Kurkukun Ƙaddara episode 35 complete

Kurkukun Ƙaddara episode 35 complete

Kurkukun Ƙaddara

 💋KURKUKUN ƘADDARA💋


daga alƙalamin Boss Bature, writer of Abban sojoji


E35 


*Back To prison*


Ƙwaƙƙwaran Juyi angel tayi da niyar ta gyara kwanciyarta,  sai ji tayi an tokare bayanta, A matuƙar ruɗe ta juyo tana kallonshi, waro ido waje tayi ganin danish saman gadonta, Aikuwa rai a6ace ta sanya ƙafarta da ƙarfi ta ture shi gaba ɗaya ya gangara ƙasa Kanshi Ya bugu sosai har saida yafirta"ash!!" saboda zafin da ya ji, Zazzaga mashi masifa ta soma Yi ta inda ta shiga bata nan take fita ba, sautin muryarta ya karaɗe Kunnuwan masu bacci ɗaya bayan ɗaya su batool suka dinga farkawa Suna tambayar lafiya me ya faru?


Nuna danish ta yi da yatsan Hannunta tace"wlh kaɗan ka gani, Idan har baka  fita sabgata ba, Ina mace kana namiji Ka kwana a gadona, Salon kawai kaja mini zunibi," Tun da ta fara Yi mashi faɗa, bai motsa daga kwancen da yake a ƙasa ba, ya dafe gefen goshin shi da hannu, Yaji zafin buguwar da kanshi yayi,


Saukowa su batool su Ka yi daga saman beds ɗinsu, fuskokinsu duk A yamutse idanuwansu sun kumbura sakamakon kukan da suka sha Jiya da za'a tafi da deeja,


Abakin gadon angel suka tsaya suna kallonsu ita da danish, Ta rufe ido sai faɗa take mashi hada pillow ta jefe mashi saman fuska, Ya rasa ina zai tsoma ranshi yaji daɗi, shouting ɗin da take yi mashi ba ƙaramin gigita shi yake yi, daurewa kawai yake yi,


"Pls angel, Ki yi haƙuri Ki ƙyale shi hakanan, kodan saboda lallurarshi ta rashin son hayaniya zai iya rikicewa, Hanna ce tayi maganar, angel ta watsa hannu tare da cewa"Idan ya tashi ya haukace ƙarewa ma, wlh ko ajikina, tun farko saida naja mashi kunne akan ya ni santa kanshi dani amma yaƙiya, saboda head fish ne dashi"


Girgiza kai batool ta ɗanyi idonta akan angel tace"Sister badan halina ba, Pls Ki bar maganar nan, Ki barshi yaji da kanshi, Nasan kina fushi dashi ne saboda abunda ya faru jiya, Ki yi haƙuri ki manta komai, kuma ki daina fushi dashi saboda Baya ƙaunar yaga ana share shi, Yana shiga damuwa" daƙyar batool takarasa maganar ganin irin kallon da angel ke jefa mata,


Gyaɗa kai tayi tare da jinjina kai tace"Shikenan zan ƙyale shi amma babu ruwanshi dani! Ni kawai bana son Yana kallona ko Yana yi mini magana, " Tana kammala maganar ta sauko daga saman gadonta ta bi ta gefensu Ta shige toilet,


Zuƙunnawa batool tayi agaban Danish Ta ruƙo hannunshi acikin nata, Ba ƙaramin tausayin shi taji ba, ganin sahun marin da angel tayi mashi asaman fuskarshi har yau bai disashe ba,


Cikin sanyin murya tace"Am sorry danish, Kamar yarda tace ka ƙyale ta, to ka rabu da ita har zuwa time da zata huce, if not zata cigaba da Ƙyararka ne, Nasan zata dawo da kanta ne ta nemi yi maka magana," sai lokacin ya samu ya miƙe zaune, ya jingina bayanshi jikin bango, ɗaya bayan ɗaya ya shiga binsu azeeza dake atsaye da kallo, matan ne gaba ɗayansu, Sai daga bisani Haris da su naufal Suka Sauko daga saman gadajensu, A inda yake zaune suka tsaya cirko cirko suna kallon shi,


