Furar DanΖ™o by π‘©π’Šπ’π’šπ’ 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 π‘ͺ𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 6

Furar DanΖ™o by π‘©π’Šπ’π’šπ’ 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 π‘ͺ𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 6

 

Furar DanΖ™o by π‘©π’Šπ’π’šπ’ 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 π‘ͺ𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 6

π“π²π©π’π§π πŸ“²

  πŸ«— π™π™π™π˜Όπ™ π˜Ώπ˜Όπ™‰π™†'π™Š.....!!πŸ«—

           π‘©π’Šπ’π’šπ’ 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 π’„π’†πŸ€™πŸ»

π‘ͺ𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 6️⃣

.......Shiru kawai yay yana kallon takarda da key Ι—in motar da sakatariyarsa ta kawo masa na tsawon lokaci, kafin ya furzar da huci mai kauri ya tashi zaune sosai da ga kwanciyar da yay a kujerar office Ι—in nasa. Wayarsa mai Ζ™yau da Ι—aukar ido ya Ι—auka. Har yay dailing number da akai saving da _Yaya Isma'il_ sai kuma ya katse yana Ι—an girgiza kansa. Dan ya san halinsa, wani lokacin ba gane abubuwa yake ba birkitaccen mutum ne. Wata number ya sake lalubowa yay dialing, ring biyu aka Ι—auka. 

        “Uncle You.. Good Afternoon”.

Aka faΙ—a daga can, muryarsa a sauΖ™aΖ™e ya amsa da “Afternoon dear! How are you?”.

    “Am good Uncle”.

“Haka ake so. Lulu ta dawo ne?”.

   “Yes Uncle tun ma Ι—azun. Sai dai tanata masifa wai Uncle Smart ya barta a airport. Amma Deen ya ce ta masa ihu ne a gaban mutane kuma bai mata komai ba kadai santa. Yanzu kuma Daddy ya goya da bayanta wai zata walaΖ™anta shi ta koreshi. Uncle ALLAH ni bana so sumasa haka, shi Ι—in mutum ne nutsatstse”.

        Wani Ι—an murmushin takaici yayi da gyada kansa kamar yana a gabansa. “Karka damu Son! bazan bari su aikata hakan ba insha ALLAHU. Kuma zai dawo aikinsa”.

    Sosai yaron ya shiga ihun murna daga can. Shi kuma ya katse wayar yana mai jin takaicin hali irin na Ι—an uwansa. Yanda yake training rayuwar Mawaddat na Ι“ata masa rai. A rayuwa ko Ι—a namiji ne bazakace komai ya nema sai ya samu ba duk arziΖ™inka da matsayinka. Balle mace da wataran aure zatayi ta koma Ζ™arΖ™ashin ikon wani. Wanin da ba lallai shi ya iya Ι—aukar waΙ—an nan Ι—abi'un nata marasa Ζ™yau ba. Da wannan Ι“acin ran yabar office ranar. Kai tsaye gidansa ya nufa dake anguwar ta Hotoro GRA shima. Sai dai ba street Ι—in su Ι—aya da gidan yayan nasa ba. Da gudu Ζ™yawawan yaransa guda uku masu kama da shi sukazo tarbarsa. Murmushi yayi cike da jin daΙ—i, gaba Ι—aya ya haΙ—asu ya rungume a jikinsa bayan sun gaidashi. Yana Ζ™oΖ™arin miΖ™ewa da Ζ™aramin Deen da sukaje Ι—aukar Lulu airport mai wayon tsiya a hannunsa idonsa ya sauka akan matarsa. Ƙyakykyawar mace Ζ΄ar duma-duma. Murmushi ya sakar mata kamar yanda take masa itama, ya miΖ™a mata hannu alamar tazo itama. A hankali ta Ζ™araso ta shige jikinsa, rungumeta yay da sumbatar goshinta kamar yanda ya saba. Ko'a jikin yaran dan sun saba ganin hakan ga iyayensu, basa aikata wani abu dazai lalata musu tarbiyyar yara, amma su tarbi juna yayin da wani yay Ι—an nesa da gida kona yini guda ne sun nunama yaransu hakan ba komai bane face Ζ™auna, kuma ya halatta miji yayma matarsa, idan sunga hakan ko'a wani waje ba haramun bane ba. Shiyyasa suma yaran suke kallon hakan a normal ne.


