Kurkukun Kaddara Takun Karshe Page 10 Complete


Health College

Kurkukun Kaddara Takun Karshe Page 10 Complete

 _ *~✊💋BOSSLADIESWRITERS💋✊~*_




سجن القدر💋✊🔥



~Takun Ƙarshe🔥~




قصة حب رومانسية غير عادية بين السجناء مع تطورات معقدة💋💘😘



An extraordinary romantic love story between prisoners with complex twists ❤💋💘




Daga alƙalamin Boss Bature💋✊




__________________________✍️





Har sai da gaban ummi ya fadi rass jin abun da yace, hatta shi kanshi taj aruɗe ya kalli fuskar shaikh imam.


 "Ya sheikh ko zan iya sanin dalilin da ya sa ka ce haka? Acewar Taj


Sheikh imam yace "Tun da nake zuwa gidan nan ban ta6a ganin ta taka zuwa ɗakin yaron nan ba, domin duba lafiyarshi, bansani ba ko tana shiga bayan bana nan amma raina na bani tamkar bata zuwa, a matsayinta na maruƙiyarsu yakamata ace tafi kowa bashi kyakkyawar kulawa ko da kuwa addu'a ne take zuwa tana yi mashi akai akai" tun da sheikh imam ya fara kora jawabi hankalin ta ya kwanta jikinta yai sanyi laƙwas.


  "sheikh maganarka gaskiya ne, ummi baki kyautawa, kinga har sheikh imam ya fahimci baki zuwa duba lafiyarki ɗan ki" ya faɗa yana kallon ta, murmushin gefen fuska ta saki, cikin sanyayyar murta tace "nagode sheikh da tunasarwa, na gane kuskure na kuma in sha Allah daga yanzu zan dinga zuwa duba shi'


  "Masha Allah, yanzu naji magana, bismillah malama ummi mu shiga ciki, kiyi mashi addu'a in gani" ta fahimci sheikh imam kamar ya gano wayanta nason ta gudu, shiyasa yake kokarin ruke ta.


    Babu yadda ta iya adole ta amince suka nufi cikin gidan atare tana mai jin wani irin sanyi aranta.


Bayan shigarsu ɗakin, kamar yarda suka barshi da asuba haka su ka taras da shi, babu abun da ya canza yana a kwance rabin jikin shi lullu6e da bargo, sumar kanshi an ɗaure mashi ita, ta kara tsayi har kusan mid back din sa, ga wani irin pure white da skin dinsa tayi har wani glowing ta ke yi, jikin ummi ba ƙaramin sanyi yayi ba, kasancewar yau ne rana ta farko da ta fara shigowa dakin danish, bata ta6a tsammanin jikin yayi tsauri har haka ba, kamar matacce babu abun da ke motsi a jikin sa.


   Tsananin tasauyin shi ne ya kama ta aranta ta ayyana wato duk kyan mutun bai isa ya hana kanshi ciwo ko mutuwa ba, jiki asanyaye ta matsa bakin gadon, sheikh imam da taj suna daga tsaye suna kallon shi, yanayin fuskokinsu ya nuna damuwa.


      Girgiza kai sheikh yayi cikin jimami ya furta"Ya Allah ga bawan ka nan, kafi mu sanin a wani hali yake a ciki, ya Allah ka sauƙaƙa mashi abun da ke damun shi, Ya Allah ka raba shi da shaidanun dake azabtar da rayuwar sa... cikin harshen larabci yaci gaba da karanto addu'o'i yana tottofa mashi, rashin lafiyar danish ba ƙaramin ɗaga mashi hankali yai ba, damuwarshi kada yaƙi tashi, duk da yayi imanin addu'o'in da yayi mashi, da sallar daren da yake yi mashi basu tafi hakanan ba, sai dai idan lokacin shi ne yayi.


  Cikin rauni na murya ummi ta furta"baya iya tashi"?

  Taj da jikin shi ya gama mutuwa laƙwas, Muryarshi babu karsashi ya bata amsa da cewa "baya iya yin komai, sai dai ayi mashi, ta hanya daya muke gane ya farka daga bacci, yatsun hannayensa dana ƙafafuwansa suke kerma"


  Jinjina kai ummi tayi, tare da kau da idanunta daga kallon Taj ta dubi sheikh imam adai dai lokacin shima ya dawo da dubanshi gare ta, haɗa ido su ka yi da juna duk saita rasa sukuninta kamar wata mara gaskiya.


  "Addu'arki yake buƙata a matsayinki na mahaifiyarsa" har sai da taji gabanta ya faɗi jin sheikh imam ya furta a matsayinta na mahaifiyarsa.

Ɗauke idanunta tayi daga kanshi, kafin ta dai daita nutsuwarta, ta ɗan ɗukar da kanta saitin inda Danish yake a kwance, cikin harshen larabci ta soma karanto addu'oi tana tottofa mashi, bayan ta gama ne ta ɗago  tare da kallon fuskar sheikh imam, tayi mamakin murmushin da ta gani ɗauke akan fuskarshi, sunnar da kanta tayi ƙasa saboda kwarjinin da yayi mata

   

  "Chief yana nan ko ya fita ne"? ya tambaya yana kallon Taj.


"Bayanan tun ɗazu da rana ya fita, yana a villa wurin daddynsa, Idan kana buƙatar yin magana zan iya kira maka shi"


  Girgiza kai sheikh imam yayi"a'a, dama na tambaya ne in ji ko yana nan"


"yanzu me yakamata mu yi sheikh"?


 "Naga har yanzu bai farka daga bacci ba, nasan dole akwai yunwa atattare da shi sannan yana buƙatar wanka, amma kada a tada shi idan har bashi ya farka da kan shi ba" amsa mashi taj yai da toh.


  "Ina sauran yaran su ke ne? Sun yi mashi addu'o'in da suka sa6a yi"? ya tambaya yana kallon Man.


     "tun da asuba rabon su da dakin, bansani ba ko sun ƙara leƙowa"


  "Inason ganin su gaba ɗayan su yanzu"


da sauri ummi ta ce"bari naje na kira su" dama neman hanyar da zata bar dakin take yi.


  Bayan fitarta daga ɗakin sheikh Imam ya ɗan haura saman gadon, tafin hannunsa ya ɗaura saman forehead din danish, ya fara jera addu'o'i na musamman yana tofe mashi jiki, tsawon lokacin kafin yacire tafin hannun ya maidashi kan saitin zuciyarshi, yaci gaba da yi mashi kira'ar alkur'ani mai girma, Taj dake kallon sheikh imam dake janyo kira'a ba karamin nutsuwa yaji ba a cikin zuciyarsa.


  Tun da ummi ta fito, a bakin kofar ɗakin ta la6e tana sauraron kira'ar sheikh imam mai ratsa zuciya, wasu irin zafafan hawayene suka cika mata idanunta, Jikinta har kerma yake yi, ga dukkan alamu akwai wani abu da yai silar jefa ta yanayin da take a ciki.


  Runtse idanunta tayi sosai, jin kukan na shirin kubce matane yasa tai saurin toshe bakinta da tafin hannunta, muryar ta na rawa ta furta 


"uhibuk kathiran ya 'abi har yanzu kai mahaifina ne ba abun da ya canza..."


Duk waɗannan sambatun da take yi, A kunnan Unaisah, wadda fitowarta kenan daga dakin su ta kamo hanyar zuwa dakin Danish don ta duba jikin shi, karaf taci karo da ummi ta runtse idanunta tana matsar kwalla.

 Muryarta da ruɗani ta furta"Aunty Ummi!" 

Furgigit ummi tay saurin buɗe idanunta wadanda suke ajike sharkaf sun kaɗa jawur


Ganin unaisah yasa tai saurin sanya tafukan hannayenta ta share hawayen dake karanyo mata


   "Aunty Ummi, yaushe kika shigo? Ina boss? Meyasa ki zubar da hawayen ki? Wani abu ya faru da danish dina ne..." hankalin ta atashe ta fada

Muryar ummi adisashe ta furta"bamu jima da shigowa ba, ni da boss tare da sheikh imam... " ta fada muryarta na ɗan rawa


 

"kada ki damu ba wani abu bane ya faru da ɗan uwanku, kawai naji tausayin shine ya kama ni, bansan ciwon nashi yakai har haka ba, naji haushin kaina da ban ta6a leƙowa domin duba lafiyar shi ba, yau da naganshi jikina yayi sanyi shiyasa kika ganni awaje ina sharar hawaye... ' wannan maganar da ummi ta furta tayi matuƙar karya ma Unaisah zuciya, idanunta tuni sun cicciko tab da kwalla, ganin hakan yasa ummi tayi saurin furta"dan Allah kada ki yi kuka, addu'armu yake buƙata A halin Yanzu"

 duƙar dakai ƙasa unaisah tayi, jiki asanyaye tace"bari na shiga in duba shi"

   ta faɗa tare da buɗe kofar tasa kai ta shige ciki, bayan shigarta Ummi ta sauko down stairs don ta kira su Haris kamar yadda sheikh Ya buƙata.


 Kafin wani lokaci gaba ɗayansu sun hallara a dakin danish, kowannansu ka kalla babu walwala, tsantsar damuwace akan fuskokin su.


  Ɗaya bayan ɗaya sheikh imam yake dubansu har sun yi shirin kwanciya bacci, kowannansu yana asanya da sleeping dress dinsa, kafin ya soma magana cikin sanyayyar muryarshi

   "Ku naso ɗan uwanku Ya samu lafiya"! har suna haɗa baki wurin furta eh

  "To ku dage da yi mashi addu'a, Ita yake buƙata daga gare ku, nasan kunayi to ku ƙara abisa wadda ku ke yi mashi, Kunga har yanzu mun rasa gane yanayin da yake aciki, yau jikin shi yayi tsauri fiye da kullum, tun safe babu alamun zai farka daga wannan dogon baccin da yake yi, shi kadai yasan me yake ji a jikin shi, addu'a da kuke gani takobin mumine ce da itane zamu yaƙi shaidanun dake sarrafa shi, kullum suna aiki akanshi, safe da dare, why mu bazamu iya tsayawa tsayin daka wurin ganin mun ruguza shirin su ba! Mu da ma mu kayi imani da Allah balle su da su ke mushirikai.... ' tun da sheikh imam ya fara yi masu magana suka nutsu suna sauraron shi, sun kewaye gadon da danish yake a kwance, kokari yakeyi ya tunzurasu donsu harzuƙa su kuma dage damtse wurin yi mashi addu'a, duk maganganun da sheikh imam keyi a kunan ummi da ke a la6e bakin ƙofar dakin tana sauraronsu.


   Sautin shessheƙar kukan unaisah ne ya soma karaɗe dakin, kamar jira sukeyi tafara kuka, Jemimah da azeeza suka fashe da kuka, suma sauran kowannansu kwalla ce a idanunsa.


 "Ba kuka yakamata kuyi mashi ba, kamar yarda na fada maku addu'arku yake buƙata, A cikin ku akwai wanda ke tashi yin sallar dare domin yi mashi addu'a akan Allah ya bashi lafiya"?


 Shiru su ka yi, saboda basu da amsar da zasu bashi, unaisah dake faman zubda kwalla muryarta a raunace ta furta"ina yi mashi, amma ba kullum ba, wani lokacin kona kwanta da niyar tashi inyi mashi bana farkawa, saboda bani da me tada ni"


 "Ni bansan yadda akeyi ba, da ace na sani har bacci zan iya hana kaina don inyi mashi addu'a, saboda danish yayi mana abin da bazamu ta6a mantawa ba, ya cancanci mu sadaukar da komai akanshi" cikin sanyin murya batool ta ƙare maganar, taj da sheikh iman sun nutsu suna sauraronsu haɗi da kallon la66an duk wanda yayi magana a cikin su.

 Cikin shessheƙar kuka jemimah tace"wallahi nima zanyi ma shi, saboda bana so Danish ɗin mu ya mutu kamar yadda na rasa Majnoon ɗina...." wannan maganar ta jemimah taja hankalin sheikh imam da taj sosai akanta, ta dage sai ku ka ta ke yi, kumatunta har sun yi ja, ruko hannunta sheikh imam yai tare da lallashin ta akan ta daina ku ka.


 Hanna dake matsar kwalla ta ce"In sha Allah babu abun da zai same shi, zamu yi iyakar bakin kokarin mu don ganin mun ceto rayuwar ɗan uwan mu da iznin Allah..." daƙyar ta ƙare maganar


    "In sha Allah daga daren yau zan fara  yin mashi nafilfili, ni saima naji haushin kaina, bamu kyauta ba, har zamu iya dariya muyi bacci, bayan ɗan uwanmu yana akwance rai hannun Allah, komai sai anyi mashi, mutumin daya sadaukar da farin cikin shi akanmu?  Ya hana idonshi bacci saboda ya bamu kariya, sai mune zamu gaza hana idanun mu bacci anya kuwa mun kyautawa kanmu"? gaba ɗaya suka fashe da kuka mai tsuma zuciya, haƙika maganar Haris Ta ta6a zukatansu, hatta ummi dake jingine da kofar dakin sai da ta zubda kwalla duk da batasan takan tarihin rayuwarsu ba, amma ta hasko wani abu.


 daga gefen gadon Danish sheikh Imam ya zauna jikinsa yayi sanyi lakwas, bai ta6a ƙaguwa da son jin labarin rayuwarsu ba irin yau.


   Cikin sanyin murya taj yace"kada ku ɗaurama kanku alhakin laifin da bana ku ba, hana ido bacci ba shi ke nuni da kun damu dashi ba, saboda ku kanku bazaku samu kwarin gwiwar yi mashi addu'a ba muddin baku da kwanciyar hankali da nutsuwa, abun da yakamata, tun da dare yayi in za ku yi bacci ku kwanta da wuri, wuraren ƙarfe uku na dare zan kira unaisah awaya in tunasar da ita, in yaso ita sai ta tashe ku daga bacci ku tashi kuyi nafilfili ku kai kukan ku wurin Allah akan halin da ɗan uwa ku yake a ciki, in sha Allah zamuyi nasara"


   Shawarar da boss man ya yanke masu tayi masu dadi.


  "Mungode sosai, Allah yasaka maku da mafificin alkhairinsa, Allah ne kadai zai iya biyanku, " godiya suka shiga yi ma shiekh imam da boss man......


"Yakamata kuje ku kwanta, ku yi bacci kada a makara" amsa mashi su ka yi da toh, bayan sunyi ma sheikh imam sallama, Suka nufi hanyar fita daga dakin jin takun tafiyar sune yasa ummi tayi saurin nufar bedroom dinta tana shiga ta fada saman gadonta taci gaba da yin kuka tamkar ranta zai fita...


   Unaisah taso ta samu damar ganin danish dakyau, amma saboda shiekh imam yasa takasa tsayawa, Idan har ba ita ta kashe mashi switch din dakinsa ba, ta kuma lullu6e shi da bargo ba, to kuwa hankalin ta bazai kwanta ba, tunani zatai tayi kamar ba'a lullu6e shi.


Ɗaya bayan ɗaya kowannansu ya nufi room dinsa bayan sunyi sallama wa junansu, zuciyoyin su cike da zullumin halin da danish yake a ciki.


    Basu bar dakin shi ba, sai da Taj Ya lullu6e shi dukanshi da bargo, ya kuma kashe switch din kafin Suka fito tare da sheikh imam, har bakin motar da aka kawo shi ya raka shi, sun ɗan juma a jikin motar suna tattaunawa duk dai akan halin da danish yake a ciki ne, har ƙara jaddada mashi sheikh yayi akan su dinga dubawa akai akai ko Allah zaisa ya farka daga baccin, kafin daga bisani su ka yi sallama.


_______________________Boss Bature✍️


💋CHIEF OWAIS💪 


Aso Villa.


A yayin da yake a kwance saman katafaren gadon shi dake a Villa tsantsaran gaske, ya lullu6e half body dinsa da lallausan duvet dinsa, cikin kwanciyar hankali da nutsuwa yake fitar da numfashin sa, ga wani irin sanyin A.c daya ƙarama dakin nashi ni'ima, babu haske dakin sai na bedside lap ɗaya da aka bari a kunne...


sautin ringing ɗin wayarsa ne ya farkar shi, da wata irin kasala ya kai hannu ya lalubo wayar, A hankali yaɗan ware reddish eyes nasa masu dauke da bacci ya duba sunan mai kiran nashi, yayi mamakin ganin kiran prime minister Hateem, slowly ya dubi agogon bango ƙarfe wani abu na dare.


  Ya ilahi ya faɗa a zuciyarsa kafin ya miƙe zaune ya ɗaga kiran ya ƙara a kunnansa


   "Uncle... " iya abunda ya iya furtawa kenan.


On the other hand muryar prime minister ta karade kunnuwansa.


  "I'm sorry na katse maka baccin ka, na tashi yin night prayers ne, shi ne na kiraka don inji awani hali yarona yake aciki, saboda mafarkinsa ne ya tada ni daga bacci" chief owais dake ta faman lumshe idanunsa, cikin yanayi na kasala ya furta"uncle saboda shi ka tada dani daga bacci"?


    "I'm so sorry my son, bansan ya zanyi maka bayani ba"


 Lumshe sexy eye dinsa yai kafin a hankali ya furta "Uncle, ka kwantar da hankalin ka, yanzu ni bana agidana, nazo Villa ne, amma in sha Allah gobe zan koma gidana da wuri saboda shi'


 Har cikin ran prime minister yaji dadin maganar Owais

  

  "Zullumi nakeyi, daga gobe shikenan bazan sanya shi a idanuwana ba, jibi da asuba jirginmu zai bar nigeria, gani nake kamar idan na tafi ba lallai na sake dawowa ba, balle har na sa ran ganawa da shi.... " dafe kai chief owais yayi da hannu ɗaya, Lamarin yafara kokarin rikata mashi lissafin kwalwarsa, aranshi ya ayyana anya kuwa Daddy Hateem bai fara zaucewa wa ba? ko dai ya samu matsalar kwalwa ne? Ko kuwa yafara ɗaga kwalba ne, Idan ba haka ba akan wani dalili zai ɗaga hankalin shi akan yaron da bai haɗa alaƙar komai da shi ba? Wannan wata irin ƙaunace? 


  Jin shiru chief owais bai furta mashi magana bane yasa shi cewa"naji kayi shiru son, ko ka koma baccin ne...

  Slowly ya mayar da kanshi saman pillow,.


"Uncle, I'm confused..." 


 kafin ya ƙare maganar prime minister ya tari numfashin sa



"I'm confused too, Owais....nasan me ka ke tunani aranka, may be ma kana yi min kallon kamar nafara zaucewa, owais na dauki soyayyar yaron nan amatsayin jarabta daga Allah, ni dai kawai fatana ya zama alkhairi agare ni, dan Allah ka tayani da addu'a Allah ya bashi lafiya...


   Lumshe ido chief owais yai, bakomai yake tariyowa ba face ranar da suka fara tozali da juna shi da danish suna a saman bene, suka jefa ma junansu kallon kallon, aranshi ya ayyana ba lallaima idan yaron ya dawo hayyacinsa ya kula prime minister ba saboda Yana da ilmin sanin halayyar ɗan adam, da ido kawai ya kalli danish ya fuskanci yana da wuyar sha'ani, yin mu'amala da shi ba abu ne mai sauƙi ba.


 "In sha Allah zan tayaka da addu'a, ni dai fatana ka daina sanya damuwa aranka, ka kwanta ka yi bacci, muna da liyafa a gobe"


  Yana iya jiyo sauke ajiyar zuciyar prime minister ta cikin wayarshi.


  "Nagode da kulawarka agareni my son, Allah yayi maka albarka" amsa mashi yayi da ameen

 Har zaiyi rejecting kiran muryarsa ta sake katse shi

  "Pls kada ka koma bacci, ka tashi ka shiga toilet ka dauro alwala, kayi mashi nafila ko da raka'a biyu ce, Allah ya bashi lafiya"


   Babu musu yace"In sha Allah zanyi" bayan sunyi sallama, chief owais yayi shiru yana tariyo kalaman Daddy hateem, shi kanshi yafara hasashen tabbas akwai wani 6oyayyan sirri dake a tattare da kaunar da uncle dinsa ke yima yaron Allah kadai yasan ko menene.


  Jefar da wayar yayi saman gadon, kafin ya miƙe ya zura ƙafafuwansa ƙasa inda ya ajiye gucci slippers din sa, yunƙurawa yayi ya miƙe ya nufi switch din dakin ya kunna a hankali haske ya gauraye ko'ina, wato wani hamshaƙin bedroom ne, komai na cikinsa launin royal blue and white colour ne.


 A gaban dressing mirror ya tsaya tare da ɗaura hannun shi ɗaya ya dafa mirror chair.


 Wasu hadaddun Cashmere pajama ne a jikinsa riga da wando masu tafshi launin sky blue, sumar kanshi tasha gyara sai daukar ido take yi ga wani kamshi dake fita daga cikin ta, chief karshe ne a fagen haɗuwa.


  Moving slowly ya nufi ƙofar toilet dinsa ya shiga daga ciki, alwala ya ɗauro ya fito fuskarsa da lemar ruwa ya nufi walk-in closet dinsa jim kadan ya fito sanye da jallabiya, ya hau kan darduma ya dai daita nutsuwarsa da kyakkyawar niya ya kabbara sallah.


 A kalla yayi kusan raka'a goma sha takwas batare da gajiyawa ba, har sai da yaji kafafuwanshi sun soma rurruƙewa tukunna ya dakata, ya zauna yana jero addu'o'i duk dai akan danish yayi su kamar yarda Uncle hateem ya nemi alfarmar yayi mashi.


Bayan ya kammala komawa yayi saman bed nasa ya kwanta, tare da kai hannu ya ɗauki wayar shi, jim yayi yana mai mamakin ganin sakonta, a kalla sunfi wata biyar ko sallama basa yi ma juna, shiga cikin message din yayi, tare da karanta sakon da ya gani, ko kusa bai ji su a zuciyar shi ba, saboda kokwanton da yake yi, video din Ya kunna ya fara kallo, yana faman lumshe idanun shi, tayi mashi kyau yaji dadin kallon video din, almost 3 times yana maimaita kallon shi, kafin daga bisani ya fita daga chat din ya daura idanunshi kan hoton wallpaper din sa.


 A tsanake yake kallon baby face dinta, ta zare idanunta a hoton daga ganin hoton screenshot din shi aka dauka, kuma anyi hoton ne batare da sanin ta ba.


   Sam baya gajiya da kallon hoton, A hankali ya ɗaura soft pink lips dinsa saitin fuskar ya sumbace ta, kafin ya ɗaura hoton saman kirjinsa a haka bacci yai awon gaba da shi.


________________________✍️


Taƙi runtsawa ta addabi kowa ta hana su bacci saboda Jazz baizo ba, tace in har baizo ba to bazatayi bacci ba suma kuma bazasu yi ba, dakyar Salsabeel Ya shawo kanta Ya samu ya lalla6ata har ta ƙyale sauran ƴan uwanta suka kwanta a dakunansu, itama takwanta harfa ya kwanta da niyar ya runtsa can tsakar dare yajiyo bugun ƙofa, a firgice ya farka Yaje ya buɗe, Khadeeja ya gani tsaye ta ruƙe qugu tana faman kumbura mashi fuska tace Ina jazz din yazo? Agogo ya kalla sam yama kasa buɗe baki ya bata amsa, tace dama nasan baizo ba, ya manta dani, wlh Allah nima nayi fushi da shi.


Cikin kwantar da murya salsabeel yace"dan Allah kiyi hakuri kije ki kwanta bacci, dare ne yanzu, gobe in Allah yakaimu da safe zan kira maki jazz"

Maƙe mashi kafaɗa tayi alamar bazata kwanta ba, ganin zata 6ata mashi lokaci yasa shi ɗaure mata fuska ya daka mata tsawa tare da fadin"Zaki wuce kije ki kwanta ko saina yi ƙwallo dake" fashe wa tayi da kuka da gudu ta nufi falo ta zauna saman sofa tana kuka, ko tsoro bata ji ita kadai kamar aljanna" ko ta kanta baibi Yaja kofa Ya rufe Ya koma ya kwanta.


   Sai da tayi kukan mai isarta, kafin Ta miƙe tana shafa ciki Alamar yunwa take ji, kaitsaye ta nufi Kitchen ta shiga ta soma kiciniyar kunna gas, tsabar rigima.


   Mutsu mutsu tajiyo a kunnanta, hakan yasa ta dakata ta juya tana ƴan waige waige don ganin menene, Karaf idanunta suka sauka akan Ƙatoton 6eran dake tafiya saɗaf saɗaf Yana tunkarota baƙi wulik da shi,  sam bata ji tsoron shi ba, Abun ka game ta6in hankali, Praying Fan ta ɗauko cikin sanɗa tabi bayan shi ta daddage ta kwaɗe shi da fan ɗin, ko shurawa baiyi ba ya sheƙa, Bindin shi ta ruƙo tana faman sakin nishi tace"Zaka ci ubanka, Kai ne 6arawon dake cinye mana sauran da muka rage a kitchen ko"? Ta faɗa tana leƙen idanun 6eran Yayi zuzuru dashi.


  "Ba zaka yi magana ba? Baka da gaskiya bakin munafuki, kai ne kake gwigwiyar mana bready, Bari na kai ka Gaban Alƙali Ya salsabeel Ya kashe min kai har lahira"


 Ta faɗa tare da fitowa da gudu ta nufi bedroom din salsabeel, Har Ya koma bacci, Yajiyo muryar khadeeja tana fadin"Ya salsabeel Ka buɗe min kofa na kama 6arawon dake cinye mana sauran abincin mu, gashi nan a hannuna, Ya salsabeel ka buɗe zai gudu'


 Afirgice Ya farka har yana tuntube garin sauri, koda Ya buɗe ƙofar Miƙa mashi 6eran tayi

  "Gashi ka kashe shi ko ka cire mashi hannayensa"

   Fuskarshi a yamutse ya kalli 6eran da idanunsa masu dauke da bacci, sun kaɗa jawur da su, yayi mamakin da har ta iya kamo 6era, tun da suka fara zama gidan bai ta6a ganin gifcin 6era ba sai yau.


 Muryarshi adisashe yace"khadeeja ba zaki barni inyi bacci ba? Ke baki runtsa ba nima kuma kin hana in runtsa, