Typing📲
CUTA TA ƊAU CUTA
_(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
Shafi na arba'in
........*_YEARS LATER_*. Shekaru sun ja, rayuwa ta canja. Tuni jiya ta sauya daga yau zuwa goben wasu. Al'amarin tamkar mafarki ko labari suma sun zama iyaye. Wannan Abaan ɗin da kowa ya sani a matsayin matashi yanzu sunan dattijo yake amsawa. Hakama Khadijah ɗin nan ta zama babbar mace uwa mai ƴaƴa har huɗu jinin Abaan. Ɗiyarsu ta farko suna kiranta Mimi, wadda taci sunan mahaifiyar Abaan ne. Sai na biyu Muhammad. Na uku Abubakar Sadiq. Sai auta Umar Fharooq. Dukansu kamanni suke da Abaan, babu wanda ya ɗako Khadijah a kamanni sai dai jini shi baya ƙarya, duk wanda ya gansu dai yasan itace mahaifiyarsu.
Ƙarfe biyar da wasu mintuna zuƙeƙiyar mota ta shigo ƙaton harabar gidan. Driver na kammala parking a gaggauce ya fito domin buɗe mata. Hamshaƙiyar mace da hutu ya nuna kansa a jikinta ce ta fito cikin yanayin gajiya. Tana sanye cikin shiga ta alfarma. Dan wani lass ne mai masifar ƙyau da ɗaukar idanu a jikin nata. Sai farar riga ta likitoci ƙal dake tabbatar da ita ɗin wacece. Sannu direban ya shiga jera mata ganin yanda take ta faman yamutsa fuska alamar a gajiye take. Ta sakar masa murmushin nan nata mai sanyi batare da tace komai ba. Kafin ta raɓashi ta wuce zuwa cikin gidan. Tarkacenta dake a mota shima ya tattaro ya biyota.
A kusan tare ƙyawawan samarin yaran dake a falon kowa na harkar gabansa suka ɗago. Sai kuma duk suka miƙe suka nufota kowa na faɗin oyoyo Ammie. Hannayen ta ta buɗe musu duk suka shige abinsu. Jikin nata suka bari kowa na jera mata sannu da nuna tausayawa. Itako na faman musu murmushi. Babban da zai iya kaiwa shekara goma sha biyar ne ya kama hannunta har tsakkiyar falon ya zaunar. Sai kuma ya duƙa gabanta yana mai kama ƙafarta ya zare takalmanta ya na danna mata ƙafafun da sukai ɗan fushi. Da sauri autanta da zai iya kai shekara goma shi kuma ya iso gabanta da ruwa yana faɗin, “Ammie tun ɗazu na fito miki da shi a freight ya huce dan kar kisha mai sanyi kiyi mura.”
Fuskarta da murmushi ta furta, “Oh my AUTA ALLAH yay muku albarka. Yanda kuke ji dani ALLAH ya baku mata da zasu ji daku kuma da ƴaƴa”..
A tare suka amsa da Amin cikin ɗoki harda na tsakkiyar da zai iya kai shekaru sha uku. Shi kuma kayanta dake hannun driver ya amso.
“Daddy fa?”.
Ta faɗa tana kallon babban. Sauran ƴan uwansa ya kalla sai kuma ya kwashe da dariya. Harararsa Khadijah tayi da faɗin, “Miye abin dariyar?”.
AUTA ne ya matsar da bakinsa saitin kunnenta. Cikin raɗa ya ce, “Ammie ya ɓuya a sama ne. Wai idan kin dawo muce bai dawo ba. Kuma ya kashe phones nashi sai kin ruɗe sosai zai sakko. Ammafa kar kice ni na faɗa”.
Murmushi Khadijah tayi mai sanyi tana girgiza kanta. Sai kuma ta miƙe tana kallonsu da kulawa. “Shike nan bari naje na watsa ruwa. A haɗamin shayi kar a saka suga. Ina Mimi?”.
