YAU ZAMU TATTAUNA NE AKAN KURAJEN FUSKA (PIMPLES)

YAU ZAMU TATTAUNA NE AKAN KURAJEN FUSKA (PIMPLES)

YAU ZAMU TATTAUNA NE AKAN KURAJEN FUSKA (PIMPLES)

kurajen taya-ni-muni pimples: kurajen pimples a turance ko acne bulgaris a likitance suna daya daga cikin larurori masu addabar samari da ’yan mata. Suna fitowa ne a daidai lokacin girma, domin a daidai lokacin ne sinadarin nan na testosterone ke yawa a jinin samari maza da kuma wasu kadan daga cikin mata. Wannan sinadari shi ke da alhakin sa maiko ya rika taruwa a fuska. Idan maiko ya taru a fuska sai kwayoyin cuta su zo su taru a wurin su kawo kurji.

Hanyoyin kariya su ne kiyayi taruwar maiko da kwayoyin cuta a fuska da kirji. Wannan kan dan yi wahala amma ta wadannan dabaru za a samu nasara:

   1-Rage maiko a cikin abinci. Misali, idan aka soya wani abinci, yana da kyau a tsane mai da mayanin kitchen wipe mai tsabta kafin a ci. Idan an yi haka an rage man kusan da kashi hamsin cikin dari ko ma fiye.

   2-Yin amfani da sabulu mai kashe kwayoyin cuta wajen wanke fuskar safe da yamma. 

    3-Shan kayan itatuwa da cin ganyayyaki a kai-a kai yakan tsane maikon cikin jini ya kara karfin garkuwar jiki wajen yakar kwayoyin cuta.

    4-Ga wanda wadannan dabaru ba su yi musu aiki ba, za su iya zuwa su nemi man shafawa a fuska da kirji mai dauke da sinadarin benzoyl perodide na shafawa safe da yamma bayan an wanke fuska.

    5-Idan hakan ta ki wadatarwa sai an je asibiti an hada da karbar magungunan kashe kwayoyin cuta.

    6-Ga wadanda wannan ma bai yi aiki ba, akwai dai magunguna masu karfi har ila yau irin samfurin bitaman ‘A’ da ake kira isotretoin da ake rubutawa a asibiti. Akan samu nasara sosai idan aka jarraba wadannan. Amma ba a bawa mai juna biyu shi.

   7-Ba a so a rika matse kurajen saboda hakan kan iya jawo tabo, an fi so a bar su su fashe da kansu sai a wanke wurin. 


  Allah yasa mudace

Mashkur Abdullahi Tsafe

Health educator

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post