Cuta ta Ɗau Cuta Page 21 by Bilyn Abdull ce

Cuta ta Ɗau Cuta Page 21 by Bilyn Abdull ce

 *_Typing📲_*

   *_CUTA TA ƊAU CUTA_*

             _(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)

_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_

_Shafi na ashirin da ɗaya_

_INA MASOYAN ZAFAFA BIYAR?_

_KU MARMATSO KUSA...🔊_

  _ZAFAFA BIYAR 2024_

_ZAFAFA BIYAR!!!_

_ZAFAFA BIYAR!!_

_ZAFAFA BIYAR!!_


_SHIN YAN UWA KUNA DA LABARIN ZAFAFA BIYAR DINKU SUN SAKE ZUWAR MUKU DA WATA TAFIYAR LITTAFAN SU MASU MATUKAR MA'ANA DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA?_


_YA KE YAR UWA KADA KI BARI A BAKI LABARI... DOMIN DA A BAKI GWARA KI BAYAR...WAI AKACE ZUWA DA KAI YAFU AIKE_


 _GA SUNAYEN LITTATTAFAN WANNAN TAFIYAR... CIKE SUKE DA  ILIMIN DARUSSAN RAYUWA KI KOYA KUMA KI GYARA DA KAN KI..CIKI HARDA ZALLAR KAUNA TACACCIYA MARAR GAURAYE_


_________


         _1_

 *_AMEENATUH_*🧕💖: _MAMUH GEE_


           _2_

*_TSUTSAR NAMA (ITAMA NAMA CE)🐛👣_*_:BILYN ABDULL_


              _3_

*_GUDUN KADDARA🏃🐾_*:_SAFIYYAH HUGUMA_


        _4_

*_KWANKWASON JIMINA(MAI WUYAR SHAFAWA)🦩🦯_*_:NANA HAFSATU (MX)_



_GUDA DAYA:400_

_BIYU:700_

_UKU:900_

_HUDU: 1200_


_BANK NAME:KEYSTONE_


_BANK ACC NO:6019473875_


_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_


_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_


__

_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_


_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_


*09033181070*


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*



_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_



.......A yanda Maman Dafeeq ta shigo gidan babu ko sallama ya saka kowa zuba mata ido batare da sun tanka ba har yaran. Dan kowa ya santa tunda ba wannan bane zuwanta na farko tai tujara a gidan. Hasalima zuwan da tai a baya rashin mutunci ne ya zama sanadin da Baba ya samu kansa a hanlin da yake ciki yanzu. 

        Khadijah da ke zaune a ƙofar ɗaki cikin tagumi da damuwa taima kallon sama da ƙasa, sai kuma ta kwashe da dariya tana tafa hannaye da riƙe haɓa. “Oh ni jikar ta-rasulu kece ɗin dai ashe ba jita-jita ba. Barikin harta ƙwaɓe miki ne zuwa ajin ƙarshe na karatun natane ki ka dawo gida ko kuwa dai kinzo kawo musu abinda kika roro ne ki koma?”.

      Ba Khadijah ba, hatta ƴan uwanta a kiɗime suke kallon Maman Dafeeq ɗin, har Ni'ima ta buɗe baki da niyyar magana Khadijah ta rigata da faɗin, “Ban gane ba, ni Khadijah ce kuma a bariki? Na sojoji kona ƴan sanda?”.

          Wata dariyar rainin hankali Maman Dafeeq ta saki tamkar Khadijahn sa'arta ce tare da faɗin, “Oh halin naku zaki nuna kenan na matasan karuwai. Ai kin san wane bariki nake nufi. K yanzu bakiji kunyar kanki ba ƴar nan? Koda yake ma miye nawa, tunda ALLAH ya ƙwacemin ɗana da ga hannunki tun baku cika wata biyu ba. Da yanzu an kwaso ɗan dakan kuka an nana mana, dan da alama dama tun ana gida dai ake ƴan leƙe-leƙe ɗakunan samarin anguwa!”.

