Kurman Baƙi Page 5
Health College

Kurman Baƙi Page 5

kurman Baki

 *_KURMAN BAƘI_*⚫⚫⚫

*HUGUMA*

PAGE 05

           Ci gaba tayi da gunaguni,Kusan wannan dabi'arta ce,ta qware wajen mita da gunagunin mai da magana a ciki. Nata ta zuba daban,sai ruqayya ta saka hannu tayi bismillah ta dauki plate din ta soma zubawa tana fatar ta iya kai abincin cikin cikinta.


            Allah ya sani har cikin zuciyarta tana jin qyamar Zainab,saboda ita din macace da qazantarta bata boyuwa ko kadan. Mafi yawa duk farar mace qazantarta tafi saurin bayyana saboda hasken guraben boye datti da take dashi. Misali yatsu da faratanta zuwa duga dugi,zaka samesu a dafe ne ko yaushe,saboda bata damu data sanyawa qafarta lalle ba koda qanqani,hasalima duk sanda me lallen ruqayya tazo yi musu kallon sakarkaru takeyi su dukka,takan tabe baki tana juya kai da kafada,har cikin zuciyarta tana jin cewa ita dince mace cikakkiya. Kamar wata rana da tayi subutar baki bayan saleem ya gaza daure kyan lallen cikin dogayen yatsun ruqayya masu tsaho duk kuwa da cewa fatarta me dan duhu ce,amma sunyi ma yatsun nata kyau sosai,ya yaba irin yabawar da har zuciyarta taji dadin hakan,sai taji ko nawa ta kashe wajen yin lallen bata fadi ba


"Uhmmm,bonono,ana gyaran badini malam wa yake ta zahiri?,an bar qofar gari babu tsaro amma an tafi ana gyaran cikin birni" a nutse ta daga kai ta kalli Zainab. Sau tari tana yawan sake mata magana,saidai ita har zuciyarta tana jin cewa bata da lokacinta,muddin ta biye mata kenan hakan yana nufin ita da ita basu da banbanci kenan.


            Ba kasafai ta fiya sakin jiki ko hira da saleem ba duk ranar girkin Zainab din. Don a gurin Zainab hakan ma duka laifi ne. Banda tsaiwar ruqayya da baiwa banza ajiyar zainab din,hatta da kwalliyarta bataso saleem ya gani,bayan ita din koda kwalli da zai nuna anihin zatin kyan mace bai dameta ba.


            Wani irin zaman cin abinci suke mara armashi duk randa ya zamana ita ke da girki,ruqayya na tafiya bisa tsarin hakanne bawai don tana tsoron zainab ba,a'ah......tun asali ita din macace marason hayaniya da kuma tashin hankali,tana da wata irin nutsuwa da hankali wanda ke sake fusgar saleem a tare da ita. Hatta da shi din da ya zama miji a gareta shekaru kusan shida kenan,kusan komai nata da wani irin aji takeyinsa da zai nuna maka meye ainihin ma'anar sanin ciwon kai.


               K'ididdigaggun lomomi yayi yaji abincin yakai masa ko ina. Yasan dama za'a rina,a lokuttan irin wannan yafi ta'ammali da fruit masu yawa da kuma damammiyar fura. Ko a yanzun ma aje cokalin yayi


"Ina nonon da na aiko isma'il ya kawo?" ya fada yana zuba ruwa a cup


"Ba'a dama ba" bai damu ba don ya saba da hakan


"Dauko ki damamin inaso nasha" sai data cika bakinta da lomar abincin,kamar batasan meye dandanon dadi bisa harshenta ba sannan tace


"Kamar fa yara sun shanyeta dazun,sun iso daga makaranta suna jin yunwa aiki yasha kaina,ban ankara ba" ruwan ya dakata da sha yana dubanta. Ba sau daya ba sau biyu ba yasha yaja mata kunne kan irin wannan dabi'ar tata


"Sau nawa zan gaya miki ne zainab?,duk sanda yara sukayi amfani da abinda bace a ajjiyemin ki dinga daukan waya kina gayamin kafin na dawo gida na buqaci amfani dashi don na taho da wani?" Kai ta langabe tanason gwada kissar da taga sauran mata nayi,duk da can qasan zuciyarta fal take da haushi,komai fa ruqayya tana gani,kuma uwa uba a yadda take mace me jajircewa da gyaran kanta dukkan ire iren wadannan  tirjiyar bai kamata ta dinga fuskantarsu daga saleem din ba


"To gashi na musanya maka da zobo ko?,kayi haquri ka sha" ta fada tana miqa masa bayan ta zuba.


