Tabarmar Ƙashi page 16 by H U G U M A


Health College

Tabarmar Ƙashi page 16 by H U G U M A

 

Tabarmar Ƙashi page 16 by H U G U M A

*H U G U M A*


_*TABARMAR ƘASHI*_💔

 

*Arewabooks: huguma*

https://arewabooks.com/u/huguma


Page 16


          Dogon tsaki taja kamar zata tsinke harshenta,saita goge saqon kamar yadda ta saba,ta bude gorar ruwan ta zuba a glass cup ta fara sha tana tunanin next abinda zata aiwatar.



        Tun daga sama zuwa qasa ta tsaya ta qarewa kanta kallo da kyau,tayi taku biyu gaba ta sakeyin taku biyu zuwa baya,taja rigarta baya kadan yadda zata dauki hankalin duk wani daka iya kallonta ko yakai idonsa kanta bisa tsautsayi ko kuma dace. Ta waiwaya kadan jikin wata qofar glass dake baka daman ganin fuskarka tamkar madubi,ta fito full hakanan dressing nata,saita saki siririn murmushi tana maida gashin kanta baya wanda tasa gantalallen scarf ta lullube rabin gashin dashi.


           A nutse ta koma ta zauna saman kujerarta ta zauna tana sake sakin murmushi,ita kadai tasan farincikin da takeji cikin ranta,tayi matuqar samun sa'ar da bata zata ba data zama secretary dinsa,bayan dogon hanyar da tabi me cike da tangarda kafin cimma muradinta. Tasan cewa a gata dukiya ilimi da kuma kyau na halitta da take dashi dukka tafi qarfin matsayin zama secretary,to amma....muddin akan MUHAMMAD TAUFEEQ ne,ta shirya zama massinger ma bawai iya secretary kawai ba. Maida qafarta tayi ta harde daya saman daya,ta bude computer din ta soma sarrafata.


      Cikin qasaita da izzar nan tasa data zame masa jinin jiki ya sanya kai zuwa babban office dinsa daya kasance na daya duk fadin company din,sauran ma'aikatansa da na biye dashi.


         Jibril ya buda qofar,dukka suka dataka ya fara shiga sannan suka rufa masa baya. Da sauri ta daga kanta tana duban qofar,saita miqe cikin sauri saidai kuma cikin salo na yanga da yauqin da take amfani dashi wajen farautar hankulan maza. Gabanta na wani irin faduwa,zuciyarta tana bugawa da qarfi sanadin ganinsa da tayi.


          Mamaki ya kusa daskarar da ita sanda taga baiko kallo koda sashen da take tsaye ba,tamkar ma baisan da wanzuwar wata halitta a wajen ba,dole ta tattare guntun iyayin kalamanta data tsara yi masa magana dasu,ta zare jikinta daga kujerar tabi sauran ayari zuwa cikin office dinsa gaba daya,gabanta na faduwa,tana fatan duk wani shiri nata ya dinga zuwa mata da sauqi fiye da yadda take tsammata.


             Kamar wanda tsaiwa ta zamewa dabi'a,ba kasafai ya fiya damuwa da zama saman kujera ba,yanzunma haka ce,daya bayan daya ya sallamesu,ya rage saura sajjad da jibril. Jibril din ya duqufa da duba wasu takardu,yayin da sajjad suke magana qasa qasa da ita,duk da cewa gaba daya hankalinta yana a kanshi,yayi mugun tafiya da ita,shigarsa ta yau ta dabance dake nuna aiki zallah.


"Ehnnnn" ya fada a taqaie yana jingine da mulmulallen table dinsa dake tsare da files da suke jiran isowarsa,ya zuba duka hannayensa a aljihun wandonsa,yayin da yayi crossing qafafunsa.


           Da sauri jibril ya dago kansa,sannan ya fara magana


"Sir,muna expecting ziyara daga gurin Dr at any moment" kyawawan idanunsa ya lumshe yakuma budesu a lokaci guda


"Okay,the meeting has been postponed,a canza date zuwa gobe"


"Zan sanarwa kowanne department" tayi caraf da zancan,ganin cewa dukka wannan abun aikinta ne,ita ya kamata ta sanar masa da kowanne tsari,amma jibril yana aiwatarwa,hakan na nufin ita 'yar kallo zata zama kenan?. Ta yiwa kanta tambayar da bata da amsarta.


