Kurkukun Ƙaddara episode 34

Kurkukun Ƙaddara episode 34

Kurkukun Ƙaddara

 💋KURKUKUN ƘADDARA💋


E34


daga alƙalamin Boss Bature writer of Abban sojoji❤


A wani dare Ne, dukkansu Sun kwanta bacci, Angel tana a kudundune cikin bargonta, kwatsam ta soma Jin shessheƙar kukan mutun acikin kunnuwanta, tun bata ɗauki abun serious ba har sautin kukan ya fara disturbing ɗinta, Sai kuma ta dinga jin hannun mutun asaman jikinta kamar ana bubbuga ƙafarta ƙasa ƙasa ta jiyo miryar mutun yana yi mata magana, A hanzarce ta yaye bargon jikinta ta ɗago da idanuwanta masu ɗauke da bacci biji biji take Iya ganin fuskarta, tana a zuƙunne gaban gadonta, fuskarta sharkaf da hawaye, 


Mutsustsuke idanuwanta ta yi da yatsun hannunta don ta samu damar ganin kowacece, koda tayi arba da deeja sai taji gabanta ya faɗi rass! Tun kafin ma takai ga faɗa mata abunda ya kawo ta,


"Angel Jinin nan ne ya dawo mini, Na shiga toilet in yi fitsari shine naganshi, hankalina Ya tashi sosai bansan Ya zanyi ba," fuskarta a yamutse tayi maganar, dafe kai angel tayi tare da ambaton"INALALLAHI WA'INNA ILAIHIRRAJI'UN! wannan wata irin masifa ce, mun shiga uku! Ni nayi tunanin Kun daina gaba ɗaya, ashe da sauranshi," idanuwanta cike tab da kwalla tayi maganar, 


Ruƙo hannunta deeja tayi acikin nata"Dan Allah angel, Ki san yadda za'ae ki hana atafi dani, wlh gani nake kamar idan aka ɗauke ni wannan karan baza'a dawo dani ba," tana kuka ta yi maganar, Hankalin angel ya tashi matuƙa, Saukowa Tayi daga saman gadon ta nufi gadon Danish, Hannu takai ta ruƙo bargon daya lullu6a dashi ta yaye shi, Bubbuga ƙafadarshi tayi tare da ambaton sunashi"Danishi!danish!" daƙyar ta samu ya farka, Yana faman yamutsa fuska Yace"menene"? 


"Pls ka tashi deeja bata da lafiya, Menstruation ne Yazo mata" ware idanuwanshi ya yi jin abunda tace, Saboda ya gane me take nufi, tun da tayi musu bayanin komai dangane da jinin,


"Dan Allah Danish kada ku bari Giants su ɗauke ta, mu taimaka mata," yunƙurawa yayi tare miƙewa ya zauna saman mattress ya jingina bayanshi jikin bango, batare daya ce komai ba, idanuwanshi na akan deeja dake a zauƙunne sai kuka take Yi,


Ganin baida niyar tanka mata yasa ta wuce gadon haris, ta tada shi, daya farka ta sanar dashi abunda ke faru wa, Jikinshi har 6ari yake Yi, duk yabi ya ruɗe ya sauko daga saman gadonshi, Yana tambayarta Ina deejan take, Tun kafin ma ta bashi amsa sai ga deeja ta nufo su, Tana karasawa gabanshi ta fashe da kuka, Ruƙo hannunta yayi acikin nashi Ya janyota jikinshi Yana lallashin ta yana faɗin"ta kwantar da hankalinta, Ba wanda ya isa ya tafi da ita sai dai ahaɗa dashi atafi amma bazai ta6a bari giants su ɗauke ta ba, muddin Yana numfashi" Angel taji daɗin kalaman da haris yayi duk da tasan zaiyi wuya ya iya hana su tafiya da ita, Ga wanda taso Ya harzuƙa can saman gado Amma Yaƙi cewa komai, Haushin shi duk ya cikata, ta tsani halayyarshi ta lalaci da rashin son ta6uka komai, 