            Duk da ransa ya riga ya baci,amma ya sani abune mai bata rai qwarai mace tayi abu don saboda kai ka wofantar kaqi amfani da shi,don haka ya danne zuciyarsa ya amsa din.


              Sanda ya fara shi ji tayi kaman anyi mata bushara da aljanna,farincikinta ya gaza boyuwa har saman fuskarta


"Lallai da alama yau bazanyi asarar kudina ba" ta fada cikin zuciyarta tana jin wani dadi yana ratsata.


             Duk yadda tazo taci abicin ya gaza wuce mata saboda zallar rashin ma'anarsa,dole ta ajjiye ta dauki wayarta dake ajjiye gefe tana fadin


"Nidai zan wuce,sai da safenku" cup din ya dire ya miqe kaman yadda ya saba


"Muje na taka muku" maganar ta fusgi zainab, fargabar kada yaje ya jima wani abu ya faru ya sanyata miqewa


"Nikam dama kin tafi dasu haneefa wallahi" tayi maganar cikin son cusa wasi wasi a zuciyar ruqayyan


"Ba school ne gobe?,nakega bacci ya kamata su kwanta ko?" Saleem din ya fada yana duba agogon wayarsa. Ido ta kanne masa guda daya,ta matsa dab dashi sosai suna gogar juna


"Na maka tanadi ne dear,inason space" dan dauke kansa yayi gefe kadan ya kuma yi taku biyu baya kadan ya rabeta yana yin gaba idanunsa akan ruqayya wadda har tayi gaba abinta. Yana mamakin yadda gaba daya baki da jikinta baya cikin damuwar da zata zanya damuwarta a kanta,baisan dsga safe har zuwa dare me takeyi da zata gagara tsaiwa gyara jiki da bakinta ba


"Suyi kwanansu a nan din" ya gadi yana qarasa ficewa. Qwafa taja tana dauke kanta daga bakin qofar,bata karanci komai a fuskar ruqayya ba dangane da maganar ds tayi,taso qwarai taga adadin tasirin da maganar tayi mata,taso ta kwana da abun ya hanata bacci, gobe da safe kuma taga sauyin da zai qarasa gigitata.


              Zaune yake daga gefan gadonsa,calculator da wasu qananun takardu ne a hannunsa yana lissafin kasuwa. Sallama zainab tayi cikin doki tana shigowa dakin bayan ta kora su haneefa dakinsu.


               Kai ya daga ya kalleta yana amsa sallamar,bai qara koda second biyu ba ya ajjiye kan nashi yaci gaba da aikinsa. Gaba gadi taci gaba da takowa cikin dakin da daurin qirjin da ta sakeyi bayan ta cire rigar data maqala a dazun. Har ta gama abinda zatayi ta wuce gadon ta sheme bai motsa ba yana qarasa lissafinsa.


"Daddyn haneefa.....kai nake jira fa,ka ajjiye aikin ka tashi ka cire kayanka mu kwanta" ta fada tana daga kwancen. Kansa ya daga haushi da takaici yana taso masa,kamar wanda zasuyi aikin gini ko na kauda itace,tana magana gatsau ba wani salo me jan hankalin miji a ciki?. Idanunsa yakai kan qafafunta dake saman cotton bedsheet din nasa,wanda asali ruqayya ce ta siyesu har guda shida tace ga guda daya kyauta ta bashi,saidai kuma a duk sanda yake kwananta ne ire irensu take canza masa a bedroom dinsa dake sashenta.


             Ba komai a qafartata face baqi da datti kwance qasan tafin qafartata,ga kaushi da qananun faso da suka tsatsagata suka bawa datti muhallin zama me kyau. Daga saman singalalin qafarta kuwa shima kaushinne da fata kanyi sanadin busawar sanyi sanyi da kuma rashin bata muhimmanci wajen shafa mata mai akai akai.