"Kuma fushi ku ke yi da ni? Kamar yadda take fushi dani"? Yayi masu tambayar idonshi akansu, atare suka haɗa baki wurin cewa a'a, Kallon haris yayi tunkafin yayi mashi magana haris yai saurin cewa"am not angry with u, kaima ka sani bazan iya fushi dakai ba,  just banji daɗin abunda ya faru ba jiya, amma komai ya riga daya wuce" jinjina kai danish yayi kafin ya kuma cewa"komi nake yi ina yi ne saboda ku, amma nasan zaiyi wuya ku fahimci hakan, sai nan gaba" 


Naufal yace"Pls danish, mu komai ya wuce awurinmu, abunda ya faru ya riga daya faru ba wanda ya isa ya dawo dashi baya, so pls mu manta kawai, baida amfani tuna baya," Danish yace"idan ku kun fahimce ni, ita taƙi ta fahimce ni, tun daren jiya nake bata hakuri amma taƙi ta saurare ni," sai lokacin suka gane inda damuwarshi ta dosa, dama shi haka yake sam baya son wani yana fushi dashi tun fil azal, gaba ɗaya yake rasa sukuni,


"Danish kada ka damu kanka, In dai angel ce Zata kula ka, Ae bata iya fushi ba, tana da saurin hawa da kuma saurin sauka," acewar javed,


Ta6e baki yai tare da cewa"Its okey, ngde da kulawarku agare ni, " daga haka Ya miƙe jiki ba ƙwari Ya Nufi toilet, domin yin wanka, 


Kafin Giants su kawo musu Breakfast ɗinsu, Sai da kowannan su Ya yi wanka, Basu jima da hallara A cikin ɗakin nasu ba, Sai ga Giants ɗin sun shigo ɗauke da kayan abincinsu,  bayan sun ajiye musu saman dining carpet, duk suka zazzauna kewaye da farantan, Yau farfesun naman kaza aka kawo musu da zafinshi hada tiriri Yaji kayan ƙamshi, ga kuma dambun nama da aka haɗo musu dashi, sai Kayan marmari kamar kullum da kuma soft drinks, Abun na ɗaurewa angel kai, ganin irin badagon da ake yi da nama agidan kurkukun, sam bata yarda da irin wannan Lafiyayyar cimar da ake kawo musu ba, kullum basu da abinci sai nama kala kala! Na kaza na shanu  na rago, wani naman ma batasan na wace dabbar bane, tana yawan tambayar kanta ko su wanene ke girka abincin kurkukun daga gani ƙwararru ne a 6angaren catering, sun iya sarrafa abinci, wani naman saboda tsabar dahuwar shi kana jefa shi abaki tunkafin ka taune da haƙori zai dagargaje da kanshi, ita dai fargabarta kada ace abincin da ake basu su naci, da ransu za'a fanshe, duk  in zuciyarta ta saƙa mata hakan sai taji gabanta ya faɗi rasss!  Don kuwa ko gwamnati bata aikin banza, balle kuma mutanan da Ba Allah ne aransu ba, Sunsan dalilin dayasa suke basu lafiyayyan abinci wata'ƙil kodan suna amfani dasu ne, Allah wa'alamu 


 kafin su  fara Shan farfesun saida ta tunasar dasu akan su yi bismilla, Kullum ne sai ta tuna musu, hatta haris yau da tace su yi bismillah sai da yayi duk da bai musulunta ba, danish ne kawai baiyi ba, Ta lura dashi duk wani abu daya ƙunshi sunan Allah aciki bai furta shi, hakan ba ƙaramin ƙona mata rai yake yi ba, Har suka kammala cin abinci, da zarar sun haɗa ido dashi sai ta dinga jefa mashi harara, duk yabi ya tsargu ya hana zuciyarshi sakat, farfesun ma ba'a cikin kwanciyar hankali yasha shi ba, 


Bayan sun kammala Cin abincin, Giants suka tattara farantan Suka fuce daga Cikin ɗakin,


Ganin suna yunkurin zuwa saman gado su kwanta ne, yasa angel ta dakatar dasu, tace su motsa jikinsu, Idan sun kammala su watsa ruwa ajikinsu, Sannan Sun kwanta su huta, babu musu suka amsa mata da toh, banda danish da haris, tuni sun haye saman gadajensu, Shi haris damuwar rashin deeja ne yasa shi ƙin ta6uka komai, tunanin abunda ya faru daren jiya kafin atafi da ita ya tsaya mashi arai, Yaji tausayinta sosai, su kansu sauran ƴan uwan nasu sun damu da deeja, Ba yadda zasu yi ne shiyasa suka barma Allah komai, 


