Kurman Baƙi Page 12

Kurman Baƙi Page 12

 *_KURMAN BAƘI_*⚫⚫⚫

*HUGUMA*

PAGE 12

            Hannu ga miqa mata zai karba key din,sai ta langabe kai tana dubansa qasa qasa


"Ranka ya dade yi zamanka kawai ka huta,yau ni zan tuqaka,nasan daka koma gida baka kai ga zama ba ka sake fitowa" shima nasa kan ya karyar


"Allah ya taimakeki ayi haka?" Girarta ta dage duka biyun


"Me zai hana?"


"Lallai na cika dan gata" ya fada yana murmushi.


              A nutse take tuqin yana daga gefanta,har cikin jikinsa yakejin bambancin komai da komai ma tsakaninta da zainab. Ya taba zama irin haka yace Zainab ta tuqasu,budar bakinta sai tace


"Tabdijan,kamar wata driver?,wannan ai aikinka ne" ta jefa masa key din,abinda ya jawo ya bata mata rai kenan shima. Yana da sauqin kai yana da daukar wasu abubuwan da yawan maza suke kallonshi a mazaunin raini,amma shi sam bai dauki hakan a bakin komai ba,saidai abu guda da baya iya dauka shine,ki kawo masa raini ko maganar banza ko ta rashin girmamawa gaban 'ya'yansa ko yaran da suke aiki qarqashinsa ko qannensa. 


                Dabi'un Zainab wasu irin dabi'u ne masu daure kai da ban mamaki. Ya jima yana mamakin halayenta,saboda shi ko kadan ba haka ya saba gani ba daga wajen ruqayya. Bazai iya cewa ga wata rana guda daya da ta gaya masa magana gatsau kwatankwacin ta Zainab ba. Tsahon shekarun da suka dauka da zainab din duk wani abu da ya kamata yayi don gyara bakinta yanayin mu'amala da tsaftarta yayi amma a banza. Sau tari hajiyarsa ke haqurqurtar dashi daga kawo wasu qorafe qorafen,a danneshi duk da sunan 'yaruwarsa ce yayi haquri.


              Bai taba kawowa auren zumunci da nasa illolin ba sai yanzu. Wasu lokutan yakan tambayi kansa da kansa. Shin wai me yasa yayi gaggawar qara aure?,da ya tashi qara auren kuma me yasa ya auri Zainab?. Duk sanda yayi wannan tunanin sai yayi istigfari,don ya tabbatar Rabon haneefa da khaleel dake jikinta nasa ne,kuma dole sai ta haifa masa Kota halin qaqa.


      Farkon aurensu ya dauka zata daina zata kuma gyara,amma zuwa yanzu ya riga yayi giving up,saidai bazai gaji ba bazai kuma daina saitata ba,hakanan bazai iya jurar wasu abubuwan nata ba.


             Hira sukeyi mai dadi da armashi tsakanin shi da ita da yaran. Irin hirar da yayi tsammanin daga sanda ya kawo zainab din gidan ta gushe a tsakaninsu,saidai a'ah hakan bata faru ba,duk da akwai abubuwa da yawa da har yanzun tunda ruqayyan ta ajesu a gefe tsakaninta da shi bata dawo dasu ba. Abubuwa ne masu yawa da yayi missing dinsu sosai,ya kuma saba da su,bai kuma taba zaton zata daina ba. Duk da bata cusguna masa ko hanashi qara aurensa ba,amma hakan sai yake ganin kamar wani horo tayi masa me kama da turin mutuwa,kuma har yau har gobe idan ya dauko zancan ta daina kaza bata taba bari suyi maganar da shi.


               A wani suya spot yace ta tsaida motar,ya buda murfin yana kallonta yana cewa


"Bari na siyo tashi watstsake" kunya ta kamata,saita kawar da kanta gefe tana murmushi. Hannu ya miqa ya mintsina gefen cinyarta kadan yadda ba zataji zafi ba yace


"Kin ajemin saqo ne ai,kuma saqon ya isa inda ya kamata yaje...."


"Please su alhassan fa" ta fada tana kare fuskarta da hanun nata,sai ya qara girgiza kai ya buda murfin motar yana ficewa.


