Cire Tallafin Man Fetur, Abinda Ya Kamata Gwamnati Ta Yi - Ƙwarmazan Zazzau
Health College

Cire Tallafin Man Fetur, Abinda Ya Kamata Gwamnati Ta Yi - Ƙwarmazan Zazzau

Cire Tallafin Man Fetur, Abinda Ya Kamata Gwamnati Ta Yi - Ƙwarmazan Zazzau


A iya nazari na, ban ga wata hanya mafi sauƙi da gwamnati ke rage raɗaɗin talauci ga al'umma kamar tallafin man fetur ba. Ta wannan hanƴa ne Ƴan Najeriya ke samun sauƙin farashin kayan masarufi gaba ɗaya. Ta hanƴar wannan tallafin ne hatta farashin gishiri da magi ke sauƙaƙa.

Tun daga kan gwamnatin Jonathan har zuwa yau, dalilan da gwamnati ke bayar wa kan cire wannan tallafi shine, "kawo mai yawa daga kuɗaɗen da ake kashewa wajen bada wannan tallafi na zuwa aljihun wasu Ƴan tsiraru ne kawai", ba wai tallafin bashi da alfanu ba. Ko da wannan dalilin gaskiya ne, a ƙalla talaka na amfana, ba wai waɗancan tsirarun mutanen Kaɗai ke amfana ba.

A tunani na, idan har gyara gwamnati keso tayi ta yanda kowani Ɗan Nijeriya zai amfana, ba cire wannan tallafin ya kamata tayi ba. Kamata yayi ta tsaftace hanƴoƴin da take bada wannan tallafin ta hanƴar toshe duk wata kafa da ake amfani da ita wajen karkatar da wani ɓangare na wannan tallafi zuwa aljihun wasu tsiraru. Ta tabbatar ta samar da hanƴa ɗaya tilo na bada wannan tallafi ko da kuwa zata Ƙirƙiro wata ma'aikata ta musamman ce domin aiwatar da hakan.

Tunda kowa yasan tallafin nan zai amfanar da duk ƴan Nijeriya, me zaisa saboda wasu Ƴan tsiraru da gwamnati ke zargin su ke cinye kaso mai tsoka na kuɗin tallafin ta ɗauki matakin da duk ƴan Nijeriya sama da miliyan ɗari biyu (200M) sun shiga mawuyacin hali? Yin hakan ya ƙara sa talaka cikin halin ƙunci ne ba waɗancan tsirarun mutanen ba.


Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post