A tsakiyar ɗakin suka Jera layi suna yin  exercise, kamar wasan ƴar tseral haka suka dinga zubawa da gudu idan suka kai ƙarshen bango sai su dawo su sake komawa, Sai da suka tara uwar zufa ajikinsu tukunna kowa Ya nufi toilet domin watsa ruwa, Bayan sun fito ne, parveen ta matsa ma angel akan tayi mata irin kalabar da tayi ma su azeeza, Dama tun ranar da ta ganta ta kwallafa rai akan tana so itama, kafin marece yayi angel tayi ma parveen kalaba biyu akanta, ba ita kaɗai ba hada rubina tayi mawa, Bayan  ta kammala musu kitson, Kowa Ya koma saman gadonshi ya zauna, Fira suka soma yi atsakaninsu acikin firar ne, suka tambaye ta, wai da tace musu wata rana zasu fita idan suka fita ina zasu je? Su da basu san komai na wajen kurkuku ba, murmushi tayi tare da cewa su kwantar da hankalinsu, Gaba ɗayansu zasu yi rayuwa agidan daddynta, Tace daddyna yana da gida, kuma gidanmu ɗaki Shida ne, Akwai palour ɗaya, dani da azeeza da batool zamu ware ɗaki ɗaya, Parveen da deeja da hanna zasu ware nasu ɗakin ɗaya, sai Eve da hibba da rubina suma zasu ɗauki ɗaya, nawa kenan? Suka ce mata Uku, tace toh, sauran ɗakunan guda uku, Javed da Naufal tare da Mubeen zasu ɗauki ɗaya, sai Haris shi da wancan Maji daɗin gadon suma zasu ɗauki ɗaki ɗaya," da ta ambaci maji daɗin gado hada harara ta wurga ma danish, ya lumshe idanuwanshi tamkar baiji me tace ba,


Azeeza tace"Saura ɗaki ɗaya ya rage, wa za'a bamawa" angel tace"Na daddyna ne idan Allah yasa yana araye, ko ince daddynmu" gaba ɗaya suka saki murmushin farin ciki, parveen tace"amma kina ganin daddynki zai so mu," angel tace sosai ma, In ma daddyn nawa baya araye, zamu zauna wurin auntyna adama ne, Ko gidansu aunty aneelerh na, zasu ɗauki nauyin duk wani abu da zamu buƙata, Cin mu shan mu da suturarmu, kuma zamu yi rayuwar ƴanci, Zamu je inda muke so, Muje  shan ice cream, muje cinema kallo, hada shopping mall zamu dinga zuwa kowa ya za6i abunda yake so, " parveen na murmushi tace"Zamu dinga samun abinci akai akai"? Dariya angel tayi tare da cewa"Sau uku arana, za'a bamu breakfast, lunch and dinner, Idan ma kinga dama tsakar dare kika farga da yunwa zaki Iya zuwa kitchen ki girka abunda ranki yayi maki, " Gaba ɗaya suka sanya ihu suna murna jin tace zasu Iya girki da kansu, Ga kuma abinci available, A lokacin jikin angel yayi mugun sanyi, ganin yadda suke ta farin Ciki, gani take kamar bazasu rayu ba, balle aje ga maganar fita daga Cikin wannan Kurman kurkukun ƙaddarar, 


Batool tace"wlh angel baki ji irin daɗin da naji ba, sai naji dama ace yau mu fita daga kurkukun nan, muje gidanku, kinga shikenan mun rabu da giants, bazasu ƙara zuwa su ɗauki wani acikin mu ba, balle har su cutar dashi," 


Azeeza tace"Nima na ƙosa inga ranar da zamu fita daga prison ɗin nan, wlh  Ina so inyi rayuwa irin wadda ki kayi tare da daddynki, ae kince mana zai so mu, muma zai maida mu kamar ya'yanshi, zai dinga zuwa damu yawo yakaimu wuraren da kika bamu labari ko"? Angel tace"Eh, kuma koda ace babu daddyna, akwai sauran dangina duk zasu so ku, kuma zasu gatanta ku kamar ya'yansu ku," acikin zuciyarta tace"sai dai fitar ce keda wuya, bansan ya zamuyi ba, gidan kurkukun nan yafi ƙarfi na, sai dai bai fi ƙarfin mahaliccin mu ba,


