kukun Kaddara Takun Karshe Page 14 Complete


Health College

kukun Kaddara Takun Karshe Page 14 Complete

Novels Elite English

 _ *~✊💋BOSSLADIESWRITERS💋✊~*_

                     سجن القد💋🔥💞    

                  ~Takun Ƙarshe🔥~

            Dedicated to Aunty Kubra💋💞

قصة حب رومانسية غير عادية بين السجناء مع   تطورات معقدة💋💘😘

An extraordinary romantic love story between prisoners with complex twists ❤💋💘

Daga alƙalamin Boss Bature💋✊

__________________________✍️

_cikin fitar hayyaci take yin sambatun tuni mayafin dake akanta ya zame ƙasa, duk tabi ta yamutsa gyaran gashi  da akayi mata tamkar mahaukaciya haka ta koma, jikinta duk ya raunata saboda bugun kofar da take yi tana faman ciccije la66anta, ga ƙarancin iskar dake a wurin ta fara affecting dinta, gwanin ban tausayi baiwar Allah, jan numfashi ta cigaba da yi tana ganin jiri jiri a idanunta kamar daga sama taji zubar wani abu a tsakankanin cinyoyinta da wani irin matsanancin ciwon mara na fitar hayyaci nan take wata juwa ta kwashe ta gaba ɗaya ta kife kan floor sumar kanta ta tarwatse har ta saman fuskarta, hannayenta daddafe da cikinta dake ta murɗamata yanayi mata zogin azaba, muryar ta adisashe take ambaton sunan Allah da daƙyar daƙyar, zufa ce ta soma tsastsafo mata ta ko'ina na jikin ta, kafin wani lokaci jikinta ya saki tamkar matacciya ko yatsanta bata iya ɗagawa ta gama fita hayyacin ta............_



*Shin Ina prime minister ya tafi da garkuwa?*



Lokacin da suka fito daga Hall hannun su ruƙe cikin na juna, Yayin da gimbiya mujeedat da Yazrin suke a biye da bayan su, gaba ɗaya hankalin Jami'an da ke tsaron wurin Ya dawo kansu, da wani irin tsantsar mamaki da Al'ajabi suke kallon fuskar Danish da ta prime minister, Musamman jami'an Canada sun yi matuƙar girgiza da ganin shi, sun ruɗe sai faman Kallo ƙurulla suke bin su da shi.


Wata danƙareriyar mota Suka nufa, irin motar da a mafarki kaɗai talaka ya ke iya ganin ta, da sauri Wani gabjejen Soja Ya buɗe masu murfinta, Cikin motar yadda kasan bedroom tsabar haɗuwarta ga wani sanyin A.c dake sanyaya zukata, a tare suka shiga ciki ba tare da sun raba hannun su daga cikin na juna ba, Gimbiya mujeedat da Yazrin motar dake a jere da tasu suka shiga, zuciyoyinsu cike fall da al'ajabin Danish....


Kusan a tare motocin suka soma tafiya A hankali, Yayin da sojoji ke take masu baya, da kafafuwansu suke tafiya ta gefe da gefen motocin nasu.


Lumshe idanu gimbiya mujeedat tayi yayin da brain din ta ke tariyo mata fuskar Danish, bata san ya akai ta tsinci kanta da jin tsantsar kaunarsa ba, farat ɗaya taji ta kamu da son shi ya kwanta mata aranta, batasan ma ya zata mistalta yadda take ji azuciyar ta ba.


Ita kanta Yazrin zuciyarta ta tsunduma a kogon kaunar matashin da bata san wanene shi ba, jin shi take tamkar ɗan uwanta na jini......


"Mommy, fatana Allah yasa ba mafarki na ke yi ba" can cikin kunnanta ta tsinkayi maganar Yazrin da tayi magana cikin harshen larabci.


Numfasawa ta ɗanyi muryarta da wani irin sanyi ta soma magana da yaren su na larabci


 "ban ga laifin mijina ba, yanzu nake danasanin maganar dana gaya mashi ɗazu da mu ka shiga restroom, ban ta6a tsammanin zanga yaron haka ba, ay dole ma ya nemi zaucewa, Ni ko a tarihi ban ta6a jin labarin kamanceceniya irin wannan ba"


"Abun da yafi ɗaure mun kai shi ne, ba mu haɗa alakar komai da shi ba, bamu ta6a ganin ba, ba mu ta6a jin labarin shi ba, sai yau da Allah Ya haɗa mu.....


Fuskokin kowan nan su da tsantsar al'ajab


Slowly motor su ta ratsa katafaren entry way na shiga gidan hateem dake a tsare da security, basu nufi ko'ina ba sai cikin Ƙawataccen Lambun gidan.


Bayan sunyi parking, da sassarfa sojojin dake safa da marwa su ka ƙaraso tare da buɗe ma su marfin motor.


A hankali Prime minister Ya dira kafarsa Ya fito tare da ruƙo hannun Danish, Lokacin daya fito daga motar kusan suman tsaye jami'an dake tsaron gidan su ka yi, sai faman yin dogon wuya suke yi suna leƙen fuskar danish, Sun saki bakunansu kamar lehen sakarai, ƙasa ƙasa da murya sautin raɗar da sukewa junansu ta soma baiyana


 "Abun mamaki bai ƙarewa"!


"Kodai idanuwana ne suke nuna min badai dai ba?


"Dama prime minister Yana da ɗa Namiji ne?


 "To ko dai 6acewa yayi ne sai daga baya aka gano shi? In ba haka ba ni dai a iya sanina ya'yan sa biyu mata....."


Murmushin gefen fuska prime minister  ya ɗan saki jin tseguminsu, aranshi yana mai jin wani irin annushuwa.

