Kurman Baƙi Page 19 by Huguma


Health College

Kurman Baƙi Page 19 by Huguma

 *_KURMAN BAƘI_*⚫⚫⚫

*HUGUMA*

PAGE 19

https://chat.whatsapp.com/KHGP5vnV6yg6X9CpkQcf39

*_Assalamualaikum warahmatullah_*

*_Kin dade kina neman gurin da zaki siya kaya amintattu masu quality cikin farashi me sauqi?_*

*_ina marabtarku zuwa cikin wannan gida tare da kasancewa da juna,WANNAN GIDANNA HUGUMA CLOSET NA BUDESHI NE SABODA NA BAKU DAMAR SIYAN KAYA MASU KYAU QUALITY DA KUMA SAUQIN KUDI CIKIN AMINCI DAGA GURINA,MASU SIYAN D'AI D'AI DA MASU SARI,NATION WIDE DELIVERY cikin aminci da izinin Allah,Kayan haihuwa na jarirai har zuwa girmansu,ina muna fatan alkhairi ni da ku gaba daya_*

____________________________



          Ta amsa ciki ciki tana maida hankalinta akan wayarta.


"Tambaya ce dani idan bazaki damu ba" 


"Inajinki" ta fada ba tare data sake kallonta ba


"Don Allah kiyimin taimako ki gayamin meye amfanin wannan dinkin da akayi miki bayan ba haihuwa kikayi ba?" Ta qarasa fada cikin d'ari d'ari tana dubanta.

  

            Wani kallon tara saura ta watsa mata,don itakam tunda ta zauna a gurin hamamin jikinta ya addabeta,batasan uwar da tasa ta kwaso jiki tazo zata dameta ba. Ta buda baki zatayi magana daya daga cikin qawayenta nurses suka shigo


"Jimmy,ya dai?,baquwa kikayi?" Maida kallonta kan nurse din tayi


"Ni bansan me yake damun mutane da shiga sha'anin da bai shafesu ba....."


"Wallahi ba haka bane,ina cikin kaidin kishiya ne,mafita nake nema don Allah ki taimaka ki gayamin" ta fada gabanta yana faduwa,kada taqi mata bayani wannan damar ta subuce mata.


"Malama me kikeso?" Nurse din ta fada cikin sakewar fuska



"Dinkin da aka yiwa qawarki nakeso ayimin bayani" murmushi ta saka suka hada ido da jimmy din,sai ta jawo kujera ta zauna tana fuskantar zainab


"Wannan dinki shine kankat a fannin matsi,babu wani magani da zaiyi miki abinda kikeso sama dashi,yanansake tsuke gaban mace ya maidata tamkar budurwa 'yar sha hudu" . Tuni jikin zainab ya dauki rawa,gaba daya hanakalinta ya daga,yanzun duk wayewarta a fannin matsi akwai wani abu da yayi saura wanda batasan da shi ba?,ashe duk wayewarta bata kai ba?,koda yake dai dama shi ilimi ance kogi ne.


"Don Allah malama ki taimakeni,nima inason ayimin,wallahi akwai matsala,na rasa hanyar da zan mallaki hankalin mijina,duk wani abu da mace zata yiwa namiji don ta mallakeshi ta hanyar shimfida nayi amma a banza,komai kyan magani nayi amfani da shi bana ganewa,idan kinga ya nuna jin dadinsa to sanda ya fita hayyacinsa ne bazai iya mallakar kansa ba wajen nunan jin dadin. Ni nafiso koda ba ranar girkina bane hankalinsa ya zamana yana tare dani,yana d'okin dawomin,wasu matan naga har satar kwana akeyi a kansu,amma ni koda wasa bai taba yi ba,tunda muka cinye amarci shikenan. Mijina ya auroni yana sona,ya auroni kuma don ya samu 'ya'ya dani,ni na fara haifa masa yara, amma bayan haihuwata ina yayewa saiga matsiyaciyar da ciki,wai data tashi haihuwa saiga twince,ina sake haife na biyu saiga wani cikij still ta sake haihuwa itama,wallahi malama asiri ne,ko cikin data samu aita hanyar tsubbu ne, mace batasan gyaran HQ dinta ba,batasan komai ba......kunsan Allah na fita hasken fata nesa da kusa ba,ita ko irin dan man nan da ake gogawa a murtsike baqi bata sawa jikinta,ko gashi ma wallahi gashinta baifi rabin nawa ba...." Tana cewa gashi jimmy data saki baki tana kallon yadda take zuba ratata kamar an kunna famfo ta maida kallonta ga sumartata. Baki ta tabe,ko ita da take mace tsantsami ta bata ta yaya zata burge namiji?,aba a qudundune?.