Har dare Yayi suna fira Gwanin ban sha'awa, ta faranta musu sosai, Bayin Allah sun ƙwallafa rai da son yin irin rayuwar da tayi, wato rayuwar ƴan ci, yanzu a shirye suke da zarar sun samu hanyar fita zasu bita ne,  hmmmmmm 


(da su kayi wannan firar sai suka tuna mini da  wani labari dana ta6a tsarawa acikin zuciyata mai suna) 


*ANYA ZAMU KAI LABARI❓*


*Amma fa bashi bane next novel dina ba, Acikin middle step na Kurkukun ƙaddara zan faɗi sunan next novel dina amma wannan karan babu wanda zai fahimta idan na rubuta😂 ɗan adam da buri, In sha Allah idan Allah yakai mu da rai da lafiya, rayuwa ba tabbas*


Saboda daɗin fira yasa suka dawo gadon angel kowa ya samu wuri a gefe da gefen gadon suka zauna waɗanda basu samu wuri ba daga ƙasa suka zauna, Javed hada ƙoƙarin ɗauko fitilun ɗakin guda uku Ya kunna a ƙasa ya ajiye su, ɗakin ya yi haske, sun ɗauki tsawon lokaci, sai da angel taga sun fara gyangyaɗin bacci, ta Katse masu firar tare da cewa"its time to sleep, Kowa Yaje ya kwanta, gobe in Allah ya kai mu da rai da lafiya zan ƙarasa baku labarin" suka amsa mata da toh, ɗaya bayan ɗaya kowa Ya miƙe suna tafiya suna bangaje juna a haka suka nufi gadajen su, har sun kwakkwanta Muryar angel suka ji yo tana cewa"Su yi addu'a kafin su kwanta" suka amsa mata da toh,


Danish yana lafe saman gadonshi, ya lumshe idanuwanshi, amma babu alamun bacci yake yi, Gyara kwanciyarta ta yi, yau bata ju ya ma shi baya ba, suna fuskantar Juna,


Ganin yana mutsu mutsun buɗe idanuwanshi yasa tayi saurin Fuskantar ceilling, tare da rufe idanuwanta, Sam bata ji lokacin daya sauko daga saman gadonshi ba, sai dai taji hucin numfashin mutun yana kokawa da Nata numfashin, da sauri ta buɗe idanuwanta, Tsabar firgitar da ta yi ne yasa ta zare ido, Ganin fuskarshi a kusa da ta ta, Saman gadonta Ya hau Ya yi mata rumfa da ƙirjinshi, ƙiris Ya rage tsinin hancin shi ya gogi nata, Tsananin mamaki ne Ya kamata, Tuni ta shiga ruɗanin kome zai yi mata, Gashi ya tsareta da idanuwanshi ko ƙyaftawa  babu, muryarta na inda inda tace"La..fi..ya"!? Yace"haƙuri nazo na baki, ki daina fushi dani, tun jiya baki yi mini magana ba, Idan muka haɗa ido sai ki ta harare na,"  daƙyar yakai ƙarshen maganar throat dinsa na moving kamar yana swallowing ɗin wani abu, yana ganin ta fara yunƙurin motsa la66anta alamar zata yi magana da sauri ya ɗaura dogon yatsan shi saman ƙaramin bakinta, Cikin sanyin murya yace"Pls don't shout at me, Idan kinsan ba me daɗi zaki faɗa mini ba, Kiyi shiru kawai, nafa baki haƙuri, Kuma na gane kuskure na,"   


Hawayen da ta gani kwance a cikin fararen idanuwanshi ne yasa taji zuciyarta ta karaya, sai ma taji tausayin shi yakamata, Shi dai haka rayuwarshi take, Yana da matuƙar saukin kai, ga haƙuri matsalar shi ɗaya ragwanci, hannu tasa ta kawar da yatsanshi daga saman bakinta,


