💋KURKUKUN ƘADDARA💋
58
Da sauri yace"ina son magana dake, tun jiya, bana so kowa ya sani, pls ki bani haɗin kai, ki taso mu shiga sashen toilet ɗin mu" yana ƙare maganar ya zame hannun shi daga saman bakinta, Ya miƙe cikin sanɗa ya nufi 6angaren toilet ɗinsu, yana tafiya yana waiwayon shimfiɗar Danish, wata irin kasalace ta baibaye Jikinta, A hankali takai hannu ta ɗauke kan Hanna daga saman laps ɗinta ta kwantar da ita ƙasa, kafin ta miƙe ta bi bayan Gabriel, tana shiga sashen toilet ɗin ta same shi atsaye ya jingina bayan shi jikin bango.
Yana ganinta yai saurin ruƙo hannayenta biyu acikin nashi, kamar wani mara gaskiya, yana magana yana kallon bakin ƙopar shigowa sashen toilet ɗin, Nan take ta fahimci cewa akwai wanda baya son yaji abunda zai faɗa mata.
"Tun jiya nake son na yi magana dake amma ɗan uwanki ya hanani sakat, na rasa gane dalilin dayasa baya son na tunkare ki"
"You mean Danish"? Ɗaga mata kai yai alamar eh"
Tace mai ka ke son faɗa min ne"? Har ya buɗe ba ki zai yi magana ya ji ta yi saurin katse shi da cewa"Oh wai kana magana akan Unaiza da aka tafi da ita jiya? Nasan ka tsorata da ganin an ɗauke ta, bawani abu zasu yi mata ba, za'a kai ta treatment room ne aduba lafiyar jikinta" tun da angel tai wannan maganar nan take Gabriel ya fahimci cewa DANISH yazo wurin, shiyasa tai saurin tarar numfashi shi, Saboda ita ta hango shi, kamar walkiya, ko yaushe ya tashi daga bacci.
ta wutsiyar ido Ya hango shi tsaye bakin ƙopar shigowa wurin ya goya hannayen shi saman ƙirjin shi, ya kafe su da ido.
Yatsina fuska Gabriel ye ba tare daya kalli fuskar Danish ɗin ba, yaji takaicin bayyanar shi, ɗan hana ruwa gudu, sauƙin ma Angel ta gan shi da baisan me zai biyo baya ba, idan ya faɗa mata ya shiga cikin kurkukun.
"Zan shiga toilet in yi wanka, yakamata kaima ka shiga ka yi" tana magana kamar batasan da zaman Danish a wurin ba, Ta juya ta nufi toilet ta buɗe ta shiga, duk akan idon Danish, Shima Gabriel ya nufi ɗayan toilet ɗin ya shiga Ciki, Ya datse ƙopa.
Sun so ace ya koma cikin ɗaki amma yaƙi tafiya, kowannan su sai da yae wanka time da suka fito daga cikin toilet ɗin, Yadda suka barshi haka suka same shi, Gabriel bai tanka mishi ba ya wuce ɗaki, Angel ce ta tsaya tana kallon shi fuskarta ɗauke da murmushi tace"ya ka ke? Fatan ka tashi lafiya"?
Wani irin kallo taga yanayi mata, kamar ba zai amsa mata ba, muryarshi da alamun kasala ya amabaci sunanta
"Angel, na tashi lafiya, ina fata kema haka" matsawa tai kusa dashi, jikinta da lemar ruwan wankan da tayi, Tace"jiya nashiga damuwa da aka tafi da unaiza, banma san time da bacci ya ɗauke ni ba, zuciyata ba daɗi" ta ƙarasa maganar kamar zata fashe da kuka, Ruƙo hannunta yae acikin nashi, ya ɗan janyota kusa dashi,
"Fuskarki harta kumbura, yakamata ki koma kiyi bacci, ko kin samu relief," girgiza mishi kai ta yi "a'a, baccin ya ishe ni, zan jira abinci ne, ka shiga toilet ka yi wanka zan jira ka anan"
(Angel sarkin wayau, tana so ne ya shiga don ta samu damar yin magana da Gabriel, ta ƙagara amatse take da taji me zai faɗa mata)
Maƙe mata kafaɗa Danish yai tare da cewa"Bana buƙatar yin wankan, mu koma ɗaki mu zauna, mu jira abinci nima yunwa nake ji," kallon shi kawai ta ke yi, wato ta fahimci wani abu agame da Danish, shegen wayau ne dashi, mutun sai yana da kaifin basira zai iya gane hakan.
