Jawaheera Complete Page 6


Health College

Jawaheera Complete Page 6

 ☘️🍀☘️🍀☘️🍀☘️

      *JAWAHEERA* 

☘️🍀🍀☘️🍀☘️☘️🍀


 *PART* 6

Daga alkaluman

      

     NUSAIBA ALKAMAWA

         PROFICIENT WRITER'S ASSOCIATION

  09030567767


DA


SAYYADA (barrister)

MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION 




______jahan tace" gaskiya jawaheer besty Allah ya zuba miki tsantsar kyau ke kingan ki kuwa kamar wata balarabiya,Allah yasa yau idan kika fita kar asamu masuyin accident da masu faduwa.


 "dariya jawaheera tayi tace kai haba dai SBD kyau na sai ace za asamu masuyin accident?kema besty kyakkyawar ce ai.



______ murmushi jahan tayi tace but kinfini kyau, murmushi kawai jawaheer tayi.


Zo muje muyi break fast Daman shigowar danayi kiranki nazo yi murmushi jawaheer tayi wanda yakarawa fuskantar ta  kyau har fararen hakoranta suna bayyana tare da dimple shima yafito radau fita sukayi suka tarar da Dady da Mamy da Jawad akan dining ɗin kujera sukaja suka xauna, sannan jawaheer tagaishe su har suna tambayarta ya kwanan baƙunta ita dai kawai murmushi tayi musu,ta kalli wajen da Jawad yake taga yana cin abinci, "mamy ta katse mata kallon Jawad take, da yake yanga wajan cin abinci,tace jawaheera ga yayanki nanfa baki gaidashi ba ko baki kula dashi bane ba ?cikin zuciyarta tace inma na gaidashi sai

yaga dama yake amsawa, Amman a fili tace eh mamy,yaya JAWAD ina kwana ?dagowa yayi suka hada ido jitayi kirjinta yabata dammm saurin sunkuyar da kai tayi shikuma ya amsa mata dacewa lpy yacigaba da cin abincin sa "itama abincin tafara ci azuciyarta kuwa Mamy cewa tayi naga alamar yaran nan basayin shiri.


"Jawad yana gama cin abincin ya mike Dady yace Jawad harka gama. "eh Dady nagama Ohk to zauna zamuyi maganar asibitin ka ,zama Jawad yayi sannan Dady yace "naxuba sabbin ma aikata kai kuma Yakamata ranar Monday kafara zuwa kaima to Dady Allah yakaimu yauwa kuma inason anjima ka kaisu shopping daman jiya nafada maka.


" da Dady ɗan anjima inaso naje gidan su shabbir ne ,"to ai babu matsala sai kuje tare,kwaɓe fuska yayi yanzu wa'yannan yaran zantafi dasu gidan abokina Dady  ?eh to menene dan katafi da su ,to shikkenan Dady xantafi dasu,  mikewa yayi yanufi dakinsa yafaɗa gado ya lumshe ido,shifa gaskiya bayason yawo da ƙananun yara shifa bayason raini in banda Dady ne da wllh da ba zaije da suba Amman ina bazai iya ketare umarnin mahaifinsa ba ,wayarshi yadauka yaga amma kirashi har  mutum uku shabbir ne sai wata number ba suna ,sai  Asiya.


_________Kiran shabbir yayi yana dagawa sallama yayi suka gaisa Sannan Jawad yake sanar dashi zuwansu, murna yayi kuwa sosai ya sanar dashi harda yaran nan xasuxo bisa tilastawar Dady shabbir yace to menene kazo ɗin dasu mana, Jawad yace kai nifa ba wai dan xanje da jahan bane damuwa wannan yarinyar ce banason naje da ita. "dariya shabbir yayi yace Ni banga aibin yarinyar nan ba da baka sonta,Jawad yace kai baza kagani bane ba Amman yarinyar tana da nutsuwa ga kyau ,Ni wllh dama ka aure ta kunyi matukar dacewa,kai shuru kadameni daga faɗa maka damuwata sai ka ɓata min rai Jawad idan baka sonta Ni inasonta,tsabar haushi ma Jawad baisan Lokacin dayaja tsaki ba yakashe wayar.