Sai da ta fara jefa mashi harara, kafin tace"Zan yafe maka amma sai ka yi mini alƙawarin wani abu" yace"komene ne zanyi" ɗan ta6a baki tayi tare da cewa"kada ka ƙara bari a ɗauki wani daga Cikin mu, Saboda nasan kana da ƙarfin da zaka Iya hana wa" tunkafin ta karasa maganar, Yae saurin girgiza kai yana faɗin"That's impossible, ki fahimce ni, Ni ba kowa bane face prisoner, bani da ƙarfin da zan Iya yin fighting da giants, sunfi ƙarfina, idan ba so kike in rasa raina ba"


tsoki taja"hmmm dama nasan haka zaka ce, Idan har dagaske baka da ƙarfi, to ta ya akai ka ke Iya shiga toilet bayan na datse ƙopa ta Ciki? Kuma ya akai ka iya 6a66ako glass door ɗin dake acikin toilet, tun daga tushen shi, taya zan yarda da maganganunka? Ta yi tambayar tana kallon cikin idanuwanshi, Har lokacin yana a yadda yake bai ɗago ba,


Runtse idanuwanshi ya yi, tare da biting lower lip ɗinshi, A hankali ya ɗan ware su akan fuskarta, Muryar shi arauna ce ya soma magana"Bansan ya zanyi in fahimtar dake ba Angel,  Ni kaina bansan Ya akai nake iya shiga wurin dake a rufe ba, Also ƙarfin da yazo mini time dana cire glashin nan yanzu babu shi ajikinta...." kawar da kanta gefe tayi tare da cewa"Ban yarda dakai ba, danish Ina zargin kai ma Giant ne, kamai da mu shashasha kana 6oye mana ainihin wanene kai, Sannan kuma kasan Komai game da kurkukun nan, Amma kaƙi ka sanar damu, kafi so mu yi ta shan wahala har mu rasa rayukan mu, Kana ji kana gani ana cutar da rayuwar ƴan uwan mu amma kai hankalin ka kwance, Ko ajikinka.....' Kafin ta rufe bakinta, Taji saukar ɗigon ruwan acikinsu, da sauri ta kalle shi, Hawayen shi ne suka sauka cikin bakin ta, Yana girgiza kai yace"angel stop accusing me, am not a giant, Bana jin daɗin maganganun da kike gaya mini, its hurting my heart," Daƙyar Ya kai karshen maganar, wani irin raɗadi zuciyarshi ke Yi mishi, idan akwai abunda ya tsana Ya biyo bayan Giant, Yaji zafin Kalaman angel fiye da zafin marin da ta yi mi shi, ita kanta angel da ta yi maganar sai daga baya ta yi danasanin furta mashi zargin da take yi akanshi, bata ta6a ganin fushi akan fuskar danish ba, sai yau, Jikin shi har kerma yake Yi, wurin saukowa daga saman gadonta, da sauri ta mike xaune tana kallon shi, Ji take kamar ta kira shi ta lallashe shi, girman kai ya hana tayi hakan, Ta yi tsammanin zai kwanta asaman gadon shi ne, amma sai taga ya ɗauki pillown shi tare da bargonshi, bai nufi ko'ina ba sai cikin toilet area ɗinsu, duk sai taji ba daɗi, Ya rasa ina zai kwanta sai cikin toilet, In da madaddalar shaiɗanu suke? Dama Ya lafiyar giwa, har ta koma ta kwanta da niyar tayi bacci amma sai ta gaza runtsawa, Damuwa duk ta cika ta, a ƙarshe dai ta ji bazata Iya jurewa ba, ta miƙe Ta sauko daga saman gadonta, sai da ta fara zuwa gaban table ta ɗauko fitila ta nufi cikin sashen toilet ɗin, Tana zura ƙafarta Ciki, ta same shi a kwance saman shimfidar da yayi, hawaye ta ko'ina asaman face ɗinshi, ya lumshe idanuwan shi jin motsin mutun yasa shi ɗan buɗe idanuwan da suka canza launi, koda ya yi arba da ita sai ya ju ya mata baya, A ƙasa ta ajiye fitilar ta zauna gefen shimfiɗar tashi, Kusan mintuna tana kallon gefen fuskarshi, Daƙyar ta iya buɗe baki ta soma magana,


