TSARIN GASAR KACICI-KACICI NA TASKAR NASABA 2023


Health College

TSARIN GASAR KACICI-KACICI NA TASKAR NASABA 2023

#

TSARIN GASAR KACICI-KACICI NA TASKAR NASABA 2023

GasarTaskarNasaba2023 

1. A zango na farko za mu yi amfani da tambayoyi 40, in da za a amsa a minti 20, mutum ashirin (20) da suka fi samun maki za su tsallaka zuwa zagaye na biyu. 

2. Zango na biyu tambayoyi 30, in da za a amsa a cikin minti 15, mutum Goma da suka fi samun maki za su je zagaye na uku. 

3. Zango na ƙarshe (uku) tambayoyi 20, za'a amsa a minti 10, mutum Biyar da suka sami nasara za a fitar da Gwarzo/Gwarzuwa a cikin su, in da za a cire na ɗaya zuwa na biyar (1-5) 

4. Za a sanyawa dukkan wadda suka shiga gasar lamba kamar haka (TNKCKC0001) har zuwa na ƙarshe, wadda kowa da shi za a ba shi lambarsa kai-tsaye da zai shiga gasar bayan ya cike a shafin Google form. Idan aka zo fitar da wadda suka yi nasara sai a fitar da lambar saboda kiyaye sirri.

5. Ɓangaren da za a bai wa mahimmanci su ne; Dukkan manufofin Taskar Nasaba, wadda suka haɗar da; Harshe da Adabi, da Al'ada, da Tarihi da Yawon Buɗe Ido, da kuma Al'amuran Yau da Kullum.

6. Za a tsara Google form guda uku ne na kowane zango (1-3) a yi masa nasa. Bugu da ƙari, form ɗin zai tafi da lokacin da aka tsara wadda loto na cika zai rufe kansa kamar yadda aka tsara shi. 

7. Kowa ya na da damar shiga gasar a duk in da yake a faɗin duniya, gasar za ta gudana cikin harshen Hausa zalla, kuma za a taɓa dukkan al'amura da ke nahiyar Afirka da ma duniya gaba ɗaya. 

Har ila yau, gasar za ta fara ne ranar Asabar 08/07/2023 zuwa Litinin 10/07/2023 daga ƙarfe tara na daren kowace rana (09:00pm). 

Duk wanda keson shiga gasar sai ya shiga wannan maɓallin: http://tinyurl.com/TNKCKC2023

8. Bayanai da za a cike a lokacin shiga gasar:

- Suna

- Adireshin Imel

- Jiha 

- Ƙasa

- Ranar Haihuwa 

- Lambar Waya 

- Maɓallin Taken gasar da za a saka a shafukan sada zumunta, 'hash tag' #GASARTASKARNASABA2023 

- Facebook

- Twitter 

- Instgram

Dama ce a gare ku domim haɗin guiwa ko bada tallafi ko ɗaukar nauyi ko kuma bada tallace-tallace, a tuntuɓe mu kai-tsaye.+2349071237014,+2348035880730, Taskarnasaba001@gmail.com


Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post