Kurman Baƙi Page 25 by Huguma

Kurman Baƙi Page 25 by Huguma

 *_KURMAN BAƘI_*⚫⚫⚫


*HUGUMA*


PAGE 25



             Ranta a bace ta soma sauya kayan jikinta,cikin ranta tana tunanin abinda Zainab keso a tattare da ita. Ta gama kintsawa ta dawo falon don su bude kyaututukan yara kafin daddynsu ya dawo,abundai bai yiwa wasila ba har sai da ruqayyan ta sake magana da ita


"Wooo wasila!......abinda tayin kina nufin ba wani abun ta taka ba a qasa?,idan kare yana haushi ai baka kulashi,ka barshi idan ya isa ya kawo maka cizo mana ya gani?,mai gidan ai zai dawo ko?,zaiga kuma komai,kanta ta haqawa rami ai ba ni ba" daga wannan ta watsar sukaci gaba da sabgar gabansu.


               Tafi awa tana sauraren ta jiyo ruqayya ko wasila ko wani nata yana maganar ta janye mota ko abinda ya danganci haka,ta rantse da Allah yau din sai tayi mata wankin babban bargo,saita basu mamaki(ni kuwa nace hmmm,bayan wanda kike basu😂),haka ta qaraci tanadin masifarta ta haqura ba tare kuma data janye motar ba.


              Tunda akace mata daddy yana kiransu a falon tsakiya tasan ba lafiya ba,tunda ya saba duk wadda ba girkinta bane yana leqawa ya sameta har sassansa su gaisa bayan ya shigo gidan sannan ya wuce sashen me girki.


              Ta gama alwalar magariba kenan duk da akwai sauran lokaci,sai ta qarasa gaban madubi ta tsane fuskarta ta shafa lotion kadan sannan ta shafa powder,sannan ta qara mulke jikinta da oil perfume ta fito.


                  A tsaye ta samesu shi da zainab din tana riqe da qugunta. Ta dauki idanunta daga kanta kamar bata ganta ba ta zagayeta ta tsaya daga damansa


"Daddy yada haka a tsaye?,ka zauna mana kaman ba cikin gida muke ba?" 


"Ba ruwanki da tsaiwarsa ko zamansa tunda ba ranar girkinki bane wannan ba huruminki bane" banza ta baiwa ajiyarta ta janye masa pillow din dake kan kujerar tace


"Have a seat please daddy" tayi maganar a sanyaye cikin tausasawa ta yadda har tsakiyar zuciyarsa sai da yaji wani sanyi ya saukar masa,ya kuma shiga kokwanton maganganun da zainab din ta tare shi dasu bayan yabi ba'asin me yasa akayi wrong parking,ga wata motar kuma a qofar gida basa tsoron yara su kakkarceta.


                 A nutse ya zauna din yana sauke numfashi can qasa,rashin ganin fuska daga kowannensu ya hana zainab din ta sake cewa komai,saidai ta qulu iyaka


"Me ya hada zainab da ke da wasila?" Yayi tambayar calmly


"Wani abu tace ya faru?,nidai a iya sanina bansan komai ba,ko magana ta fatar baki basuyi ba bare ace ma wani abu ya hadasu"


"Dole kice haka mana,ki sakata tana sakarmin baqaqen maganganu tana min kallon raini,to wallahi kashedint......."


"Ke da Allah malama dakata,da mijina muke magana ba dake ba,idan kuma kin gwammaci nayi magana dake din to daidai nake dake,ki kiyayeni ki fita idona don ni ba sa'ar yinki bace.......shashasha mara kunyar qarya da wofi ke duk tsiyar da kika shuka kina da bakin yin magana inda ace ke din me kunya ce?,kina nufin inda na barki da wasila zaki tsira ne?, wallahil azeem da wannan rashin kunyar da kika tsaya kina yima baki isa ki yita ba"


"Ya isa ruqayya......"


"Ai ba dogon magana na fito nayi ba dama,ka jawa matarka kunne,taci gaba da ji da abinda ya dameta,don ni bani da lokacinta ina da masu jimin da ita idan hakan ta kama" tana gama fada tayi gaba abinta


"Kaji ko?,tabbacin ita ta sakata tayimin diban albarka"


"Ya isa haka da Allah" saleem ya fadi cikin gajiya da soki burutsun qorafe qorafen zainab din.


