Jawaheer Page 3 Complete

Jawaheer Page 3 Complete

Page 3 Complete

 🍀☘️🍀☘️🍀☘️🍀


        JAWAHEERA


☘️🍀☘️🍀☘️🍀☘️🍀




Part 3



Littafin haɗaka

    

       Ne

Daga


NUSAIBA ALKAMAWA 09030567767✍️

       Da 

SAYYADA ummul Ummu abiha

................✍️


_______Washe gari kuwa jawaheer nafaɗawa ammie maganar zuwa gidansu jahan

Ammy tace "saikin dawo Amman karki kai dare"


"to ammy na saina dawo , Ammi tayi min addu'a.

"Fita nayi baba  audu yakaini har cikin gidan, parlour nashiga bakina dauke da sallama Amman  naji shuru, kiran jahan nayi awaya nace mata na iso, ina parlour.


"ganinan fitowa"cewan jahan.


Tana zuwa parlour taga Jawaheera

Azaune da murna ta tare ni, jawaheer ta tambayi jahan mamy da dady jahan tace dad yafita ita kuma mamy tatafi taro yaya jawad," Ohk to Allah yataimaka,  nafaɗa nan dai  muka shiga daki domin jawah besty ta ajjiye mayafinta aikuwa tana ajjiye mayafin muka nufi kitchen girki muka fara,mai rai da lpy munayi muna ɗan hira wanda duk yawanci ma jawaheera ce tafiyin aikin.



***** JAWAD****



_______Wani kyakkyawan saurayi na hango yana saukowa daga step din jirgi ganinshi nayi tamkar balarabe ammafa saurayin yahaɗu sai dai fuskar nan tashi amur tike take babu fara'a inka ganshi baxa kataɓa cewa yana  dariya ba,wajan wata kyakkyawar mata naga yanufa ya rungume ta yace   missing u mom. "missing u too my son matar ta fada murmushi dauke akan fuskarta tana shafa laulausan gashin kansa wanda yasha gyara sai kyalli yake ,waiwaye  naga yanayi daga baya yajuyo da kyakkyawar fuskarsa, cikin shagwaɓe fuska yace  mammy ina daddy da  jahan baby?mammy tace dadynku suna da meeting ne ita kuma jahan tana cen agida tana aika ce _aikace murmushi kawai yadanyi sannan yaja trolly dinshi.



___________Mota suka shiga  suka nufi gida bayan sun isa ,karar motar da jahan tajine wanda suna ɗaki suna hira bayan sun kammala lafiyayyan girki.


"hakan yasa tafito da dan gudunta tana zuwa ta rungume shi tace welcome my brother murmushi yayi yace har yau baki daina wannan shagwabar taki ba,turo baki tayi tace to ai yaya nayi missing din kafa" to naji Little sister.


"Shiga sukayi ciki yacewa mamy nifa sai naje na watsa ruwa tukunna,to tace masa shikuma yanufi dakin sa yarage kayan jikinshi  yashiga toilet 20 minute yadauka sannan yafito,dauko turarruka  yayi yafaffesa hardai yagama abinda yake sannan yafito yana fitowa yatarar da mamy azaune da jahan, zama yayi kusa da mamy,mamy tace har kahuta sai yace "eh" mamy,jahan tace ga abincin nan akan dining mikewa tayi tabude kulolin kular farko fried rice ce dauke da yankakken hanta saita biyun papper Chicken ne saita ukun sakwara da miyar kwai saita hudun taliya da miya saikuma lemuka kala hudu kowanne saida taxuba masa  Sannan taxubawa mamy ma sannan taja kujera taxauna .


"Mamy tace waini jahan ina jawaheer ne ? saurin mikewa tai tace la mamy namanta tana ɗaki mamy tace wato kam kinga yayanki kin manta da ita to ai saiki kirata tafito ko ?


"To Mamy jahan tafaɗa ɗakinta ta nufa kai tsaye tana bude kofa taganta akan gado ina chart ɗaka min duka tai tace shine kika tsaya bakixo muntari yayan dake ba to ai sai kitaso mamy tace kixo ,mikewa nayi batare da na kulata ba tayi parlour akan kujera one sitter tazauna cikin xaƙakkiyar muryarta tace mamy ina wuni lpy lau Jawaheer shine kikazouna adaki baki fito ba ita kuma Wannan me shirmen ta manta dake dayake taga yayan ta murmushi tai tace ai mamy babu komai kallon wajan dayake xaune nai nace ina wuni? banza yayi min yaci gaba dacin abincin sa kamar bayason ci,"mamy tace jawad anafa gaishe ka baka amsa ba , "lpy" yafada atakaice axuciyata nace lalle wannan dan girman kaine dan yasamu na gaishe sa ya wani amsa da kyar.


"Shikuma axuciyar shi  yarinyar batai masa ba  daga gani zatai rashin kunya gatadai da kyau ahaka.