"Haris Bari in tada su Naufal, In yaso sai mu haɗu mu duka mu hana su tafi da ita" Yace mata"toh" ɗaya bayan ɗaya tabi kowannan su saman gadanshi ta tada shi, duk wanda ya farka, Yaji abunda ke faruwa sai gaka ya zare ido saboda fargaba da tashin hankali, A tsakiyar ɗakin suka hallara su goma sha huɗu, sun sanya deeja a tsakankanin su suna jiran giants su ƙaraso, da alama yau sun shirya yin faɗa da Giants,


Motsin buɗe ƙopar ɗakin tsohuwa suka Jiyo, Da sauri suka kai idanuwansu kanta, a lokacin ta ƙarasa fitowa daga Cikin ɗakin Hannunta ruƙe da sanda, fuskarta a yamutse babu annuri babu walwala, Ɗagowa tayi tare da kallonsu


Babu wanda yayi yunƙurin yi mata magana, Sun ɗaure fuskokinsu, Saboda mugun haushinta da suke Ji,


Azeeza ce tace"ni dai bari in je in roƙeta kada ta bari atafi da deejan mu" har ta ɗaga ƙafa zata je wurin ta, Haris Ya damƙi hannunta tare da cewa"Ashe baki da hankali? Idan kinje kin roƙe ta me zata Iyayi mana? In banda ƙarya"? Wannan maganar ta haris tayi matuƙar girgiza tsohuwa,


Angel tace"Allah ya kamata ki roƙa ba ita ba, saboda shi kaɗai ne zai Iya taimakon mu amma waccan matar, Ba abunda zata yi mana," takai karshen maganar idonta akan tsohuwa,


Jinjina kai tsohuwa ta yi jin abunda haris yace,  daga bisani ta Dogara sandarta zuwa inda suke atsaye taci burki ta tsaya, ɗaya bayan ɗaya ta shiga binsu da wani irin kallo, sun rasa gane kallon menene take Yi musu, Juyawa tayi tare da kallon danish dake zaune saman gadonshi, Dama shi kaɗaine baiyi yunƙurin miƙewa ba, da alama baya goyon bayan abunda suke shirin aikatawa,


"Saboda shi yafi ku wayau da hankali shiyasa bai biye maku ba," tsohuwa ce tayi maganar a lokacin da ta janye idanuwanta daga kan danish ta mayar dasu kan angel, Ido cikin ido suke kallon juna,


Murmushin takaici ne ya bayyana akan fuskar tsohuwa, 


"Koda gigin wasa kada ku kuskura kuce zaku Hana giants tafiya da deeja!! ina gargaɗinku idan har kuna son zaman lafiya to ku daina yunƙurin shiga huruminsu....." Haris ne ya dakatar da ita ta hanyar daka mata tsawa yace"Wai ina ruwanki da rayuwarmu ne? Bakin nuna baki damu da mu ba? To ki fita sabgarmu mana? Idan ke bazaki Iya hana su tafi da ita ba, to mu ki barmu muyi da kanmu" rai a6ace yai maganar,


Muryar danish ce ta ratsa kunnuwansu, a yayin da yake saukowa daga saman gadonshi yace"Haris ka sassauta kalamanka, Abunda tsohuwa ta faɗi gaskiya ne, Baza ku Iya ja da giants ba, Kuna Yunƙurin jefa rayuwarku cikin hatsari ne, Na rasa ya zanyi in fahimtar daku," wani irin mugun kallo haris ya jefa mashi,


"Danish kana goyan bayanta ne? Bayan duk irin ƙarairakin da take yi mana, da kuma Nuna rashin damuwarta akanmu , Sannan da ita fa ake haɗa baki ana cutar da rayuwar ƴan uwanmu amma duk ahaka kake binta"? Zuciyarshi a hasale yayi maganar, sam baiyi tsammanin danish zai mara mata baya ba,


"Haris u ave to understand me, Bazamu iya yin komai ba, saboda mu ba komai bane, Ni bana so na rasa wani acikin ku......." Kasa karasa maganar yayi ganin irin kallon hararar da angel ke jefa mashi, shiru yayi tare da duƙar da kanshi ƙasa,