"Dan Allah ka shiga ka yi wanka, inaso ne kaima ka ji irin daɗin da naji ajikina, idan ka kammala sai mu koma ɗaki,"
kamar maroƙiya haka tadinga yi mishi magiya akan yaje yae wanka, hada bubbuga mishi ƙafa da shagwa6a, sai taga ya saki ƙayataccen murmushi akan fuskar shi, ta yi tsammanin zai amince ne hakan yasata sakin murmushi tace"Ka amince zaka shiga ka yi wankan"? Ɗaga mata gira yai tare da cewa"Eh amma atare zamu shiga, sai kiyi min, idan har baki amince mun shiga atare ba, to ki daina roƙona akan yin wanka don ba inda zanje INA ATARE DA KE!" takaici ne ya isheta
A ƙule tace "ai ni nayi wanka akan me zan bi ka mu koma toilet"? Tai maganar tana gatsina mishi hanci, yace"nasan kinyi ae, ni zaki yi mawa yanzu" tsoki taja tare da bi ta gefen shi ta wuce cikin dakin, Ya juya yabi bayanta, Suna shiga Ciki suka sami Gabriel zaune gefen gadonshi ya zabga uban tagumi, Takaicin Danish ne ya ishe shi, sam baya son aja tsawon lokaci ba tare da yayi gaggawar sanar da angel game da yarinyar nan ba, zata iya rasa ranta.
Saman gado Danish ya zauna, angel kuma ta nufi akwatin kayansu, ta ɗauko red vest ɗinta, tare da dogon wandonta baki, Ta nufi sashen toilet dinsu ta shiga, acan ta canza kayan jikinta, ta cire tsaffin ta maida sabon, Vest ɗin tabi jikinta ba ƙaramin kyau ta yi mata ba, duƙunƙune tsohon uniform din ta yi a hannunta.
Bata fito ba, sai ta tsaya tana leƙen Cikin ɗakin su daga cikin sashen toilet ɗin, bakowa take kallo ba face Gabriel, ranshi ne ya bashi cewar ana kallon shi, hakan yasa shi juyowa don ya tabbatar, Cikin sa'a su ka haɗa ido da ita, Da hannu ta dinga yi mishi alamar ya iya rubutu? Ta kwatanta mishi biro ta hanyar yin amfani da hannunta na dama kamar tana rubutu, nan take ya gane me take nufi, bai amsa mata ba saboda Danish daya tsare shi da ido, shiyasa ya kawar da kanshi gefe ɗaya, Fitowa angel ta yi daga cikin toilet din ta shiga ɗakin ta zauna gefen gadonta, ta daura idonta akan Gabriel, so take ya bata amsar tambayarta idan ya iya rubutu, tana so ta sanar dashi akan ya buɗe backpack ɗin Unaiza ya ɗauko jotter dinta da biro yae mata rubutu, Ya jiye mata, ta hakanne kaɗai zasu iya magana da juna, if not Danish bazai ta6a bari su ke6e ba, sai dai batasan koya iya rubutun ba, zaiyi wuya ma ace bai iya ba, tun da a hasashenta ba rainon kurkukun ƙaddara ba, Akwai wayewa atattare da shi.
Yaso ya bata amsa amma Danish Ya kafe su da lumsassun idanuwanshi, Su uku ne idonsu biyu acikin ɗakin, Sauran har yanzu basu farka ba, Sai daga bisani ne Ɗaya bayan ɗaya su azeeza suka soma tashi daga bacci, da tunanin unaiza suka farka, suna ta jimamin halin da aka tafi da ita jiya, abun ya ta6a zuciyoyinsu, Angel tace dasu suje suyi brush suyi wanka, idan suka fito zasu motsa jiki yau, hakan yasa suka miƙe atare suka nufi sashen toilet ɗinsu, kafin wani lokaci duk su kayi wanka, kowa ya sanya red vest din shi da dogon wandon shi na sabon kaya ba ƙaramin kyau, su ka yi musu ba.
Ba su kai ga fara motsa jikin nasu ba, Giants suka kawo musu abinci, Dama da yunwa suka farka, Kowa ya samu wuri ya zauna, tsiren nama ne aka kawo musu da kayan marmari, hada robobin lemu dana ruwa, suna cin abinci idon Gabriel akan fuskar angel, yana so ya bata amsar tambayar da ta yi mishi ɗazu shiyasa ma ya zauna yadda zasu fuskanci juna, ko da ta ɗago suka haɗa ido dashi, saboda rashin gaskiya atare suka saci kallon Danish, shi da yafi su iyawa, ashe tun ɗazu ya ajiye cin tsiren naman don kada ya janye mishi hankali daga kansu har su samu damar yin wani abu ba tare daya gani ba, kyawawan idanuwanshi na akan faces ɗin su.
Danish bai ta6a bata mamaki ba irin na yau, ashe dama yana da wayau? Yake nuna kamar sakarai ne shi? yau dai ta shaida hakan, har tambayarshi ta yi meyasa bazai ci Abincin shi ba? ya ce mata kada ta damu, zai ci ne zuwa anjima.
tasa naci akan saiyaci, yace idan har tana so yaci, to ta dawo saitin inda yake zaune, don yaji daɗin ganinta da kyau, ba tare da ta yi mishi musu ba, ta miƙe tabar saitin Gabriel ta koma saitin inda ya ke ta zauna, Sai gashi ya sanya hannu yana ci yana kallonta, a haka har suka kammala Cin abincin, Giants suka tattara farantan kayan abincin suka bar ɗakin, fitarsu ke da wuya, Angel ta nufi toilet, Da sauri Danish yabi bayanta, tana shiga ya fado ciki, murmushi ta sakar mashi tare da cewa"My bodyguard, wankan zaka yi ne"? yace mata a'a, ita ya biyo tace mashi toh, su shiga dama tazo duba furenni ne taga awani hali suke ciki, ta kuma basu ruwa, Atare su ka shiga, da kanshi ya ɗabo mata ruwa a bucket yazo da shi gaban tukunyar fulawar, har yanzu dai furen batul Yana nan yadda yake, ya bushe Ganyan sun tsamure, suna a tsaye ta kalle shi tare da cewa"furen batul ya nuna alamun bata da ƙoshin lafiya, amma banji ka ce komai ba"? Ba tare da ya ɗago ya kalle ta ba, ya bata amsa da cewa"bani da masaniya akan yanayin ganyan jikin shi, zai iya yiwuwa ruwa furen ke buƙata" ya ƙarasa maganar tare da kwarara ruwan da ya ɗabo saman furennin, bayan ya kammala ya sauke bucket ɗin,
Kallon juna su ka yi ita da shi, ba tare da ƙyaftawar ido ba,
"Irin wannan kallo haka, me kake gani akan fuskata"? Tae tambayar tana dan harararshi,
Bai bata amsar maganarta ba, sai ce mata yai
"Pls angel, bana so in gan ki tare da yaron can, ni ban yarda da shi ba, kuma na lura kamar yana son shisshige miki ne......" dariyar da tayi ne ya sa shi dakatawa da yin maganar, sai da tayi mai isarta tukunna ta dai dai ta natsuwarta.
"Ka faɗi min dalili ɗaya da zaisa in janye jiki da shi, in banda abun ka ni menene alaƙa ta dashi? Ko ka ga wani abu ne"? Shaking head ɗinsa yai "just ni bai kwanta min araina ba" fuskarshi ayamutse ya bata amsa, ta6e baki ta ɗan yi, tana ƙoƙarin motsa lips ɗinta da niyar ta yi magana, ɗan juyi da zatayi keda wuya ta hango wani sabon tsiron fure kyakkyawan gaske a gefen na daddynta, waro ido waje tayi cike da mamaki, Ta zuƙunna gaban tunkunyar fulawar, a gefen ta Danish ya zuƙunna, launin ganyen furen pink colour, tsabar kyau kamar ka cinye, A ruɗe ta kalli Danish Alamar tana son ƙarin bayani game da sabon furen daya fito, girgiza makai yai alamar shima baisan ya akai ya futo ba, wani irin kallon rainin wayau tayi mashi tare da cewa"Ni dai ka faɗa min ran wanene akan sabon furen nan" shiru yai still idonshi akan fuskarta, sam baiso ta canza musu firar da su ke yi ba, Yaji haushin fitowar sabon furen da bai san Ran wa ke akanshi ba, saboda ya katse musu maganar da su ke yi.