      Tunda Khadijah take a rayuwa ba'a taɓa faɗa mata kalmar data gigita rayuwarta ba kamar wannan. Zaram ta miƙe jikinta na ƙyarma. Ta bi mahaifiyarta da ƴan uwanta dake tsaye ƙiƙam babu mai alamar cewa komai sai ma zuba mata ido da sukai da kallo. Atake ta sake jin zuciyarta ta girgiza. Kenan kallon da suke mata ashe na wadda ta fito a yawan bariki suma kamar yanda mutane ke faɗa. (Ya arrahaman) ta faɗa tana mai girgiza kanta hawaye masu zafi na rige-rigen sakkowa saman kumatunta. Cikin sassarfa ta ƙarasa gaban maman Dafeeq da ke wani male baki da shan ƙamshi ita adole tayi tonon silili. Tsakkiyar idonta Khadijah ta kalla tare da nuna kanta. “Ni Khadijah ki ke ambata da sunan wadda ta fito a karuwanci? Ashe haka shi ɗan naki da yay sanadin komai yazo ya sanar muku? Naji zan ɗauka idan kince ni na jayeshi gareku kamar yanda kuke kallo bisa son zuciya, saboda ya zama hukunci a gareni nayin kuskuren bijirema iyayena nabi ɗan hau irin ɗanku saboda yaudararrun kalamansa gareni da ruɗanin wata abar banza wai ita soyayya. Sai dai ki sani idan ma ya ɓoye muku ne. Dafeeq ƙarya yake yi ni Khadijah shekararmu uku kenan tare da wasu watanni ba wata biyu daya sanar muku ba. Tun a satin da muka bar gida tare aka ɗaura mana aure a Adamawa. Bamu kuma taɓa rabuwa ba sai a satin daya shuɗe sakamakon jin da fahimtar shi ɗin wanene. To ashe ma halin nasa yasha ne gareki ban sani ba, a yanzu kam na daina mamakin halayensa dan madubinki ya sake haskamin ɗanki Dafeeq mayaudari daya zama sanadin rabuwa da iyayena ya dawo yana zuwa ku gareku, Dafeeq ɗin daya dinga zubamin ƙwaya batare da sani na ba ina ɓarin ciki, Dafeeq ɗin daya saka a asibiti aka sakamin abinda zai hanani sake ɗaukar ciki, Dafeeq ɗin daya auri sa'arki a yanzu saboda kuɗi.  To idan kina tunanin daga karuwancin na fito tare da ɗanki mukeyi a ƙarƙashin igiyar aure. ALLAH shine shaidata, wanda suka ɗaura mana auren suna nan a raye suma shaidane, gidan da muka rayu da maƙwafta da yan anguwar duk shaida ne. Wannan tabbunan dukan da kike gani a jikina naɗe da bandage badaga kowane lalataccen ɗan barikin da kike tunani bane face lalataccen tataccen ɗanki a dalilin jin gaskiyar shiɗin makiri ne azzalumine mayaudari, dan har a yanzu kuma akwai igiyar aurensa a kaina.....”

         “Har abada kin masa nisa. Ɗaya daya rage ma bai ƙarasaba ni da kaina zan kaisa inda zai tsinketa!!”. Muryar Baba ta daki kunnuwansu a bazata batare da sun san da shigowarsa gidan ba. Batare da ya jira cewar waninsu ko damuwa da kallon da Khadijah ke masa ba ya nuna Maman Dafeeq cikin tsantsar ɓacin rai. “A baya kin shigo wannan gidan kinci mutuncin mu son ranki, kin kuma dawowa a karo na biyu kika ƙara dai. Kin san miyasa a wancan lokutan bance da ke komai ba?” ya saki murmushin takaici, batare da ya jira ta sake cewa komai ba ya cigaba da faɗin, “Saboda darajar igiyar auren da ke tsakanin ɗanku da Khadijah. Saboda bana son nai shishshigi akan al'amarin UBANGIJI. Saboda bana son na sake maimaita kuskuren farko. Saboda ni ɗin UBA ne. Shi kumai UBA a duk inda yake mai haɗiyewa ne, domin ɗan kuka shike jama uwarsa jifa. Da'ace Khadijah ta kasance mai jin magana da tausayinmu matsayin iyayenta da tabi nasiha da shawarwari da faɗan da mukai mata akan ɗanku da k baki isa ko kallon Kamalu dake ɗa na ƙarshe gareni ki ci masa mutunci ba balle mu. Da ace sanda ɗanku ya fara zuwa nan ƙofar gidan na taka masa birki akan ahalina, da ke baki isa ko kallon bangon gidana ba balle dafawa da sunan shiga ciki. Amma duk na amshi ƙaddarar data zama jarabawar da bazan taɓa iya gogeta a cikin zuri'ata ba da hannu biyu, Alhamdullah kuma ina ji a jikina mun cinyeta, tunda gashi ta tafi da ƙafarta taje tai rayuwa a ƙarƙashin igiyar aure, da kuma dawo da ƙafarta batare da aikata abinda kuka jima kuna jifanta da shi ba. Dan haka kije ki sanarma shi ɗan naki da yazo ya ɓata sunanta bayan tana acan matsayin matarsa cewar ku shirya, ku shirya sammaci dan zamuje gaban alƙali ya ƙarasa cikasa saki ɗayan daya rage bai rubutaba akan wannan biyun daya rubuta anan”. Ya nuna mata takarda daya warware. 

