Nihaad page 28 by Khaleesat Haiydar complete

Nihaad page 28 by Khaleesat Haiydar complete

 

Nihaad page 28 by Khaleesat Haiydar complete

💖💖 *NIHAAD*💖💖

28

 Ganin Nihal taki tanka ta sai kuka take, Nihad ta mike da sauri ta koma cikin gidan zata kira Khalil, a bakin kofa ta kusa buge sa ya turata tayi baya xata fadi ganin hakan yayi saurin jawota ta fado chest dinsa, ta zaro ido ta daga kai tana kallonsa, ba tare da ya kalleta ba ya turata gefe ya sauka xuwa wajen Nihal, bin sa tayi da kallo, yana isa wajen ya durkusa gabanta a hankali yace "Ki yi hakuri Nihal, don't take all what she said personal" tana goge hawayen da ya ki tsaya mata tace "Ka bude min gate in tafi gida" Yace "Ba amfani hakurin da nake baki kenan?" ta girgiza masa kai kawai, yace "Now, Behave like the good girl u always are, tashi mu koma ciki" Daga haka ya mike, ita ma ta tashi tana ci gaba da goge idonta, yana gaba tana bin sa har xuwa parlon, Nihad ta riga su shiga parlon kafin su karaso, bayan sun shigo tana kallon Nihal a hankali tace "Kiyi hakuri plss, i didn't mean it" Nihal dai bata ce mata komai ba ta yi wucewarta daki, Nihad ta jefa ma Khalil wani kallo tace "Ai dai kaga abinda ka jawo, kawai ka sa yarinya a gaba kana koya mata gulma da munafurci alhalin ba halinta bane" Daga kai yayi ya kalleta, speaking calmly yace "Idan kina ci gaba da min rashin tarbiya, Billah xan tattara ki in mayar da ke kauyen can" Shiru tayi tana kallonsa, sai kuma ta 6ata fuska tace "Toh ni nace wani abu ne?" Bai sake kallonta ba, ta turo baki ta juya ta koma dakinta. Har Nihad ta gama shirin bacci Nihal bata ce mata komai ba, Nihad ta gama saka kayan baccinta wanda shi kadai ta tsira da shi a gidan ta dawo gefen Nihal da damuwa tace "Shine ina ta maki magana kin ki cewa komai ko?" Nihal ta daga ido ta kalleta tace "Me kike son in ce maki?" Nihad tace "Wallahi kema kinsan i didn't mean it, you know i love u to the extent that i will never hurt you" Nihal ta ɗan yi murmushi tace "Amma duk kwanan nan jaraba kike min a waya ai" Nihad ta marairaice tace "Toh me yasa xaki dinga magana da worst enemy dina a waya? Yanxu da Amina ce ke waya da shi ko wasu can daban ai ni baxan damu ba, amma ke fa kinsan i Cherish u so much, why will u be communicating with my worst enemy?" Nihal tace "Toh shikenan, na maki alƙawarin baxan sake waya da shi ba, dama yawanci ina ce masa ya kai maki waya ne...." Nihad tace "No, just block him kawai" Nihal tace "If that will please u" Tana fadin haka ta dauko wayarta tayi blocking number Khalil sanan tayi deleting number daga wayar tana kallon Nihad tace "Done!!" Nihad tayi Murmushi tace "Kin hakura yanxu?" Nihal tace "On one condition" Nihad na kallonta tace "Ina jin ki" Nihal tace "Ki tashi ki tafi dakinsa" da mamaki Nihad ke kallonta, can tace "Amma  ina ga baki da hankali, inje dakinsa inyi masa me? So now u are keeping it in mind cewar mijina ne shi da har xa ki ce in je dakinsa? Why will u leave such thought a xuciyarki idan har ke masoyiyata ce?" Nihal bata ce mata komai ba ta ja bargo ta lumshe ido, Nihad ta ja tsaki ta mike ta koma can edge din gadon, ta fi minti sha biyar zaune kafin daga karshe ta mike fuskarta daure tana