Wasan Kanawa da Zage-Zagi

Wasan Kanawa da Zage-Zagi

 

Wasan Kanawa da Zage-Zagi
Dandalin Taskar Nasaba

Kamar yadda masana tarihi kan faɗa, “Mai ƙarfi shi ke da iko.” To, a wancan zamani, daular da ta yi ƙarfi sai ta yunƙura ta je ta mamaye wata. To, in da aka yi nasara, sai ka ji, amma in da aka gwabza, aka yi kare jini biri, ko kuma kowa ya tare kan iyakarsa, sai ka ji irin waɗannan wasannin su na aukuwa.

Haka ma in da aka sami nasarar cin su da yaƙi, sai ka ji irin wannan wasanni su na faruwa. Misali; Za mu ga Katsinawa da Gobirawa ana irin wannan wasa.

To, Kanawa da Zage-Zagi ma akwai wannan wasa, cewa ita Sarauniya Amina ta kai hari Kano har Ƙofar Mata. Wannan ƙofar an nuna cewa, nan ne aka dakatar da Sarauniya Amina, aka hana ta shiga cikin birnin Kano.

A wancan zamani na mulkin Haɓe dai, an ce wani sarkin Kano ya kawo farmaki har Zariya, amma aka tare shi a tsakanin yankin da a yanzu aka sani da Ƙaramar Hukumar Kubau, wajen garin Kargi. Aka yi ba-ta-kashi.

Saboda haka, ba mamaki ka ji ana wasa tsakanin Fulani da Barebari, tsakanin Katsinawa da Gobirawa, tsakanin har Yarabawa da Gobirawa. Kuma za ka ga irin wannan wasa ya na daɗa ɗinke zumunci ne, ba ya na ɓatawa ba ne.

Wannan dai duk a zamanin mulkin Haɓe ne aka yi ire-iren waɗannan hare-hare. Amma yayin da aka sami shigowar Daular Usumaniyya, sai ƙasashen suka zama ɗaya, Addinin Musulunci ya haɗe su. Saboda haka, wata ƙasa ba ta kai wa wata ƙasa farmaki ba a cikin tutocin da Shehu Usmanu Ɗanfodiyo ya kafa. Sun zama abokan aiki, abokan hulɗa, kuma abokan shawarar juna.

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post