"Yana gama cin abinci ya mike yazo yaxauna kusada mamy wanda tarigashi kammala cin abincin,jahan tace abincin yayi dadi? cikin Muryar shi mai daɗi yace mata yayi dadi mana sosai " tace ai bani kadai ce nayi girkin ba ni kawai ma tayata nayi muda jawaheer mukai itace ma karfin maiyin girkin."


" daure fuska yayi yace axuciyar shi dama nasani banfaɗi haka ba ammafa azahiri abincin yayi masa dadi dan rabonshi da cin abinci medadi haka tun mamy nayi da kanta bata sakarwa ƴan aiki ba a lokacin.


"kallon mamy yayi cikin shagwaɓa yace wai yaushe dady zaidawo wllh bansan lokacin dazai dawo ba ,murmushi yayi wanda ya kara masa kyau dai_dai lokacin da jawaheer tadago dara_ daran idanunta suka haɗa ido galla mata harara yayi tayi saurin sunkuyar dakai, mikewa tayi tace mamy


Nizan tafi jahan tace kai tun yanxu gaskiya kibari sai anjima, "murmushi tayi tace ammy tace karna dade mamy tace to ai kya tsaya kikarbi tsarabar ki jawad jeka dauko mata tsarabar ta zata tafine," to mamy mikewa yayi yace jahan xoki karbar mata ,jahan taturo baki tace to yaya tabika takarba mana wani kallo yayi mata dayasa tayi saurin tashi tabishi tsantsareren dakinsa suka nufa suna shiga yafada kan gado cike da gajiya, nunawa jahan akwatin kayayyakin yayi yace kibude kidaukar mata abinda yadace saura kuma kizaƙe, don yasan halinta sarai.


"Nufar akwatin tayi tabude kayan alawa tagani  aciki haɗe da chocolate sai kuma wani ring mai dan karan kyau sai sheƙi yake ,dauko mata tayi da kuma sweet da chocolate din tace yaya nagama to yace mata yacigaba da danna wayarshi fitowa tayi tasami mamy suna hira da jawaheer zama tayi akusa da jawaheer ,"besty yace ga tsarabar ki nan nasanki da son zaki mamy tace aikuwa dai kirage son xaƙi Yana da illa to mamy xanrage Bara natafi mamy Ngd sosai,"to kigaida gida da  mamanki xataji momy fita sukayi parking space sukaga ma har baba audu yazo sallama sukayi wa junansu har jahan tana cewa agaida yaya imran jawaheer tace anya jiya baku daidai ta junan kuba?


______Hararar wasa jahan tayi min tace banson iskanci nidai kawai nace kigaidashi to xaiji shikkenan?nandai nashiga mota .


"Ina isa gida na tarar da Ammi a parlour tare da abeed akan cinyarta  ,zama nayi  akusa da ammy nace washh wllh nagaji," ammy taɗan dungureni tace aikin me kikayi daza ki gaji kedai kirage shagwaɓa," turo baki gaba nayi nace ammy ga shagwaɓaɓen nan akusa dake nanuna abeed dake cinyar ammy SBD tsabar shagwaɓa harwani kwanciya yayi akan cinyar ki.


" kishi kikeyi dashi kenan?kuka abeed yafara yi cike da shagwaɓa ammy ta tambayeshi meyafaru yace ba ya jawah ce take cemin shagwaɓaɓe ba ,dariya jawaheera tayi tace gashinan yanxu ka karayin shagwaɓar ,"ammy tace kyaleta babana ita lokacin da take kamar ka tafika shagwaɓar ,"batarai nayi nace kai ammy ai saiki sa yarainani nafada ina turo ɗan bakina.


" ammy abinma dariya yabata saita kawar da xancen ta hanyar cewa yakika baro su "suna lpy? Eh tace agaidaki,to  ina amsawa tunawa nayi da tsarabar da jahan besty tabani  daukowa nayi nabude wani dan kareren zoɓe yayi kyau wani daka tsalle nayi nafaɗa kan Ammi hartana bige kan abeed nace ammy Kinga wani zoɓe maikyau da yayan besty yabani tsaraba kamar kuwa yasan ina son zobe.

" murmushi Ammy tayi tace zoben yayi kyau kuwa amman daganinshi xaiyi mugun tsada kuwa .


 sweet din nadauka nabawa abeed dayawa Sannan nabawa Ammi, Ammi tace bada itaba wannan kayan zaƙin.

Murmushi kawai nayi nace Ammi ina yaya imran ne ?yatafi gurin aiki ko kin manta ne ?la na sha'afa hmmmn kedai kika sani dariya nayi tashiga daki, nashiga toilet nawatsa ruwa sannan nafito mai nashafa tare da powder sannan nasaka abaya bakaramin kyau tayi ba  zoɓen nadauka nasaka wanda hannuna yasha jan kunshi gashi ɗan yatsun hannun zara_zara saiyakara haskaka min hannun ni kaita nasan nayi kyau , azuciyar ta cewa nake naji dadin xoɓen nan kai nifa banyarda ma shi yabani zoben ba yanxu hakama acikin tsarabarta tadauko tabani baisani ba don tafaranta min rai tsaki nayi nace wannan

Ɗan girman kanne zaibani zoɓen Ni mutumin ma  baimun ba haushi yake bani gashi dai da kyau tamkar balarabe don haryafi jahan kyau  duk da itama tana da kyau.