   

sai bayan da suka soma tafiya tukunna motarsu gimbiya mujeedat ta ƙaraso, sam bai son sun biyo su ba, saboda ya makance idanunsa danish kadai su ke iya gane masa, Fitowa su ka yi a tare suka bi bayan Su prime minister, wanda Ya miƙi hanyar shiga wurin shaƙatawarsa da ke a cikin garden.


Yayin da suke tafiya wata irin ni'imtacciyar iska ce ke ratsa fatar su hakan bakaramin ƙaimi ya ƙarawa yanayin ba, danish Ya nutsu Yana bin furannin dake a garden din da kallo, dama can shi ma'abocin son furannine da alama dai Garden din ya burge shi...


Hateem sai satar kallon shi ya ke yi kamar zai lashe shi, shi kuwa wanda akeyiwa kallon bai ma son anayi ba.


Su Gimbiya Mujeedat da Yazrin suna a biye da su ba tare da sanin su ba.


Sauke idanunsa yayi akan Peacocks da ke yawo a garden din sun bubbuɗe Tail feathers dinsa gwanin ban sha'awa, ba karamin burge shi su ka yi ba..


Wani ƙawataccen wuri suka nufa, inda akayi shimfiɗa ta alfarma irin ta sarakuna, a kewaye yake da furanni launuka daban daban, Ga wata lumbutsetsiyar Round mattress mai tudu lallausar gaske, an kewaye ta da matassan kai masu laushi.


"Bismillah mu zauna" muryar Hateem ce ta dawo dashi daga kallon gardeen din da yake yi, A hankali suka zauna saman shimɗidar.


Daga inda suke a zaune suna fuskantar swimming pool tamfatsetse, launin ruwan da ke a cikinsa blue sky ne pure, ga wasu fararen agwagi saman ruwan suna ta shawagin su.


A ƙalla sun dauki tsawon mintuna babu alamun danish zai mayar da hankalinsa akan prime minister, ya nutsu sai kallon agwagin ya ke yi.


Yayin da shi Hateem din gaba ɗaya ya tattara nutsuwarsa da hankalinsa akan danish, wani irin kallon kurulla yake jifar shi da shi mai dauke da zallar kaunarsa, Jin shirun yayi yawa yasa shi yin gyaran murya, hakan Yaja hankalin Danish zuwa gare shi, slowly ya juyo tare da ɗaura fararen idanunsa akan fuskar minister, a karo na farko kenan daya fara kallon shi, nan fa suka fara jifawa juna kallon kallon, ko ƙyafta ido ba sa yi, sai da suka kusa shafe mintuna batare da sun kau da ido ga juna ba, su gimbya mujeedat dake a tsaye can gefen wata bishiya mai yalwar rassa da ganyayyaki sun kura ido suna kallon su, Ita da yazrin dake a gefen ta.


Wani irin ƙwarjini Danish yayi mashi, da sauri ya katse kallon da suke jefawa juna ta hanyar yi mashi magana

  

  "Sorry ban gabatar maka da kaina ba, Ni sunana Prime minister Hateem Obinna, kai fa"? Ya faɗa yana duban shi har lokacin danish bai daina jefa mashi kallon ba, babu alamun zai tanka mashi kamar akwai wani abu daya ja hankalin da yasa shi kallon nasa.


"Ka yi shiru baka ce komai ba," kamar kurma haka danish yayi mashi.


Dafe kai Hateem yayi muryarshi da kasala ya furta"please ka yi min magana, ba ka son yadda na ƙagu da son ganin ka samu lafiya ba, na damu da kai kamar yunwar ciki na, dan Allah ka saki jiki dani, kada ka azabtar dani da kaunar ka...." fuskar shi a yamutse yake yi mashi magana.


"Ina fata babu inda ke yi maka ciwo yanzu"? Ya jefa mashi tambayar, lumshe mashi idanu danish yayi alamar eh.


"Ya Ilahi, ba zaka yi min magana ba, sai dai ka yi min nuni da ido, ni bana so ka daure ka yi min magana, Inason jin muryarka ko hankalina ya kwanta, namanta ban faɗa maka ba, gobe da asuba zan bar ƙasar ba lallai mu sake haɗuwa ba, shiyasa nakeso ka bani haɗin kai mu more lokacin nan da muka samu...." cikin sanyin murya ya ƙare maganar.


  Har lokacin kallonsa danish ya ke yi, abun ya ɗaure mashi kai, Ya rasa gane ma'anar kallon nan.


  "Ko dai kana mamakin kamannina dakai ne"? shiru yayi mashi.


  "Wayyo Allah na, to ko dai baka jin harshen hausa ne inyi maka da turanci ko larabci ko french wanne yare kafi ji a cikin wadannan"? A ƙagare da son jin amsar shi ya faɗa yana kallon la66ansa burin shi ya motsa su don yayi magana.


Ƙiri ƙiri danish yana neman ya zautar da prime minister, zuciyarshi a jagule yace"nayi maka uziri tun da ba ka jima da farkawa ba, may be har yanzu baka gama dawowa normal ba, a hakan ma na samu kwanciyar hankali, ganin ka da nakeyi ba karamin faranta raina yayi ba" ya fada yana ɗan murmushi sama sama.