Shiru yaran sukai saboda tambayar ƙarshe. Sai kuma babban ya ja numfashi muryarsa da alamun ɓacin rai ya ce, “Ammie ta fita. Kuma da alama wannan shegen yaron ne yay kiranta. Ta ƙofar baya ta fita batare da tasan na ganta ba. Naso binta sai nai tunanin kar Daddy ya ji”.
Shiru Khadijah tai tana kallon yaron nata. Sai dai gaba ɗaya fara'ar dake saman fuskarta ta gushe. Wani kalar bugawa zuciyarta keyi da sauri-sauri. Dan al'amarin yarinyar tata ya fara caja mata ƙwaƙwalwa. Ɗakinta ta nufa, sai kuma ta fasa ta nufi upstairs. Da kallo samarin yaran nata duk suka bita fuskokinsu cike da damuwa. Dan sun san al'amarin yayar tasu shine abu mafi zama damuwa ga mahaifiyar tasu a kwanakin nan...
Tun kam ta ƙarasa hawo steps ɗin ƙamshinta ya gama cika masa hancinsa. A hankali ya ɗago daga abinda yake ya zuba ma hanyar fararen idanunsa dake cikin glasses fari tass da alama na ƙara gani ne. Saurin ture laptop ɗin saman cinyarsa yay yana mai riƙota ganin yanda take tafiya kamar zata faɗi. Muryarsa na rawa alamar ruɗewa ya ce, “Boddo am mike faruwa? Yau ma daga asibitin ne? Ko kuwa n.....”
Da sauri ta girgiza masa kai hawayen da take ta son riƙewa na gangaro mata. Sai kuma ta faɗa jikinsa tana mai ƙanƙamesa da sakin kuka mai ƙarfi. Sake rikicewa Abaan yayi. Dan babban abinda ya tsana a rayuwarsa shine ganin matar tasa cikin ɓacin rai ko damuwa. Yana ƙaunar baiwar ALLAHr nan. Ƙauna irin wadda baisan yaya zai misaltata ba ga mai saurarensa. Domin ta gama masa komai. Ta riƙesa amana. Ta ƙautata ma mahaifiyarsa a lokacin da take jiyya har ALLAH yay mata rasuwa. Ta haifa masa yara har guda huɗu. Ta tsaya tayi karatu kamar yanda yay fata ta zama babbar likita saboda shi yana son hakan. Ta bama yaransa tarbiyyar da suka zama abin sha'awa a wajen duk wanda ya sanshi dama wanda bai sanshi ba. Tayi hakuri da abubuwa masu yawa domin shi.....
“Hamma har abada bazan daina nadama ba. Bazan daina takaicin kaina ba akan bijirema iyayena. Duk da sun yafe min kafin su bar duniya hakan bai hana tarihi neman maimaita kansa ba. Ashe da gaske ne duk abinda ka aikata ga iyayenka kaima sai ƴaƴanka sun aikata gareka....”
“Haba Boddo am miyasa kike irin wannan maganar ne. Abinda ya faru ya riga ya wuce ai. Baba da bakinsa ya sake maimaita ya yafe miki a randa zai bar duniya. Hakama Mama bata gushe ba sai da ta sake nanata yafiya a gareki tare da sanya miki albarka ke da zuri'armu. Miyasa zaki faɗi haka?”.
