BBC/REUTERS |
Shugaban sojojin Wagner, Yevgeny Prigozhin, ya yi maraba da juyin mulkin da sojoji suka yi a Jamhuriyar Nijar.
Wani kamfani da ke da alaƙa da ƙungiyar Wagner ɗin ne ya fitar da sautin muryar Mr Prigozhin, inda ya ke magana kan juyin mulkin.
A cikin sautin muryar da ba a tantance sahihancin sa ba, ya bayyana hamɓarar da gwamnatin Bazoum a matsayin yaƙi da masu mulkin mallaka.
Dakarun Wagner na ayyuka a wasu ƙasashen Afirka inda aka zarge su da aikata laifuka.
Duk da rashin nasara a boren da wagner ta yi a Rasha, shugaban ƙungiyar ya cigaba da ayyukansa.
A ranar Alhamis wani bidiyo ya nuna Mista Progozhin ya na ganawa da jami`an gwamnatin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.