RAMIN HAKORI DA ABUBUWAN DA KE KAWOSHI


Health College

RAMIN HAKORI DA ABUBUWAN DA KE KAWOSHI

Da yawan mutane na fama da lalura ta ramin hakori musamman a irin wannan lokaci na sanyi.wani da zaran yaci wani abu mai sanyi ko zafi kokuma zaqi sai hakorin yafara ciwo wani kuwa haka Kawai.

  Ramin hakori, (Dental caries/Tooth decay), na faruwa ne da farko ta haɗuwar abubuwa kamar haka: 

1.Kwayoyin halittu(Bacteria): Kasancewar wasu kwayoyin cuta, kamar Streptococcus mutans, a cikin baki yana taimakawa wajen samuwar plaque akan hakora.

  wanda wadannan kwayoyin halittu Allah yayisu ne a baki,asali basa cutar da mutum(normal flora) amma da zaran mutum yaci abu me zaqi da zai iya makale masa a hakori, matuqar be wanke bakinshi ba yadau lokaci wadannan halittu zasuci daga wannan abun, Sanan su samar da wani acid (lactic acid) dayake da karfi wanda shike sabbaba ramin hakori.

2. Sukari (Refine carbohydrate):Cin abinci mai sikari da sitaci kamar bredi,biscuit ko minti DSS na samar da makamashi ga kwayoyin halittu, wanda ke samar da sinadarin acid da ke zubar da enamel din hakori. 

3.Rashin Tsaftar Baki:Rashin wanke baki musamman bayan cin Abu mai zaki, yana ƙara haɗarin kamuwa da ramin haƙori, akalla ko kurkura baki kayi bayan shan abu Mai zaki dan ragewa kanka hadarin kamuwa da shi

    Akwai bukatar wanke baki a kalla sau 2 a rana (kapin a kwanta bacci da bayan anyi breakfast) 

4.Abinci da Abin sha mai dauke da acid:Abubuwan sha da abinci mai acid da yawa kamar lemon tsami na iya raunana enamel hakori(ma'ana hakorin kanshi), yana sa haƙoran su zama masu saurin lalacewa.

5.Rashin samun wadataccen yawu a baki (Dry Mouth): Rage kwararar miyau zai iya haifar da bushewar baki, wanda ke hana aikin tsaftacewa da wanke hakwara da yawu keyi. 

 Cigaba na tafe a kashi na biyu

6.Gado (genetic): Wasu mutane na iya gadan yanayi (enamel)na hakwaran iyaye ko kakkanin su wanda wannan hakwara na iya zama marar karfi.hakan ka iya haifar da saurin kamuwa da ramin hakori in ba akula sosai ba.

7.Rashin sinadarin fluoride:fluoride yana taimakawa wurin karfin enamel (hakori) kuma ana iya samun wannan sinadari ckn a cikin man goge baki(toothpaste), ruwa, da wasu magungunan hakori.

8.Yanayi na rashin lpy: Wasu yanayi na kiwon lafiya, kamar reflux acid da rashin cin abinci, na iya ba da gudummawa wurin samuwar ramin hakori.

9.Shekaru: Yara kanana da tsofaffi na iya zama masu saurin kamuwa da ciwon  haƙori saboda wasu dalilai (a cikin yara) da canje-canje masu alaka da tsufa

 10.Rashin cin abinci me gina Jiki: Abincin da ba shi da mahimman abubuwan gina jiki na iya raunana hakora da kuma ƙara haɗarin kogo.

 Kula da tsaftar baki, rage shan sukari, da duba lafiyar hakora na yau da kullun suna da mahimmanci don hana aukuwar ramin haƙori.

    In sha Allah a rubutu na gaba zan tattauna akan hanyoyin magance ramin hakori.

  Allah ya karamana lafiya Amin.

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post