              Waiwayawa tayi ta yiwa su alhassan daketa hayaniya maganar su rage hayaniyar tayi yawa,juyowar da zatayi kamar ance mata kalli gefenki. Kyakkyawan gani ta yiwa wasila zaune cikin farar motar dake daura da su. Tana zaune a gaban motar ta bada dukka attention dinta ga matashin saurayin dake zaune mazaunin driver shima yana dubanta. 


           Chiffon gown ce a jikinta sai yalolon mayafin da ya dace da material din,kanta ba hula ba dankwali kana iya ganin gaban gashinta.


               Wani malolon abune ya taso ya tokare mata wuya,duk yadda taso ta hana kanta fita amma hakan ya gagara,saita waiwayo ta kallo alhassan


"Kada ku fito ina zuwa" ta cire key din motar ta fita tana dosar motar.


              Daga baya baya ta tsaya tayi musu knocking,dukka su biyun suka leqo ita da saurayin,saidai kuma kamar yadda taso wasilar ce ta ganta sosai.


               Sosai fuskarta ta nuna mamakin ganin ruqayya da dan shock kadan,amma saita daure ta bude murfin motar ta fito


"Ya na ganki a nan?" Wasilan ta tambaya


"Ke za'a yiwa wannan tambayar ai wasila,umma tasan da fitowarki?" 


"A'ah don ba jimawa zanyi ba" haushi da takaici suka cika zuciyar ruqayya. Ranta idan yayi dubu ya baci


"Yanzu don girman Allah hakan mutunci da martabar ahalinmu kika siya mana ko sarayarwa kikayi?" Ta mata tambayar hannunta goye a qirjinta. Hannu wasilan ta yarfar tana dan buga qafa


"Kin cika matsala wallahi ruqayya,yanzun wani abun kikaga inayi?,kun hanani karbar waya na haqura,yanzu 'yar pizza da shawarma din ma da zan karba sai ace a'ah don me?"


"Idan yaa Bashir ya ganki kuma kice masa me?" Ta tambayeta tana ritsata da idanu


"Yayi miki fada kice an matsa miki ko?"


"yanxu yanzu zan koma,don ma sun jima wanda muka saka order din wajensa bai kawo ba da bazaki sameni a nan ba bare akai ga yaa bashir" kai ruqayya ta jinjina cikin zafin rai,dai dai sanda saurayin ya leqo yana cewa


"Baby zo mu wuce gashi an kawo" wani kallon bamza ruqayya ta watsa masa,sannan taja hannun wasila kai tsaye ba tare data tsaya saurarenta ba ta wuce mota da ita.


             Kaman qaramar yarinya ta bude mata seat din baya ta turata,itama ta koma mazauninta ta balbaleta da masifa. Tun wasilan na kare kanta har ta kasa cewa komai sai shuru da tayi tana bin ruqayyan da kallo


"A irin wannan abun kinsan 'yan mata nawa ne suka rasa budurcinsu?,kinsan yammata nawa aka yiwa ciki wasu suka haihu?,kinsan cewa daga zarar kin daga qafa kin shiga motar saurayi baki da guarantee akaran kanki dama abinda zai sameki?,kuma ko meye ya sameki ke kika rattaba hannu akan hakan"


"ki daina wannan batun mana haba,nace na daina"


"Kindai fada yanzu,kuma tabbas kinsan maso abinka ai ya fika dabara ko?" 


"Don Allah mana ruqayya" inda taga wasila na kalla ta maida hankalinta,sai taga saleem ke tahowa,alamu suna nuna batason yaji zancan


"Saina gaya masa ai kima daina wani boye boye"


"Ki rufan asiri karku cinyeni,ki barni na dan karbo pizza din mana na saka rai"


"Ko mayya ce ke saidai ki mutu" ruqayya ta fada tana tayar da motar kafin saleem ya qaraso ya bude ya shige.


            Baice komai ba sanda tace zasu aje wasila gida duk da yasan ba tare suka fito ba,mutum ne shi da ba akan komai yake magana ba musamman akan lamuran ruqayya,ya sani duk da dan adam ajizi ne amma komai tana yinsa ne bisa doron hankali da sanin abinda ya kamata.


               Sai da suka sauketa ta dauki tata ledar da saleem ya bata ta miqa wasilan taja motar suka wuce.