             Da ya maida dubansa ga zanin jikinta kuwa,farin siririn layin dake qasan bakin kowacce atamfa dake dauke da sunan atamfar ya sirka laifinsa. Alamu dake nuna dattin atamfa da kuma neman agajin wanki da takeyi. Hannunta na ajjiye daga qugunta,fararen faratanta da babu digon Jan lalle ko baqi ko misqala zarratin na shimfide a jikinta. Sake gyara kwanciyarta tayi tana jin farinciki cikin ranta,kallon da yake mata sai zuciyarta ta fara qissimamata lallai maganin ke aiki a jikinsa. Eh zai iya cewa tunda ya zauna a gurin yakejin sauyin a jikinsa,saidai kuma a yanzun da yake kallonta ya rasa wani abu guda da zaiyi masa tasirin da zai shauqantu zuwa gareta. Tana murmushin haqoranta da suka komawa ruwan madara qarfi fa yaji suka bayyana,ta miqa hannunta tana sosai gashinta dake a cunkushe wanda yaci arziqi saboda zuwanta ta shafeshi da man gelo fes,abinda yasa yake fesar da wani qamshi mara dadi kenan


"Yanzu kin gama shirin bacci kenan?" Idanunta ta fiddo waje


"Eh mana,kai nake jira" ta fada tana murmushi dadi yana ratsata. Kansa ya mayar ga aikinsa yana jin buqata tana tasiri a jikinsa


"Ki shiga toilet dina kiyi wanka ki fidda zanin nan,ki bude wardrobe dina akwai wata rigar bacci black and white,ki dauki black din.


"Wanka kuma yanzu?,bayan tuni nayi wanka na?, gaskiya dare yayi" ta fada tana jin wata muguwar ganda da qyuya tana ratsata. Ita batasan me yake damun saleem ba,ya fiya zafafawa da yawa,shegen sanabe da tsafta kamar d'an kwad'i


"Umarni nake baki" ya fadi bayan ya dago idonsa ya zube a kanta.


              Batason tayi asarar kudinta shine babban dalilin da ya sanyata ta jawo jikinta ta sauko ba don taso ba. Ya bita da kallo yana girgiza kai. Wanka ma na shiga dakin miji sai ance da mace tayi,wacce irin rayuwa ce a wannan. A sassan ruqayya shi ake sanyawa yayi wankana,amma a nan sashen abun yasha banban.


              Ko minti hudu batayi ba sai gata ta fito daure da maqalallen zanin da ya rasa na meye,ta qarasa wardrobe din ta ciro rigunan kamar yadda yace,ta farke baqar tana dagata sannan ta dubeshi


"Daddyn haneefa,rigace wannan ko matacin koko?" 


"Shafa kiji" kawai yace mata saboda takaici,abinda yakeji cikin jikinsa zuwa yanzu ya fara haukata,sai ya fara tattare kayan aikin nasa yana zubawa a bedside drawer dinsa.


"Nifa wadan nan rigunan banga wani amfaninsu ba,banda asarar kudi,abu kamar sange(ragar net),da kudin aka baka ka qaro maganin harka da baifi ba wannan me zata tsinana maka,bakaci a bakinka ba ba baka matsa a qasanka ba sai kuma ace tana da amfani" ta fada cikin qunaquni. Qunaqunin da tsaf ya jita amma yayi banza da ita. Sai data gama qananun mitocinta sannan ta saka rigar. Rigar tayi sama abinta,saboda bata bada hankalinta wajen daidaitata a jikinta ba,gurin breast curves din yayi sama breast din kuma yana a qasanshi. Gwanace gurin shan magungunan mata,amma sai bata taba lura da cewa breast na daya daga cikin abinda ke tafiya da hankalin saleem din ba,itadai can qasan shine muhallin harinta ko da yaushe.


              Duk wani lungu da saqo dake isar da saqo a jikin mace yayi qoqarin ya aika saqo can,saidai da ya cusa kai ko harshensa wani qaqqarfan abu ke ingizoshi waje. Yayi wani irin rudewa da gigicewar da shi kansa ya dinga tuhumar kansa abinda ke faruwa,saboda a yadda yasan jikinsa yanayin da yake cikin ya wuce dabi'arsa. Duk sanda aka koroshin sai zuciyarsa ta tunasar dashi BA RUQAYYA BACE. dole daga qarshe ya haqura da nufin aika zafafan saqonnin ya koma kan hanyar da itama zainab din ta baje take jira ya isa ga gurin,a wajenta duk wadan nan abubuwan da yakeyi din bata lokaci ne kawai,tafi ganewa kai tsaye a shiga karatun.


