Kurman Baƙi Page 26 by Huguma


Health College

Kurman Baƙi Page 26 by Huguma

 *_KURMAN BAƘI_*⚫⚫⚫


HUGUMA 


PAGE 26



             "ma sha Allah,me muka samu?" Ya fadi yana dan murmushi. Murmushin itama tayi cikin salon tsokana


"Gani ya kori ji ai daddy duk da babu yawa" . Ledar ya qaraso ya dauka,har sannan idanun zainab na akai tana son ganin qwaqwaf.


"Kin gama komai ai,dama sauran abinda ya rage naketa tunani ban siya ba sai gashi kin kawomin,Ma sha Allah,ma sha Allah,Allah yayi albarka na gode qwarai" ya fadi yana buda kayan sosai.


               Tsam zainab ta miqe tsaye tana maganganu qasa qasa kafin daga bisani tace


"Wannan ai cin fuska ne,me ya hana sanda ya shiga gurinki tun dazun ki bashi har sai da kika biyoshi gabana saboda tsabar iyayi da son nunawa?" Kallon tsaf ta yiwa zainab din,tana da amsoshin maida mata masu tarin yawa,to amma idan ta tuna gobe xai tafi ya barsu tare,kome zasuyi dashi zai tafi a tsaye cikin ransa sai kawai ta kauda kai ta bawa banza ajiyarta,ta kuma miqe a nutse tana dubansa


"Zan wuce daddy,saida asubar?"


"Alla ya tashemu lafiya maman twince"


"Na gode abban twince" ta maida masa tana murmushi ta gota zainab din


"Au aina dauka kwana zakiyi da sai na tattara nabar muku dakin"


"Hakanma ba laifi bane tunda mata kuma uwar gidan saleem nake" ta amsa mata ba tare data waiwayo ba tana qarasa fita a dakin.


              Amsar tayi masifar qona mata rai,ga sunan da ya kirata dashi na maman twince sai take ga kamar gatse yakeyi mata,wannan ya hadu ya sakata rushewa da kuka.


              Tamkar baya ma dakin gaba daya,ko gezau baiyi ba bare ya nuna yasan da wanzuwarta ita da kukanta a wajen,ko sau daya tak bai daga kai ma ya kalleta ba bare ta sanya ran zai tanka ta Hankali kwance yaci gaba da hada kayanshi,har sai data gaza don kanta


"Ko bakayi haka ba dama nasan ka gaji da zama dani matarka ce a gabanka,twince kuma itama ba ita baiwa kanta ba,wanda ya bata nima shi nake fatan ya bani" saita miqe ta bude zaninta tana bar masa dakin.


                Bai motsa ba har ta fice sannan yabi qofar da kallo,shi kansa da yake namiji yana mamakin sokonci da dolanci irin na Zainab din,mijinki zaibar qasa a gobe maimakon ki tattalashi ku rabu lafiya amma inaaa.......baki ya tabe,ko kadan fushinta da bar masa daki ba wai wani baqon abu bane a wajensa,qauracewar zainab daga gareshi ya riga ya saba da hakan tunda dadewa(karki soma hora mijinki da irin wadan nan abubuwan,hanashi kanki don ya bata miki rai da sauransu,duk sanda ya saba da hakan zai zame masa jikine har ya dinga jin hakan ba komai bane,kuma muddin kina hakan tabbacin baki cika mace bane,ba kuma ki iya horo ba).


             Tunda ta tashi sallar asuba ta kirayi wayarsa kamar tasan zainab din bata kwana a dakin ba. A lokacin ya idar da sallah yana shirin shiga wanka kenan,ta gaidashi cikin kulawa ya amsa mata


"Ka shirya ne daddy?"


