Kurman Baƙi Page 9

Kurman Baƙi Page 9

 https://chat.whatsapp.com/EKyzZCUEGyRAEGGAnTHmGF

_KURMAN BAƘI_*⚫⚫⚫

*HUGUMA*

PAGE 09 

          Murmushin takaici ruqayya ta saki,gaba daya babu nutsuwa ga matar bare ka samu gamsuwar abinda take saidawa


"Kiyi haquri banacin bashi,ma hadu wani jiqon idon da rabo"


"Allah ya qara,mtsweew......banda rainin hankali na gama siyan kaya a wajenki saboda saiki tallatawa kishiyata,idan baki wasa ba billhuwallazi bazan qara siyan kaya a wajenki ba" zainab dake jibgawa basira harara ta fada. Ganin zatayi asara ba wan ba qanin saita tura dankwali gaban goshi

"A'ah me yayi zafi?,idan ma kin ajiye yo ba kanki kika yiwa ba,itama da bata siya ba kanta ta yiwa"


"Gwara data yiwa kan nata,indai itace zatayi miki cinikin maganin mata zaki daina cin abinci da kudin magani a duniya,banda taci kayan ganye taci nama da coca-cola batasan komai ba" Dariya muqarraban Zainab din suka saki. Sarai ruqayya taji,amma hankalinta yana kan fatima suna maganarsu.


"Ba yunwa kika ce kinaji ba amma zaki balle magunguna ki fara sha?" Raliya ta fada tana kama haba idanunta akan fuskar zainab


"Bana bori da sanyin jiki nifa,gobe nike da turaka gwara na watsa tun yanzu subi jikina,yunwa wannan ba matsalata bace,don bata hanani shan magani abuna" tana gama fadi ta fara tuttula na sha da dama sauran da suke na gari.


               Sallama aka sakeyi daga bakin qofar,na'ima ce wadda daya ce daga cikin family din nasu,kakanni suka hada dasu saleem,saidai ita babarta 'yar Maiduguri ce. Hannunta dauke da wata babbar jaka tayo sallamar,sallamartata kuma ta hade da qamshi wanda ya cika dakin lokaci guda.


"Nima ga hajata ayimin ciniki bayin Allah" ta fada tana dariya tare da kutso kai cikin dakin. 


"Hajiya zee,a zazzagen bakin jaka" ta fada tana murmushi idonta kan zainab wadda tayi tatul da maganinta tana jin tabbas gobe zata sake jarraba sa'arta. Ko da saleem baiyi appreciating nata ba tayi imanin da taimakonsu take zaune a gidan,kuma yana jin dadinta ne,wannan ya hanashi asirin farraqun da ruqayya keta qoqarin yi musu ya kasa kamashi


"Ai kinzo a makare hajiya niimatu,na cinye kudin jakata harda bashi ma a kaina" zainab ta fada tana basarwa,don batajin zata wani tsaya siyan turare bayan saleem ne yake siya musu,wanda yake siya dinma ita idan suka dameta kyautarsu takeyi,ko kuma idan tana da buqatar magani ayi ban gishiri na baka manda,ta bada su a bata magani hankalinta kwance


"Aikodai ban makara ba,shi turare da kike gani shine mace ai,bari na bude miki su ko baki shirya ba kikaji qamshinsu saikin siya"


"Allah fa ni bani siya,karma ki buden qamshinsu ya cikan ciki magani na gama sha yanxu" ta fada tana yamutsa fuska


"Wayyo Allah ya baki lafiya,ko an gamu ne?" Na'ima ta fada tana dariya


"In sha Allah kwanan nan za'a gamun dai" ta fadi tana dan washe fuska,don yanzu duniya kaf burinta shine ta samu cikin 'yan biyu maza kamar yadda ruqayya ta haifa,idan hakan ta kasance kuwa gida ya gama tabbata nata ne kaman yadda ta gama sakankacewa da hakan a baya.


               Ta danyi ciniki,wasu a dakin sundan sissiya,saidai ko kwatar wadanda suka siya maganin basu siyi turaren haka ba,wasu dai sun shanshana sun kuma yaba sun aje suna addu'ar Allah ya bada sa'a.