________Aikuwa kamar jira ake yakashe wayar sai ga kira da wata bakuwar number kin dagawa yayi Saida yaga kiran yayi yawa sannan ya daga batare da yayi magana ba muryar mace yaji tana cewa hello, "shuru yayi mata dan yagane ta sarai  rufaida ce wacce take sonsa a u.k suka hadu


"Saida takara maimaita" hello sannan ya amsa mata da hy kamar wanda akayi masa dole, "murmushi tayi tace komai zaka min baxan taɓayin zuciya ba amatsayin wanda nake sonka bazan taɓa ganin laifin kaba duk laifinane dana ce ina sonka SBD kana da abubuwan da mace zataso awajen ɗa namiji, kana da kyau, ga hankali, ga kuma ilmi, hade da dukiya, da tarbiya, to kaga ba wacce macen da xata ganka tace bata soka ba .


"Shidai harga Allah yanajin tausayin rufaida da Asiya SBD tsantsan soyayyar da suke nuna mishi duk Wannan wulakancin dayake musu yaci ace sunbarshi Amman SBD sonshi da suke yi sun jure,gashi matsalar shikuma mata basa gabanshi. 


_______Katse masa zancin zucin da yake tayi tace hello beb bakajine ? inajin ki yafada atakaice,"Amman shine kashareni,shi rasama abinda xaice mata yayi kawai yace mata yanzu ina wani abune dan anjima zan kiraki,tace dan Allah beb karka manta ka kirani katse wayar yayi ya kwanta batare da yabata amsa ba.


______Ɓangaren su jawaheer kuwa Jawad yana tashi suka cigaba da hirarsu tasake sunata hira hardai dady yagama cin abincin shima yatashi itama mamy tashin tayi tabi bayan mijinta suna shiga suka zauna Dady ya kalli mamy yace nikam akwai wani abu da yake daure min kai ," menene shi  alhaji?hmmn kinsan Wannan yaran basa shiri da juna ?


"Wane yaran kenan alhaji?Jawad da jawaheer mana, 


"murmushi Mamy tayi tace Nima naga alamar haka nibansan mai yasa ba kuma duk laifin Jawad ne SBD rannan lokacin da suka fara haduwa dashi data gaishe shi bai amsa ba Saida nace masa ana gaishe shi tukunna ya amsa ciki _ciiki ,dady yace hmn halin Jawad da ban yake kuma in Allah ya yarda wannan tsanar saita koma soyayya,Allah ya yarda to ,"da kuma xumincin mu yakara kulluwa ina masa sha'awar aurenta SBD naga yarinyar tana da nutsuwa dan yakamata jawad yayi aure eh kam Alhaji Allah dai yabasu masu kula dasu amen ya rabbi.



"Ɓangaren su jawaheer kuwa su Dady suna tashi suma suka wuce dakin jahan suna zama Jahan ta kalli jawaheer tace besty dan Allah na tambaye ki meyasa bakwa shiri da yaya Jawad ne ?naga ko dazu da kika gaisar dasu Dady baki gaishe shi ba .


"Murmushi tayi tace ke kuma abin yadame ki kenan dole yadame ni mana nidama nakeso naga an hadaku aure sai dai nida yaya Jawad Kinga wajan kwanciya ta ko  to karma ki kara Wannan zancen naje abu yatabbata kisani cikin ha'ula'i.


" nikam ma bacci zanje nayi kinsan fa yaya zezo muje shopping kuma bayasan jira "to nafasa komawa tayi ta zauna karar wayar ta taji duba wayar tayi taga bakuwar number dagawa tayi taji ance Assalamu alaikum wa'alaikum salam ta amsa mai "nasan baki gane wake magana ba ko eh nidai sunana Sharif nasan baki gane niba abokin Jawad ne da fatan imran yayi miiki bayani na eh yamin to dan Allah kibani dama wllh da gaske auren ki zanyi kuma banason wannan auren yadauki lokaci dan agida an matsa min da nafito da matar aure saiyanxu Allah yahada Ni dake dan Allah kada kiyi watsi da SOYAYYA ta hmmmn kawai tace dan surutunsa yaɗata saka mata ciwon kai dan madai yana da dadin murya "dan Allah kije kiyi tunani anjima zan kiraki domin naji sakamakon"'allah yakaimu yana faɗar 'yakashe wayar , kallon jahan tayi tace kinsan waye wannan?


__________Wai abokin ya Jawad ne yake sona shine yanxu ya kirani wai aurena zaiyi wai yanxu nayi tunani,"toke yanzu mai zakice mai ? to ai shine nake neman shawarar ki, murmushi Jahan tayi tace kawai ki amince kusha soyayyarku kice kin amince kawai." karar wayar Jahan ce ta katse musu hirar tasu, yaya Jawad ne yake kira jawaheer tafaɗa.