"Waye zai shiryani tunda ba wajenki nake ba,komai da kaina nakeyi banga ma me shirin ba bare na saka rai"


"Uhmmmm" kawai tace dashi don tuni ta fuskanci inda maganarsa ta sanya gaba. Bata fiya jan zancan zainab ba a tsakaninsu don haka tace masa


"Idan ka gama shiryawar kayi min magana mu fito rakiya"


"Alright" ya amsa mata har cikin qirjinsa yana jin kewarta. Yayi imani inda a bangarenta tafiyar ta riskeshi gata babu kalar wanda bazai gani ba.


               Koda ya fito dakin shuru sai ya kasa jurewa,ya daga waya ya sake kiran ruqayyan


"Har me?"


"Na kusa gamawa,ki kawomin manki zan shafa"


"Daddy mai kuma?,ina umman haneefa akwai gurinta"


"Naki nace ki kawomin" dan jim tayi tana kallon agogo,kaman yayi safiya da yawa ta shiga mata sashe,to amma tunda shi ya kira ba damar masa musu.


             Man shafawar nata ta dauka wanda tasan daman time to time yana shafawa shima suna sharing. Har zata gifta kitchen wani tunani ya fado mata,tasan ba lallai ta bashi wani abun da zai sanyawa cikinsa,don haka ta tsaya ta hada masa black tea a gurguje ta fito masa dashi.


            Sanda ta isa shi ya bude mata qofar ta wuce ciki,har ya kammala shirinsa saidai singlet ne kawai jikinsa da boxer,tana gama ajjiye kayan ya jawota jikinsa ya rungumeta tsam yana sauke ajiyar zuciya. Jikinta ta janye gefe tana noqe kafada


"Umman haneefa fa"


"Ba wani umman haneefa,gari ya kusan yin haske,a qa'ida ma an shiga ranar girkinki ai......i missed you a lot ruky na" ya fada yana lumshe idanunsa. Murmushi ta saki,duk sanda ya kirata da wannan sunan yana tuna mata da wasu abubuwa masu dadi da suka shude a tsakaninsu.


                Duk da tana daddojewa amma haka ya jata sai data tayashi shiryawa


"Kayi haquri ba ranata bace,kaima kanka kasan da cikin hurumina kake ko......" sai tayi shuru kawai tana girgiza kai


"Yanxunma ai ni nakine ko?"


"Ni da wata,dole kuma a fidda mata haqqinta" ta amsa masa kai tsaye tana duban idanunsa,sai yadan kau da kai. Sau tari idan tayi wata maganar yana jin ta daureshi ne da jijiyar jikinsa ko kuma magana take maida masa a fakaice(uta tsarguwa fa ba dadi maganar gaskiya 😂😂😂😂).


            Abinda ya daure mata kai har ta tayashi ya kammala shiryawa ba zainab bare motsinta


"Daddy ka tasheta,bai kamata ace bata nan gurin ba yanzun,zan jiranka a waje" ta fada tana yin wuf ta fice don tasan idan bata haka ba zai tsaidata ne,kuma idan zainab din ta ganta ranta ba zaiyi mata dadi ba. Ballantana ita da ba haquri ne da ita ba ki dauke kai akan abubuwa.


               Da sallama ya tura qofar dakin,sai ya hangeta magashiyyan tana bacci abinta Jamar dazun mai mata knocking yace ta tashi tayi sallah ba. Takaici ya kamashi ta miqe tana hada rai ita ala dole jiya an mata laifi. Dankwalinta da ya cire ta jawo tana daure kan nata dashi sannan ta fara saukowa daga saman gadon da nufin shiga bandaki


"Tsaya ni wucewa zanyi don n gama shiryawa,sufyanu yana waje yana jirana zamu dauko hajiya"


"Allah ya kiyaye sai ka dawo" ta fada har yanzu fuskarta ba walwala tanason ya gane cewa lallai yayi laifi


"Ki kula da yara ki kula da gida,banda fita barkatai don Allah,ko meye ya taso ga waya nan a shaidamin"