        Da Ζ™yar ya samu ya gudarma Deen dake bashi labarin faΙ—an aunty Lulu a airport. Bayan yay wanka falon ya dawo ya zauna cikinsu yana shan fruit salad. Matarsa Saleeha da kowa ke kira da Aunty a family Ι—in ta kallesa cikin damuwa da sauΖ™aΖ™a harshe. “Abul Mahsin kamar kana cikin damuwa? Wani abun ya sake faruwa ne a office Ι—in?”.

      Ƙaramin tsaki yaja da Ι—an girgiza kansa. Kamar bazaice komai ba sai kuma ya numfasa. “Mawaddat! Halin yarinyar nan nacimun rai matuΖ™a Sweetheart. Kullum maimakon abubuwan su dinga sauΖ™i tana hankali amma sake jagulewa yake. Abinda yafi Ι“atan rai Yaya. Shi sam nunawa yake kamar ma komai yana tafiya daidai ne a rayuwar yarinyar. Safiyya ina tsoron UBANGIJI ya tuhumemu akan amanar da baiwar ALLAHr nan ta tafi tabar mana fa...”

       “Tabbas hakane, to amma ya zakayi tunda Yaya yana sama da kai ne. Ita kuma Ι—abi'un sun riga sun shigeta tankwarata abune mafi wahala duk da ma kana iya bakin Ζ™oΖ™arinka tun bata kai haka ba. Amma babu abinda ya canja”.

     “A wannan karon ina son ya canja kota Ζ™arfi Saliha. Dan gaskiya na gaji da gani, bana son yarinyar nan ta kuma fi haka gagara...”

   “Tankwarawar ta Ζ™arfi kam akwai damuwa, dan shi icce tun yana Ι—anye ake tankwarashi. Idan ya bushe akace za'ayi zai iya karyewa. Sai dai ni inada shawara. A yanda Deen ya bani labarin abinda ya faru tsakaninta da drivern nan nasan zasu ce zasu koresa ne, inaga karka bari hakan ta faru, inma da dama ya zama driver nata ita kaΙ—ai, dan shi naga ba mutum ne mai wasa ba, ba kuma zai Ι—auki halinta ba”.

        A hankali ya sauke ajiyar zuciya. Sai kuma ya furta, “Nagode miki dan tunaninmu yazo Ι—aya. Sai dai magana ta gaskiya bamma san yanda zan tunkari yaron ba. Kedai kin san a yanda na samosa ai, aikin nan kuma yana yinsa ne saboda tsare mutuncinsa bawai irin sauran drivers nada bane da take takawa yanda take so. Sannan Aliyu yanada zuciya fiye da yanda kike tsammani da hasashe bar ganinsa hak shiru-shiru baya son magana”.

     “Duk Ι—an halak dole ya kasance mai kishin kansa Abul Mahsin. Sannan wannan itace cikar kamalar duk wani Ι—an adam na Ζ™warai. Karka Ζ™asΖ™antar da kanka ga kowa ga komai saboda talauci, ka kasance mai tsaftatacciyar zuciya a baΙ—ini da zahiri, ka kuma zama jarumi a neman na kanka koda duk jama'a na kallon hakan da faΙ—uwa. Ni nasan baka kawosa yay wannan aikin da Ζ™asΖ™anci ba, sai dan wani dalilinka da kuma kare mutuncinsa daga taΙ“arΙ“arewar abubuwan da ba'asan mafari ba a rayuwarsa. Kamar yanda kuka samu mahaifinsa a farko kai da Ahmad yanzu ma ku sake samunsa insha ALLAHU zai dawo ya cigaba har ALLAH shima ya kawo masa iyakar komai na jarabawarsa”.