"Nasan kana jin yunwa bari nayi magana akawo mana abinci" wayarsa ya zaro daga aljihunsa har time din yana lura da kallon da danish ke jefa mashi har ya fara jin shakkar ko dai ifritan dake jikinsa ne suka motsa, dauriya ce kawai irin ta Hateem

     

"Namanta ban tambayeka ba, wani kalar abinci kake son ci"? Shiru yai masa, hakan yasa shi yamutsa fuska "Okey,Tun da baka iya yi min magana kar6i waya ka rubuta min ta text message sai in karanta" ya faɗa tare da miƙe ma danish wayar, baiyi tsammanin zai kar6a ba, sai gani yayi yasa hannu ya kar6a, Ya soma daddanata, Wani irin dadine ya lullu6e hateem, abun mamaki ya dauki lokaci yana yi mashi dogon typing har mamaki ya kama Hateem sai da ya mula yasha iska tukunna Ya miƙa ma Hateem wayar, Cike da zumuɗi ya kar6a don ganin me ya rubuta mashi

Har saida gabanshi ya ɗan faɗi ganin jagwalgwalon da danish ya rubuta mashi, irin wanda yara sukeyi idan suka damƙi waya.


da sauri ya dago suka haɗa ido da juna, baisan sa'adda dariya ta kubce mashi ba, ya dinga 6a66aka dariya har fararen hakoransa suka bayyana masu kyan gaske.


    Shi duk a tunaninshi dagangan Danish ya rubuta masa jagwalgwalo awaya, alhalin shi baisan amfanin wayar ba, Shi bai ma ta6a ganin waya ba sai da suka shigo duniyar mutane, sannan bata ta6a zuwa hannunsa ba, yadai san ana daddanata da yatsun hannu shiyasa ya kar6a ya yi mashi abun da zai iya.


"Please meke damunka ne"? Bayan Ya tsagaita da yin dariyar ne yayi mashi maganar, shiru yayi bai tanka mashi ba.


Yanke shawarar kiran Chief Owais yayi saboda ya tambaye shi dangane da Danish don kada a samu matsala tun da shi baisan ya rayuwarshi take ba, yana son yaji ko kurma ne.


Bugu uku Chief yayi picking call din


"Uncle yanzu nake shirin kiranka, Don inji ko lafiya"?


 "Owais baisan ya zanyi da shi ba, dama ka fada min yana da wuyar sha'ani, wallahi tun ɗazu yaƙi yi min magana sai dai kallona da yake ta yi, na rasa gane kanshi, har waya na bashi don ya rubuta min abunda yake son ci amma a karshe sai ma ya rubuta min jagwalgwalo, Ko dai kurma ne"? 


muryarshi tamkar zai fashe da kuka yayi maganar.


 Da buɗar bakin chief sai cewa yayi"ina fata akwai sojoji a kewaye da ku"? ya fadi hakanne gudun kada lalurar Danish ta motsa musamman yanzu da yaji halin da suke a ciki.


"Babu, Mu kaɗaine"!


"Uncle ka sanya sojoji su yi maku ƙawanya saboda yaron ba shi ɗaya bane, bana so asamu matsala" 


"In sha Allah ba za'a samu matsala ba, kafin mu zauna nayi mana addu'a, kuma nayi imanin babu abun da zai cutar da ni ko shi bi'iznillahi" da kwarin gwiwa prime minister yayi maganar


Yana iya jiyo sautin ajiyar zuciyar owais.


"Uncle, ba kurma ba ne, abun da nake so da kai, ka ɗauka tamkar Jiriri ne sabon haihuwa, saboda bai son komai ba, wayar da ka bashi baisan amfanin ta ba, please ka bashi kulawa yadda ya dace sannan ka ƙara haƙuri da shi, A hankali zai fara sakewa" amsa mashi yai toh, kafin yai katse kiran.


Danish nata kallon sa bayan ya gama, har zai kira don a kawo masu abinci, ya jiyo motsin tafiyar mutane da sauri yakai idanunshi kansu, Hadimai ne su biyu sanye da uniform na ma'aikatan gidan, kowaccensu hannayenta na a ruƙe da faffaɗan faranti, daga saman su anjera kayan abinci nau'i daban daban, wannan ba aikin kowa bane face Gimbiya mujeedat, itace tayi tunanin zasu buƙaci abinci shiyasa tayi saurin kiran landline na gidan ta isar da sakon a kawo masu abinci.


Ya ɗanyi mamakin ganin su da abinci, bayan bashi ya bada umarnin su kawo ma su ba, kwata kwata baisan da zaman gimbiya mujeedat da yazrin ba, har yanzu bai gan su ba, saboda bai son sun biyo su ba. 


Cikin girmamawa hadiman suka russina har suna hada baki wurin furta"sannu da hutawa yalla6ai" suna magana suna satar kallon danish kamar kwayan idanunsu zasu faɗo ƙasa.


 "Wanene ya bada iznin a kawo mana abinci"?


 Da sauri sukace"umarni ne daga wurin gimbiya mujeedat"! nuna masu tsakiyar shimfiɗar yayi, anan suka ajiye masu kayan abincin kafin suka juya zasu bar garden din suna tafiya suna waiwayon Danish har da tuntu6en su tsabar gulma da kitsibibi.


ta riga tasan halin hateem bai cika yarda ba, hakan yasa ta tura mashi tezt message.


  _I ordered them to bring you food because I was worried about you, tun da muka shiga dinner hall baka ci komai ba_

 

Murmushine dauke akan fuskarshi bayan ya gama karanta sakon nata, yai mata reply da cewa"Nagode Gimbiyata"


Tuni ƙamshin soye soyen da aka kawo masu ya buɗe hancinansu, shi kanshi danish din yunwa yake ji, tamkar baici abinci ba.


Farantin farko yana dauke da banƙararrun kaji anyi masu jar suya sai maiƙo sukeyi, ga tsiren nama daban kuma, yaji kayan lambu dana kamshi, ga wasu luxury warmers daga gani abinci ne a cikin su, ɗayan tray din Glasses ne da ke dauke da exotic sodas Fresh coconut water, premiun juices and coconut milk, sun haɗo masu da silverware and tissue box duk wani abu dai da zasu buƙata......