“Dolene na faɗa Hamma. Domin kuwa Mimi data kasance ya ɗaya mace tilo a garemu. Ta kuma farko da muka fara gani a duniya ta fara ɗakko irin wacan hanyar da nabi da har yau ban daina nadamar binta ba. Na ɓoye maka ne da tunanin zan iya control ɗinta. Sai dai ba hakan bane. Sati uku kenan Sadiq ya sanar min duk sanda driver ya kaisu school ya ajiye sai ta koma ta fita. Hankalina yay masifar tashi da jin zancensa. Amma sai bance da shi komai ba washe gari na kaisu school ɗin da kaina. Bayan na ajiyesu sai na samu wani waje na ɓuya. Ban rufa mintinan biyar ba sai gata ta fito. Da ƙyar na iya riƙe kaina saboda hajijiya data nema ɗibata ganin wani saurayi da bai wuce shekara ashirin ba ta nufa. A mota ya ɗauke ta suka bar makarantar, hakan yasa na bisu da sauri ta yanda bazasu gane ba har zuwa wani sabon garden da Fharooq keta maka nacin muje ɗin nan. Na ɗanji nutsuwa ganin ba wani wajen ashsha suka nufa ba. Haka na ɓata lokaci a wajen har awa kusan uku suna tare kafin ya ɗauketa su koma. Makarantar ya sake maidata ta shiga shi kuma ya tafi. Ranar nayi kuka, na kira Ni'ima na sanar mata ita da aunty Noor. Shine suka bani shawarar kar nai mata magana kaima haka na cigaba da bibiyarya na sati guda. Haka nabi shawarar tasu har sati ɗayan kullum ina zuwa school ɗin nasu batare da ta sani ba kaima haka. Kuma kullum sai sun fitan sai dai garden ɗin nan dai yake kaita suje suyi zaman awa uku ya maidata. Ranar da sati ya cika Aunty Noor taje ta ritsasu a garden ɗin. Tun a can ta faffalesu da maruka su duka ita da yaron sannan ta ɗaukesu zuwa gidanta. Nasiha tai musu sosai bayan ta tambayi yaron ya sanar mata yana lavel 100 ne a jami'a baima cika wata hudu da farawa ba. Bayan ta musu nasiha da faɗa sosai muka cigaba da bibiyarsu. Sai naga ya daina zuwa ɗaukarta akaf satin can daya gabata. Ganin haka yasa na saki jiki nabar bibiyarsu saboda ayyuka sun min yawa ma a asibiti a satin nan gaba ɗaya. Hamma ashe yaran nan basuji faɗa da nasihar Aunty Noor ba. Yanzu na shigo gida shine yaran nan ke sanar min tana ganin ka hawo sama ta fita ta kofar baya. Muhammad ya kuma tabbatar min yaron nan ne yay kiranta. Hamma duka shekarar Mimi nawa ne? Hamma wlhy ji nake kamar zuciyata zata fashe.....”
“No Please calm down Baɗɗo am.” ya faɗa cikin jarumtar danne nashi tashin hankalin tare da saka mata ruwa a baki. Da ƙyar ta iya shan makwarwa biyu. Ya rungumeta a jikinsa yana shafa bayanta batare da yace komai ba. Sun ja tsahon lokaci a haka kafin ya miƙe da ita zuwa ɗakinsa. Shine ya taimaka mata ta cire kayanta ya jata zuwa bathroom. Sun ɗan jima a ciki kafin su fito. Da alama wanka ya taimaka mata tayi, kasancewar tana da kaya a ɗakin ya taimaka mata ta shirya. Shayin da tace Muhammad ya haɗa mata da kansa yaje ya amso yazo ya bata tasha. Sannan cikin lallashi yace mata tai salla shima zasu je massalaci. Kanta kawai ta iya ɗaga masa. Shi kuma ya sakar mata murmushi tare da sumbatar goshinta sannan ya fito.
Ya iske su Muhammad duk sunyi alwala shi suke jira. Baice da su komai ba ya shiga ɗakin Mimi da ke kusa dana Khadijah. Babu kowa alamar bata dawo gidan ba. Baice komai ba ya maida ya rufe. Inda samarin yaransa suke ya dawo. Ya kama hannun Auta su Muhammad biye da su zuwa masallaci.
Ana idar da salla ya fito a massalacin. Duk da kuwa hakan ba ɗabi'arsa bace dan sai yayi isha'i yake fitowa. Gaban gate ɗin gidansa ya dawo. Da sauri maigadi ya kawo masa kujera daya buƙata. Bayan ya zauna wayarsa ya fiddo ya shiga traicing layin Mimi. Ya jima yana kallon alamar da aka nuna take. Sai kuma ya ajiye wayar yana mai lumshe idanunsa da fara karanto addu'oi a ransa. Yana a wajen har akai kiran sallar isha'i. Miƙewa yay zai koma massalacin. Yana gab da shiga ya hangota tana tahowa cikin dogon hijjab har ƙasa. Yanda take tafiyar tana waige-waige zai tabbatar maka a tsorace take. Sosai take kama da shi itama. Dan kasancewar ta mace ma yasa har tafi sauran ƙannen nata ƙyau da haske. Sosai ya jima yana kallonta har sai da taje gaban gate. Ta kai hannu zatai knocking idanunta na kallon massalacin suka haɗa ido. Wani kalar rikicewa tai da diriricewa jikinta na rawa sosai, sai kawai ya ɗauke idonsa ya shige massalacin kamar bai ganta ba...
Bayan an idar da salla kamar yanda ya saba ya taso yaransa gaba suka shigo gidan. A falon ƙasa suka sami Ammie da masu aiki suna ƙoƙarin shirya table domin yin dinner. A kallo ɗaya da yay mata yasan tasha kuka. Bai ce komai ba suka zazzauna. Fharooq ya kalla cikin kamilar muryarsa yace masa yaje ya kira Auntynsu. Kai yaron ya ɗaga masa da faɗin, “To Daddy” ya tashi ya wuce. Babu jimawa sai gashi ya fito. Itako sai da taja kusan mintinan huɗu dan harma Ammie ta kammala zubama Daddy nashi abincin zai fara ci sai gata ta fito tana rabe-raɓe kanta a ƙasa. Babu wanda yace da ita komai. Dan hatta Ammie batako kalleta ba ma. Hakan ya ƙara sakata shan jinin jikinta har sai da Daddy ya ɗago ya kalleta.
“Kina lafiya kuwa Mamina? Ko bazaki ci abincin bane?”.
Yanda yay mata maganar kamar yanda ya saba ya sata zabura. Sai kuma ta shiga ɗan rawar jiki na rashin gaskiya. “Za...z...zanci Daddy. Ammie ina yini”. Ta faɗa duk a tare muryarta na rawa. Murmushi Abaan yayi da ɗan girgiza kansa yana kallon Khadijah da ko kallon inda Mimin take taƙiyi. Kansa ya ɗauke tare da maidawa ga Mimin ya ce, “Zoki zauna”.
Zaman tazo tayi, sai dai idonta nakan Ammie cike da tsarguwa. Shi kansa Daddyn yanayinsa da yanda ya nuna tamkar bai ganta ɗin ba firgitar da ita yake yi. Haka dai ta zuba abincin ɗan kaɗan ta fara tsakura dan a ƙoshe take. Fitar da sukai da Yazeed wani haɗaɗɗen gidan abinci ya kaita suka ciwo kayan ƙwaɗayi..........✍️
_🤦Kunga na ɓata ɓat ko, Hummm abubuwa sai addu'a. Kudai ku sani a addu'oi ku kawai dan ALLAH 😭🙏_
_INA MASOYAN ZAFAFA BIYAR?_
_KU MARMATSO KUSA...🔊_
_ZAFAFA BIYAR 2024_
_ZAFAFA BIYAR!!!_
_ZAFAFA BIYAR!!_
_ZAFAFA BIYAR!!_
_SHIN YAN UWA KUNA DA LABARIN ZAFAFA BIYAR DINKU SUN SAKE ZUWAR MUKU DA WATA TAFIYAR LITTAFAN SU MASU MATUKAR MA'ANA DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA?_
_YA KE YAR UWA KADA KI BARI A BAKI LABARI... DOMIN DA A BAKI GWARA KI BAYAR...WAI AKACE ZUWA DA KAI YAFU AIKE_
_GA SUNAYEN LITTATTAFAN WANNAN TAFIYAR... CIKE SUKE DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA KI KOYA KUMA KI GYARA DA KAN KI..CIKI HARDA ZALLAR KAUNA TACACCIYA MARAR GAURAYE_
_________
_1_
*_AMEENATUH_*🧕💖: _MAMUH GEE_
_2_
*_TSUTSAR NAMA (ITAMA NAMA CE)🐛👣_*_:BILYN ABDULL_
_3_
*_GUDUN KADDARA🏃🐾_*:_SAFIYYAH HUGUMA_
4 KWANKWASON JIMINA(MAI WUYAR SHAFAWA)🦩🦯_*_:NANA HAFSATU (MX)_
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*