"To" ta fada bayan ta tura baki gaba. Har ya juya ya dakata


"Kinsan dai har yanzu akwai case dinki kan tarkacen magungunan nan........kuma baki manta da sharudan da na aza miki ba?........ kiyi qoqari ki kiyaye,ki zauna a hakanki ni bana buqatar wani gyara indai na magani ne,akwai gyararraki da yawa da ya kamata ayi amma ba wannan ba" ranta ya sake baci,tana matuqar jin haushin taji yace basai tayi amfani da komai ba hakan da take ya gamsar da shi,yo ita din goyon mahaukaciya ce da zata biyewa dadin bakin namiji?,tana da kishiyar irin ruqayya ai bataga ta bacci ba,zama bai ganta ba


"Sai na dawo" ya sake fada yana saka kanshi waje


"To" tace masa a cunkushe tana tura bandaki ta wuce ciki tana abunda tafi qwarewa akai wato qunaquni. Baiga alamun yaran sun tashi ba suma,yasha mata fadan tashinsu sallar asuba amma a banza,yo itana bata tashi ba sai anyi fama ina ga yaran.


              Tashinsu yayi yasa sukayi alwala suka watstsake sannan yayi musu sallama ya fito.


                A farfajiyar gidan ya samu ruqayya ita dasu alhassan,har iftee ma na maqale a gefe, dukansu sanye da jallabiyyar da ya siya musu ne saboda sallar asuba. Kusan tare yaran suka gaidashi,ya tsugunna gabansu yana amsawa hadi da jawo iftee dake maqale da qaramin hijabin dake nuna tare akayi sallar asubar da ita ya rungumeta yayi kissing nata yana amsawa hadu da tambayarsu yadda suka tashi. Duka suka rankaya har bakin gate din,ya hanasu fita saboda yayi sassafe da yawa,dukansu suka hada baki wajen masa addu'a har ana rige rige tsakaninsu da umman tasu,hatta da iftee, addu'ar da basu daina ba har zuwa sanda motarsa tabar qofar gidan ta dauki hanyar ficewa a layin.


               Sosai tafiyar saleem ta bawa zainab daman yin al'amuranta a tsanake,komai nata sai ya ninka fiye da na baya,qazanta sai abinda yayi gaba,don kuwa tana iya shafe kwanakinta biyu cur bata duqa tayi shara ba,kamar yadda wanka ya tafi hutu a tattare da ita. Abinci kuwa ba ita ba hatta yaran za'a iya cewa horon yunwa take musu,don saidai su shiga sassan ruqayya suci,wasila tayita mita don takaicin zainab takeji kamar kamar me amma hakanan ruqayya ke cewa ta basu ba komai bane,lada zasu samu. Da wannan damar zainab tayi amfani ta riqe 'yan kudadenta ta siya magunguna ta adana wanda zatayi amfani dasu bayan anyi mata aikin,sauran 'yan canji ta duba ma haneefa atamfofi a 'yan pieces ta siyawa khalil gumama da pieces na shadda aka dinka masa duka a zuwan kayan sallarsu. Ba wani takalmin arziqi bare jaka mayafi da sarqoqi da ubansu duka ya fidda kudinsu,nata kayan kam ba tasu take ba,don ta tsara gaya masa cewa an sace a wajen tailor dinta,shikenan hankali kwance.


                   Tuni sun tsara da nurse din satin farko da aka kama azumi za'a yi mata dinkin,a lissafinsu kafin ya dawo ta warke sumul muddin zata kula da wajen tana tsaftaceshi da shiga ruwan zafi. Wannan ya sanya ta tura neman me zama da ita,bata samu ba sai safina ta samo 'yar wan babansu. Ba yarinyar taso ba,saboda basu cika jituwa can can ba saboda banbancin halaye dake garesu. 


"Ni umma yarinyar ta fiya tsaurin ido,ga shegiyar kafiya da taurin kai"


"Eh amma ita kadai zata iya da aikin gidanki,don bata da son jiki ko kasala,da qyar fa nasha kanta ta yarda,kinsan abdurrahimu baya barinsu zuwa ko ina su kwana,sun riga suma da sun saba,yanzu ma a qila wa qala ake"


"Shikenan,ki lallabata tazo din,don azumin bana da alama zai bada kashi" a haka sukayi sallama da umman nasu.