     Cikin ɓacin rai da rawar jiki Maman Dafeeq ta ce, “Wlhy ƙarya ne, ku kun isa kuma yarona sharri, dan kuna son wanke ƴarku a wajen al'umma dan kar ace ta dawo daga yawan tazubar shine kuka kirƙiri takardar ƙaryarnan....”

       “Mu nan da kike gani munfi ƙarfin ma wani sharri balle ɗanki. Amma kije idan ma sharrin muke masa zai amsa a kotu. Na baki kuma minti biyu kibar min gida, in ba hakaba Ni'ima! Jamilah! Zuhrah! Kamal! Ku raka min ita da itace”.

      Ai tamkar dama wannan umarnin su Zuhrah dake faman cika da batsewa ke yi a cikin abinda bai gaza sakan uku ba kowa ya rarumi maɗaɗɗare dama duk abinda hannunsu ya kai sun raraki Maman Dafeeq da ta ɗauki abin wasa, dan harta buɗe baki zata fara zubama Baba tujara taga yaran sunyo kanta kamar an kama mayya a gidan yawa. Zo kuga gudu fiyyyy!! Fiyyyy!! Kamar kazar mayu dan dama haka take fingau-fingau babu wani ƙiba a jikin nata ko kaɗan. Har cikin anguwa suka bita atake aka ruɗe da ihu-ihu ana son hanasu amma ko'a jikinsu. Sai da ta faɗa wani gida ta banko murfin soron sannan mutane suka zagayesu ana basu haƙuri. Dan gaskiya abune da ba'a taɓa gani ba. Kowa a anguwar yasan su Ni'ima yarane kamilallu masu hankali da nutsuwa ga girmama mutane. Hatta ita kanta Khadijahn da ake kace nace a kanta yanzu kowa yasha mamaki lokacin da akace tabi Dafeeq sun gudu. Sai dai akoda yaushe mutum mai iya canjawa ne daga yanda aka sanshi, shiyyasa sanda yazo da batun sun rabu ta shiga duniya kuma mutane da yawa suka yarda, dawowarta a wani hali kuma ya sake saka zukatan mutane waswasi. Sai kuma a yau ga wani sabon zance ya fito dan tuni abinda ya faru a gidan Baban da kalaman Khadijah ga mahaifiyar Dafeeq dana baba har sun fara zagaye anguwar. Wasu ko dama akan kunnensu akai musamman ma maƙota.


     An lallaɓa su Ni'ima sun koma gida da ƙyar. In da suka tadda wasu a cikin dattawan anguwa zagaye da Baba a soro. A cikin gida Khadijah na durƙushe inda suka barta tana faman kuka. Ga Mamansu a gefe zaune itama tana nata hawayen ta juyama Khadijah dake magiyar su yafe mata baya.. Sun kai mintuna goma da shigowa gidan Baba ma ya shigo, kamar jira yana shigowa aka sake kwaɗa sallama. Komawa yay da baya ya sake fita, sai dai me yana fitowa yaci karo da ƴan sanda. Sun sanar masa cewar sunzo tafiya da shi ofishin su sakamakon ƙararsa da Maman Dafeeq takai wai ya saka yaransa su kasheta, sun kuma biyota da wuƙaƙe da iccina har cikin anguwa, da ƙyar mutane suka taimaketa. Murmushi kawai Baba yayi yace suje amma bari ya sanarma iyalinsa. Sun nuna basu amince ba, kawai ya bisu. Bai sake cewa komai ba ya bisun sai shigowa akai aka sanar dasu ai ƴan sanda sun wuce da Baba. A take hankalin kowa ya sake tashi a gidan, musamman Khadijah dake jin zuciyarta na barazanar bugawa ma......



