Tabarmar Ƙashi page 21 by H U G U M A


Health College

Tabarmar Ƙashi page 21 by H U G U M A

 

Tabarmar Ƙashi page 21 by H U G U M A

*H U G U M A*

*_TABARMAR ƘASHI_*💔

Page 21

         Tana da tabbacin meeting hall din ya nufa,dole yana gaba tana biye dashi. Tun daga nesa dukka guards nashi suka zama ready da isowarsa,daya daga ciki ya iskeshi a hanya riqe da suit jacket dinsa,ya taimaka masa ya saka,sannan ya karba komai dake hannunsa suka take masa baya har zuwa bakin madaidaicin hall na musamman da aka tanada saboda ganawa me muhimmanci irin wannan da manyan masu ruwa sa tsaki cikin company din.


             Dai dai sanda ta iso dab dashi ya gama magana dasu,kusan lokaci daya suka tura qofar,suka kuma sanya qafafunsu,sai ya zamana tamkar dama a tare suke.


              Hankula da idanuwan dukka board members din dake hall din yayo wajen, kasancewar shi kadai dama ake jira,a hankali kallon dake saman fuskokinsu ya canza,idanuwansu na karakaina saman kyakkyawar fuskar sãahar dake cike da fushi,baquwar fuskar dake dauke da wani irin sassanyan kyau me jan hankali,wasu kuma cike da mamakin wacece ita?,meye alaqarta da CEO dinsu?,wanne irin matsayi gareta da har sai daya jirata suka taho tare?,take wutar kishi ta kunnu a zukatan matan dake zaune a wajen,harda wani sashe na mazan gurin,saura kuma zukatansu suka cika da wasu wasi,take wutar jita jita ta fara tsiro a wajen,aka fara qus qus a tsakanin juna,ko kusa daga shi har sãahar da ranta ke abace basu ma lura da hakan ba.


           Kujerarsa ce qwaya daya tal daga can saman qololuwar table din,daga gefanta ya tsaya ba tare daya zauna ba,sannan cikin husky voice dinsa dake da wani irin amo na zallar kwarjini yace


"I apologize for not arriving on time" a nutse sãahar dake zaune cikin tata kujerar dake daura da tashi ta daga kanta,tanason kallon qwayar idanunsa ne cike da mamaki,bata taba tunanin zai iya apologizing wani akan wani abu ba


"let's start for what brought us together here" ya kuma fada yana zube hannayensa cikin aljihun wandonsa,fuskarsa cike da seriousness dake cakude da kwarjini.


            Cikin wani irin salo na tsari meeting din ya fara gudana,tsarin da kana gani kasan ya samo asali da tushe ne daga wajen CEO din yasan abinda yakeyi,dukka tsahon zaman nan yana tsaye ko sau daya bai zauna ba, saidai time to time ya durqusa ya danyi rubutu a system dinsa ya same miqewa,duk kuwa da cewa saima tana wajen,kuma aikinta ne ta nadar masa dukka bayanai.


          Tunda aka fara tattaunawar batace komai ba,a nutse take sauraren komai tana kuma sake samun ideas sosai,saidai gaba daya a takure take,hakanan ranta kuma a bace yake.


          Tun daga sanda ta shigo gurin ido yayi yawa a kanta,daga mazan har matan wanda ita batasan meye dalilin kallon ba,bayan ta zauna ta samu raguwar idanun da sukayi mata caaa,saidai har kawo yanzu idanuwan mutum biyu hudu sun hanata sakat. Biyu daga cikinsu mata ne,don haka kallonsu bai wani dameta ba,sauran biyun kuma dukkansu sun fito daga jinsin da basa ga maciji watonJINSIN MAZA. Dayan ta fahimci shike riqe da muqamin chief financial officer (CFO) a bayanan daya gabatar,dayan kuma batace ga nasa muqamin ba,saidai tunda har yake cikin board members wani ne tabbas cikin kamfanin.