kallon Nihal tace "If that will please you shikenan" Daga haka ta dau Hijab dinta ta fice daga dakin kamar xata tashi sama, bayan ta saka hijab dinta ta kunna wutan corridor din tana kallon kofar dakinsa, can ta kyabe baki a ranta tace ba gwara taje parlor ta kwanta abunta kawai, kashe wutan tayi ta karasa cikin parlon tana tafiya a hankali sbda duhu, laluban dogon kujeran da xata kwanta ta shiga yi bayan ta shigo tsakiyar parlon, a tsorace ta koma baya rana zaro ido bayan lalubenta ya kai ta har jikinsa, ya mike zaune yana haskata da karamar wayarsa, kunya taji ya kamata ta juya tana sosa kai xata bar wajen, yace "Da wani abun da kike so ne???" Ta juyo duk da bata ganin fuskarsa sbda haskata da yayi ta daure fuska tace "Wani abu kamar me?" Yace "Kin fi ni sani ai tunda kika biyo ni nan kina tattaba ni" Tsayawa tayi tana kallonsa kamar me son fahimtar abinda yake nufi, can tace "Kai kasan abinda kake nufi ni ban sani ba" yace "Aa ki dai fada abinda kike so" a takaice tace "Abinda ke ranka shi nake so" daga haka ta xabga masa harara xata bar wajen ya fixgota ta fado gefensa, a tsorace tace "Don Allah kayi hakuri wallahi kwanciya na zo in yi, ni ba wajen ka na zo ba" Cikin husky voice dinsa yace "Duk dakinki babu wajen kwanciya sai kin fito parlor?" Ta boye fuskarta a huge muscles dinsa tace "Nihal ce tace idan ina son ta hakura sai na je dakinka, to ni kuma ina son ta hakura" kallonta kawai yake yana kara tabbatar da ainahin childishness dinta, Wani sanyayyen kamshi ke tashi a jikinta har gashin kanta, lkci daya kuma ya hade rai ya saketa, ta dago kai a hankali tana kallonsa, matsawa yayi daga kusa da ita ya koma daya side din kujeran, With full audacity tace "Xan shiga dakinka in kwanta kuma kar ka sake ka shigo har sai na fito" Bai tanka ta ba, ita ma bata jira yace komai ba ta mike ta nufi dakinsa, murda kofar dakin tayi ta shiga tana bin ko ina da kallo, wani kamshi ke tashi a dakin, ta kalli jakarsa dake dakin ta juya ta kalli kofa, tana ta tsaye tana kallon kofar sai kuma ta nufi jakar ta tsugunna ta bude zip din, Chargern Iphone ta fara cin karo da, ta dinga kallon chargern tana jujjuyawa, wannan kuma na waye? Ko dai na Nihal ne? Tabe baki tayi ta ajiye, ta maida idonta kan Diary Milk chocolate masu uban yawa a jakar, kai....a ina ya samu kudin siyan wannan uban chocolate din, ko da yake kudin babanta ne, wato saboda samun waje har da su siyan chocolate, wani hoto ta gani ta dauka tana kallon matar da ke jikin hoton warce baxata wuce shekaru 54 ba, kana ganinta kaga halfcast, keenly Nihad ke kallon hoton tana ji a jikinta kamar ta ta6a ganin wannan matar, amma a ina?? Duk yanda ta so tunawa ta kasa, as in, she k6s sure ta ta6a ganin hotonta but where?? Bude kofar dakin aka yi ta mike a rikice, da sauri ya nufota ya warce hoton daga hannunta ya hadeta da bango yana mata wani mugun kallo lkci daya kamanninsa suka sauya, Sosai ta tsorata jikinta na rawa tace "A bude fa naga jakar xan...." Turata yayi har sai da ta fadi kasa rigijib, ya dau jakar gaba daya ya fice daga dakin. Da safe karfe tara saura khalil na zaune parlor Nihal ta fito, ta tsaya jikin kujera ta gaishesa ya amsa yace "How was ur night?" Tace "Alhamdulillah, Nihad bata tashi ba har yanxu?" Duk da tun jiya da daddare rabonsa da dakin bayan ya fita amma haka yace "Probably" Tace "Ohk, ni xan tafi" Yace "Ina za ki tafi?" Ta sunkuyar da kanta tace "Umma ta aikeni gidan wata frnd dinta in amsar mata sako, so karfe tara matar ke fita aiki, shine tace in je kafin tara" Khalil yace "But baki yi breakfast ba ai" Tace "Na tashi da azumi yau" Shiru yayi yana kallonta tace "Idan ta tashi kace mata naje amsar ma Umma sako" Yace "Toh mu je in ajiye ki" Da sauri tace "Aa ba fa nisa, kuma in sha Allah xan dawo anjima" Yace "Are you sure?" Tace "Sure" Yace "Toh Allah ya tsare" Tace "Ameen" Daga haka ta nufi kofa ta fita. Goma saura Khalil ya tashi ya shiga dakinsa don wanka yake son yi kuma yaga bata da niyyar fitowa, kwance ya sameta a kasa, ya tsaya bakin kofa yana kallonta, ta mike xaune cikin rawar tace "Ba shkkn ba hankalinka ya kwanta kafana na min ciwo yanzu" Kallon kafar yayi, kafin ya karasa kusa da ita ya durkusa ya daga kafar, ta sakar masa kuka ta janye, hade rai yayi yana kallonta sai kuma ya sake jawo kafar,  ihu ta kwala tace "Wallahi ciwo yake min" Targade ya ga tayi a kafar, ya mike ya fita daga dakin ta bi sa da kallo, da kyar ta iya daurewa ta shiga bandaki da asuba ta wanke bakinta da mouth wash ta dauro alwala ta fito tayi sallah, kamar kar ta ɗan motsa xuwa bandakin shine kafar yayi mata tsami kafin gari ya waye, dawowa dakin yayi ta daga kai tana kallonsa, ya karaso gabanta ya durkusa ya bude man zafin hannunsa, ita dai kallonsa kawai take, bayan ya debi man zafin ya kamo kafarta, zaro ido tayi tana kokarin janye hannunsa a kafarta ya daure fuska yace "Kar ki sake ta6a ni Malama" yana gama fadin haka ya fara ja mata kafar yana kokarin gyara mata targaden, ai bata san sanda ta yunkuro ta rirrikesa ba tana kukan azaba tace "Nashiga uku Abba" Bai sarara mata ba har sai da ya tabbatar kafar ta dawo dai dai, kuka kawai take ta kankamesa duk ta hada zufar wahala, bayan ya sakar mata kafa shi ma ta sakesa tana komawa baya, kallonta kawai yake, ta turo baki tana share idonta, yace "Sallan asuban ma yafe maki aka yi sbda kinyi targade ko" Ta hade rai tana kallonsa tace "Ai ni ba kafura bace" Bai ce mata komai ba ya mike ya nufi kofa, da sauri tace "Ka kira min Nihal plss" yace "Warce kika kora ko wacce?" daga haka ya fita dakin, a hankali ta lallaba ta mike ta hau saman gadon ta kwanta tayi lamo a saman pillow, wato tafiya Nihal tayi upon all her pleas. Kafin azahar Nihad taji tana iya taka kafar, a hankali take dingishin ta fito daga dakin, ta shiga nata dakin, kallon katon ledan dake saman gado ta dinga yi, kafin ta karasa ta bude ledan, abaya ta gani masu ɗan karan tsada sun kusa kala goma, da mamaki ta dinga kallonsu tana warwaresu, sannan ga undies da cream din shafawa da turarurruka duk a cikin katon ledan, da sauri ta fito parlor tana kallonsa tace "A ina ka samu kudi ka siya min abayan nan?" Ya kalleta a takaice yace "Kudin babanki mana" Nihad tace "To amma wa ya zabo abayan?" Yace "Ni ɗan aike ne, kasuwa kawai aka aike ni naje na amso" Ta kyabe baki tace "I thought as much" Daga haka ta juya ya bi ta da kallo har ta shiga daki, wani Murmushi yayi