"A'ah, aunty ruqayya?" Na'ima dake shirin barin dakin ta fadi don sai a sannan ta ganta


"Hajiya na'ima inata miqo gaisuwa ai bakijini ba" ruqayyan ta fadi tana murmushi. Sauya akalarta tayi zuwa sashen da take zaune


"Wallahi hankalin yayi gaba" ta fadi tana zama gabanta.


"Bari kiga asararriya,duk gefen kama turaka babu ita,ta saki bishiya gaba daya ta kama ganye" zainab da dariya ke cinta ta fada tana tabo raliya.


"An fara DJ" wata muryar mace data leqo ta fadi,take kuwa kamar ana jansu da majayi suka fara miqewa suna fita da kadan kadan,sai gashi dakin ba kowa daga ruqayya sai fatima dake canza kaya sai na'ima da batulu dake ninke kayan da fatiman ke cirewa.


"Ga turare a siyawa yaaya saleem" na'ima ta fada tana murmushi. Murmushin itama ruqayya tayi


"Ai dole na siya turaren nan,tun kina shigowa naji yamin qamshi" sosai na'ima taji dadi, ruqayyan nada wani irin karamci da bata taba iya kushe abinka.


"Allah aunty?"


"Allah,wancan da kika bani kyauta yamin dadi sosai,yanzu ma nake son dama na tambaya ko kinzo?"


"Nazo anty ban shigo bane da wuri" na'ima ta fada tana fiddo mata da turarukan.


                Da gaske turarukan masu kyau ne sosai da tsananin qamshi,guda hudu manya ruqayya ta ware sai humra baqa da fara da kwalaccam sukayi total ta miqawa na'ima kudin. Tana ta qoqarin neman canji ruqayyan tace


"A'ah ki riqe ki siyawa mutuniyata najma biscuit"


"Har haka anty?,na gode sosai,Allah ya qara rufa asiri"


"Ameen ba komai" (don Allah mu rage qanqamo,kowa baya banbararki ke ba'a morarki,motsi kadan kice dangin miji basasonki,sun tsaneki saboda Allah ya miki rufin asiri,ko miji yana wadataki,ba dole su tsaneki ba babu ihsani tsakaninki da kowa?,kowa idan abinsa ya taso saiki kama hannu ki rungume,kice sai ya baki zaki basu bayan kina da wadatar da ba lallai saishi ya baki ba?,karku manta,kyautatawa tana saka d'a ya zama bawa ba tare da ya sani ba,kyauta da ihsani tana saka soyayyarka a zuciyar mutane,Allah yasa mu dace)".


"Ni anty wallahi banji dadin rashin siyan maganin nan ba,bakiga yadda su anty Zainab ke dariya ba da sukaga zaki siya turare"


"Au haba?" Ruqayya ta fada tana dariya sanda take zuba turarukanta a babbar ledar da na'ima ta bata


"Allah,dama sunata gulmar haka kike zaune sakaka,banda asirin ma da kikewa yaa saleem da tuni ya sakeki" 


"Hmmmm"batulu ta fadi kawai ba tare da tace komai ba,don itama abin yana bata takaici. Zainab ce 'yaruwarta,amma har ga Allah yadda takejin ruqayya a zuciyarta take kuma burgeta Zainab bata taba burgeta ba,tun zamanin 'yammatanci ma,saboda ko a sannn din Zainab din ta fiya rawar kai da zaqewa,ga shiga abinda shekarunta basu kai ace ta shiga din ba tun a lokacin.


"Ashe ni ban cika mace ba amma ban sani ba,indai sai na siya irin wadannan tarkacen lallai ko bazan taba amsa sunan mace ba,Allah yasa kuma bakwa kwasar ire irensu " ta fadi tana duban idanunsu.


                Girgiza kai batulu tayi da sauri


"Nikam bani da juriyar irin wannana abun ma,fruit kawai sun isheni"


"Kefa?" Ta fada tana duban fatima. Dariya tayi a kunyace


"To aunty mu duka duka yaushe muka shigo sabgar ma,haihuwar fari fa nayi yanzu"


"To duk ku zauna" ta fada tana gyara zaman babyn dake kan cinyarta.