'Bismilla me zamu fara ci ko in za6a mana"? Cikin kulawa yayi maganar yana duban danish dake ta faman haɗiyar yawu.


Bai jira amsar shi ba, Ya zuba masu sakwara with egusi soup, taji uban naman ganda manyan yanka ta dahu tu6us.


      Ya lura bai da alamar ci, Hakan yasashi yanke shawarar bashi abaki,. 


Wanke hannunsa yayi a bowl kafin ya zura shi a plate din ya debo sakwarar da miya yakai mashi saitin bakin shi, bai yi tsammanin zai ci ba, ganin ya damtse bakinsa can kuma ya ɗan buɗe kananun la66ansa a hankali hateem ya sanya mashi abaki, yadda yake tauna tamkar baisan ci nan da nan ya haɗiye, cigaba da bashi yayi abaki yana ci, kamar wani karamin yaro, shi kuwa hateem dadi yake ji yana bashi abinci yana ci, Ba zato ba tsammani yaga danish ya sanya hannun shi ya ɗebo sakwarar ya miƙa mashi don yaci shi ma, yaga tun dazu yake ta bashi shi baici ba...


Wani irin sanyi ne ya ratsa zuciyar Hateem, bakomai ne ya faɗo masa a ransa ba, face maganar Owais da yace yaci gaba da bashi kulawa a hankai zai saba da shi, tabbas kuwa hakane.


  Buɗe baki yayi danish ya sanya mashi ya soma ci, yayin da suke kallon juna, tuni yaji hawaye sun cika idanunshi sai dai bai bari sun zubar masa ba, da sauri yayi kokarin danne su...


 Cigaba da bama juna abinci su kayi, su gimbiya mujeedat dake kallon su ita da yazrin, murmushi ne ɗauke akan fuskokinsu, tsabar Jin dadin yanayi yasa suka samu wuri saman wasu kujerun shan iska suka zauna...


Bayan sun gama da plate din sakwarar,  Tsiran naman suka fara ci, Idan ya bashi shima sai ya bashi abaki, suna ci suna kallon juna.


 Saboda tsantsagwaran kauna da zarar abincin ya 6ata ma danish gefen bakinsa da sauri yake cirar tissue ya goge masa bakinsa, daga shi har danish din sun jima basu ji abinci mai yawan gaske ba irin nayau, kusan rabi da kwatar abincin saida suka cinye shi, bayan sun gama suka koma suna shan   coconut milk da fresh juice.


Sauke farantan hateem yayi can gefe ɗaya ƙasa, kafin ya mayar da hankalinsa akan danish, rungumo shi yayi ajikinshi, hannun shi ɗaya dafe da bayan shi, ɗayan hannun yana ruke da wayar shi, Camera ya shiga don ya yi masu hotuna ko ya samu waɗanda zai dinga gani yana ɗebe kewarsa, da sauri Danish ya runtse idanunsa alamar baya so, kokari yake ya buge wayar gaba ɗaya hakan ba karamin ɗaga hankalin hateem yayi ba, cikin sanyin murya ya furta"pls ka bari nayi mana hoto mana, inaso na samu wanda zan dinga kallo bayan na koma ƙasa ta," cikin sigar lallashi yake yi mashi magana akan ya buɗe idanunsa, dakyar ya samu ya ɗan buɗe su, maimakon ya kalli camera din sai ya dinga kallon fuskar hateem din, babu yadda baiyi dashi ba akan ya kalli camera amma yaƙiya kamar wani karamin yaro, A haka hateem yadinga daukarsu hotuna idanun danish akan fuskarshi, wasu hotunan ya rufe idanunsa, hada video yayi masu mai ɗan tsayi, ya kwantar masa da kanshi saman kafadarsa, da wanda ya sumbaci forehead dinsa, kamar wani ɗan cikinsa, A kalla ya dauki hotunansu sunkai Talatin, bayan video da yayi masu kusan goma.


Kafin ya gama ɗauke ɗauken hotunan, kwatsam Yaji danish Ya ƙanƙame shi da hannayensa da farko ya ɗan ji fargaba amma daga bisani da yaga yana lumshe idanunsa sai yaji hankalin ya kwanta, wani baccine mai daɗi yayi awon gaba dashi, kanshi asaman shoulder din hateem, A hankali Ya gyara mashi kwanciyarshi, ya rungumo sa, kamar zai maidashi cikin shi, hannayen danish na abayan hateem ya ƙanƙamesa kamar wani yace zai ƙwace masa shi.


Wani kallon so da kauna hateem yake binsa dashi yayin dayake yin baccin, A hankali ya soma shafa bayan shi da yatsun hannayensa kafin ya zura hannun cikin sumar kansa tamkar yanayi mashi susa, harta numfashin danish sai da ya canza saboda daɗin da yaji na abunda Hateem ke yi ma sa.


Bakinsa yakai saitin kunnan danish, cikin muryar raɗa yayi mashi magana.


 "Do you feel what I feel about you?" 


Ya faɗi hakan batare daya sanya ran danish zai tanka masa ba, a tunaninsa yayi zurfi a baccin nasa.


   Kamar daga saman yajiyo daddaɗar muryarsa tamkar ana busa sarewa ta ratsa kunnansa da cewa "Yes, I do. I feel more than you might think" 


wayyo Allah dadi prime minister tamkar zai zauce tsabar murna da jin maganar danish, Cigaba da kallon fuskarsa yayi tamkar zai haɗiye sa.


  "Nakasa yarda cewa kaine kayi min magana da bakin ka, ko dai kunnuwana ne suke jiyo min ba dai dai ba"? da biyu ya fadi hakan saboda yana son ya ƙara jin muryar shi.


"No, ni na maka magana" danish ya bashi amsa idanunsa a rufe, har time din basu raba jikin su daga na juna ba


     "Meyasa ka damu dani"? Danish ne ya jefa mashi tambayar

Murmushi hateem yayi kafin ya furta"tun lokacin da nafara Yin tozali dakai, Naji na kamu da matsananciyar kaunarka, duk da bansan wanene kai ba, amma naji ka kwanta min araina, ka sace min zuciyata, babban abinda yafi jan hankalina gare ka shine kama da muke da juna, Ina jinka tamkar ni na haifeka, Allah ne kadai yasan son da nake maka Danish, wallahi bana son rabuwa dakai, bana son in tafi in barka, don bani da yarda zaniyi da natafi da kai" Kalaman da yake furtawa daga cikin zuciyarsa suke fitowa, abunda ke ransa ne yake bayyana masa ko ya rage radadin da yake ji na kaunarsa .


A hankali danish ya ɗan buɗe idanunsa yana satar kallon fuskar hateem dake a dab da tashi, wani irin kallo yake jifar shi da shi mai wuyar fassaruwa batare da prime minister Ya ankara ba.


  "Bansan su wanene Iyayenka ba, bansan dalilin dayasa sukayi watsi da rayuwarka ba, amma bana tsammanin akwai wanda zai samu ɗa kamarka ya jefar sai dai idan da wani dalilin"


  Runtse ido danish yayi sam baya son anayi mashi maganar iyayen sa.


  Muryarshi na dan rawa ya furta"ka daina yi min magana akan iyayena, bana son su bana son duk wani abu daya shafe su, If I could see them, I would kill them." 


 A ruɗe prime minister ya dubi fuskar danish da tsantsar mamakin yadda kalaman suka fito daga bakinsa, har kokwanto yayi anya shi yayi maganar?


  Ko da yai yunkurin tambayarshi meyasa yace haka, sai jinshi yayi shiru alamar wani baccin ya dauke shi....

Haƙiƙa furuncin da ya yi akan iyayen su sun tada masa hankali, sun tsaya masa a ƙahon zuciyarsa, duk da baisan dalili ba amma yaji fargaba aransa, musamman da ya ambaci Idan ya gansu zai kashe su .......

Lumshe idanunsa yayi, tare da ƙara janyo danish ajikinshi, yaci gaba da ɗan bubbuga bayansa kamar mai lallashin ƙaramin yaro a haka harshima baccin yayi awon gaba dashi, wata irin iskace mai ni'ima taci gaba da kaɗa wurin da suke.......


gaba ɗaya abun da ke faruwa akan idanun Yazrin, sai dai basu samu damar jin komai da suke tattaunawa ba atsakanin su saboda akwai tazara.


Nannauyar ajiyar zuciya Gimbiya mujeedat ta sauke tare da kallon Yazrin dake a gefenta"gwanin ban sha'awa, sun burgeni,  a yadda suka kwanta kamar Uba da ɗansa, ban ta6a jin zafin rashin ɗa bamiji ba sai ayau dana kalli Hateem da yaron nan, wallahi sunyi min kyau sun tafi da imanina ......." Cikin sanyin murya Gimbiya mujeedat tayi maganar.


  Jikin Yazrin yayi sanyi lakwas tamkar wadda aka zarewa laka, idanunta sun ciko tab da kwalla ta soma magana ba tare data janye idanunta daga kan shimfiɗarsu Hateem ba.


 "Daddy ya bani tausayi, na tausaya masa mommy, daga shi har matashin nan, Ina kaunarsa Ina jinshi kamar ɗan uwana na jini... " da raunatacciyar murya tayi maganar.


 "Mommy abun da yafi ta6a zuciyana, yaran ba su da kowa a daji aka tsince su kamar yarda naji akhi owais Ya faɗa, wallahi banji dadin yadda Su oum saratu suke jifarsu da munana kalamai ba, ni abun da ya daure min kai Yaran sunyi kama da family din daddy sosai"



Jinjina kai Gimbiya mujeedat tayi ba tare da ta iya furta komai ba, Ta yunƙura ta miƙe Cikin takun nutsuwa Ta nufi shimfidar su hateem, Yazrin na zaune bata bi bayanta ba, bakomai zuciyarta ke tariyo mata ba, face lokacin data haifi baby boy din su da suka rasa, haƙiƙa taji bakin cikin da bata samu damar ganin ko da gawarsa bane, taso ace ko da fuskarsa ne ta gani, tuna wannan yasa taji hawaye sun taru cikin idanuwanta


 Adai dai bakin shimfiɗar ta ɗan zuƙunna tana kallon danish from head to toe, yayin da zuciyarta ke azalzalarta da kaunarsa, sai kallon shi takeyi babu kyaftawa, ranta ne ya raya mata wani abu da bata da tabbaci akanshi, hakanan taji tana son ta jaraba gwadawa, Miƙewa tayi da sauri ta zagaya ta dayan bangaren da farantan abincin da aka kawo masu suke, ta zaro ƙaramar wuƙa ta yanka fruit, ta dawo bangaren inda danish Yake ta zuƙunna duk akan idon Yazrin da mamaki yagama cikata, zuciya da sake sake arude ta furta me mommy zatayi wuƙa"? hankalin ta yadan tashi tsoron ta kada ta aikata wani abu duk da tasan hasashenta bazai ta6a zama gaskiya ba...


A hankali ta ɗaura ziraran yatsun hannunta kan sumar danish ta ruƙo ƙasanta, Cike da fargaban kada su farka, tana yi tana kallon fuskokinsu cikin kwanciyar hakali suke fitar da numfashinsu, bacci yayi dadi


Yatsun hannunta na kerma ta yanki sumar kan danish da wuƙar, ajiyar zuciya ta sauke tare da miƙewa ta mayar da wukar cikin kayan abincin kafin ta juya tana faman sauke ajiyar zuciya ta nufi Yazrin tunkafin ta ƙarasa yazrin ta miƙe tana tana fadin"mommy! Meyasa kika datsar mashi gashin kai"! Idanunta azare ta fada tana nuna ziraziran gashin danish da gimbiya mujeedat ta cira daga kanshi


Fuskarta dauke da murmushi tace "Ki kwantar da hankalin ki, kinsan dai mom dinki ba matsafiya bace," dariya yazrin tayi"ina kyautata maki zato a koda yaushe Rabin raina" lumshe ido gimbiya mujeedat tayi"ki ajiye min gashin nan a wurinki, Idan muka koma gida zan tambaye ki shi" da sauri Yazrin ta kar6i gashin daga hannun mom mujeedat,  ta cire cover din wayarta ta ɗaura gashin abayan wayan kafin ta mayar da cover din sosai ta  matse shi ta yadda bazai ta6a faɗowa ƙasa ba.


"Yanzu ki zo mu koma dinner hall, kada aji shiru babu ni babu hateem bayan saboda mu akayi taron" amsa mata yazrin tayi da toh" a jere suka nufi hanyar fita daga garden din, suna tafiya Yazrin na waiwayon shinfidar su danish, har saida ta 6ace ma ganinta tukunna ta dauke idanunta daga gare shi. 


*Dinner Hall*


Bayan zahra ta kammala yin wayar, Jiki na rawa ta dawo Ciki tana nema unaisah, kamar zata zauce sai ƴan waige waige take yi babu ita babu alamarta,  kusan sau uku tana zagaye tsakar hall din wurin neman unaisah amma babu ita, zuciyarta ba ƙaramar karaya tayi ba, Har cikin ranta bata ji dadi ba, saboda taso su sake ganawa da juna, Yarinyar ce ta kwanta mata aranta, musamman yadda ta sakar mata fuska har ta amince mata su kayi hutuna, dabara ce ta faɗo mata, ganin ɗaya daga cikin matasan ƴan matan a tsaye tana kallon masu yin rawa akan dance floor sai murmushi take saki, da sauri Zahra ta nufe ta, muryarta da sanyi ta furta"sannu baiwar Allah" firgigit batool ta dubeta da alama ta razana don bata tsammaci jin muryar wani a kusa da ita ba 


"Kiyi haƙuri na baki tsoro ko"? da fara'a zahra tayi mata maganar, batool kuwa sai kallon bakuwar fuskar takeyi taƙi tanka mata, gani take kamar zata cutar da ita ne tun da ta fahimci basa son su


Miƙa mata hannu zahra tayi"ni suna zahra, ke fa"? Cike da rashin yarda ta furta"batool" muryarta da ɗan rawa tayi maganar, ba tare da ta ɗaura hannunta asaman na zahra ba, nan take zahra ta fahinci tsoron ta take ji hakan yasa tace"ki kwantar da hankali yar uwata, Bana ɗaya daga cikin waɗanda suka ci muku mutunci ɗazu...." still bata saki fuskarta ba


"Shikenan, yanzu ki faɗa min ina ƴar uwarku Unaisah? Muna cikin magana da ita ɗazu aka kirani awaya sai naje amsa kiran kafin nadawo na taras bata nan, Ko kinsan inda take"!?


Sai da ta ambaci sunan Unaisah batool tafara kyafkyafta idanunta tana bin dakin taron da kallo, sai yanzu ta tuna da tsawon lokacin da bata ga gifcin unaisah ba, kuma bata cikin masu yin rawa, nan fa hankalin Batool Ya fara tashi ta fara ƴan waige waige fuskarta a yamutse babu nutsuwa


Ganin yadda ta ɗaga hankalinta ne yasa Zahra cewa"ko kema bakisan inda taje bane" ɗaga mata kai batool tayi muryarta adabarbace ta furta"ban..bansani ba, bamu jima da rabuwa da juna ba, atare muke zaune  can mu da su chief kafin tashin ta" ta fada Tana nuna mata wurin..


Ruƙo hannun batool zahra tayi "zo muje mu nemo ta," da sauri batool tabi zahra suka soma bi sako da lungu na hall din suna neman Unaisah, ba tare da sun fada ma kowa ba ...


____________________________💋✍️



Jin ta ruƙo hannunshi yasa shi yin sauri fusgewa Yana bin ta da kallo mai cike da fargaba


Jikinshi har kerma yake yi saboda matar bata kwanta mashi aran shi ba, 


Murmushi ta ɗan sakarmashi cike da fargabansa ta furta"kayi haƙuri dan Allah, bawani abu zanyi maka ba, Inaso mu yi hoto ne" ta fada tana nuna masa i phone din hannunta, maƙe mata kafaɗa naufal yayi muryarshi da yar tsiwa tamkar zai fashe da kuka yace"banso, Ni ki ƙyale ni, kuma wallahi ki daina kallona," Ranshi a6ace yayi maganar, arude hajjaty ta soma lallashin shi gudun kada ya janyo hankalin mutane gare su.


 "Dan Allah ka yi hakuri, Idan na bata maka rai, alfarma ɗaya nake nema a wurinka, Ka fada min sunanka"?


Harara naufal ya wurga mata, Yana faman haɗe rai yace"sunana Sajeed"


Tuni yanayin fuskarta ya canza, tayi zaton zataji irin sunan ɗanta,

Gyaɗa kai tayi"masha Allah, Allah yayiwa rayuwarka albarka, amma baka ga muna kama da juna ba"? ta faɗa da fara'a akan fuskarta, Ta6e baki naufal yayi alamar ta takura masa hada ɗan bubbuga kafafunsa"Ni bani kama dake, bansanki ba, dan Allah ki ƙyale ni, In shaƙi iska" yanayin yadda yayi maganar yaso bata dariya, 

"Naji zan ƙyaleka, ka shaƙi iska but pls ka bari na dauki hoto dakai"!