Kiran sallah magrib tashi nayi nashimfida sallaya daman nayi alwala dana shiga toilet na idarwa nayi addu'a nashafa.


" fitowa parlour nayi naga babu kowa zama nayi nafara danna wayar ta ina cikin haka ne saiga ya imran yashigo bakinshi dauke da sallama amsawa nayi ina murmushi nace kaga na jahan bada kanka asare.


Murmushi yayi man cike da son kanwar tashi  zama yayi akusa da ita "nace yaya ranar    tunda naga kana mata wani irin kallo na soyayya anan nagane kana ciki amma dai kundaidai ta da itako yaya?, 


"murmushi yayi yace tun lokacin na ƙarɓi number ta da haka harna  samu soyayyarta,"daman yanxu soyayya kuke yaya? sosaima Kuma ai gaskia kawar nantaki ta iya soyayya oh Shiyasa dazu tace min tana gaidaka ashe da wannan goro amiya,suna cikin wannan hirarne saiga ammi tazo taxauna tana maicewa mai ake tautaunawa ne?


 sai jawaheer   nace Ammy Wannan tsaka ninmu ne da yaya da kanwa sai ammy tace kwaji dashi dai intayi wari maji, mikewa yayi yana dariya yace Bara nashiga daki na watsa ruwa nahuta to yaya saika fito ahuta lpy.


Kiran sallah ishai mukaji tashi mukayi kowa yahuce dakinshi mukayi sallah tana idarwa nashiga kiran jahan besty bata daga ba  saidaga baya  kiran jahan  yashigo dagawa tayi dagacen bangaren tace hello jahan, kinje gida lpy yasu Ammi ?


"wllh naje gida lpy ammy kuma tana nan klau to kigaidata zataji Saida safe Allah yakaimu fitowa tayi taga ammy akan dining tana dinner zama nayi akusa da Ammy nace  shine baki jiraniba ai nasan xaki fito ne Shiyasa cewan ammy cigaban sukayi da cin abin cinsu.


"Bangaren Jawad yana kan gado yaji kiran wayarshi lalubo wayan yayi yakara akunne muryar abokin shi yaji shabbir dayake baiduba sunan mai kiran ba.

akasar dayayi karatu suka hadu da  shabbir yace ya abokina kaje gida lpy?jawad yace yanxu zaka min waya kace naje gida lpy don baka da mutunci.


" ayi hakuri  tuba nake ,mutuniyar takace ta kanainayeni da salon soyayyar ta itama yanxu tace tanayi maka bangajiya.


"kai ammanfa madam din nan sai ahankali kodayake ba laifinta bane hamago kawai kana nan mace najuya ka ,"dariya shabbir yayi yace nabaka lokaci mutumina

Lokacin da ƴa mace zata hanaka,sakat,tsaki jawad yayi yace Allah yasauwake kai nifa banga macen dazata burgeni ba har inxauna ina ɓata lokacina akanta shabbir yace abokina itafa rayuwa dole Saida mace ko kaki ko kaso dole wata rana saika shiga.


"cikin fushi yace kaga malam dakata karka batamin rai indai ta mata xakabi to baxa kayi komai ba," tuba nake bokan turai yanxu abar wannan maganar daman asiya tace takira wayanka akashe don Allah jawad kada kaiwa aseya haka wllh tana sonka dayawa niban san meyasa kake wulakanta ƴammata ba.


" tsaki yayi  yace Ni wllh wannan takura to dole saina daga wayar ta kaga nifa kadaina zuwarmin da xancen ƴammata dariya yayi yace to ranka yadade sallama sukayi yakashe wayar rufe idonshi yayi maixai gani Wannan fuskar yarinyar yake gani saurin bude idonshi yayi yace lalle wannan yarinyar duk lokacin da muka hadu saina koya mata hankali shifa kwata _kwata yarinyar batamai ba daga ni xatai rashin kunya daukar wayar shi yayi yakira jahan yake tambayarta dady yadawo tace masa yadawo kashe wayar yayi yacanxa shiga direct dakin dady  yanufa cike da kewar mahaifinsa da  sallama dauke abakishi.


"amsawa sukayi yaxauna akusa da dady, dady ina yini? lpy lau my son yagajiyar ai gajiya baxa tabarka kafito ba naxata ma kayi barci , murmushi Jawad yayi yace dady ai tuntuni nake tambayar mamy kai tacemin ai katafi meeting bansan dai karfe nawa kadawo ba shine fa saiyanxu natambayi jahan baby tacemin ai kadawo shine nace Bara naxo nakwashi gaisuwa.


",Dady cikin jin dadi yace Allah yayi maka albarka yabaka mata tagari yarabaka da sharrin mugayen abokai yatsare ka aduk inda kake murmushi yayi najin dadi adduar mahaifinsa suka amsa da amen gaba ɗayansu



Share it

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post