               Basu musa ba kuwa suka zauna din kowa yana bata hankalinsa


"Fruit kadai basu wadatar dake ba batulu,haihuwarku uku,haka kema Fatima bazaiyiwu ki zauna haka ba,dukkanku don baku da kishiya ne shi yasa a yanzun ba zaku fahimci komai ba,saboda hankulanku a kwance suke,baku da maraba da mutumin dake dakin mamansa a kwance yana bacci" idanu suka zuba mata suna dubanta,sai ta saki murmushi tana gyada kai


"Eh,a baya nayi tunani irin naku,bayan auro zainab naci gaba da rayuwata daga abincina sai fruit,sai a hankali na fara karantar canji daga wajen saleem. Ban rasa tsafta iya girki haquri ladabi da biyayya ba,hakanan bai taba muzantani da ki cusgunamin da gangan ba,amma a aikace ina lure da rawar qafar da yakeyi akan zainab,sai daga baya na gane cewa tabbas dukkan mace tana buqatar gyara,amma gyara wanne iri?,ingantaccen gyara da bai wuce qa'ida ko hankali ba,gyaran da ko meye zataci tasan me taci,kome zata sha tasan me tasha,Allah ya sakawa anty deeja da alkhairi,bazan taba mantawa da ita ba cikin babin rayuwata,itace mutum ta farko data fara dorani akan hanya. Ta tunasar dani hatta iyaye da kakanni suna amfani da magungunan gargajiya gurin gyaran diya mace,kamar bagaruwa,ganyan magarya da sauransu. Inno kakata ta gayamin,yadda muke samun qaruwa(yagewa) yayin haihuwa haka suma suna samu,amma saidai su basusan wani dinki ba,ana gyara mace ta koma fes da bagaruwa da sabulun salo ta hanyar tsarki da shiga ruwan bagaruwan. Na baku misali mana" 


"Muna jinki" suka fada a tare saboda yadda bayaninta ya fara musu dadi da tasiri


"Zai yiwu ki siya mota ya zamana kullum kin hawa kina sabgoginki,ko engine generator kuna kunnashi kullum amma ba'a masa service?" Kai suka girgiza a tare alamun a'ah


"Idan hakan ya kasance wataran ba za'a wayi gari ya tashi a aiki ko yana aikin dai amma lallabawa kawai akeyi ba baya bada abinda akeso?"


"Tabbas" batulu ta fadi


"To kamar haka yake a wajen mace,kiyi gyara saffa saffa da ingantattun itatuwa da abubuwa natural,karki tsaya a gyaran qasanki,ko ina na jikin mace yana buqatar kulawa da gyara,saidai kuma komai da zakiyi gyaran dashi ki tabbatar ingantacce ne. Shi kansa engine din idan aka yawaita yi masa service din da juyen mai haka ba gaira ba dalili ba tare da alamu sun nuna yana buqatar hakan ba me zai faru?" Kai batulu ta jijjiga


"Gaskiya akwai matsala, za'a yita sakwarkwatashi ne ana raunata qarfinsa"


"Wani notin ma idan aka kwance ba lallai a iya mayar dashi wajensa a daure,shikenan sai ya fara rawa,sanadin hakan sai wani gurin ya kuma saki" fatima ta qara dorawa


"Yauwa,alhamdulillah,komai idan yayi yawa yana da illa ga jiki da lafiya,hatta natural ways din idan ka dauke 'ya'yan itatuwa da su basa yawa ga lafiya"


"Gaskiya ne" batulu ta fada


"Duk shan maganin matanki ko acan da ake hadawa saikin kiyaye wasu abubuwa sannan zasuyi tasiri,suma masu kyan ba daka ake shansu ba ai"


"Kamar me da me?" Fatima ta fada tana komawa ta zauna


"Yauwa,dole ki zama mai tsafta,babu ta yadda zaki tuttuli magani ki nemi kasancewa da me gida amma ko ina yakai hari sai a koroshi waje....." Bata qarasa ba suka sheqe da dariya su dukka biyun. D ido ta bisu tana son jin ba'asi,batulu ta yanke mata tunani


"Kamar dai zainabunki?"