"Magana fa nake maka, inaso nasan furen wanene wannan mai kyan gaske," motsa lips ɗinsa ya soma yi
"Angel, bansan na wanene ba, Amma tabbas mallakinsa, zai iya kasancewa wani ne daya maye gurbinki a wurin daddynki, ina nufin wanda daddynki yake matuƙar ƙauna kuma yake atare dashi" kallon harara angel ta jefa mashi,
"Lier, Ae daddyna baida madadina a duniyar nan, Ni ɗaya ce tak, babu wanda zai iya replacing ɗina acikin zuciyarshi, balle ma baya araye da har za'a samu wani ɗan shisshigi ya amshi matsayin da nake dashi awurinsa" murmushi ne ya bayyana akan fuskar Danish maganar da ta yi ba ƙaramin nishaɗi ta sanya shi ba,
Cigaba da magana tayi"daddyna da kanshi yace min ko aure zanyi bazan iya rabuwa dani ba, sai dai mijin ya dawo gidanmu ya zauna, ko kuma shi daddyna ya koma gidan shi da zama idan har yace bazai zauna a gidan mu," gaba ɗaya ta manta atare da wa take magana, surutu take ta zubawa kamar radio mai jini.
"shi kanshi daddyna yasan irin burin da nake dashi, Ni nan da kake gani Hamshaƙin mai kuɗi zan aura, wanda ya shahara a duniya, ko Jinin sarauta, Hatta aunty aneelerh tasan da wannan maganar, wai hada ce min banson talaka nace mata Annabi ma yace mu nemi tsari da talauci, atoh, wa zai kai kanshi inda zai sha wahala, ae wlh ƙwara inda zanyi rayuwar hutu, adinga take min baya......." shiru ta ɗanyi kamar mai tunanin wani abu, shi ko mutumin ya tsareta da ido yana jiran ta ƙarasa sambatun nata, don ya lura kamar bata acikin hayyacinta ne.
"Kurkukun ƙaddara Ya canza min rayuwata, na ɗauki darussa sosai na zaman duniya, a yanzu bani da wannan burin da nake dashi a lokacin da nake agidan daddyna, na faɗi maka ne kawai, ni da ma bani da tabbacin zanyi tsawaicin kwana" yanayin fuskar Danish ne ya sauya ganin ƙwalla sun tarar mata acikin idanuwanta,
"Burin da nake dashi A yanzu shi ne, In taimaki ƴan uwana mu fita daga cikin wannan Kurkukun ƙaddarar, Su yi rayuwar ƴanci kamar kowa, wlh Ni ban damu da in tsira ba, su kawai nake so su ku6uta, bayin Allah ina amfanin ma iyayen da zasu sadaukar da ya'yansu don neman wata biyan buƙata ta duniya, yanzu jibi Unaiza, mugun ubanta da ya ke yasan bayar da ita zaiyi shiyasa bai bata tarbiya ba"
sosai ta fashe da kuka, har cikin zuciyarshi ya ke jin kukan nata, hannu biyu ya sanya wurin janyota jikin shi ya ɗan kwanto da ita saman ƙirjin shi, yana lallashin ta.
*PRISONERS✍️*
Tun lokacin da Angel ta shiga toilet Danish yabi bayanta, Gabriel yae saurin miƙewa ya nufi saman table din dakinsu inda unaiza take ajiye backpack ɗinta, Sai da ya tabbatar babu mai kallon shi, dama already ya ɗauke musu hankalinsu, ta hanyar basu training ɗin rawar da za su yi, Sun dage sai tiƙar rawa suke yi atsakiyar ɗakin,
Zuge zip ɗin jakar yai, Jerin text books ne da jotter hada diary ɗinta, wanda ke ƙunshe da tarihin rayuwarta, biro ya ɗauko tare da jotter ɗin ya ɗaura saman table, bayan ya buɗeta a tsanake Ya soma rubutu cikin harshen turanci, kusan shafi ɗaya ya cika, ya yagi paper ɗin da yayi rubutu akanta, Ya maida jotter ɗin da biron cikin jakar, Ya zuge mata zip ɗinta.
