Wahalhalun da ƴan Najeriya ke fuskanta za su zamo daɗi nan gaba- Tinubu


Health College

Wahalhalun da ƴan Najeriya ke fuskanta za su zamo daɗi nan gaba- Tinubu

 

Wahalhalun da ƴan Najeriya ke fuskanta za su zamo daɗi nan gaba- Tinubu
BBC

Shugaban Bola Ahmed Tinubu ya yi kira ga al'umma, musamman matasan ƙasar da su ƙara haƙuri kan halin matsin rayuwa da suke fuskanta a yanzu.

Tinubu ya bayar da tabbacin cewa wahalhalun da ƴan Najeriya ke fuskanta a yanzu za su zamo daɗi a nan gaba.

Shugaba Tinubu ya bayyana hakan ne ranar Alhamis a fadar gwamnatin ƙasar yayin da ya karɓi baƙuncin shugabannin matasa na jam'iyar APC daga jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya, Abuja.

Ya shaida wa matasan cewa gwamnatinsa za ta yi aiki tare da matasa a dukkan matakan da za ta riƙa ɗauka, ya kuma ƙara da cewa "ba zai yi shakkun ɗaukar kowane mataki da zai kawo ci gaba da haɗin kan ƙasa ba."

Shugaba Tinubu ya ce ya fahimci irin raɗaɗin da ƴan ƙasar ke ciki "Na yi rantsuwa ga ƙasata cewa ba zan yi shakkar ɗaukar kowane irin matakin da zai samar da ci gaba da tabbatar da haɗin kan ƙasar nan ba.

"Matakan farfaɗo da tattalin arziki kan ɗauki lokaci kafin a fara ganin alfanunsu. Ku ƙara haƙuri kaɗan."

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post