Juya mata ƙeya yayi atakure yace"sai dai ki ɗauki bayana" dariya tayi sosai tana kallon bayan shi.

   "Kaga dan Allah ka juyo na dauki fuskarka, Ita nakeson gani, Harma In nunawa Mijina shima yaga mai kama dani" maƙe mata kafaɗa naufal yayi alamar a'a.

 Magiya tadinga yi mashi amma yaƙi juyawa, ta rasa ya zatayi da shi.


Sajeed da ke ta kallon su, baisan me suke tattaunawa ba, A hankali Ya nufo su, 

   "Bro, meke faru ne"? Ya faɗa yana kalon fuskarshi dake a daure

 Da yatsan hannu ya nuna mashi hajjaty dake abayn shi"matar nan ce ta ɗazu da take ta kalllona, shine ta biyu ni wai dole sai ta dauke ni hoto ni kuma nace mata bana so" 


  Ɗagowa naufal yayi su ka haɗa ido da Hajjaty, harta bude baki zatayi mashi magana sai kuma ta fasa, saboda ganin suffar Sajeed kamar zaifi naufal din taurin kai, a tunaninta amma ga mamakinta sai ji tayi yace mashi"to meye aciki? Ba hoto kawai ta buƙata ba"? Ɗaga mashi kai naufal yai, Ruƙo hannunshi sajeed yayi" dallah juya kaje ku ɗauki hoton, In ba haka ba bazan ƙara taimaka ba wurin koya maka karatu" ba don yaso ba, ya juya yana jifar hajjaty da harara kwayar idanunsa kamar zasu faɗo ƙasa, 

"Nagode sosai, Kai meye sunanka"? fuskarta dauke da murmushi ta tambayi Sajeed, Kafin yai yunkurin bata amsa naufal yai sautin cewa Sunan shi Naufal, Wani kallo Sajeed Yayi mashi da ruɗani akan fuskarsa jin Ya canza mshi suna, da ido yai mashi alamar da nan take ya gane me yake nufi wato Ya faɗa mata sunan sa amatsayin nashi, shine yace shi sunansa Naufal


Jim ta ɗanyi har cikin zuciyarta sunan ya dake ta, Taso ace mai kama da itan ne yake da suna Naufal sai dai kash shi sunan shi Sajeed.


"Kawo wayar nayi maku hoton" da sauri ta miƙa ma sajeed wayar ya kar6a, ya soma daukarsu hoto, Hada kokarin Jan naufal Ya matsar dashi jikin hajjaty gaba ɗaya ya takura mashi, duka hotunan sunyi bala'en kyau kamar ɗan ta, sai dai fa babu fara'a akan fuskar naufal  har ya kammala daukar su, hajjaty ta kar6i wayar tana yi masu godiya.


Suma su jamimah anyi masu hotuna tare da Sir mubarak da Mom turai, harta su Zaki sai da su kayi hotuna da su, kamar ƴan uwan juna.


Haka zalika Su Haris da Javed suma hada su akayi hotunan, kowa ya yi kyau ana ta kwasar shagali.


Hajiya saratu dake ta faman satar  kallon parveen duk in da tayi akan idonta, ta sanya mata ido sosai, tsabar ji da kai ne ya hana ta nemi alfarmar ta su dauki hoto atare, sai ta koma tana daukarta a fakaice da wayar hannun ta ba tare da ta ankara ba.


Hankalin Batool ba karamin tashi yayi ba, Ko'ina sun duba ita da zahra babu Unaisah, Jikin ta har Ya fara kerma tsabar tashin Hankali, sune har wajen hall din neman Unaisah, Dawowa ciki su kayi cike da fargaba, can zahra ta tuna da akwai restrooms a dakin taron,  ajiyar zuciya ta sauke tare da kallon batul tace su ɗan jirata, watakil ta shiga toilet ne, zama sukayi a table daya ita da batool suna jiran unaisah ta fito.. ..



*Chief Owai*



A tsaye yake a wani area dake a hall din, Ya juya bayansa, hannunsa ɗaya ruke da phone dinsa yayin da dayan hannun ya zuba sa a trouser pocket dinsa, bai jima da kammala yin wayar da ta yi silar tada sa daga wurin zaman sa ba.

   

 Layin boss Ya danna ma kira bugu ɗaya yayi picking.


    Muryarsa ƙasa ƙasa tamkar ta me yin raɗa ya furta" ina fata ka same su lafiya"? 


 On the other hand muryar boss ta karade kunnansa"tun dazu na shigo gidan, suna nan cikin koshin lafiya yalla6ai, yanzu haka ina atare da salsabeel sai fada yake min wai jiya hankalinsa ba akwance yake ba, sun ji shiru Dr jazz bai leƙo su ba, sannan mu ma bamu kira ba kamar yadda muka sama"


  Daga can cikin wayar yajiyo muryar salsabeel yana fadin"ka fada masa jiya ko isasshen bacci ban samu ba, deeja ta hanamu sukuni daga ni har ƴan uwanta daƙyar na samu yarinyar nan tayi bacci".


   Lumshe ido yayi ahankali Ya furta" Please tell him I'm sorry. It won't happen again. We were busy with dinner preparations yesterday. in sha Allah, cikin kwanan nan zasu baro anguwar nan su dawo cikin ƴan uwan su"


   Taj yace"amma naji dadi Yalla6ai, saboda bani da burin daya wuce inga an haɗa kan yaran nan, su gana da ƴan uwansu, hankalin su sai yafi kwanciya"


   Sun ɗan jima suna yin wayar, kafin daga bisani su ka yi sallama, tunkafin ya sauke wayar daga kunnansa daddaɗan ƙamshin turarenta ya daki hancinsa har sai da lumshe idanunsa saboda yadda fragrance din Ya ratsa shi, tuni ranshi ya bashi cewar itace  saboda haddar turarenta da yayi


Shiru yayi batare daya juya sun fuskanci juna ba, sai ma ya ci gaba da danna wayarsa.


Sautin tarin ta da yaji ne yasa shi saurin juyawa yakai idanunsa saitin inda take, hannunta ɗaya dafe da gefen cikin ta, ɗayan hannun kuma yana ruƙe da Mayafinta da ya zame, lallausar sumar kanta ta lullu6e bayanta baƙa wulik da ita, babu alamun tasan da zaman shi a wurin, yanayin ta kamar bata a hayyacin ta, ganin tana kokarin faɗuwa kan fillow yasa shi yin saurin nufarta, ya sanya hannu ya janyota gaba ɗaya ta fada kan broad chest dinsa, luf ta kwanta masa, ta daddafe waist dinsa da hannunta, yana iya juyo fitar numfashin ta da sauri da sauri, hankalinsa ba karamin tashi yayi ba.


   "Nazli! Are you okay? What's wrong? Are you alright?" a ɗan ruɗe ya yi maganar.


   Ƙara ƙanƙameshi tayi muryarta da wani irin sanyi da zaƙi ta furta"bana jin daɗi, kaina da ciki na ciwo su ke min, sannan bana son hayaniya, kwata kwata bana son zama awurin nan" yanayin yadda take yin maganar ba karamin narkar masa da zuciya yayi ba, ƙamshin turarenta ya kanainayesa.


   "Bana son zama anan, rikicewa nakeyi" cikin wani irin salo take maganar, Nazli karshe ce, babu namijin da zai haɗa jiki da ita batare dayaji sauyi atare da shi ba, koda kuwa zuciyarsa dutse ce.


  bakomai yasa shi yadda da kalamanta ba, face sanin lalurarta na rashin son hayaniya, tun da kuruciyarta, daga bayane ta samu sauƙi bayada likitoci suka tsaya tsayin daka don ganin ta dawo normal, tunaninsa abunne ya dawo mata yan zu shiyasa ya aminta da ita......


Yanke shawarar fita yayi da ita daga hall din kota samu lafiyar jikin ta,


"It's okay, Let's go. I'll take you home and you can rest."


maƙe mashi kafaɗa tayi tana fadin"I can't walk. My legs hurt."


Kallon takalman kafarta yayi wasu matsiyatan high hills ne masu tsini na fitar shariya, irin takalman da tafi sha'awar sanyawa kenan, mafi yawan lokutta suna jaza mata ciwon ƙafa, sai da ya fara duddubawa ya tabbatar babu mai kallon su, kafin ya sanya hannu ya ɗauketa gaba ɗayanta Ya nufi second door da ake fita hall din bai bi ta ainihin kofar fita ba, don bayason wani yagansu.


Bayan sun fita, yayiwa ɗaya daga cikin sojojin dake tsaron ƙofar magana akan ya kawo mashi motarsa, bayan ya miƙa masa key, jim kadai sai gashi ya kawo motar, ya fito tare da buɗe masu, a backseat ya shigar da Nazli, sai faman lumshe idanunta takeyi masu kama dana ɗawisu saboda kyau


Cikin kulawa yace"Calm down, He will take you home."

ya fada yana nuna mata sojan daya kawo masa motar, girgiza mashi kai tayi da wata irin kasalalliyar murya tace"I want you to take me. Don't you have time for me?" She bit her soft, pinkish lips.


   "Tomorrow, I will leave the country. I am not sure if we will meet again," 


 her words touching his heart deeply sai yaji kamar bai kyauta mata ba, a matsayin ta na yar uwarsa rabin ransa kuma jinin jikinsa.


 Bai gama yanke shawara da zuciyarsa ba, Yaji ta ruƙo hannunsa baisan sa'adda Ya shige cikin motar ba, sojan da zaiyi driving dinsu Yai wa motar key,  driving slowly suka miki hanyar zuwa gidan prime minister.


  A lokacin da baiyi tsammani ba, yaji ta ɗaura kanta saman broad shouder dinsa, ta ruƙo yatsun hannayenta a cikin nashi, wani irin sanyi sanyi ne ya ratsa zukatan su, Tsawon Lokaci basa kula juna till to day.


   Ranta ne ya bata cewar yana kallon ta, A hankali ta dago da sexy eyes dinta akan fuskarsa karaf suka shiga cikin nashi, cigaba da kallon juna su kayi babu alamun gajiya.



_Unexpectedly, she planted a kiss on his chin. He closed his eyes for a moment, put one hand on her hair, and slowly put his smooth lips on her forehead, gently pecking it._


_Gaba ɗaya sun shiga yanayi, sai dai fa duk da haka babu fara'a akan fuskokin su kamar basa son kasancewa da juna, bayan motar ta isa gidan, bata bari chief ya kubce mata ba, don ta fahimci hankalinsa na akan dinner hall kuma tasan bai wuci saboda yarinyar nan ba, jan shi tayi da ƙaryar ciwo da kisisina har ta samu yabita Part din ta don taji dadin ruƙe sa kamar yadda faryat ta tsara mata.........👀_




  



*Daga Alƙalamin Boss Bature💋✊✍️*




 *Littafin kurkukun ƙaddara 500 ne, dukanshi Book One two and 3 Idan kin shirya biya ga Details da zaki tura*


3196407426


First bank 


Bature Hafsat Muhammad,


 *bayan kin tura zaki bada transaction reciept ko screenshot na debit alert a matsayin shaida ta wannan layin 08169856268*

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post