Sai da ya ninke takardar, tukunna ya doshi gadon angel, Haris da deeja idonsu na akan Su parveen dake rawa, Haka zalika su naufal da mubeen duk hankalinsu akansu yake, Tsabar iyayi hada Majnun da Jamima cikin masu yin rawar uwa uba, Sarah, kamar macijiya sai karkarɗa ƙugu take yi, ita ala dole rawa take yi,
Ya rasa a ina zai ajiye mata takardar inda zata gani, fargabarshi kada ya ajiye inda Danish zai iya ganinta, don zai iya yage ta ne. A ƙarshe ya yanke shawarar tura mata ita Cikin rigar pillow, ɗaukar pillow ɗin yai ya zuge zip ɗin jikin shi, ya saƙa takardar aciki, " kafin ya ajiye mata shi, a hankali yake ja da baya, cike da saran Allah yasa Angel ta karanta saƙon nashi.
💌
Koma wa Gabriel yae saman bed dinsa ya zauna yana kallon masu yin rawa, yayin da acan cikin zuciyarshi tunanin yadda za'ae angel taga wasiƙar daya ajiye mata ya ke yi.
Jin ta yi tsit ta manne masa a saman chest ɗinsa, yasa shi ɗan leƙa fuskarta, ta lumshe idanuwanta tamkar mai yin bacci, cikin sanyin murya ya ambaci sunanta"Angel"! ba tare da ta buɗe eyes ɗin ta ba, ta amsa mashi "na'am" a hankali ya ɗago da hannun shi zuwa saman sumar kanta, buɗe idanuwanta ta yi jin saukar hannun shi asaman gashin kanta, tana kallon cikin idanuwanshi, hakanan taji gabanta ya ɗan faɗi, launin idon shi ba ƙaramin kyau ne da shi ba.
"Mu koma ɗaki, kada dare yai mana anan" yawu ta haɗiya kafin tace mashi"wankan fa? Haka zaka kwana ba tare da ka yi wanka ba, bazan ji daɗi ba gaskiya" tai maganar tare da ɗaure fuskarta.
"Zanyi, amma sai dai in kulle ki a cikin toilet ɗin nan, in shiga ɗayan idan na kammala zan buɗe ki, mu koma ɗaki a tare" da mamaki akan fuskarta ta ke kallon shi, jin wani ƙarfin hali, shi ala dole baya son ta nisanta da shi, kuma tasan duk akan Gabriel ya ke wannan kishin.
"Okay, I'll wait for you here. je ka yi wankan, idan ka kammala don't forget to come and open the door for me." ya amsa mata da toh, kamar kar ya raba jikin shi daga nata, haka yake ji, yana matuƙar ƙaunar kasancewa tare da Angel ɗinsa, ɗagowa da kanta ta yi daga saman ƙirjinsa, ya yunƙura ya miƙe ya fuce daga cikin toilet ɗin, tare da ja mata ƙopa ya rufe, ganin ya fita yasa ta miƙe ta nufi ƙopar don taji idan dagaske locking ɗinta yai, hannu tasa taja ƙopar taji ta adatse, Girgiza kai ta ɗan yi lamarin Danish ya fara tsoratar da ita, Ga shi yabar ta garƙame cikin toilet. A bakin ƙopar ta tsaya na tsawon 30 mins, tana tunanin ko awani hali Unaiza da Batool su ke a ciki, ta yi matuƙar damuwa da waɗannan bayin Allah.
Motsin buɗe ƙopa taji da sauri ta ɗan ja da baya, ya turo ƙopar, tun daga ƙasa ta soma kallon shi, dogon wandon shi ne baƙi na old uniform ɗin sa, bai sanya rigar shi ba, fatarshi har wani salƙi take yi saboda tsabar haske da kyau, cikin shi a ɗame ya ke, kamar ba a zuba abinci a cikin sa, jikin shi hada lemar ruwan wankan da ya yi.
Kallon kallon suka tsaya suna yi ma juna, ƙarasa shiga ciki yai tare da miƙa mata rigar hannun shi, aɗan rude ta kalli rigar, harara ta wurga mashi
"Me zan yi da ita"? Fuskarshi babu wasa yace"jikina zaki tsane min" ta6e baki ta ɗan yi, can kuma sai ta saki murmushi tunawa da Aunty aneelerh, da ta ta6a leƙen su a ɗaki, tana goge ma uncle uzair jikin shi da towel, lokacin ya fito daga wanka.
"Meyasa ki ke mirmishi"? Muryar shi ce ta katse mata tunanin nata, har lokacin bai janye rigar tashi da ya ke miƙo mata ba.
Maƙe mashi kafaɗa tai tare da cewa"ae babu kyau, bazan goge maka ba, sai mun yi aure" maimaita kalmar aure yai"what does that mean"? Jujjuya eye balls ɗinta ta yi, tare da sauke su kan fuskar shi tace"Zan faɗa maka amma ba yanzu ba, sai mun fita daga cikin kurkukun nan," ta ƙarasa maganar tare da fashewa da dariya, tabi ta gefen shi, ta fuce daga cikin toilet ɗin, bin bayanta da kallo yai har ta 6ace ma ganin shi, ta tafi tabar shi da aikin maimaita kalmar Aure, tunawa da Gabriel dake acikin ɗakin, yasa shi yin saurin bin bayanta.
Tana shiga ɗakin ta samu su azeeza zazzaune saman dining carpet ɗinsu kamar masu cin abinci, Alhalin nan kuwa fira suke yi a tsakanin su, gwanin ban sha'awa, Gabriel Na ganin ta yae saurin yunƙurawa zai miƙe daga zaunan da yake a gefen gadon shi, suna haɗa ido da ita, Sai ga Danish Ya faɗo ɗakin, da sauri Gabriel Ya koma ya zauna fuskarshi babu walwala, bai ta6a ganin ɗan takura irin Danish ba.
A bayan angel ya tsaya tare da yi mata magana"muje ki kwanta" ba tare da ta kalle shi ba tace"bacci a yanzu? A'a gaskiya, Ni sai dare yayi zan kwanta, Zanje wurin su hanna mu yi fira ne, " yace mata"Okey, my eyes on u," yana faɗin hakan ya nufi akwatin kayan su, ya buɗe ya ajiye rigarshi, ya ɗauko red vest ɗinsa ya zura ta a jikin shi.
Su hanna na ganin Angel, suka soma sakar mata murmushi suna faɗin Ga Masoyiya angel nan, Ku bata wuri ta zauna, mayar musu da martanin murmushin ta yi, taji daɗin sunan da suka kira ta dashi Masoyiya Angel.
A tsakankanin Jamima da azeeza ta zauna, tana fuskantar Hanna da parveen, kowannansu yai zaman cin tuwo kamar ɗaliban makaranta allo.
"Ku fada min akan me ku ke tattaunawa ne"? Tai tambayar tana kallon fuskar kowannan su,
Sarah ce ta fara magana"Labari su ke bamu akan abubuwan da ki ke koya musu, Lokacin da bamu nan" Parveen tace"Namanta ban faɗa maki ba, lokacin da ki na yin bacci kamar jiya ne, Gabriel ya tambaye mu, wai mu bashi labarin ki sannan mu faɗa mashi abubuwan da kika koya mana, kuma duk mun faɗa mashi" a tsanake ta ke sauraron su, yayin da idanuwanta ke a kan la66an masu yin maganar.
"Yau har training ɗin rawa ya bamu, duk mun gaji, shiyasa muka zauna muna ɗan zantawa" acewar Hannah.
"Pls Angel, ki koya mana abunda ki ka koya musu muna so" Jamimah ce tai maganar, Hibba tace"damuwa tasa kin daina koya mana karatu," numfasawa tayi kafin ta soma magana
"In sha Allah zamu cigaba da yin karatu, nima ban ji dadi ba, dana daina koya ma ku, yanzu dai kowa ya faɗi abunda yake so mu dinga yi, don mu sanya junan mu farin ciki"
Duk wani a bu da suke tattaunawa akan kunnan Danish, da ke a zaune saman gadon shi, nan ya zauna bayan ya sanya vest dinsa, idon shi akan la66an Angel da ke cikin yin magana tana kora masu parveen jawabi akan abubuwan da zasu dinga kullum.