"Banaso, ba'a gulmar 'yaruwata a gaba na"


"Ita tayi taki ai,har ta taya a zageki" batulu ta fada tana tabe baki cikin jin takaicin sakarkarun halayen zainab. Murmushi ruqayya tayi


"Taga zata iya ne" ta amsa a taqaice sannan ta dora


"Abu na gaba ba yadda zakisha maganin mata baki da lafazin baki,ladabi biyayya haquri da juriyar zaman aure wanda sune jigon zaman ba wai maganin ba,shan magani kawai yana armasa auratayya ne da hanata ta gunduri abokin zama"


"Gaskiya ne wannan,na yarda da haka" batulu ta fada tana jinjina kai


"Sai kuma babban abun,mata ne ku ba kunyarku zanji ba........shan maganinki bazai taba miki amfani ba ba tare da kin iya sarrafa me gidanki a turaka ba,dole ki koyi salo da dabarun kasancewa da me gida sannan tasirin maganin zai fara aiki a jikinki,wannan dole ne,ba kuma kiyita gyara kanki shi bakya gyarashi ba indai akwai fahimtar juna da sauqin kai a tattare da shi"


"Suma ana gyaransu kenan" fatima dake dan qunshe dariyar kunya ta fada


"Eh,sosai ma" ruqayya ta fada tana kallonta


"Kinga maggi?,kinga maggi?,yana bala'in taka muhimmiyar rawa wajen qarawa maza rauni,zaqi,maiqo,yawan yi musu ta'ammali da man gyada,shan sanyi,shan abubuwan da suke da sinadari caffeine da yawa a ciki,shan lemukan nan masu gas irin coca-cola da sauransu,ki yiwa miji natural drink kamar zobo,karkice zaki zuba tiara ko baby mix ko cola a ciki,ki dafashi natural da cocumber ginger cinnamon cardamom na'ana'a scent leave (daddoya) kanunfari da abarba,ki tace kisa masa sugar kadan yafi ki bashi wadan nan lemukan kaf dinsu,ku daina jibgawa mazanku magungunan qarfin maza,kashesu kawai kukeyi, za'a kai jallin da ba zasu iya tsinana komai ba muddin basusha wannan maganin ba,ke kanki idan kika ta'allaqa rayuwarki da shansu akwai matsala wataran zakiyi expire wallahi" dariya dukka ta basu,har itama suka saka ta dara(akwai hadin salad da na baku a last page,shima yana da matuqar muhimmanci wajen qarawa maza kuzari a turaka)


"Eh mana,sanda kike da buqata kiyi service kiyi,service me ma'ana da hankali,ko meye na gyara zaki iya siyan kayayyakin a ganyensu ko asassaqensu guda ki dafawa kanki,idan ba zaki iya ba ki karba a gurin wadda kike da tabbaci a kanta hundred percent. ammafa kome zakisha indai ba zaki dinga ci kina qoshi ba akwai matsala, ba'a son ki dinga zama da yunwa,ko a abincinki ya zamana babu wani abu da zai qareki a lafiyar jikinki".


"Amma matsi fa mata na sonshi Anty" murmushi ta kuma saki,mata da yawa sun halaka ta sanadiyyar matsi


"Akwai natural ways shima"


"A bamu anty" fatima ta fadi da sauri sai kuma kunya ta kamata.


"Zaki samu sassaqen bagaruwa,kanunfari,bagaruwa sai magarya,ki tafasasu ki dinga shiga ciki idan ruwan ya huce,kunga duk a ciki meye me cutarwa?,meye wanda baku sanshi ba?"


"Babu wallahi anty" fatima ta fada cikin gamsuwa


"To kun gani,ku damu kanku da sabulun tsarki,bayan babu sabulun da yakai sabulun salo indai kin samu original din"


"Gaskiya ne" batulu ta fadi


"Allah yasa mu dace" ruqayya ta fada tana miqa batulu babyn


"Zaki tashi muna qaruwa dake" murmushi ta saki


"Muna gaisawa da hajiya na shigo banko zauna ba,kuma inason na leqa gidan umma binta,zan jira shukra zata kawomin su iftee zasu wuce gida dasu"


"Anty kafin nayi arba'in zanzo gida na sameki don Allah a bani sauran sirrikan"


"Saikinzo fatiti,kawai dafe dafen nama kala kala da zakiyiwa kanki,a baki da dadi a jiki da aiki ba wani sauran fargabar meye a ciki" cike da murna tace

"Zanzo in sha Allah"

"Qafarki qafata" batulu ta fada tana dariya

"Duka sai kunzo" ruqayya ta fada tana murmushi.

              La'asar liqis ta baro gidan sunan tayi sallama dasu don ta qarasa gidan umma binta kamar yadda tace. Qanwace ga mahaifiyarta kuma a nan bayan layin gidansu fatiman take. Don haka cikin qasa da minti daya ma ta isa tunda a mota take.

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post