Tsohuwa ta dasa da cewa"Bawai bana son taimakon ku bane, kawai ba yadda zanyi ne, Ni kaina giants sunfi ƙarfi na, matsayinsu da nawa ba ɗaya bane, sunfi ni ƙarfin iko, Idan nace zan hanasu tafiya da wani daga Cikin ku zan rasa raina ne......" Angel tace"Oh ashe ta ranki kike Yi? Su baki damu da rayuwarsu ba, Ae ni nayi tsammanin har rayuwarki zaki iya sadaukarwa akansu ashe ba haka bane, ƙaunar da kike yi musu ta bogi ce, Ni na tabbata da ace ƴa'ƴan da kika zuƙunna kika haifa ne da baki faɗa musu wannan maganar ba"


Girgiza kai tsohuwa tayi wannan karan idanuwanta hada farin ruwa kwance acikinsu tace"Bazaki ta6a fahimtata ba, Koda ace na sadaukar da rayuwata akansu nayi abanza, saboda yin hakan bazai canza komai ba, Ae ƙwarama Ni dana 6ata tsawon shekaru ina rainansu, Iyayensu fa da suka sadaukar dasu? Suna can suna sharholiyarsu sun ma manta da suna da wasu ƴa'ƴa da suka sadaukar, Nifa kaɗaice na damu daku, Ni da ban haɗa alaƙar komai daku ba, ae na cancanci a jinjina mini" 


Maganar tsohuwa ta yi matuƙar girgizasu, Kallon kallo suka shiga yi atsakaninsu, batare da wani ya kuma Yin magana ba,


"zan Koma ɗakina, Amma kafin nan zan ƙara ja maku kunne, Kada Ku kuskura ku shiga hurumin giants, Idan Kunne Yaji Jiki ya tsira" tsohuwa na kammala maganarta, Ta juya tana dogara sanda ta shige Cikin ɗakinta, Idanuwansu akan abayanta har saida ta 6ace ma ganinsu....


Haƙiƙa maganar tsohuwa ta yi matuƙar ta6a zuciyoyinsu, Jin cewa Iyayen su suna can suna sharholiyarsu sun manta da suna da wasu ƴa'ƴa da su ka sadaukar, Wai ashe dama su ba Marayu bane marasa Iyaye! ? Jikin su ya yi mugun sanyi, kamar waɗanda aka zarewa laka, ita dama angel ta san da wannan shiyasa ta ƙudiri aniyar idan har Allah yasa tayi nasarar fita daga Cikin kurkukun, Kaitsaye zata fara neman Azzalumin da ya yi sacrificing ɗinta acikin danginta, don a halin yanzu kowa suspect ne awurinta, Mahaifinta da aunty aneelerh kaɗai ta cire aciki, Amma sauran dangin nata da wanda ta sani dama wanda bata sani ba, Kaf ɗinsu she's suspecting them,


 ɗakin nasu ya yi shiru babu mai magana saboda ruɗanin da tsohuwa ta jefa su aciki, Kowa da abunda yake saƙawa aran shi, kuma har lokacin suna atsaitsaye kewaye da deeja, babu wanda Ya motsa, danish Yana a gefe ɗaya ya goya hannayenshi saman ƙirjinshi, 


Lokaci ɗaya kamar an zungure su gaba ɗaya suka ɗago da idanuwansu suna kallon saman benan Jin motsin buɗe ƙopa, Hankalin deeja yabi ya tashi haiƙam Jikinta ya soma kerma ta ƙanƙame Jikin haris tana kuka tana faɗin kada su bari atafi da ita, duk ta cukuikuye mashi rigarshi, Hankalinsu ba ƙaramin tashi yayi ba, 


"Pls kada wanda yayi yunƙurin dakatar dasu, am warning u," danish ne ya gargaɗe su, 