               A yadda komai ke tafiya ya saka farinciki a zuciyarta ya kuma tabbatar mata da lallai yau din taci kudinta. Saidai a gefen saleem tun yana fahimtar abubuwan suna masa yadda yakeso har ya fara shiga wani yanayi na mamaki. Buqatuwarsa ta yau ta wuce ta kullum,abinda bai taba tsintar kansa a ciki ba muddin yana tare da Zainab dinne. Lokaci da qa'ida daya kamata ace komai ya lafa yazo qarshe sai ya kasa dakatawa. A hankali jikinsa ya fara weakening bugun zuciyarsa yayi mugun linkuwa,abinda ya haifar masa da haki da wani mahaukacin gumi.


              Bazai iya cewa ga yadda akayi ba,shi dai ya samu kansa da yin wani dummmm,kafin daga bisani yaji kamar jijiyoyin jikinsa basa aiki,ya sulale a hankali yayi kwance a gefe yana fidda numfashi.


              A qalla ya kusa mintuna goma a haka,sam bata lura ba tana daga kwance ta sheme tana sakin murmushi hadi da kada idanu,lallai yau akwai babbar kyauta da zata samu daga wajen saleem. Komai ya gudanar cikin wani irin zafi da kalar buqatuwar da takeso kullum ta ganshi a ciki.


              A hankali numfashinsa ya fara dai daita saidai yanzu kansa bai sauka daga nauyin da yayi masa ba,hakanan gangar jikinsa babu wata gaba dake da qarfi ko kadan.


            Miqewa yayi ya zauna yaja jikinsa da qyar ya wuce bandaki,da kallo ta bishi tana gyara kwanciyarta murmushi yana sake fita a fuskarta. Har ya fito tana kwance,ya goge jikinsa da towel ya sanya baqin gajeran wando da singlet ya dawo gefen gadon yana takawa a hankali ya zauna yana bata baya.


"Tashi" yace da ita. Wannan ba sabon abu bane,duk sanda mu'amala ta shiga tsakaninsu shike fama da ita akan ta tashi ta tsaftace jikinta,har yau har kwanan gobe kuma bata canza ba,koda alwala kadai sai yayi yaqi takeyi bare wanka da sai da safe ma wani zubin sannan ta rattaba sallarta ta kuma hau shirya yara zuwa makaranta,wannan ya zama silar da duk sanda wani abu ya shiga tsakaninsu sai yara sun makara a makaranta,koda su alhassan sun shirya da wuri kuwa,tunda tare driver yake kaisu. Wannan ya sanya tun hankalin ruqayya baikai ba har ta fahimci abinda ke jawo hakan,saidai koda wasa koda saleem din bata taba nuna masa tasan dalili ba har yau har gobe.


"Ni gaskiya bazan iya tashi ba,haba kaman ba kaga rashin imanin daka yimin ba yau,alwalar ma idan Allah ya kaimu asuba nayi" ta fada tana wani narkewa. 


"Me kika bani na sha zainab?" Ya jefa mata tambayar ba tare da ya waiwayo ba.


              Ido ta fidda waje hadi da tashi ta zauna ba tare data shirya ba


"Me kuwa zan baka daddyn haneefa,me ya faru?" Waiwayowa yayi yana dubanta da idanunsa da suka sauya launi saboda kansa da yakeji ya masa nauyi


"Yanayina ya canza,ba haka nake ba"


"Okay,inda a tattare da ruqayya ka samu hakan ba zakace komai ba,saini saboda ban cika macen da za'a ji haka tare da ita ba?"  Sai ta fashe masa da kuka. Can qasan ranta tasan tabbas ta kusa jawowa kanta matsala ne kawai,dose din maganin qwaya daya ne amma ta saka uku,kuma taji suna shaqiyanci a group din tare da gargadin masu wuce gona da iri din irinta  ko ita a yanzun bawai ta gama sauka bane,amm bataga ta bakin cewa komai ba gudun tabbatar masa da zarginsa.


            Zazzabi yakeji a jikinsa baya kuma buqatar wata doguwar hayaniya ko qorafi,don haka ya dauke kansa yaja jikinsa ya koma saman gadon yana rufa da blanket idanunsa a rufe yana ambatar ALLAH qasa qasa.

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post