Ko ƙyaftawa baiyi, Gabriel kam Idon shi na akan Danish, lamarin ya ɗaure mashi kai, ganin irin kallon ƙurullan da ya ke yi ma Angel, kamar zai lashe ta,
Firgit! ya yi jin saukar hannun mutun saman kafaɗar shi, da sauri yakai idonshi kan wanda ya ta6a shi, Haris ne ya zauna gefen shi.
"Da alama ka manta da ɗan uwan ka, na lura kwanakin nan hankalin ka gaba ɗaya yana akan Angel tun da ku ka shirya da ita, wai menene a tsakanin ku ne? Tell me ɗazu ma mu na kallon ku ni da Deeja, Angel ta shiga toilet ka bi bayanta, tsawon lokaci ba ku fito ba, sai daga bisani mu ka ga ta fito, kai ma ka biyo bayanta kamar ma wanka ka yi" tun da haris ya soma magana Danish Ya baza kunnuwanshi yana sauraron shi, sai dai har yanzu bai janye idanuwanshi daga kan fuskar Angel ba saboda tsabar jaraba.
Da mamaki akan fuskar Haris yace"kai magana fa nake maka? Ko kallo ban ishe ka ba kenan," motsi yae da la66ansa wurin furta mashi"Am all ears," haris yace"ae nasan kana ji, saboda ka maidani shashasha ina magana idon ka na akan Angel, wai me ka ke kallon akan fuskarta ne"? Yai tambayar yana leƙen fuskarshi, da buɗar bakin Danish sai cewa yai"kyau nake kallo, ko ba ka gani ba" sakin baki haris yai,"Dama kyau yana kallon kyau"? ɗaga mashi kai ya yi alamar Eh.
"Bari na tashi na baka wuri, ka gama kallon kyan, don na lura gaba ɗaya bata ni ka ke ba," kafin haris ya miƙe Danish yai saurin ruƙe hannun shi yace"Hankalina akan yake, idanuwana ne kawai basu atare da kai, amma ina sauraronka" Guntun toki haris yaja"dalla ni sakar min hannu na, ɗan rainin wayau," Ƙin sakin hannun nashi yai, ya damƙe shi acikin nashi, su naufal dake zaune saman beds ɗinsu, gaba ɗaya hankalinsu na akan Danish da haris, Mubeen yace"ku tashi muje wurin su mu ma muyi fira, tun da suma matan sun haɗa kansu" Kamar dama jira su ke yi yai maganar, kowannan su ya sauko daga saman nashi gadon su ka nufi Danish, gefe da gefen mattress ɗin suka zazzauna.
Javed yace"me kuke tattaunawa ne? Shi ne baza a kira mu ayi zantawar damu ba," Haris yace"kun ga alamun muna tattaunawa ne? tun da nazo na zauna gefen shi, bai juyo ya kalle ni ba, idanuwanshi na akan Angel, na rasa gane me yake kallo akan face ɗinta, ya dai ce min kyau yake kallo" dariya su ka saki gaba ɗayan su, naufal yace"abun mamaki, kyau na kallon kyau," Ba tare da Danish ya kawar da idanuwanshi daga kan fuskar Angel ba ya bashi amsa da cewa"ba abun mamaki ba ne, ni nasan me nake kallo" mubeen yace"ban yarda ba, sai dai wani abun na daban, idan kyau ka ke son kallo, ka ɗauki mirror ka kalli fuskarka mana," shiru bai tanka mashi ba, don ba ƙaramin takura shi su ka yi ba, Gabriel da ke zaune gefen gadon shi, a takure, yaso ace angel tana fuskantar inda yake ne don ya ji daɗin faɗa mata inda ya ajiye mata wasiƙar, sai dai ta juya mashi baya.
(Zan ƙara maku free pages Amma fa Sainaga like da comment, don haka indai kinason a ƙara kiyi liking, Masu so karanta middle Step book 2 whatsapp suyi min magana 08103884440 masu son facebook paid group Ga link ku danna shi za kaiku ga wadda zaku yi ma msgana👇
https://www.facebook.com/manal.muhd?mibextid=ZbWKwL