Babu wanda Ya kalli inda yake sai dai duk sun sare zuciyoyin su sun karaya, 


Takun tafiyar giant ne Ya ja hankalinsu zuwa ga kallon staircase ɗin dayake saukowa, Shi ɗaya yazo musu wani gabjejen ƙato dashi a bubbuɗe yake tafiya, Ganin Yana tunkarosu gadan gadan Yasa duk suka watse saboda tsoratar da suka Yi, batool taja hannun azeeza duk suka ja gefe, Ya rage daga angel sai haris daya fusata Yana jiran shi ya ƙaraso, da sauri danish ya sanya hannyenshi biyu ya ruƙo wuyan rigar haris dana angel da ƙarfi Ya janyesu gefe ɗaya batare daya saki wuyan rigarsu ba, duk yadda suka so su kwace daga ruƙon da yayi musu sun kasa, Angel hada yakushin shi tadinga yi da hannayenta amma ko ajikinshi, 


Giant ɗin na ƙarasowa Ya sanya hannayenshi biyu ya ɗauki deeja saman kafaɗarshi tana ta kuka baiwar Allah, a haka Ya juya da ita ya fuce daga Cikin ɗakin, suna ganin an tafi da ita, su ka fashe da kuka kamar ransu zai fita,


Kamar Jira take Giant ɗin Ya fita, Danish na sakin wuyar rigarta, Awani fusace Ta juya ta fuskance shi ta ware yatsun hannayenta biyar cuf, ta wanke shi da zazzafan mari ji kake tasss, Har saida kanshi yayi gefe ɗaya,


Ranta amatuƙar 6ace tace"Banza daƙiƙa, ban ta6a sanin kai wawa bane dolo sai yau, Kana ji kana gani za'a tafi da ita baka iya ta6uka komai ba, don me zaka hana mu taimakonta? Ta yi maganar tana ciccije le6enta, ɗagowa yayi da fuskarshi, tafin hannunshi dafe da inda ta mara, wurin yayi ja saboda hasken fatarshi ga sahun dogayen yatsun hannunta nan ruɗu ruɗu asaman fatar,  wani irin raunataccen kallo yake binta dashi batare daya furta komai ba, Sauran ƴan uwan nasu duk suna a tsaye cirko cirko suna kallonsu, Haris dai baice komai ba, duk da baiji daɗin marin da angel ta yi ma danish ba,  Sai dai shi kanshi yaji haushin yadda danish yaƙi nuna fusatarshi akan tafiyar da aka yi da deeja,


"Angel meyasa kika mare shi? Kalli yadda kika raunata mashi fuska! shi fa bashi da laifi, yana ƙoƙarine Ya dakatar da ku gudun kada ku jefa rayuwarku cikin hatsari, saboda Lafiyarku yayi hakan, taya zamu Iya ja da giants? Kin manta irin wurgin da su ka yi damu lokacin da muka yi yunƙurin hana atafi dasu Hannah"? Juyawa angel tayi tare da kallon batool da ke magana, nuna danish tayi ta yatsan hannunta tace"batool kina supporting ɗinshi? duk irin halin ko in kulan da ya nuna akan deeja? Kowa ya nuna tausaya agareta ganin irin halin da take ciki tana kuka tana roƙonmu akan kada mu bari atafi da ita, Amma wannan Kwankon ashanan Koda naje na faɗa mishi Ba abunda yace saima ya share ni kamar wata ƴar iska, ni shi ne abunda yafi ƙona mini rai" azafafe ta ƙarasa maganar tana jifarshi da harara, duk ya sha jinin jikin shi,


Muryar azeeza kamar zata fashe da kuka tace"Ni dai dan Allah kowa yayi haƙuri, tun da an riga an tafi da deejan mu, Muje mu kwanta dare yayi sosai," harara haris ya wurga ma azeeza duk da bata iya ganinshi yace"Baki da ƙafa ne? Ki wuce kije ki kwanta ko wani ya ruƙe ki ne"? Da alama dai duk sun fusata, 