            Har yanzun bai nuna alamun yasan da wanzuwarta a wajen ba,bare maganar da tayi,yaci gaba da magana da jibril ya sallameshi. Sajjad ma ya ajjiye masa dukka files din daya kamata ya juya ya fita,cikin zuciyarsa tausayin SAIMA yana kamashi,tabbas SON MASO WANI qoshin wahala ne,yayi imanin babu abinda zata tsinta daga wajensa face tsantsar bacin rai da kuma batawa kai lokaci,inda zata dauki shawararsa,abu daya zaice da ita,ta kama kanta,ta kuma kama martaba da kimarta ta diya mace,shine kadai abinda zaisa ta tsira a idanun TOUFEEQ din.


            Kujera yaja ya zauna har yanzu dai bai bata hankalinsa ko da na second guda ba,wannan duka bai sanya ta sare ba,ta tako zuwa gaban table din a hankali ta tsaya,dai dai sanda yake rubutu saman wani file


"Sir.....akwai wani abu da kake buqata?" Tayi maganar tana dan zame rigarta kadan don ta bawa qirjinta damar fitowa,ko Allah zaisa ya daga kansa gareta,sai daya bude page din gaba na file din sannan ya fara magana,cikin muryar sa din nan dake cike da zallar qasaita da kuma izza


"Banason yawan magana,bana kuma son shishshigi,kiyi qoqarin cire kanki daga dukkan abinda ban gayyatoki a ciki ba,karki soma wuce limit dinki,any moment kuma kamfani zai iya sauyaki idan aikinki baiyi ba,these are my conditions,you can go". Wani abune yazo ya tsaya mata a wuya,ta dan zuba masa ido tana jin sonshi yana ninkuwa a ranta,amma bata taba kawowa zaiyi mata irin wanna yankan qaunar da wuri ba haka,tasan halinsa,fes zai iya yanka mata jan card idan ta tsallake abinda ya gaya mata yanzun,dole ta miqe jiki a salube ta fita a office din,tana saqawa ranta abinda zai fishsheta,ba zata taba iya jure irin zaman da shi ya tsara zasuyi ba.


          K'arfe daya na rana zuwa biyu shine lokacin break na kamfanin,masu cin abincin rana da masuyin sallah ga musulman ciki,wannan kuma duk umarni ne na CEO,ya sauya fasalin abubuwa da yawa cikin sati guda a kamfanin,da yawan ma'aikatan abubuwan sun musu dadi,amma ga wadanda sharholiya kadai suka sanya a gabansu wasu abubuwan basu yiwa tsarinsu dai dai ba.


         Bata da ra'ayin zuwa kitchen,wanda aka tanadeshi musamman saboda manyan offices kamar nata,don haka ta umarci miss sameera ta samo mata coffee kadai. Ba kasafai take sakewa taci abinci ako ina ba,shi yasa ma baaba rabi taso shirya mata wani abun ta taho dashi,duk da tasan babu lallai ta maida kai taci yadda ya kamata.


          Cikin toilet dinta dake office din ta daura alwala,ta dawo corner ta musamman da aka tanadarwa office din don yin sallah,ta gyara lullubinta ta tayar da sallar. Kafin ta idar miss sameera ta dawo,ta ajjiye mata coffee din,ta koma ta tsaya tana jiranta ta idar da sallar.


         Cikin girmamawa ta matso bayanta kadan bayan ta idar


"Akwai email da aka turo miki daga ceo office,kusan minti talatin kenan,ina kyautata zaton baki gani ba" kai ta gyada mata a nutse tana dubanta


"Boss ne ya iso,yana office na ceo,he wants meet you" jim tayi na wasu 'yan mintuna,sannan ta maida dubanta ga miss sameera,kai ta gyada mata a natse,ita kuma ta jinjina kai ta juya ta fice.


             Fuskarta da daurinta ta gyara kamar yadda yake,kamar bata sanyawa fuskarta ruwa ba,tanana da qyallin nan da gogewar fatarta,saika dauka tayi amfani ne da powder. Ta gaban table dinta ta tsaya ta danyi sipping coffe din,bata ma iya shanyewa ba ta fito ta cimma miss sameera na jiranta a farfajiyar data fi kama da parlor wadda zata sadaka da office dinta.