"Don Allah nurse ki gayan bakya tsuke guri baka damsasashi ta yaya miji zai soki?"


"A'ah babu fa zee baby" nurse ta fada tana qarewa zainab kallo a fakaice dariya da takaici suna kamata


"To kin gani.....yanzu yaushe za'a yimin dinkin?,kuma nawa ne?" Ido nurse din ta dan juya


"Eh to,ke zaki zabi watanni,dinkin kuma na musamman ne ai,a qalla zaki ajjiye dubu tamanin haka,don idan akayi miki kuma shikenan keda neman maganin matsi har abada,shi kansa oga idan ya kawo ziyara kullum inajin saikin taimaka masa zai samu gurbi" Duk da kudin da nurse din ta cika mata yayi yawan da bata dasu amma kuma amfanin dinkin take dubawa. Fuskarta ta yalwata sosai da fara'a


"To shikenan,yanzu dai bani da wannan kudin a hannuna,amma mai gidan zai tafi umra inajin nan da kwana goma ne ko sati biyu,yana tafiya da sati daya za'a yimin kafin nan na hada kudin,sannan ma zai kasance kafin ya dawo na warke,zansan yadda zanyi zan lissafa kwanakin yabar qasar nan cikin kwanakina,yadda idan ya dawo kwanana ne "


"To shikenan,ba laifi " nurse din ta fada. Godiya sosai zainab ta dinga kwarara mata,tana ji a jikinta lokaci yayi na maganin matsalarta. Wannan karon indai ta samu yadda takeso hatta saleem sai ta garashi yadda takeso,ba kullum zai samu ba,don ta tabbatar muddin yaji yadda ta sake komawa sai abinda hali yayi.


              Bayan zainab ta wuce bandaki duban nurse din jimmy tayi


"Amma dai talatu baki da imani,yanzu don Allah don Allah inake ina wani dinki bayan ke kanki kinsan ba'a nan akayi dinkinnan ba?,nazo ne kawai nan na warke saboda kawar da hankulan jama'a?" Gyara zamanta tayi tana dariya


"Allah ne kawai ya kawomin rabona har gida, karba zanyi na kankareta na dinke abinda ya samu"


"Amma dai da kin gaya mata gaskiya ina ganin da shi zaifi,taje ta fara gyara jikinta,baiiji irin samamin da take bugawa ba?" Dariya talatu ta kece da ita har sai data kama bakinta ta riqe gam bayan data tuna zainab din tana bandakin


"ke ni Allah yasa ma na iya bankadata,don wallahi wannan da alama can wajen ma ba sauqi,danqari!" Ta sake fada tana dariya.