Jikin danish a sanyaye Ya juya ya nufi azeeza ya ruƙo hannunta yaja ta har zuwa saman gadonta ta hau ta kwanta ya sanya mata bargo ya lullu6e mata Jikinta, kafin Ya koma Saman gadonshi Ya kwanta idanuwanshi na fuskarta ceilling, Angel itace mutun ta farko da ta ta6a bugunshi, karo na biyu kenan tana ta6a lafiyar jikin shi, abun ya tsaya mashi arai,


Ɗaya bayan ɗaya suka nufi gadajensu kowa Ya haye ya kwanta, Ya rage saura angel ita kaɗai a tsaye, tsabar baƙin Ciki Ya hana taje ta kwanta, saboda mugun haushin danish da take ji, ga zarginshi da take Yi, gani take kamar shi ɗin secret Giant ne acikinsu,


Sai da ta bari Kowa Yayi bacci, Ta haura saman gadonta ta janyo pillow ta ɗaura kanta akai, Yau ta juya ma danish baya, ada kullum Juna suke fuskanta idan zasu yi bacci,


Sam ta kasa runtsawa tunanin deeja ya hanata sakat, tarasa ina zata tsoma ranta taji daɗi, 


Muryar danish ce ta ratsa kunnata, 


"Angel" Ya kira sunanta, Yana daga kwance saman gadonshi, tana ji tayi banza ta ƙyale shi, ya kasa bacci saboda fushin da take yi da shi, Sake kiran sunanta ya yi"Angel" kusan sau Biyar amma bata amsa ma shi ba, miƙewa yayi tare da saukowa daga saman bed ɗinshi, Ya matsa daga gefen gadonta ya zauna, hakan ba ƙaramin ƙona mata rai yayi ba, duk da bata waigo ta kalle shi ba amma taji alamar yana akusa da ita,


Cool voice dinshi ce ta kara ratsa kunnanta, "Am really sorry, I don't mean to hurt u, just bana son Su cutar da ku ne that's the reason why na hana ku abunda ku ke ƙoƙarin yi, Giants sunfi ƙarfin ku, ba zaku iya ja dasu ba....."kamar an katse shi ya dakata da yin maganar yana kallon gefen fuskarta, pillow yaga ta sanya saman kanta ta toshe kunnanta, don ma yasan ba sauraronshi take yi ba, duk sai yaji ba daɗi, Gaba ɗaya ya rasa sukuni, shi dai bai ƙaunar yaga wani na fushi da shi, ko zafin marin da ta yi mashi ɗazu baiji ba, da ace wani ne tayi ma marin nan ko bai rama ba sai ya fusa ta,


"Angel pls talk to me. i realized my mistake, and I regret it, ba zan sake ba" shiru bata tanka mashi ba, " wannan karan muryarshi tayi zaƙi da sanyi kamar zaiyi kuka, Miƙa hannunshi yayi tare da ruƙo doguwar sumar kanta, aikuwa a fusace ta sanya hannunta da ƙarfi ta ka6e mashi hannunshi,' batare da ta yi magana ba, 


Still baiyi fushi ba ya kuma cewa"Angel if you don't talk to me, I won't sleep, I will spend the whole night here"  babu wasa a fuskarshi yayi maganar, 


Ji take gaba ɗaya ya takura mata, zaman shi agefen gadonta kamar saman kanta take jin shi, Tasan halin shi Ba cikakken hankali ne dashi ba, Yana iya aiwatar da abunda ya fada, Tuna wannan yasa ta miƙe xaune har ya fara sauke ajiyar zuciya atunaninshi ta yafe mashi ne, ashe masifa ta tashi ta zazzage mashi,


Cakumar wuyan rigarshi tayi da hannayenta biyu, ta zazzare mashi manyan gray eyes ɗinta Ta jijjiga wuyan rigar tashi, Saboda masu bayyaci yasa ta sassauta muryarta,


"Wai menene alaƙata dakai ne? Ka addabi rayuwata ka hanani sakat, kai nifa bansan ganin wannan mummunar fuskar taka, na tsani ragon namiji irin ka, pls na roƙe ka ka tashi kabar gefen gadona ko na samu inyi bacci" Takai karshen maganar tare da ture shi gefe, ko motsi baiyi ba, kallonta kawai yake yi da lumsassun idanuwanshi, 