********Ranar da aka sauke azumi na uku ne,bayan an gama shan ruwa kafin akai ga tayar da sallar asham ruqayya ta shiga dakin d wasila ta sauka.


             Da sallama ta shiga ta sameta saman dadduma,dakin ya kaure da qamshin turare,sai wasu mayuka dake zube ta budesu tana hadasu guri guda.


              Guri ta samu ta zauna suna yiwa juna sannu,don wasilan ba laifi idan taso akwai aiki. 


"Nikam tunda aka fara azumin nan kamar baki da walwala sosai" dubanta wasila tayi kai tsaye sannan tace


"Bazan boye miki ba,wata jarrabawa ce ta shigo min rayuwa,kinsan zaid?"


"Zaid?,zaid?,wanne?"


"Abokin yaa bashir wanda ya tafi madina karatu satin da aka fara bikinki?"


"Oh.....ya zan manta da yaa zaid da ya kawo me lecture ranar wuni na"


"Exactly......ya dawo nigeria ruqayya,shi zuciya ta kuma ya jarabtu da so,nayi addu'a nayi addu'a amma ba abinda ya canza,naje wajen malam yacemin lamarin akwai rikitarwa,amma yace zaiyimin aiki a kansa cikin satin nan ya gani idan akwai alkhairi"


"A irin wannan watan wasila?" Ruqayya ta tambayeta cikin tsananin tashin hankali kwance a fuskarta,abinda ya Sanya jikin wasila yin sanyi ta bita da kallo. 


              Sassauta fuskarta tayi ruqayyan ta zamo ta zauna gaban wasila


"Wasila,wasila......babu wata addu'a da zakice ba zaki iya yiwa kanki da kanki ba sai wanine zaiyi miki,muddin kikaga kina addu'a kina ganin kaman bata karbuwa cikin daya biyu ne,kodai kin saka shakka a ranki game da addu'ar kin sawa ranki bata karbuwa,ko kuma kin saka gaggawa lokacinki yana tafe amma saboda gaggawa irin ta dan adam ya sanya kike ganin har yanzu shuru"


"Wasila"


"Na'am"


"Kinsan Allah da kansa yace yana kunyar bawansa ya daga hannu ya roqesh ya hanashi abinda ya roqa?,kinsan ko sau daya kikayi addu'a zuciyarki tayi rawa akan cewa wannan addu'ar bata karbu ba to tabbas kin jawowa addu'arki matsala,annabi S A w yace kuyi addu'a kunajin yaqinin ta amsu cikin ranku,koda bakaga haka a zahiri ba ka sanyawa ranka cewa ta karbu din" shuru wasila tayi tana jinjina kai



*_ZAFAFAN DAI_*🫡🫡🔥🔥🔥🔥


*_NEW HOT BATCH 2024 DA ZAI TASHI KANKU FIYE DA NA BAYA IN SHA ALLAH_*🥵❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥🔥🔥🔥



*_KASANCE D'AYA DAGA CIKIN ZAFAFA FAMILY NA WANNAN SHEKARAR TA 2024 TA HANYAR SIYAN TIKITIN SHIGA GROUPS NASU NA ZAFAFAN LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA_*


🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥



_WANNAN DIN WATA DAMA CE TA MUSAMMAN A GAREKU WAJEN ZAMOWA CIKIN AYARIN IYALAN ZAFAFA_


*_LITATTAFAN SABUWAR SHEKARAR SUNE KAMAR HAKA_*


*KWANKWASON JIMINA miss xoxo*


*TSUTSAR NAMA Billynabdul*


*GUDUN K'ADDARA Huguma*


*AMEENATU Mamuhghee*



_GUDA DAYA:400_

_BIYU:700_

_UKU:900_

_HUDU: 1200_


_BANK NAME:KEYSTONE_


_BANK ACC NO:6019473875_


_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_


_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_


__

_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

_MARABA  LALE DA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post