          A nutse take takawa cikin shigar tsadaddar laffayar data lullube ilahirin jikinta,duk inda ta gifta sai tayi gaba da hankula da kuma idanun kaso mafi yawa na ma'aikatan kamfanin,walau maza ko mata,ko ina akwai shige da ficen ma'aikata,kasancewar lokaci ne na hutu. Ko daya babu wanda ta baiwa hankalinta,cikin kamewa da nutsuwa har suka isa qofar office din,mr sameera ta tura qofar tayi gaba,sãahar tabi bayanta.


          Wani irin katafaren office da babu irinsa kaf kamfanin,wanda ke dauke da sassa biyu zuwa uku,waitin parlor wanda saima ke ciki ita da tarin takardu da kujerun da aka qawata gurin,sai rest room daura dashi kuma main office din da zaka gudanar da ayyukanka. Idan ka kira office din da aljannar duniya akai tsaye sam bakayi laifi ba,saboda ya amsa sunan,wasu irin colors da design me matuqar tsari da aka qawata kowanne sashe na office din.


          Sallamar miss sameera ya sanya saima daga idanunta daga kan computer,maimakon idanunta su sauka kan sameera,sai suka fada kan sãahar dake qoqarin daga kiran daya shigo wayarta


"Zaki iya sanarwa da sir isowar president?" Sameera ta yiwa saima tambayar,lokacin da ta tattara dukkan hankalinta akan sãahar da nata hankalin yake kan khalipha dake mata complain na tafiyar da tayi baya nan,lallausan murmushin dake masifar qawata mata fuska ne kwance saman fuskartata,har jerarrun fararen haqoranta da suka zama tamkar hasken lu'ulu'u suna fitowa,wani luguden abu taji ya saukar mata,tana da labarin dukka sabbin ma'aikatan kamfanin a yau zasu kama aiki kamar dai ita,tabi diddigin kowacce mace dake cikinsu,musamman wadanda ya zamana mu'amala zata iya hadasu da office din TOUFEEQ dinta,to amma ita din ita kadai tak! Ta kasa samun komai a kanta,ta gaza cimma wani bayani daya shafeta har zuwa lokacin data taka qafarta ciki kamfanin,sai yanzu,karo na farko


"Excuse me,ko ta shiga ne?" Sameera ta fada cikin girmamawa da kuma zaquwar ganin yadda saima ta kasa amsa maganarta ta farko.


         Iska taja sosai a cikin hunhunta,ta qanqance idanu tana duban sameera,duban da zataso ace president din da kanta ta yiwa shi,saidai ba zatayi garajen aikata hakan ba,don batasan wace ita ba,kada ta aikata abinda zai zame mata matsala,ya kuma zama silar cisgeta daga bigiren data dora buri akai


"Sir yana tare da babban baqo wato mahaifinsa,saidai ku dawo wani time din,kafin lokacin na sanar masa" tayi maganar tana ci gaba da dannan system dinta,dai dai sanda sãahar ta gama wayar,ta zameta daga kunnenta tana kallon sameera dake jiran ta kammala wayar tayi mata bayani. Kafin tace wani abu sãahar ta rigata


"Thank you,na gode da rakiya,zaki iya komawa office" tayi maganar kanta tsaye tana kyakkyawar qofar da a samanta take liqe da takardar dake bayanin inane nan gurin ba tare data waiwayi saima ba.



FURAR DANKO

Billyn Abdul


-ZAFIN KAI

Mamuhgee


-TABARMAR ‘KASHI

Safiyya Huguma


-BAKON MUNAFIKI

Miss xoxo


Duka hudu 1k

Uku 800

Biyu 600

Daya 400


Pay at👇


1487616276 

Access Bank

Bilkisa Ibrahim

Sai katura shedar biyanka anan👇


09032345899


Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇

09033181070


VIP🔥💯

Zafin kai 3k

Furar danko 3k

Tabarmar kashi 3k

Bakon munafuki 3k


*Al'ummar NIJER ku kira wannan number don yin naku pyment din*


+22799643131


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


*THANKS FOR CHOOSING US*🥰


Zafafa🫶🔥

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post