A hasale tace"idan har bazaka sauko daga saman gadon ba, Ni zan tashi in baka wuri," ganin tana ƙoƙarin saukowa daga saman gadon yasa shi yin saurin damƙar hannunta, wani irin mugun kallo ta jefa mashi"sakar mini hannu na," ba musu ya saki hannun. ta sauko daga saman gadon, Ta dauƙi bargonta da pillow, Ta juya ta nufi tsakiyar ɗakinsu Ta shimfiɗa bargon ta jefa pillown saman shi, Ta haye ta kwanta, duk yana a zaune gefen gadonta yana kallonta, 


Lumshe idanuwanta ta yi da niyar bacci ya ɗauketa, kamar daga sama taji an sanya hannu an ɗauketa da ita da bargon da pillown duka ya tattare su ya ɗaga sama Ya nufi gadonta, Yana zuwa ya jefe ta saman gadonta, aɗan tsorace ta ware idanuwanta tare da wurgasu kan fuskarshi Yana atsaye ya kafe ta da ido, Tsabar mamaki ya hana ta furta komai, kamar walƙiya haka Yaje ya daukota, 


Cikin nuna jin takaici tace"Nashiga uku! Wai ina ruwanka dani ne? idan na kwana a ƙasa matsalarka ce ko tawa"? Ya bata amsa da cewa"tamu" guntun tsoki taja, bata ƙara furta mashi komai ba, tana jin motsin shi abayanta, haukanshi na matuƙar ɗaure mata kai, Lokacin da bacci yayi awon gaba da ita, A zaune ya fara gyangyaɗi, A ƙarshe da baccin yafi ƙarfinshi a bayanta ya kwanta saman gadonta, lallai ya taro march,


*ANEELAH*


Wuraren ƙarfe 12 na safe, Tana a ƙudundune Cikin bargonta, Tun bayan sallar asuba data kwanta bacci bata farka ba, wani irin nauyin bacci ne ya ɗauketa, Hada ƙarin maganin muran da tasha a daren Jiya,


Baby junaid ne ya shigo cikin ɗakin yana azaune Cikin  motar shi ta wasan  yara, Da hannu Yake juya streering wheel ɗin motar, Ba ƙaramin kyau yayi ba, jump suit ne a jikinshi launinsu ɗaya da ƴar motar wasan shi, Army green, da alama ba ƙaramin daɗin motar yake ji ba, daga ya juya steering saita tafi da gudu, agaban gadon Mommynshi Ya tsaya, tare da kai hannu ya danna wani maddani A jikin motar, nan take motar ta soma yin Jiniya, Afirgice aneelerh Ta farka tare da yaye bargon data lullu6a dashi hannunta dafe da ƙirjinta, jallabiya ce a jikinta, Muryarta na kerma take ambaton" Innallahi wa'inna ilaihirraji'un"


tayi matuƙar tsorata, Duk a tunanin ta ƴan sanda ne suka zo gidan ashe motar wasan junaid ce, Fuskarta a yamutse take kallon shi,  ya wage baki yana dariya fararen hakoranshi tar dasu, Dimples ɗinshi biyu sun lotsa sosai, a fusace ta miƙa hannu ta ɗauki pillow ta wurga mashi saman fuskarshi, nan take ya kwa6e fuska zai yi kuka, 