____________★



           Tunda ya shiga bayin domin yin wanka da ruwan data haɗa masa zuciyarsa keta kai-kawo. Ya jima yana kallon ruwan da yay butsa da alamar akwai abinda aka saka a ciki, sai dai ƙamshin turaren dake tashi cikinsa zai saka kai tunanin turaren ne kawai. Lips ɗinsa ya ciza da ɗan ƙarfi, sai kuma yay murmushi da jan towel ya ɗaura ya fito a bayin. Dama a ɗakinta ta haɗa masa ruwan. Dan haka ya je ya sakama ƙofar key. Bincike ya shigayi a ɗakin tun daga cikin wadrobe ɗinta data cinye bango guda har zuwa ƙasan katifar gadon. Bai yarda yay wani motsin da zai iya jawo hankalinta ba, haka ma bai canja duk abinda ya ɗaga ba daga yanda yake. Itako tana can da tunanin ya gama wanka barci ya kwashesa kamar yanda malam ya faɗa zaiyi barcin kusan 1h kafin ya tashi, da ya tashi kuma komai zai iya faruwa. Idan a wannan step ɗin kuma ya tsallake da zaran yaci abinci yasha lemon data haɗa da magani shima shike nan rikici zai ɓalle tsakaninsu har takai su ga zuwa matsayin da take so. Abinda bai sani ba tun sanda yabar gida mai ɗaukar mata rahoto na biye da shi. Hakan yasa tasan duk motsinsa a kwanaki biyun nan da baya nan har zuwa kan tahowarsa gida. Ko abincin data shirya masa a table ba itace ta girka ba, sayowa akai da sauri, driks kam dama ta tanada a freight tun jiya, tana jin zai taho ta fiddoshi ta sake masa kwaskwarima, sannan itama ta gyara jikinta da turare da faudan malam da kwalli. Yanda taga kuma ya saukar da kansa sai take jin tarkonta na farko ya kamashi yanzu kuma ana kan na biyu tunda dai baya jimawa a wanka. Bazataje ɗakin ba saboda malam yace kar taje har sai shi da kansa yayi barcin ya tashi yazo inda take. Cike da nishaɗi ta buɗe ledar tsarabar daya shigo mata da shi batare da tunanin komai ba ta ciri shawarma ɗaya ta fara ci tare da buɗe kwalin yogout ta hau sha tana faman lumshe idanu da sakin murmushi. A ranta kam cewa take celebration ne take na cikar burinta. Tana kammalawa wani shegen barci ya fara rinjayar idanunta. Duk yanda taso hana kanta ta kasa saita ɗan kai kwance tana jan ƙaramin tsaki dan tasan barcin da bata sami tayi bane a kwanaki biyun nan saboda ƙulle-ƙullen da take akan Dafeeq ɗin, dama daurewa kawai take tun ɗazun, amma tunda yanzu ya riga yazo hannunta bari ta ɗan kwanta itama kafin ya kammala nasa barcin awa ɗayan. Wannan shine ya bama Dafeeq damar cin karensa babu babbaka batare da ita ya kawo komai a ranta ba game da dukiyarta yake hari. 

     Tsaf ya tattara duka takardun daya tabbatar masu amfani ne, tare da golds ɗinta tun daga kan sarƙa, yan kunne, warwaraye zuwa zobuna. Bayan ya kammala tsaff bayi ya koma, ya zubda ruwan data haɗa masa ya zuba wani yay wankan sannan ya fito a ɗakin, a hankali ya fara leƙa ƙasan benan, cikin mamaki ya hangota kwance a kujera kwalin yogurt da takardar shawarma yashe a ƙasa. “Ƙuda wajen ƙwaɗayi....” Ya faɗa yana ƙyalƙyalewa da dariya. Ƙasan ya sakko a cikin sanɗa, wayarta ya ɗauka ya koma saman dan ya riga da ya gama gane password ɗinta cikin hikima tun kan aurensu.........✍️




_INA MASOYAN ZAFAFA BIYAR?_


_KU MARMATSO KUSA...🔊_



  _ZAFAFA BIYAR 2024_


_ZAFAFA BIYAR!!!_

_ZAFAFA BIYAR!!_

_ZAFAFA BIYAR!!_


_SHIN YAN UWA KUNA DA LABARIN ZAFAFA BIYAR DINKU SUN SAKE ZUWAR MUKU DA WATA TAFIYAR LITTAFAN SU MASU MATUKAR MA'ANA DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA?_


_YA KE YAR UWA KADA KI BARI A BAKI LABARI... DOMIN DA A BAKI GWARA KI BAYAR...WAI AKACE ZUWA DA KAI YAFU AIKE_


 _GA SUNAYEN LITTATTAFAN WANNAN TAFIYAR... CIKE SUKE DA  ILIMIN DARUSSAN RAYUWA KI KOYA KUMA KI GYARA DA KAN KI..CIKI HARDA ZALLAR KAUNA TACACCIYA MARAR GAURAYE_


_________


         _1_

 *_AMEENATUH_*🧕💖: _MAMUH GEE_


           _2_

*_TSUTSAR NAMA (ITAMA NAMA CE)🐛👣_*_:BILYN ABDULL_


              _3_

*_GUDUN KADDARA🏃🐾_*:_SAFIYYAH HUGUMA_


        _4_

*_KWANKWASON JIMINA(MAI WUYAR SHAFAWA)🦩🦯_*_:NANA HAFSATU (MX)_



_GUDA DAYA:400_

_BIYU:700_

_UKU:900_

_HUDU: 1200_


_BANK NAME:KEYSTONE_


_BANK ACC NO:6019473875_


_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_


_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_


__

_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_


_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post