            Tayita zuba idanu ruqayya ko zataji wani abun ya sake tasowa amma taji shuru,batasan yadda suka qarke ba,don ko abinci ma ranar cewa tayi bata ci,qememe taqi fita,saima tayi kwanciyarta ta tura yara. Koda ya shigo da kansa ma laga laga tayi tace masa batajin dadi haka ya koma. Wannan ya bata ran zainab,don ta shirya abubuwa masu yawa a zaman cin abincin amma ruqayya taqi bata wannan damar,don tun daga ranar ma sai ta janye zaman cin abinci,idan ta gama zata shirya musu ta koma sashenta,idan ya shigo zaiyi qorafi takance yau batajin dadin cikinta ko qamshin abincin ya cika mata ciki ba zata iya ci ba don zata iya amai. Sai ya zamana duk ran girkin ruqayyan suna gama cin abincin yake tattarawa ya wuce sashen ruqayyan sai kuma da asuba idan ya shigo tayar dasu sallar asuba.


              Yadda taga hankalinsa kamar yana sake karkata ga ruqayyan ya tashi hankalinta matuqa,ta kasa zaune ta kasa tsaye,hankalinta ya kasa tsaiwa guri guda. Hatta dasu haneefa yanzun duka sukeci a wajenta,ta kasa zama da kowa lafiya saboda tana ganin ubansu kamar baya yi mata adalci.


                Komai da yasan zasu buqata ya kammale waje daya kafin tafiyarsa,mutum ne tsayayye wajen kula da hidimar iyali da buqatunsu,ya danqawa kowacce adadin abinda zata buqata na cefane da hidimar gida,don ba zasu dawo ba sai ranar jajiberin sallah. 


              Tuni zainab tayi nisa wajen hada kudin dinkin da za'a yi mata,ta zabge fiye da rabin kudaden da saleem ya bata ta sakasu a lissafin. Ta riga ta tsara abinda zata diba cikin kayan abincinsu ta saida ta sake hada wasu kudaden masu kauri,wannan karon sam ba zatayi wasa ba,tanason sanda saleem ya tsoma qafarsa a qasarnan ya dawo hannunta,ya koma mata bita zai zai,tanason ranar daya dawo dakinta daukacin al'ummar gidan su shaida,muryarsa tayi kururuwar da kunnuwan ruqayya zasu jiyo,ta gogewa idanunta dukka wani sauran bacci da ya rage mata,bayan wayewar gari kuma taci karo da gagarumin sauyin da zai ruguza duk wata kissa tata da take taqama da ita. Tanason ruqayyan ta zame masa kamar namiji dan uwansa,duk sanda zasu kasance da juna ya dinga jinta tamkar abincin da babu maggi ba gishiri,tayi imanin indai wannan buri nata ya tafi a haka komai zaizo mata a yadda takeso.


               Ana ya gobe zasu tafi ta yiwa wasila waya tazo ta tayata zama,saboda yanayin laulayi,kuma tayi imanin ba wanda zai iya zama da halin Zainab dai dai da halin nata sai wasilan,saidai ta sanya ta bawa umma wayar cikin zolaya take cewa umma


"Zan dauke miki auta har zuwa sallah,amma  ki jawa auta kunne wallahi kar tazo ta zaka kishiya ta babbakani" Dariya umman ta dinga yi,saboda tasan barkwancin wasila da ruqayya baya qarewa.


               Da daddaren ranar cikin girkin Zainab yake,wanda a washegari inda yana qasar nata girkinne. Tsaf ta shirya qananun jakankuna data masa qananun siye siye da tasan zaya buqata a can,ta kuma yi masa packaging na qananun snacks da ba zasuci masa guri ba ire iren wadanda tasan yana so.


                 Bata jima da fitowa a wanka,don wani dogon bacci tayi,har ya shigo nemanta ya fita ma bata sani ba. Wata sabuwar doguwar riga ta siya me sulbi cikin ribar business dinta. Sunyi nacin rigar ita da zainab sosai,shima kuma yaso siya musu don tayi masa kyau amma wasu hidimomin suka shigo ciki sukayi gaba da kudin rigunan kusan 60k. A lokacin har sabani suka samu shi da zainab akan hakan,tace ya sanya musu rai dama dai baiyi niyyar siya musu ba. Wannan kalmar ta qona masa rai matuqa da gaske,saboda shi din duk wanda ya sanshi yasan me fada da cikaawa ne,muddin kaga bai cika ba to akwai babban dalili.