Cikin nuna 6acin ranta ta soma Yi mashi magana"Karka kuskura kace zaka yi mini kuka stupid, Wlh nayi regretting dana fidda kuɗina na siya maka motar nan ashe kaina abun zai ƙare!, bazaiyiyu ba ka hanani kwanciyar hankali, zan 6a66alla motar In jefata cikin bola kowa ya huta" Jin wannan maganar yasa shi ƙara sautin kukan nashi, Ganin tana yunƙurin saukowa daga saman gadon yasa jin tsoro, gudun kada ta 6alla mashi motarshi kamar yadda tace, aikuwa da sauri yaja streering Ya juya motar da gudu yajata ya nufu ƙopa, Murmushi ta saki tana bin bayanshi da kallo, aranta tace"Allah kaɗai yasan irin ƙalin sharrin da zaije yayi mini a wurin mami, yau nifa na shiga uku, Wata'ƙil ma yaja a hanani Yin breakfast, " takai karshen maganar tare da saukowa daga saman gadon takai hannu ta ɗauko filon data jefa mashi a ƙasa ta wurgo shi saman gadon, miƙa tayi tare da yin hamma ta wuce toilet, after some minutes ta fito tana tafiya a slow ta nufi gaban mirror ta zauna, wata irin yunwa take ji kamar taci ƴan hanjin cikinta, wayarta ta ɗauka dake ajiye gaban mirror, ta danna power hasken screen ɗin ya kawo, hoton angel ne a matsayin wallpaper ɗinta, ta yi mata hoton ne saman gado tana bacci ta saki baki, Tana matuƙar son angel, Tayi missing ɗinta sosai, duk rana ta Allah idan tafarka daga bacci ta ɗauki wayarta saita sumbaci hoton, Yanzu ma kiss ta manna mashi, aranta tace"I really missed u angel, kamar in yi hauka, Allah ya kare mini ke aduk inda kike, Inaji araina cewa Kina araye kuma kina tunani na, I luv u so much" tuni hawaye sun Cika idonta,


Tana yunƙurin miƙewa daga saman mirror chair ɗin, Sai ga Ana Mai aikin gidansu ta faɗo Cikin ɗakin tana Haki hannunta ruƙe da wayarta, Jikinta sanye da Riga da skirt, Sun matseta, Hankalin aneelerh ba ƙaramin tashi yae ba, Ta cikin mirror ta hangota, da sauri ta ƙarasa Juyawa Baya tana kallonta tace"Ana lafiyarki kuwa? Babu neman excuse kin faɗo mini ɗaki? Kamar wadda tasha ƙwaya"? Tayi maganar tana tunkararta, Duƙar dakai ƙasa ana tayi Muryarta na ɗan  rawa tace"Am sorry madam, Wani abune na gani daya bani mamaki, shi ne nazo in nuna maki," 


Matsawa aneelerh tayi kusa da ita, Tare da miƙa hannu ta kar6i wayar Ana, tana ɗaura idanuwanta kan screen ɗin, Ras taji gabanta ya faɗi  waro ido waje tayi tana kallonta, mamaki ƙarara akan fuskarta tace"Abun mamaki! ana a ina kika samu hoton nan? Kuma daga gani sabuwar ɗauka ce!" murmushi ana ta ɗan saki kafin tace"Yanzun nan Na ganshi A instagram, shafin twins Na  Family ɗin Obinna, Zayn da zaid pravin Obinna, Su ne su ka yi posting ɗin a page ɗinsu na insta, madam  i was shocked da naga pic ɗin nan nace ashe matar nan tana araye da ranta da lafiyarta! " jinjina kai aneelerh tayi da alama tayi matuƙar girgiza tace"Wonders shall neva end" kallon  Ana tayi tare da cewa"Ki jira ni ina zuwa, dole mami taga hoton nan, amma dai matar nan ta bani mamaki matuƙa"  Jiki na rawa aneeleh ta fuce daga Cikin ɗakin, gudu gudu sauri sauri ta nufi bedroom ɗin mami, bayan tafiyarta ana ta fito ta tsaya a falo tana jiran dawowarta,


Aneelerh Na yunƙurin yin sallama a ƙopar ɗakin Mami, sai ga mamin ta fito Jikinta sanye da riga da zani na atampa, Ƙiris Ya rage su bangaji juna ita da aneelerh, Sakin baki mami tayi tana kallonta,