      “Shike nan in sha ALLAHU zan gwada nagani. Ita kuma zuwa anjima zanje gidan na sameta”.

   “Hakan yayi, amma Please smile”. Ta faΙ—a tana kwatantawa da hannunta a kan baki. Hararta yay yana sakin murmushin.....


           ∆••••∆ ★ ∆••••∆


   Washe gari ma baiyi yunΖ™urin zuwa aiki ba, sai ma tunanin neman wata mafitar da ya tashi da shi. Kamar yanda ya saba bayan dawowa sallar asubahi ya shiga sashen mahaifinsu domin gaishesa duk da tare suka fita massalaci suka kuma dawo. ƘyaΖ™yΖ™yawan dattijon mutum mai cike da tarin nutsuwa. Da ga gashin kansa har zuwa na gemu fari ne fat. Duk da tsufansa ya bayyana a kallo guda zaka tabbatar da zamanin Ζ™uruciya ansha Ζ™yau. Duk da ya Ι—an Ι—ago ya dubesa a lokacin da yake shigowa bai ajiye littafin dake a hannunsa ba. Sai ma Ι—an turΙ“une fuska da ya sake yi. Tsahon mintuna uku baida alamar kulashi, har sai da wasu samari biyu suka shigo, abin mamaki sai ga murmushi ya mamaye fuskar tashi, ya ajiye littafin cike da kulawa idonsa akan samarin dake gaishesa bayan sun ma Uncle Smart kallo Ι—aya a gatsine sun Ι—auke kai. Oho baima san sunai ba, dan basu isa masa a ido cikin ido ba.

       “Abba Barka da safiya”.

Suka faΙ—a kusan a tare. Cike da kulawa yake jinjina musu kansa. Ya amsa da “Har an shirya fita kasuwar? Ζ³an albarka”.

     “Eh Abba”.

Suka bashi amsa suna miΖ™ewa. Albarka ya shiga saka musu, suko tunda suka amsa sau Ι—aya ma basu sake ba. Har zasu fice ya dakatar da su. Cikin Ζ΄ar damuwa yake kallonsu. “Nabeel yau kam da ban takuraku ba da kun bama iyayenku kuΙ—in cefane. Na tashi banda ko nera a jikina gashi babu hanyar samuwarsu garan a yau”.

      A turΙ“une wanda aka kira da Nabeel ke dubansa. Bakinsa a sama ya ce, “Abba kafa san abubuwan sai a hankali. KuΙ—in cefanen gidan nan inba kaiba kuma wazai iya. Sannan jiya fa sai da kasa na baka dubu biyu”. 

     “Nima ai sai da na bashi dubu Ι—aya”.

   ΖŠayan ya amshe da sauri shima rai Ι“ace. Ɗan murmushi Abban yayi, yayinda Uncle Smart kejin wani irin raΙ—aΙ—in zantukansu ga mahaifinsu akan abinda bai taka kara ya karya ba. Mahaifinsu jarumin ubane da ya tsaya a kansu da Ζ™are Ζ™arfinsa wajen gina rayuwarsu. Amma yau sun zama wani abu kowa najin Ζ™yashin taimaka masa. Ɗari biyar-biyar suka ajiye masa saΙ“anin abinda ya tambaya suka fice rai Ι“ace. Gaba Ι—aya sai yaji jikinsa ya Ζ™ara sanyi, cikin Ζ™arfin hali ya fara gaida Abban dake sake Ζ™oΖ™arin Ι—aukar littafinsa bayan ya kwashe dubu Ι—ayan da suka ajiye masa. Maimakon amsa masa gaisuwar a zafafe ya ce, “Shima wannan aikin sun korekan?”.