  "Danish fushi ka ke yi dani? nayi nadama, da nasan kalamaina zasu 6ata maka ranka, da ban furta maka su ba, nima na faɗi ne kawai badan ina nufin hakan ba, " Babu irin lallashin da bata yi mishi ba, amma ɗan tahalikin nan yaƙi tanka mata, Muryarta a karye tace"Nagaji da lallashinka, Kaga Idan ma bazaka haƙura ba, to ka tashi mu koma ɗaki ka kwanta, Amma kwana a wurin toilet ɗin nan sam bai dace ba, Akwai shaiɗanun aljanu zasu iya cutar dakai,' sai lokacin yace"Meye damuwarki idan sun cutar dani? Jikin ki ko nawa"? Ta bashi amsa da cewa"Namu, saboda na damu dakai, dani dakai abu ɗaya ne, jinin dake yawo ajikin ka shi yake yawo ajikina, taya ɗan uwa zai share ɗan uwansa? Duk da nasan laifina ne amma na gane kuskure na na yin fushi dakai bazan ƙara ba," Bai ƙara tanka mata ba,


  "Pls danish, mu koma ɗaki, " magiya ta dinga yi mashi amma yaƙi tanka mata, har ta fara tunanin ko ya yi bacci ne jin shiru, matsawa ta yi sosai kusa dashi, ta ɗan kwanto saman jikin shi tana leƙen fuskarshi, ya rufe eyes ɗinshi, kamar ya fara bacci, yanke shawarar ɗaukar shi ta yi kamar yarda ya ɗauketa jiya da ta yi fushi ta kwanta a ƙasa tsakiyar ɗakin su, Murmushi ta saki yayin da take nannaɗe hannun rigarta, tana kammalawa, ta soma kiciniyar ɗaukar shi, duk yana jin motsin hannayenta a bayanshi, wani irin nauyi ne dashi yadda kasan dutse, Ta tattara Iya ƙarfinta na ƙarshe ta ɗaɗɗago dashi, ta samu ta raba shi da saman bargon, tana ƙoƙarin Juyawa don ta nufi ɗaki dashi, wani irin nauyi Ya fisgeta, ba arziƙi ta sake shi ta rubza saman jikinshi, tana faman haki hana nishi kamar wadda tayi uban gudu, bawan Allah, kanshi ya bugu sosai, ba yadda ya iya, Jarabar angel tafi ƙarfin shi, har time ɗin bai buɗe idanuwanshi ba, bai kuma motsa ba, saboda nauyin jikinta dake asaman nashi, Babu alamun zata ɗaga shi, ta kifa kanta saman kirjinshi, sumar kanta duk ta tarwatse, slowly ya ɗan ware idanuwan shi, ya ɗaurasu akan sumar kanta, Muryarshi na ɗan rawa ya ambaci sunanta""An..gel" Ƙasa ƙasa ya furta sunan, bata amsa mashi ba. Kuma bata ɗago ba, ranshi ne ya bashi cewar kodai tayi bacci ne 


Zagayo da hannayen shi yae saman bayanta, a wannan yanayin bacci ya yi awon gaba su, manne da juna,


A washe gari


Haris ne ya fara farkawa daga Bacci, Cikin buƙatar zuwa toilet, Saukowa Ya yi daga saman gadonshi ya nufi toilet yana hamma tare da yin miƙa duk a lokaci ɗaya, Zura ƙafar shi keda wuya ya yi arba da su angel dake a kwance saman bargon danish, sun ƙanƙame juna suna bacci, Yadda kasan tip da tyre, Tsabar mamaki ne ya kama dashi,  har wani leƙen su yake yi don ya gane ma idonshi da kyau, hada sanya hannu ya ruƙe ha6arshi, can kuma sai ya saki murmushi, Mutumin da ke jin fitsari maimakon ya shiga toilet, Sai ya juya saboda gulmar data ciyo shi, Jikin shi har rawa yake Yi, wurin komawa cikin ɗakin, agaban gadajensu Javed, Yaje yana tashin su daga bacci, ɗaya baya ɗaya ya dinga tada su, Kowa Ya mike yana miƙa da hamma tare da tambayar shi lafiya? Yace musu Su zo suga wani abun ban mamaki, Koda jin haka jiki na rawa, Kusan atare suka sauko daga saman beds ɗinsu,  lokacin da su batool suka shiga, Suna Yin arba dasu Danish manne da juna, Kowa Ya buɗe baki haɗi da zare ido, Kamar sun samu tv, A kewaye da shimfidar Suka zuƙunna suna kallonsu, Yayin da su masu baccin basu san wainar da ake toya ba, 


(Akwai Sauran free pages amma yakamata ku fara yin payment, nayi kokari dai na baku book one kyauta, nima sai ayaba mini, Masu son shiga paid group na Facebook sun tuntu6i 08169856268, for whatsapp 08103884440)

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post