Furar DanΖ™o by π‘©π’Šπ’π’šπ’ 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 π‘ͺ𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 7

Furar DanΖ™o by π‘©π’Šπ’π’šπ’ 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 π‘ͺ𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 7

 

Furar DanΖ™o by π‘©π’Šπ’π’šπ’ 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 π‘ͺ𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 7

π“π²π©π’π§π πŸ“²

  πŸ«— π™π™π™π˜Όπ™ π˜Ώπ˜Όπ™‰π™†'π™Š.....!!πŸ«—

           π‘©π’Šπ’π’šπ’ 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 π’„π’†πŸ€™πŸ»

π‘ͺ𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 7️⃣

.........Hannu ya basu batare da ya yarda ya kallesu ba. Uncle Yousuf yay murmushi da amsar hannun sukai musabaha bayan ya gaisa da Ahamd dake Ζ΄ar dariya saboda harar da Uncle Smart Ι—in ke masa Ζ™asa-Ζ™asa. 

        “Idan ban takura da yawa ba ina son muyi magana Please Smart Mawashi”.

     Karan farko ya Ι—an Ι—ago idanunsa da har yanzu suke da damuwa ya dubi Uncle Yousuf mai maganar. Kamar zaiyi magana sai kuma yayi shiru. Uncle Yousuf ya sake murmusawa da faΙ—in, “Please”.

        Bashi da yanda ya iya dole ya amince masa, sai dai maimakon cikin motarsa da ya buΖ™ata suje anan cikin soron gidansu suka zauna saman bench. Shiru na wasu mintuna kafin Uncle Yousuf ya nisa. “Jiya na dawo na samu takarda da key Ι—in mota a hanun sakatariyata Aliyu, sai dai ban gamsu da bayanin dana gani a rubuce ba shiyyasa nace Ahmad ya rakoni nazo da kaina”. Ya Ζ™are maganar idonsa a kansa alamar son jin amsa. 

       “Na ajiye aikin ne kawai”.

   Ya faΙ—a cikin dakewarsa.

“Ko miyasa?”.

Ahmad ya tambaya cikin kafesa da idanu.

Kansa ya jinjina yana Ι—an furzar da iska, sai kuma ya dubu Uncle Yousuf maimakon Ahmad da yay tambayar. “Saboda bazan iya ba Alhaji. Ni mutum ne da ba komai zuciyata ke iya Ι—auka ba duk da na kasance talaka mai nema.”

      “Haka ake so duk mutum na Ζ™warai ya kasance Aliyu Hydar. Amma har yanzu baka faΙ—a mana dalilin ba?”.

    Murmushi ya saki mai ciwo a karo na farko. Ya Ι—an dubi Uncle Yousuf Ι—in sai kuma ya Ι—auke kai. “Miye amfanin maimaita abinda bashi da muhimmanci koya wuce Alhaji. Kawai na ajiye shikenan ya wuce. Nasan insha ALLAHU zaku sami wanda ya fini, ni kuma zan tara gaba maybe abincina ba'a nan yake ba”.

         “Nasan bazaka juraba kamar na baya da suka shuΙ—e domin Kanada banbanci da su. Sai dai irinka na jima ina fata ni kuma, dan kai kaΙ—aine zaka iya da ita har ma ka tankwarata. Har yanzu nasan baka san ni wanene ba Aliyu Hydar, sai dai ka sani ban nema kamin wannan aikin ba dan kana buΖ™atar aikin da kuΙ—i zai shigo maka. Tun randa na ganka wajen abokina yayan abokinka Ahmad naji a raina ka cancanta zama wani Ι“angare da zai jagoranci haska wata fitila ta rayuwarta. Ita Ι—in a fanΙ—are take, tabbas a haka ta tashi shiyyasa tanΖ™warata yayma kowa wahala a cikinmu. Ada kallon komai muke a bigire na Ζ™uruciya da tunanin wata rana zata daina, sai dai ranar har yanzu taΖ™i tazo, bamu san kuma ranar da zata zo ba, ko kuma tazo ne ta wuce batare da mun farga ba oho?. Nasan kana da Ζ™anni mata maybe ma harda yayu, kasan irin zafin da nakeji a raina koda a kwatance ka kwatanta da ace sune, miyasa bazaka gane ba ne....?”