    Kasa amsawa yayi ya Ζ™ara Ζ™asa da kansa zuciyarsa na Ζ™una. Ba'a kan Ζ™addararsa ba, ba kuma akan abinda mahaifinsa ke tuhumarsa ba, sai akan damuwa da halin da mahaifin nasu ke ciki....

      “Wai halan bada Ali nake magana ba?!”.

   Ya faΙ—a cikin fusata.  

“Kayi haΖ™uri Abba dama....”

“Dama mi? Mi kake son faΙ—amin? To wlhy bari kaji a wannan karon bazan Ι—auka iskancinka ba. Bari ma na faΙ—a maka gaskiya in har maganar banzarka ce da ka saba to a wannan karon ka shirya barmun gida, dan bazan iya cigaba da wahala da kai ba bayan wadda nayi kana yaro. Na ciyar da kai abinci, na tufatar da kai sutura, na sakaka a makaranta islamiyya data boko har matakin digiri na biyu sannan na cigaba da wahala da kai. Ga kanenka nan na bayan baya sun tsaya da Ζ™afafunsu harda masu aure amma kai ban daina cidaka abinci ba, wannan wace irin rayuwa ce. To ba asiri ba a wannan karon ko kukar bulukiya aka sauke a kanka bazan Ι—auka ba na gaji da shashancin ka, tashi ka ficemin daga nan na baka zuwa dare wlhy ka tsara mai yuwuwa sakarai kawai cima zaune”.

         Idanunsa da suka kaΙ—a sukai jazur ya Ι—ago kaΙ—an ya subesa. “Kayi haΖ™uri Abba ALLAH ya huci zuciyarka, dan ALLAH ka gafarce ni”.

    Banza ya masa bai sake tankawa ba. Yasan minene shiru a wajen mahaifin nasu. Dan haka ya miΖ™e ransa a matuΖ™ar Ζ™untace ya fice. Har ya nufi hanyar sashensu na samari ya fasa. Ƙirjinsa zafi yake masa. Ji yake kamar ya saki kuka amma bazai iyaba saboda taurin zuciyar tsiyarsa. Sosai mutane ke kai kawo a cikin layin nasu. A halin da yake ciki baya buΖ™atar yin magana da kowa, dan haka yay Ζ™oΖ™arin juyawa zai koma ciki. Daga motar da tun fitowarsa idonsa ya sauka a kanta amma ya kauda kai aka danno masa horn. Ƙin juyawa yay har sai da aka sake na biyu da ambaton sunansa. Cak ya tsaya amma bai juyo ba har Uncle Yousuf da abokinsa Ahmad suka Ζ™araso garesa.

       “Kayi haΖ™uri”.

    Kalmar data tilastashi juyowa da ga bakin Uncle Yousuf..........✍️



_Alhmdullah, mungode da haΖ™urinku. Bari muga a fara ko kaΙ—an-kaΙ—an kafin na murmure. Mungode sosai da addu'oin kuπŸ™._



_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_


*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*


FURAR DANKO

Billyn Abdul


-ZAFIN KAI

Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI

Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI

Miss xoxo

Duka hudu 1k

Uku 800

Biyu 600

Daya 400

Pay atπŸ‘‡

1487616276 

Access Bank

Bilkisa Ibrahim Musa

Sai katura shedar biyanka ananπŸ‘‡

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura ananπŸ‘‡

09033181070

Ζ³an Niger kuma ga naku. Kuyi magana ta wannan number Ι—inπŸ‘‡

+22799643131

VIPπŸ”₯πŸ’―

Zafin kai 3k

Furar danko 3k

Tabarmar kashi 3k

Bakon munafuki 3k

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*πŸ₯°

Zafafa🫢πŸ”₯

*_ALLAH ya gafartama iyayenkuπŸ˜­πŸ™_*

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post