata biyuda hawanta mulki, sannan ta zo ta kawo wani ƙuduri wanda ƙarara zai saka wa masu kuɗi da ke riƙe da muƙaman gwamnati, ba tare da duba halin da talakawa ke ciki ba."

"Abin da hakan ke nufi shi ne gwamnati na neman hanyoyin da za ta sace dukiyar talakawa 'yan Najeriya, su kuma masu kuɗi su ƙara kuɗancewa."

NLC ta ce ba za a lamunci waɗannan ƙudurori ga ma'aikatan Najeriya ba kuma matakin ya fi kama da kama-karya don haka ya saɓa da tsarin dimokraɗiyya.

"Muna nanata cewa ba mu da ƙwarin gwiwa kan hanyar da aka bi aka tattara bayanan da ba sa canzawa na gidajen mutanen da suka fi talauci su miliyan 12, sannan ba mu da ƙwarin gwiwa a kan tsare-tsare da za su bi wajen raba wannan kuɗi."

Sanarwar ta ƙara da cewa matuƙar gwamnati ba ta son dakatar da irin waɗannan matakai da suna rage raɗaɗi, za su tilasta mu sae nazarin matakinmu na tattaunawa da gwamnati a kan wannan batu mai cike da ɓacin rai kuma za mu yi gaban kanmu.

Source: BBC

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post