                Tabe baki jimmy tayi tana gyara zamanta


"Kyaji dashi dai,ni mijinne ma nake ganin qoqarinsa da yake iya maaja din jikinsa da nata"


"Ke qazaman matannan ai jarababbun maza ne,yo ita ai na tabbatar miki ko abinci ya hanata ba lallai ta damu ba akan ya hanata abinsa,shan HARKA MEDICINE ai yafi musu komai muhimmanci koda sallah bata fiya samun lokacinsu haka ba" baki ta sake tabewa


"Lallai,irin wannan ba dole mu qadangarun bariki 'yan kwalta mu qwace musu maza ba,kiga mace kamar tsohuwar jaka a gidanta amma wai a haka take so ta mallaki miji?,wata macen ko ke bakya bata burgeki wallahi bare miji. Jikina talatu duk wata sai nayi masa gyara,gyaran fata kawai fa na dubu hamsin,a turarani,a qamsasa ni,to ta yaya maza ba zasu liqemin ba?,kazo nan kaji lumus,can qamshi can taushi,ka koma gida ka tarar da qamaya maya........Da anyi motsi mace take miki namiji bashi da adalci,namiji dan kunama ne,namiji bashi da mutunci,namiji batulu ne da sauransu,bayan ke kika siyawa kanki,habba.....muddin akwai mata irinsu zainab a duniya to kasuwar karuwai ba zata taba mutuwa ba" Dariya talatu ta saka


"Yo yanzu wannan kika jera da ita ai cewa za'a yi 'yar aikinki ce"


"Allah ya kiyaye,wallahi ko masu aikina basu isa su zauna da irin wannan qazantar ba" jimmy ta fada tana kyabe baki alamun mugun tsantsami ya kamata.


             Ranta fes ta koma gadonta,duk bayan mintuna biyu saita kalli jimmy ta sakar mata murmushi tare da yi mata sannu. Gaba daya jimmy ta gama tafiya da ita,jikinta ya bata tsabar yadda HQ dinta ke a gyare ne take juya gidanta, don da ganin kura taci mutum,yadda jimmy din keta wayoyi cikin isa da qasaita y tabbatar mata isassar macace ita a gidanta,kuma komai tace tanaso zataji nurse tayi sallama ta miqo tace inji wane,hakan kadai ya isheta amsa.


             Murmushi ya kubce mata,Allah ya nuna mata wannan ranar,ranar da saleem zai dawo tafin hannunta,dole ruqayya ta dandana kudarta yadda ya kamata.


                 Tare suka jero shi da ita cikin asibitin,yana riqe da kwandon kayan abincin tana a gefansa. Kallonta yayi kadan ta gefan ido


"Yane?,tunda muka shigo naga kinata faman toshe hanci?" Fuska ta yamutsa tana sake jan gyalenta zuwa hancinta


"Warin asibitinne baiyimin ba,sai shigarmin hanci yakeyi yana damuna" ta fada tana jin har cikinta yadda yake hautsina mata 'yan hanji.


"Sannu,ai ba jimawa zamuyi ba,nasan sallama likitan zaiyi"


"Ba komai" ta amsa masa tana sake toshe hancinta da kyau.


            Sallamarsu ita ta farkar da ita daga saqar da takeyi cikin mugun zare. Tare suka daga kai da jimmy kowa ya amsa sallamar gwargwadon muryarsa. 


            Fuska zainab din ta tsuke ganinsu tare,ranta ya raya mata ita ta riqeshi basu fito ba sai yanzu har qarfe goma. Qarasawa ruqayyan tayi ta jawo kujerar da hajiyayye ta tashi dazu a kai zuwa gaban gadon tana cewa da saleem


"Bismillah" kwandon ya ajjiye


"Kai haba,nifa namiji ne,zauna kedai"


"Muna gaisawa zan baku guri ai,ka zauna kafijin dadin dubata" 


"Dubiyar kukazo ko wasan kwaikwayo?,ko baqincikin daka saba cusan na jiya da ba'a cusan ba aka biyoni asibiti a cusamin" zainab ta fada tana hade fuska kaman zataci babu.


             Bai dubeta ba yaja kujerar ya zauna,ruqayya ta matsa gaba kadan tana cewa


"Sannu maman haneefa,ya jikin?,Allah ya mayar kaffara"


"Gani me tulin zunubi ba,dole ki kiramin kaffara ga bijirarriyar musulma" ta maida mata cikin zafi. Kullum sai taga wata sabuwar suturar a jikin ruqayya,kullum walau a cikin gida ko a waje ruqayyan cikin ado da sauya suttura take. Tayi ado duk da baby kwalliya ko kadan saman fuskarta amma adon dake jikinta zaka tsammaci bawai asibiti zataje ba


"Zunubi kam aikowanne bawa yana tattare dashi,saidai ka zama me neman yafiya wajen Allah" ruqayya ta maida mata tana takawa a hankali tana barin wajen don ji takeyi kamar amai zai taso mata 


"Idan baka zalunci bayinsa bafa" zainab din ta fada cikin son maida raddi


"Ya isa haka,likita ya shigo?"


"Eh ai bazai zauna jiran zuwanku ba,yace qarfe sha biyu zai sallameni idan likitan rana yazo" ta fada tana hade fuska.


"Sannu" ruqayya tace d jimmy sanda ta isa daura da ita zata zauna a kujerar da take a wajen.


"Yauwa sannu" jimmy ta amsa da fara'a sassanyan qamshin dake tashi jikin ruqayya na burgeta(qamshi fa yana jawo maka farinjini a wajen mutane tabbas,ku zama masu qamshi don Allah yan uwa mata😄). Haka kawai taji ruqayya ta burgeta,tuni kuma ta fahimci itace kishiyar da zainab ke qorafi akai


"Kayyasa,wutsiyar raqumi tayi nesa da qasa ai" ta fada can qasan ranta. Tazarace mabayyaniya me dimbin yawa tsakaninta da ruqayya. Ko a yanzun taga dabbanci da hauka a wajenta. Sun iso ruqayya na tattalinsa duk da tare suka kwana,ke anzo dubaki ba wani feleqe ba komai,jiya baki wanka ba me makon yau kafin su iso ko fece jikinki ko yaji dadin kallonki amma kin zauna kamar tsumammiyar jaka,sun iso da kayan abincin ba gaisuwa ba ya ka kwana ba sannu ba godiya kin buge da qorafi ke 'yar sakin zuciya,kamar ke kikafi kowa zuciya,BA KISSA BA SIYASAR ZAMA DA MIJI BA TSAFTA BA MAGANA ME DADI amma tsohuwar ballagazar dinki take buqata ayi mata, tabdijan!,Allah yasa ranar farko ya balle matsiyaci!. Jimmy ta raya a ranta dariya na balle mata har sai data toshe fuskarta da pillow.


             Tunda ruqayyan ta fidda wayarta take danne danne abinta,ko sashen da suke bata sake kalla ba bare taga abinda ranta zai baci. Yanayin basarwarta da kawaicinta ya sake burge jimmy qwarai,ta tabbatar da wata ballagazar ce itama da tuni tana gabansu ta kafa ta tsare,zainab zata yita yin abu da gayya ita kuma nata ran yana baci.


                A hankali ta dafe qirjinta saboda taso mata da amai yayi. Jimmy daketa aikin jarida tsakaninsu ta kula da haka,saita aje wayar hannunta


"Lafiya?" Dan murmushi ta sakar mata


"Lafiya ba komai,na gode"


"Kaman yunqurin amai naga kinayi,ga leda don kada yazo bagatatan ya bata jikinki" jimmy ta fada tana cire wata leda da aka siyo mata gasashen nama a ciki ta bata. 


              Qamshin Naman da ya daki hancinta ya sanya tasowar amai din gaba daya,tasoma kwarashi cikin ledar. Qarar aman ya jawo hanakalin saleem da Zainab,saleem din ya miqe da wani irin gaggawa ya isota yana tallafeta. Zainab na zaune ko motsawa batayi ba,wani abu ne kadai ke yawo mata cikin kai


"Ruqayya da amai?,tabbas amai na daya daga cikin manya manyan sign na samun cikinta,cikine da ita?,ciki fa!!" Ta fada cikin zuciyarta wani tashin hankali yana zarto mata tun daga tsakiyar kanta har zuwa yanzun qafafunta.

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post