      Yanda ya Ζ™are maganar a raunane cikin sigar tambaya yasa Uncle Smart fesar da iska mai nauyi. A Ι—an zafafe batare daya dubesu ba yace, “In dai har ku da kuka haifeta kun gagara tanΖ™warata ni kuma taya kuke tunanin iyawa? Mahaifinta fa na raye, hakama mahaifiyarta, sannan gaku ku Ζ΄an uwanta, Alhaji Please kayi haΖ™uri bazan iya ba fa. Bana son raini, bana iya jurarsa ga kowa. Bana son wulaΖ™anci ko Ζ™asΖ™anci duk da kasancewata talaka mai nema. Ina ganin kimarka dan ALLAH karka bari mu shiga wata hanya daba ita ta dace mukai ba dan alkairi ya haΙ—amu kuma bazan taΙ“a na manta da kai ba, dan kamun abinda mutane da yawa basu minba na alkairi ka gaida gida”. 

       Yana gama faΙ—a ya miΖ™e. Dakatar da shi Ahmad yayi, kamar bazai tsaya ba sai kuma ya dakata tare da juyowa. MiΖ™ewa shima Uncle Yousuf Ι—in yayi yana Ι—an murmushi. Hannu ya kai ya dafa kafaΙ—arsa, “Shike nan na fahimceka kuma nagode sosai. Ina son mutum irinka mai tsayawa akan ra'ayinsa da riΖ™e mutuncinsa. Zan jima inajin raΙ—aΙ—in rabuwa da kai Aliyu. Amma dan ALLAH ina roΖ™on alfarmar kazo office ko zuwa gobe ne domin amsar hakkinka, kuma bana son kace da ni a'a”.

        Baki ya buΙ—e zai yi magana Ahmad ya dakatar da shi. “Dan ALLAH karkace a'a Smart, ban sanka da musu ba karka fara akan Yaya Yousuf, sannan kayi nazari akan roΖ™on da yay maka, nasan kanada damar taimakons.....”.

     Hararar da ya Ι—an ballama Ahmad Ι—in ce ta sashi yin Ζ™aramar dariya batare da ya Ζ™arasa ba. Ɗauke idanunsa yay da faΙ—in, “Shike nan insha ALLAHU idan na samu lokaci zanje, amma kai ma kasan kawai dai dan ta Yaya boss ne wlhy”.

        “Na sani Mawashi. Yaya boss kuma na godiya da wannan karamci”. Bai ce komai ba, sai murmushi da Uncle Yousuf dake saurarensu yayi. Har cikin rai Ι—abi'un yaron birgesa sukeyi matuΖ™a. Yana son ganin mutum mai nutsuwa musamman matashi kamar haka. Ba irin matasan yanzu da shegen rawar kai yayma mafi yawansu katutu ba...