Da sauri aneelerh tace"Am sorry mami, a ruɗe nake ne, wani abun mamaki ne Ana ta gwada mini acikin wayarta, Shi ne na kawo maki kema ki gani" tana inda inda tayi maganar, tare da miƙa ma mami wayar hannunta, tasa hannu ta kar6a, koda mami ta kalli hoton saita ruƙe ha6arta da hannu ɗaya, ta ɗan zaro ido da mamaki akan fuskarta tace"Kai! Wa nake gani kamar BENAZIR"! aneelerh tace"Mami itace, Kalli dakyau ki gani, ba'a jima da yin posting ɗin ba, " Mami tasha ruwan mamaki, Sai ƙarewa hoton kallo take yi,  dagaske ɗin dai benazir ce, Daga gani hoton batasan an yi mata shi ba, tana a tsaye, hannunta ɗaya ta dafa murfin danƙareriyar motarta, tsadaddiyar gaske, jikinta na sanye da business suit black colour sunbi shape ɗinta sun zauna mata cuf cuf, kamar don ita aka ƙera kayan, hips ɗinta sun fito sosai, hannunta ruƙe da wayarta ƙirar i phone 15 pro, kanta babu hula ko ɗan kwali, Zallar gashin kanta ne daya sha gyara Har midback dinta, idanuwanta na manne da glass, idan ka ganta a hoton ba zaka ta6a yarda cewa ta ta6a aure ba, Ko tana da ƴa, saboda tsabar haɗuwarta, Jikinta Badai kyau ba, agogon diamond ɗin dake sanye a hannunta, a ƙalla Price ɗinta yakai 100m, 


Kallon Juna mami da aneelerh su ka yi kowa Fuskarshi ɗauke da al'ajabi, mami tace"Abun mamaki baya ta6a ƙarewa, Wai dama ƴar nan tana nan da ranta da lafiyarta? Hankalinta kwance tsawon shekara da shekaru bata ta6a waiwayar ƴarta da mijinta ba, Anya kuwa benazir ce aneelerh? Kodai watace me kama da ita? to ae abunne da ɗaure kai wlh, ' 


Murmushin takaici aneelerh ta saki tare da cewa"wlh mami itace! Babu shakka benazir ce, ae ina ganin hoton ko doubting ban yi ba, na shaida  itace, Kinsan dama ita tun fil'azal wayayyiyar macace akwai son gayu, Kuma tafi sha'awar rayuwar ƴanci, " mami tace"Haka fa take, Oh Ni ƴarsu, duniya da abun tsoro take, Anya kuwa Benazir tasan ciwon kanta"? aneelerh tace"Ina fa, ae babu alama, Yanzu haka ko Iyayenta basu da masaniya akan inda take rayuwa, Duk da Naga kamar Ƙasar waje ne, idan kika ƙura ido a jikin Ginin dake a bayan hoton an rubuta Rbc (Royal bank of canada) dake acikin toronto,  Kuma ga dukkan alamu mami hoton bada saninta aka ɗauke shi ba, don da ace ta sani da bata bari an ɗauke shi ba, kodan kada asirinta ya tonu agane inda take, tun da ko Iyayenta basu son awace nahiya take zaune ba suma nemanta suke Yi ruwa ajallo," 


Mami tace"Nama rasa me xance, kawai dai Allah ya shiryeta in me shiryuwace, amma dai wannan rayuwar da ta ɗaukarwa kanta bamai 6ullewa bace, Wlh zata yi danasanin mara amfani, kwata kwata benazir bata yi wayau ba, Allah kanta tayi mawa, Ace da ranka da lafiyarka, Ka gudu kabar Jinjira acikin kwamin wanka, da mijinka batare da ka waiwaye su ba almost 15 years, Saboda shafewar basira da rashin hankali, tana can tana yawon biɗiɗi," takarasa maganar tare da jan dogon tsoki Ranta ya 6aci ta miƙe ma aneelerh wayar"kar6i nan nagaji da ganin kayan takaici," kar6ar wayar aneelerh Tayi, Har ta juya zata Bar ƙopar ɗakin mami sai kuma ta ɗan dawo baya tace"mami Baby junaid fa"?

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post