"  daga wayar Jahan tayi tace hello yaya,"idan kunshirya yanxu kufito  kawai yace ya katse wayar ,batare da yajira amsar da zata bashi ba. ,kekam besty jawah basai kin canja kaya ba nice dai zan canza Bara naxo nayi sauri dan bayason jira, "jawaheer tace kedai kika sani shigewa jahan tayi bedroom ita Kuma jawaheer tana xaune hardai jahan   tagama shiryawa tasha kyau kuwa,ke kinga yacce kika zuba kyau kuwa ai duk kyauna bankai kiba,

 kezo mutafi kar muje yaya yayta jiranmu fita sukayi parlour suka zauna kan yaya Jawad yafito,wani kamshi sukaji kai azabar dadi ita kanta jawaheer kamshin turaren yayi mata dadi.



" shigowa parlour yayi,yayi masifar kyau wani rantsattsan yadi yasaka sky blue yayi matukar kyau ,ganinsu yayi akan kujera kallon Jahan yayi yace jeki cewa mammy zamu tafi to yaya mike wa tayi   tanufi dakin mamy shikuma zama yayi akan kujera ciro wayarshi yayi acikin aljihu yafara dannawa dawowa Jahan tayi taca yaya mamyn tace sai mundawo ,"Ohk kawai yace yamike yanufi hanyar fita suma bayansa sukabi awajan motarsa suka tsaya shiga cikin motar sukayi suka tafi sai wajan shopping shiga sukayi ciki suka fara daukar abinda sukeso suna cikin daukane jawaheer takai hannu zata dauki wani perfume yayi daidai da wani shima zai dauka saurin janye hannunta tayi ta kalli gefenta wani kyakkyawan saurayi tagani murmushi yayi mata yace na barmiki,"itama murmushin ta mayar masa tace kai yadace ka dauka dai_dai Lokacin da Jawad yashawo kwana yagansu suna magana jiyayi duk baiji dadi ba yacewa Jahan wacce ta iso yanxu," lokacin yayi inkunga dama kuzo mutafi jahan takarasa gurin takira jawaheer.


______Wajan biya yanufa suma suka bishi sukasa kayan da suka dauka ana sallamarsu yanufi mota yashiga ya kifa kanshi akan sitiyarin motan gaba dayansa bayajin dadin jikinsa suma shiga sukayi afusace yaja motar sukansu saida sukaji tsoro hanyar gida yanufa dasu suna isa yafara horn har saida maigadi ya tsorata ,gateman yana fitowa yaga ashe Jawad ne saurin bude gate din yayi Jawad ya shiga cikin sauri yanayin parking  yabude murfin motar kamar zai ɓallata darectly part dinshi ya nufa  yazauna akan kujera yadafe kanshi dake tsananin masa ciwo tashi yayi yanufi fridge yadauko ruwa mai sanyi yasha sannan ya fara dawowa daidai yarasa meyake damunsa ,zama yayi karar wayarshi yaji,kamar da baxai dauka ba kuma sai ya dauka.


"Daga ɗaya bangaren akace hello Jawad inata jiran zuwanka ko ince bakuzo ba,  munfasa zuwa dan yanxu ma muka dawo daga shopping kuma banajin dadi ne shiyasa banxo ba nan duk ya kwashe abinda yafaru awajen shopping yafaɗa abokinsa har tsayawar da jawaheer tayi da saurayi.


" Shabbir yana gama sauraron maganar abokinshi nashi yasauke ajiyar zuciya yace Jawad koda nafaɗa maka wata magana baza kayarda ba .


Kafaɗa min mana zanyarda hmmmn kasanme Jawad son yarinyar nan kake duka alamu sun nuna haka nasan kaima bakasan da haka ba Saida nafaɗa maka kuma na fahimci tun lokacin da sharif yace yana sonta naga yanayin ka ya canza tun alokacin na fahimta.


"Murmushi me haɗe ta takaici Jawad yayi yace Mus'ab idan kagama zan kashe wayata dan bazan jure wannan zancen mara fa'ida ba, mezanyi da Wannan yarinyar wadda cikakkiyar tarbiya ma bata da ita kana ganin kofa gaishe da mutane batayi,kuma abinda yasa duk naji babu dadi sona ke ta zauna haka babu mijin aure naga karshen girman kanta wllh ina tausayin namijin da yace yana sonta bare akai ga aure.



"Eyeehh Jawad kasan kuwa abinda kake faɗa?to Allah yakyauta to baza kataɓa gane wa ba SBD baka taɓa soyayya baneba Amman muna fatan kiyayya takoma soyayya ,


"Karamin tsaki Jawad yaja yace kana batamin rai sai anjima kit yakashe wayar .



Suma suna fitowa daga motar suka wuce parlour








Plz Share it fisabilillah

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post