*_ZAINAB_*


            Tunda ta isa gida ta kasa zaune ta kasa tsaye saboda wani mugun kartawa da cikinta yakeyi. A iya tunaninta a gidan sunan yau duka bata ma wani ci cikakken abinci ba,saboda batason cikinta yayi cushewar da magungunanta zasu kasa samun matsugunni a cikinta.


               Duk da kartawar cikinta amma hakan bai hanata dage labule lokaci lokaci ba tana hangen gurbin da ruqayya kan aje motarta,har yanzu bata dawo ba,kuma yaran sun gaya mata ga abbansu can ya fita sanda suke shigowa gidan a tata motar.


             Koda ba ranar girkinta bane ta tsani taga saleem din sun fita da ruqayya,takanji zuciyarta kamar zata faso qirjinta. Tasha gwada su fita din itama dashi amma sai ya noqe ko ya kawo uzurin rashin kudin yanzun sai yace sai wani lokacin


"Amma inda ruqayya ce ba wanda zaiji bari ya gani,saidai mutum kawai yaga ka shigo yi masa sallama,kuma lokacin da nake waje ai baka taba kawomin uzuri ba idan na buqaci mu fita,sai yanzun da ka gama cin moriyar ganga ko?" A lokacin tashi yayi sosai yana dubanta. Harshenta kullum a tsaye yake carrr kamar wadda ak yiwa gorin harshe. Yana mamakin tarin rashin hankali irin na Zainab din,a lokacin da take maganar kudade masu yawa ya kashe a ranar ya gyaro mata wayarta data barwa yara suka jefata a ruwa,ko awanni biyu ba'a cika ba amma take wannan qorafin


"Itama duk sanda kikaga mun fita din cikin ribar business dinta ne,kinga baki da bakin yin qorafi,tunda dai tare na raba muku jarin nan,amma naki har yau bansan ina yake ba,bansan kuma taqamaimen abinda kikayi dashi ba" fuskarta ta bata sosai. Tayi mugu mugun tsanar ayi mata zancan ruqayya bare jarin da tamkar bakin wuta aka bata. Duk da tasan ina ta zuba kudin suka narke,amma baqincikinta yadda ta saka rai kudin zasu jawo ninkinsu amma sai abun ya tabarbare mata kudin yabi ruwa.


"Ni ina ruwana da wani business dinta?,nidai abinda na sani kawai cikin gidan nan sam ba'a kwata adalci ba,inda kasan ba zaka iya ba da barina kayi gaban iyayena baka nuna duk duniya babu yani ka tattagoni ka kawoni gidanka ka hadani da makirar matarka me shegiyar kissa da kisisina wadda babu Allah a ranta" daga wannan maganar ta miqe ta fice daga bedroom din nasa, ficewar da bata sake dawowa ba sai da safe.

   

            Ko kadan bai wani damu ba,bajewa yayi abinsa yayi kwanciyarsa. Don a ranar dama tuwo tayi musu,miyar ta cika daddawa har tayi baqi warinta yayi yawa. Da zanin data gama madaqalar tuwon dashi ta shigo masa bedroom,ba niyyar wanka bare brush. Tunda ya kwanta bai tashi ba sai da safe,kullum dai baya gajiya da mamakin yadda kishi ke rufe idanun zainab din ta gaza koyi da abinda zai amfaneta.


             Horn din motar da taji ya sanyata miqewa daga kujerar da ta tattakure,zanin atamfar jikinta ne tayi daurin qirji dashi sai dankwalin data daure kanta shima dashi. Ko kadan bata damu da kayan jikinta masu tsada bane,idan ta dawo unguwa ta nema masu sauqin ta saka ba, hakanan zata wayi gari dasu taci gaba da sabgoginta,ita da cire zanin har sai ita a karan kanta ta tabbatar yayi dauda yadda ya kamata.


"Umma ni bana hangowa" khalil da yabi ta qasan uwar ya fada yana tura kai jikin window din da zainab ta yaye labulen tana son ganin tare da waye ruqayya ta dawo?. Daidai sannan cikinta ya sake kartawa tasa hannu ya dafe amma duk da haka taqi gusawa daga wajen sai taga abinda takeson ganin.


*HUGUMA*👑

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post