Bayan ƙorafin JNI, gwamnatin Plateau ta musanta jerin sunayen waɗanda suka samu tallafin matar Tinubu

Bayan ƙorafin JNI, gwamnatin Plateau ta musanta jerin sunayen waɗanda suka samu tallafin matar Tinubu

Abban Sojoji

Gwamnatin jihar Plateau ta nesanta kanta da jerin sunayen wadanda suka ci gajiyar tallafin naira miliyan 500 da uwargidan shugaban kasa, Remi Tinubu ta bayar ga iyalan da rikicin jihar ya raba da muhallansu.

A tuna cewa kungiyar Jama’atul Nasrul Islam, JNI, reshen jihar ta nuna kin amincewa da ware iyalan musulmi wajen shirin bayar da tallafin.

A cewar kungiyar ta Musulunci, babu wani musulmi ko daya da aka saka a cikin jerin wadanda za a rabawa kuɗin tallafin.

Da ya ke mayar da martani ga ƙorafin na JNI, Gyang Bere, mai magana da yawun gwamna Caleb Mutfwang, a wata sanarwa a jiya Alhamis, ya ce jerin sunayen da ke yawo a shafukan sada zumunta ba su da inganci don haka ya kamata a yi watsi da su.

A cewarsa, an yi amfani da kudaden ne domin samar da kayan agaji ga wadanda matsalar tsaro ta shafa a wasu kananan hukumomin jihar.

"Muna so mu fayyace ba tare da wata shakka ba cewa labarai da lissafin da ake yadawa a yanzu a kan kafofin watsa labarai ba na gaskiya bane kuma ya kamata kamata a yi watsi da su.

"Wasu mutane ne ke daukar nauyin wannan farfaganda don bata sunan gwamnati da kuma kudurin inganta rayuwar wadanda abin ya shafa,” in ji shi

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post