             A nutse ta maida dubanta ga takardar da take kusan hannun kowa dake wajen,wadda tsari ne na abinda za'a tattauna a wajen. Yadda tattaunawar ta dauki zafi,sai take ganin kamar ana shirin sauka daga kan ainihin abinda ya tattarasu,zuwa sanda MT jarma ya dan buga table din gabansa,dakin ya dauki shuru,ya gyara tsaiwarsa da take qara fidda zatinsa,cikin qwarewa da fasahar iya magana dake cakude da taushin muryarsa me zurfi ya fara nasa bayanin. Shuru gaba daya hall din ya dauka,maganganunsa da iya sarrafa harshensa sunja hankalin kusan kowa dake gurin,har zuwa sanda ya kammala ya rufe da fadin


"Ina buqatar tattararren bayani daga kowanne member personally,you can ask question if anything seems unclear or confusing" ya qarashe fada yana sauke dubansa akan kowa dake cike da gamsuwa akan bayanansa,a hankali har idanunsa suka fada a kanta,lokacin da ta bude folder dinta tana dubawa,tamkar ma bata a wajen ake dukka wannan zazzafar tattaunawar. Janye idanunsa yayi,ransa na baci,baiga amfaninta cikin kamfanin ba har yau ,wannan zaman yana daya daga cikin tattaunawa me amfani da zata iya zama tushe na fitar company din daga matsalar da yake shirin afkawa,yaja qaramin tsaki,yana shigar da wannan bayanan cikin system dinsa.


         Cikin jikinta taji kamar ana kallonta sama da idanuwan da suke kallon nata a dazu,don haka ta rufe folder din nata a hankali ta daga kanta,ta jjiye folder din daga gefe ta gyara yafen laffayarta,dai dai sanda suka sake hada idanu dashi karo na barkatai. Qasa qasa taja tsaki tana gyara abun maganar dake ajjiye a gabanta,tunda suka zauna gurin yake qare mata kallo iya son ransa kasancewar yana zaune ne kujerar dake fuskantarta


"Akwai muhimman abubuwan daya kamata ace anyi magana a kansu,saidai ba wanda yayi magana akansu din duk tsahon zaman, though dai we've got ten minutes left..." A nutse ya daga kansa daga system ya saukesu a kanta,a take idanuwansu suka gauraya waje daya,cikin qasa da second uku kowa yayi saurin janye nasa,saita juya ga abun maganarta ta fara nata bayanin a taqaice.


            Kamar sanda yake magana,ko a yanzunma shuru ne ya sake wanzuwa a dakin taron,amon muryarta da nata salon turancin tatacce kamar nasa,mintuna shida kacal ta tattara komai A taqaice,sannan ta miqa file ga mr sameera tace a sadar dashi ga office na ceo,suna buqatar sanya hannunsa don aiwatar da aikace aikacen da team dinta suka tsara.


"Any questions?" Ya tambaya kai tsaye,saidai ba wanda yace komai,hakan ya tabbatar da zuwan meeting din qarshe.


           Tana zaune saman kujerarta bata motsa ba har sanda mutane suka fara fita,kusan hakan al'adarta ce,bata yunqurin fita daga guri irin wannan me hadakar maza da mata ba,har sai an samu ragowar cunkoso gudun hada jiki dasu.


"Madam,banga kinsha komai ba" taji an fada daga gaba da ita kadan,a nutse ta daga kai tana kallon mai maganar,shine dai na dazun,me shegen nacin kallon tsiya,CFO,ya kafeta da mayun idanunsa yana jifanta da murmushi


"Thanks" ta fada masa a gajarce,saita fasa ci gaba da zaman,ta miqe tana daukar hand bag dinta tare ta yima Mr sameera inkiya,ta fara takawa a nutse,nutsuwar data haifarwa da takun tafiyarta wani irin salo da zaka dauka tsabar yanga gayu da kuma yauqi ne,saidai ita din tun asali naturally haka halittarta yake.


         K'arfe shida da mintuna motocinsa suka dauki hanyar gida dashi,a mugun gajiye yake jinsa,kowacce gaba ta jikinsa tana da buqatar hutu,banda hutu na gangar jiki,harma da hutu na zuciya.