     Har mota ya musu rakiya. Bayan wucewarsu sai yaji ya kasa komawa cikin gidansu dan baisan da wane irin harshe zaima Ammah bayani akan sake rasa wannan aikin ba shima, duk da dai jikinsa yay Ι—an sanyi da kalaman Ahmad na Ζ™arshe, amma dai bai yanke hukunci ba na sake amsar aikin har yanzu. Sai dai in ya tuno bayanin Abba ya kanji faΙ—uwar gaba. Tabbas yasan wanene Abbansu, sam baya magana biyu. Mutum ne tsayayye da idan yace e to e Ι—inne da har ransa. Idan kuma yace a'a to a'a Ι—in ce fa. Da Ζ™afa yabar cikin anguwar tasu, rashin abunyi da sanin ina zai dosa ya sashi miΖ™ewa a titi yay ta tafiyarsa kawai. Yayi tafiya mai nisa da bai san ina yake jefa Ζ™afa da Ι—aukewa ba ya fahimci kamar binsa akeyi a baya. Tsamm yayi na tsarguwa tare da tsayawa, sai dai abin mamaki babu alamar wani tare da shi a Ζ™afa, wanda ke a kan mashina ma da napep babu alama, hakama na mota. Dakewa yay ya cigaba da tafiyar, still dai ya sake jin tabbas akwai mai binsan. Yanzu kam bai juyo ba sai ya yanke titin ya shiga cikin wani layi, ya Ι—an yi nisa da layin sosai ya samu rumfar wasu masu kayan kafinta ya Ι—an dakata cikin dabara kamar mai gyara igiyar takalmi. Ta cikin mirror da aka jingine ya hango wasu samari biyu, sai dai suna Ι—an waskewa cikin Ι“adda kama. Hakan ya Ι—an bashi mamaki, dan shi dai a rayuwa duk da yana da tsatstsauran ra'ayi bashi da abokin faΙ—a. Cigaba yay da tafiyar dan son gane iya gudun ruwansu badan yasan sirrikan layukan inda yake ba. Sai da sukaje Ζ™arshen layin sosai ya fahimci akwai matsala, ya Ι—an ji wani abu a ransa amma sai ya dake, wata hanyar da yake Ζ™yautata zaton zata Ι“illesa da titi ya bi, sai dai yana shan kwanar tsukin wajen suka sami nasarar rufesa ruf ata gaba da bayansa. Ɗaya bayan Ι—aya ya bisu da kallo har ya sauke akan napep Ι—in da aka faka a gabansa. Cikin dakewa da ambaton sunan ALLAH ya ce, “Ku kuma fa?”.

     “Zaka sani amma ba'a nan ba”.

Ɗaya ya bashi amsa cikin gatse da nuna masa bindiga dake soke a Ζ™ugunsa. Bindiga bata kasance abar wasa ga kowa ba. Duk Ζ™arfinka da taurin kai a duk inda mai ita ya kasance shike zama a saman Ζ™arfin ikon ka. Dan haka ya shiga napep Ι—in zuciyarsa na saΖ™a masa abubuwa masu yawa game da mutanen. Biyun da suka dinga binsa ne kawai suka shiga gefe-da-gefensa, mai napep yaja suka fice daga layin, sai da suka fita gaba Ι—aya wanda ke gefen haggunsa ya jefa masa wani Ζ™yalle a fuska, da sauri na kusa da shi ya kama ya Ι—aure masa idanu yayinda wanda ya fara jefa Ζ™yallen ya Ι—ora masa bindiga a gefen ciki ta yanda bai isa musawa ba. Duk da ya sake firgita haka ya dake a zahirance, a baΙ—ini kuwa yana mai ambaton sunan ALLAH......


    Tofa, su kuma waΙ—an nan daga ina?. Wayyo Uncle Smart Ι—inmu😫😒


          ∆••••∆ ★ ∆••••∆


   Tun daga main falour na gidan kana iya jiyo tashin sautin kiΙ—an dake fitowa da ga Ι—akinta, duk da kiΙ—ane mai taushi na mawaΖ™iya Shakira yanda ta Ζ™ure voluen yasa ake iya jiyowa. Tun safe babu wanda zai ce ya ganta yau a gidan har zuwa yanzu da agogo ke nuna Ζ™arfe takwas da wasu mintuna. Mafi yawan yaran rai a Ι“ace suke fitowa daga Ι—akunan su dan sautin kiΙ—an data saka ya takurasu da hanasu barcin safen. Hatta da Ζ™ananun Suhaib da Imran da fita makaranta kan hakanasu barcin safen ji suke ta takura musu, musamman Imran dake son Ζ™arasa Assagment Ι—insa amma ya gagara fahimtar komai. Kaf Ι—insu sun gama hallara a dining, sai dai fuskar kowanne a turΙ“une da takaici. A haka Daddy da Mommy suka fito suka samesu, a kallo Ι—aya zaka fahimci itama Momy ranta a Ι“ace yake, sai dai shi Daddy kam ko'a jikinsa. Yaran ma na gaidashi bai wani saurarensu ba hankalinsa nakan kiran Tabawa mai aiki. Da Ι—an gudu-gudu ta fito a kitchen hannunta riΖ™e da Ζ™aramin ludayi da alama girki takeyi.

       “Babyna fa?”.

Ya faΙ—a kai tsaye yana nuna upstairs. Itama upstairs Ι—in ta kalla, cikin sake rissinawa tace, “Barci takeyi Alhaji, tace zuwa Ζ™arfe tara da rabi na tadata”.

     “Shi kuma wancan kiΙ—an da ga ina?”.

“Itace ta kunna”.

Nunin ta tafi kawai ya mata batare da ya sake cewa komai ba. Mommy da tai kicin-kicin da fuska ya kalla, sai kuma yabi sauran yaran nasa da kallo. Hafiz dake Ζ™oΖ™arin kai shayi bakinsa wanda a haihuwa shike bima Lulu ne ya ce, “Humm Daddy yanzu bazakace komai ba kenan?”.

    “Akan me?”.

“Aunty Lu. Ai ko kafiri ba kowa ke iya saka kiΙ—a ya kwanta da shi ba. Kuma ina da tabbacin ko sallar asuba batayi b.....”

     “Kai ban san shashanci da Ζ™azafin banza, wai Hafiz ita Ι—in sa'arka ce? Kuma kai ubanwa yace maka batai sallar ba”.  

    “Ai ba sai wani ya faΙ—a masa ba abinda kowa ya sani ne. Ni ban san wane irin makahon so kakema Mawaddat ba a gidan nan, kuma ka sani wannan ba gata bane kashe mata rayuwa kakeyi matsayinta na mace. Da haka kowace yarinya ake rainonta a gidansu da baka gammu haka ka aura ba matsayin iyayensu Alhaji. Dan ALLAH ya kake so nayi da raina akan Mawaddat ne?”.

       Wani banzan kallo ya galla mata ita da yaran baki Ι—aya yana cika da batsewa, sanin yanzu zasuyi sama ya sata miΖ™ewa tabar dining area Ι—in zuciyarta na Ζ™una da raΙ—aΙ—i. Ta rasa mike damun mijin nata akan babbar Ζ΄arsu mace, yana nuna mata Ζ™azamar rayuwa a matsayin soyayya, iya bakin Ζ™oΖ™arinta tana yi akan Mawaddat amma abubuwa sake taΙ“arΙ“arewa sukeyi. A hankali hawaye masu raΙ—aΙ—i suka silalo mata saman kumatu.........✍️





_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_


*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*


FURAR DANKO

Billyn Abdul


-ZAFIN KAI

Mamuhgee


-TABARMAR ‘KASHI

Safiyya Huguma


-BAKON MUNAFIKI

Miss xoxo


Duka hudu 1k

Uku 800

Biyu 600

Daya 400


Pay atπŸ‘‡


1487616276 

Access Bank

Bilkisa Ibrahim Musa

Sai katura shedar biyanka ananπŸ‘‡


09032345899


Idan katin waya ne kuma saika tura ananπŸ‘‡

09033181070



VIPπŸ”₯πŸ’―

Zafin kai 3k

Furar danko 3k

Tabarmar kashi 3k

Bakon munafuki 3k


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


*THANKS FOR CHOOSING US*πŸ₯°

Zafafa🫢πŸ”₯

*_ALLAH ya gafartama iyayenkuπŸ˜­πŸ™_*

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post