"Bari naje gurin daddynsu muyi sallama,don shida na safe sun fita a gidan nan"


"Okay bari nima na amsa wayar wannan dan anacen" ta fada tana miqewa. Kai ruqayya kawai ta girgiza,dole tayi bakin qoqarinta adan zaman nan da zasuyi da wasila ta canza tunaninta.


                 Yana daga cikin bedroom dinsa yana hada kaya zainab na zaune a gefe tana qara masa wani sabon lissafin,don so take kota halin yaya ta sake samun wasu kudaden da zata maida asarar da basira ta janyo mata,ta hada kudin dinkinta tsaf,ta kuma fidda kudin hidimar gidan dai daya bayar.


                  Sallamar ruqayyan ta ratso har dakin,ya amsa yana bata izinin shigowa,saidai dan tsayawar da tayi tana gyarawa haneefa assignment dinta na islamiyya ya bawa zainab damar yin magana


"Ya muna daki zakace ta shigo mana fisabilillahi?" Bai kalleta ba yace


"Bedroom dina nace ta shigo ba naki ba,ke shigarki nawa bedroom dina na sashenta?,kin taba ji tayi qorafi?" Tasan magana ya yaba mata,lokacin amarcinsu idan taso tsiya ma tana tuburewa ne tace tsoron sashenta takeji a nan zata kwana,wani lokaci saidai yabar mata nan din su kwana a bedroom din ruqayyan. Haka taci gaba da faruwa har sai ranar da ruqayyan ta gaji tayi maganinsu sannan aka samu sauqi.


               Da sallama ta shigo,idon zainab ya fara sauka a kan rigar jikin ruqayyan. Tashi daya fuskarta ta sauya,ta gane rigar sarai,tashi daya zuciyarta ta bata saleem ya zagaye ya siya mata,ko kuma ya bata rabin kudin a bayan idonta.


"Aiki kake da kanka" ruqayya ta fada tana murmushi sannan taja stool ta zauna tana masa barka da dare. Cikin kulawa ya amsa duk da yana takatsantsan,yasan tsaf zainab din zata jawo wani maganar da rayuka duka zai baci.


                 Tana so ta saka masa hannu a gyaran kayan amma tana gudun magana,don duk hirar da sukeyi zainab din na wajen,ita bata tanka ba ita kuma bata fita ba,hakanan bata tayashi da komai ba.


             Ta dan jima suna hirarrakinsu sannan ta miqa masa ledojin


"Gashi daddy ba yawa" ita da ba ita aka bawa ba amma ta riga saleem din sanya idanunta akan ledar cikin son bin diddigi da tantance meye a ciki.



*_ZAFAFAN DAI_*🫡🫡🔥🔥🔥🔥


*_NEW HOT BATCH 2024 DA ZAI TASHI KANKU FIYE DA NA BAYA IN SHA ALLAH_*🥵❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥🔥🔥🔥



*_KASANCE D'AYA DAGA CIKIN ZAFAFA FAMILY NA WANNAN SHEKARAR TA 2024 TA HANYAR SIYAN TIKITIN SHIGA GROUPS NASU NA ZAFAFAN LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA_*


🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥



_WANNAN DIN WATA DAMA CE TA MUSAMMAN A GAREKU WAJEN ZAMOWA CIKIN AYARIN IYALAN ZAFAFA_


*_LITATTAFAN SABUWAR SHEKARAR SUNE KAMAR HAKA_*


*KWANKWASON JIMINA miss xoxo*


*TSUTSAR NAMA Billynabdul*


*GUDUN K'ADDARA Huguma*


*AMEENATU Mamuhghee*



_GUDA DAYA:400_

_BIYU:700_

_UKU:900_

_HUDU: 1200_


_BANK NAME:KEYSTONE_


_BANK ACC NO:6019473875_


_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_


_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_


__

_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_


_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_


*09033181070*


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*



_MARABA  LALE DA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post