          Tare da sajjad suke cikin motar,duk da suna hanya amma sajjad din na hirar yadda taron ya gudana


"But...... sabuwar president din nan,ta bani mamaki beyond my expectations,she's very talented" 


"I don't know" taoufeeq da hankalinsa ke kan qaramin screen din dake liqe a kujerar gaban seat dinsa ya amsawa sajjad a taqaice,sam baya son zancanta,tunanin da yaketa kokawa dashi kenan tun dazun,abubuwan data gabatar ne sukata yi masa yawo akai,to ko su din bayason tunawa,haka kawai zuciyarsa ke gaya masa ta fiya zaqewa,kamar tanayi saboda ta sake samun shiga jikinsu da sanin abinda yake mallakin dr ahmad jarma din.


"She's the best president da companyn nan ya taba samu I think" zuwa yanzu maganar ta fara gundurarsa,ba a bakin sajjad ba,kafin sajjad din yace wani abu kusan mutum biyar daga cikin board members din abinda ya barosu suna tattaunawa,bashi da sauran shaida data rage akan diya mace,banda mutum uku zuwa hudu daya ware,don haka yasa hannu ya ciro headphone ya toshe kunnuwansa dasu yaci gaba da abinda yakeyi. Sam sajjad dake bin tsarin aikin nata yana dubawa gami da ci gaba da yi masa zancanta bai lura ba,sai daya waiwayo da nufin nuna masa wata agenda sannan ya gani,baki kawai ya sake yana kallonsa,ya gaji da jinsa,amma bazai buda baki ya fada masa ba,ya gwammace ya toshe kunnuwansa da bututun sauti?,sai kawai ya rufe folder din ya adanata cikin wata ma'ajiya dake jikin kujerun me kama da akwatu,ya maida gurin ya rufe. A yadda ya nuna baida interest muddin bai adana folder din ba yasan bashi da asara na koma meye da zai sameta,bazai damuwa ba,illa iyaka yace yayi cancelling,ko ya sasu wahalar sake tsara wani jadawalin.


            Su biyu ne rak a babbar farfajiyar gidan a zaune,kamilar dattijuwa baaba rabi na zaune saman couch din da aka qawata gurin da ko ruwan sama bai sauka,sai daddadar iska me sanyi,qamshin furanni da koke koken tsintsaye kala daban daban.


            Saman cinyarta kyakkyawar farar yarinya ce, siririya sosai mara jiki ko kadan,sai zallan madarar kyau da Allah ya zuba mata,wanda tayo gadonsa ne daga gurin mahaifinta,matashin attajirjn dan kasuwa MT jarma.


          Fararen kaya ne sol a jikinta,dogon lallausan wando da rigarsa me dogon hannu,saidai akwai zanen pink din teddy daga gaban rigar,da siririyar sarqa me ruwan gwal a wuyanta,sai dankunnen barima shima da yafi kama da na gold din,sosai mayalwaciyar sumarta ke a gyare kuma a daure cikin farin ribbom,yankan farce baba rabin takeyi mata,gefe daya kuma tanata qoqarin karbar surutun da take mata cikin nuna kulawa babu gajiyawa ko kadan saman fuskarta.


             Hon din motocin kadai taji ta gane dawowar mahaifinta,mahaifin da duk fadin duniya baaba rabi takance,ta jima bataga irinsa ba shida diyarsa,wata irin shaquwa da qaunar juna ce a tsakaninsu me tarin yawa,duk da nakasu me tarin yawa dake tattare da rayuwar kowannensu,kamar a duniya basu da kowa sai junansu.


FURAR DANKO

Billyn Abdul


-ZAFIN KAI

Mamuhgee


-TABARMAR ‘KASHI

Safiyya Huguma


-BAKON MUNAFIKI

Miss xoxo


Duka hudu 1k

Uku 800

Biyu 600

Daya 400


Pay at👇


1487616276 

Access Bank

Bilkisa Ibrahim

Sai katura shedar biyanka anan👇


09032345899


Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇

09033181070


VIP🔥💯

Zafin kai 3k

Furar danko 3k

Tabarmar kashi 3k

Bakon munafuki 3k


*Al'ummar NIJER ku kira wannan number don yin naku pyment din*


+22799643131


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


*THANKS FOR CHOOSING US*🥰


Zafafa🫶🔥

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post