ya maida idonsa kan tv da yake kallo. Bayan ta yi wanka ta shirya cikin daya daga abayan, sosai yayi mata kyau ya amshi fatarta, ba laifi haskenta ya fara dawowa amma ramar na nan, ta fito parlor, kallo daya yayi mata ya dauke idonsa, ta wuce kitchen sauran abincin da Nihal ta dafa daren jiya ta kara dumamawa ta xuba ta koma daki ta ci, har kusan la'asar Nihad na ta xuba ido taga ko Umma xata zo yau din ko sai gobe, amma bata zo ba, wajen karfe biyar ya bude kofar dakinta yace "Ki sameni a mota" Da ido ta bi sa har ya bar wajen, sai kuma ta mike ta dau mayafinta ta bi bayansa, duk da yana cikin motar ta ki shiga, she can't take that risk anymore, tana kallonsa da kyau tace "Ina za mu je?" Yace "Gidanku" Ta ɗan yi jim, sai kuma dai ta shiga bayan motar ta kulle, suna barin gida taga sun dau hanyar gida, ta ma rasa ko farin ciki xata yi ko akasin hka, the only good thing of going to that house is that xata ga Umma bayan nan ita bata marmarin ma zuwa gidan.... Sai da suka kusa yace "Ki bude kunnuwanki ki saurareni da kyau, zan kai ki gida ba don komai ba sai don ki gaida mahaifiyarki da bata da lafiya, idan Abba na nan shi ma ki gaishesa, bayan haka xa mu fito daga gidan..." Da mamaki Nihad tace "Kana nufin sai in shiga har gidanmu in fito ban je bangaren Umma na gaidata ba??" Dai dai nan suka shigo layin, yana kallonta da kyau ta madubi yace "Ba don ki je bangarenta ki gaidata na kawoki gidan ba, a duk inda kika hadu da ita a nan xaki gaisheta babu xancen xuwa ɓangarenta, idan kuwa kika ce baxa ki bi umarnina ba, Billah na maki alƙawarin muna fitowa daga gidan xan maida ke garinmu da zama na har abada" Shiru Nihad tayi bata ce komai ba, bayan yayi parking yace "Kin ji ko baki ji ba?" Ta hade rai tace "Na ji" Bude motar yayi ya sauka ita ma ta sauka fuska daure, har sannan dingishi take, Aminu kamar xai goya Khalil tsabar farin cikin ganinsa, Nihad ta kara tsuke fuska ko kallonsa bata yi ba ta shige cikin gidan, Aminu yayi kasa da murya yace "Ciwo ta ji a kafar take dingishi?" Khalil yace "Zan fito yanxun nan" Daga haka ya bi bayan Nihad, Umma ta fito daga bangarenta kenan ganin Nihad ta hau tafa hannu tana cewa "Oyoyo oyoyo" Nihad ta ɗan saci kallon Khalil dake bayanta yana kallonta, ta sunkuyar da kai a hankali tace "Umma ina yini" Umma tace "Karaso mu shiga ciki daughter" Nihad tayi karfin halin cewa "Xan shiga wajen Mumy ne tukunna" Umma ta saki baki tana kallonta, tuni khalil yayi part din Mumy, Nihad ta bi bayansa kamar xata yi kuka, haka Umma ta bi su da kallon mamaki, kai ko makaranta Nihad ta dawo ba wani lallai taje bangaren Mumy ta gaidata ba, Umma kuwa dama kafin ta fita sai ta shiga ta gaya mata ga inda xata, haka kuma idan ta dawo, abinda Nihad tayi yanxu sai yayi mugun daure ma Umma kai. Nihad ta kasa hada ido da Mahaifiyarta bayan sun shiga parlon, Mumy ta amsa gaisuwar khalil da fara'a, Yace "Ya karfin jikin?" Tace "Alhamdulillah jiki da sauki" Nihad na wasa da veil dinta tace "Mumy ya jikin?" Mumy dake kallonta tace "Alhmdlh" cousin din Mumy ce ta fito daga bedroom suka gaisa da khalil cikin mutuntawa, Nihad dai sae kallonta take, ganin ta juya ta koma daki ba tare da ta bi ta kanta ba,  Nihad ta mike a sanyaye ta bi bayanta, gaisheta tayi, maimakon ta amsa sai ta hau ta da fada, tace "Ban kara tabbatar da cewa ke mahaukaciya bace shashasha sai yanxu, ace uwarki ba lafiya tun da kika bar gidan nan amma kika rasa inda xaki samu wayar kiranta? nan kuwa a duk sanda matar nan Umma ta shigo sai tace ai kunyi waya, anya kina son gamawa da duniya lafiya kuwa Nihad? Kullum bawan Allahn nan sae ya shigo gidan nan gaida uwarki amma sbda ke ba yar halaq bace baki ta6a cewa xaki biyosa ki duba jikinta ba, to duniya ce dai wanda bai zo ba ma jiransa take, idan kuma Umma ce tayi nakudarki ta haifeki xa mu ji" Nihad ta zauna hawaye na sauka idonta tace "Aunty ni tsoro nake ji shi yasa ban kirata ba, kuma wallahi bai ta6a ce min xai zo nan ba ban biyosa ba" a fusace Aunty Zulai tace "Sai yace maki xai zo?? Shashasha kawai kin bi kin ja mana abun kunya a duniya wanda har yanzu kukan wannan mugun abun naki muke, wallahi sai nan gaba xaki yi kukan gaske da hawayenki a kan wannan video din Nihad, nan gaba xaki san illar da kika ma kanki a duniya a kan video din nan, kuma yau da ace wannan mijin naki iyayensa da danginsa yan boko ne ko a cikin gari suke wllh baxa su ta6a bari ya aureki ba ko da kuwa shi ya ganki yace yana so balle wannan manna masa ke kawai aka yi sbda babanki ya yaba da hankalinsa, amma da ace ɗan birni ne wllh gori wajen danginsa da yan uwa ma kawai ya isheki ki hadiye xuciya ki mutu wataran, kina ganin kamar abu ya lafa ai shkkn an manta, yarinya sai nan gaba xaki gane abinda nake gaya maki ba yanzu ba, don haka in zaki rungumi mijinki ki bisa ki masa biyayya ki lallaba aurenki, to gatanki, idan kuwa kin ce ba haka ba kika kuskura kika bari aurenki da bawan Allahn nan ya samu matsala to idan ba kauyen ubanki xai sake komawa ya samo maki wani mijin ba ina me tabbatar maki babu wanda xai aureki don ma in gaya maki ki ji da kyau" kuka kawai Nihad take tana kallonta, Aunty Zulai tace "Shikenan ni abinda xan gaya maki kenan, tashi ki bani waje" Nihad ta mike tana goge hawayen da ya ki tsaya mata ta fito parlor kanta a kasa, zaunawa tayi saman Carpet ta dago kai a hankali ta kalli Mumy taga kallonta take, cikin sanyin murya tace "Mumy ina su Sudais" Mumy tace "Sun tafi makaranta" Nihad bata kuma cewa komai ba, bayan few minutes Mumy tace "Kin ga wancan bawan Allahn dake zaune?" Nihad ta daga kai ta kalli Khalil da Mumy ke nuna mata bata dai ce komai ba, Mumy tace "In har kina son gamawa da ni lafiya to ki zauna lafiya tare da shi, idan kuwa kince ba haka ba, ba baki na maki ba amma baxa ki ta6a ganin daidaituwar lamarinka ba, don haka kika kuskura kika kashe auren nan naki sae dai ki nemi warce ta haifeki ba ni ba" Nihad ta fashe da kuka sosai tana kallon Mumy, shi dai Khalil bai iya ya daga kai ya kallesu ba, Mumy ta kallesa tace "Ku gaida gida Ibrahim....  nagode sosai, xan shiga ciki" Yana kallonta cikin sanyin murya yace "Allah ya kara lafiya" Ta amsa da Ameen ta mike ta shiga dakinta, kuka kawai Nihad take kamar ranta xai fita a parlon, bayan few seconds Khalil ya mike ya fita daga parlon, mikewa ita ma tayi tana kuka ta bi bayansa.

Twins Ne

...

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post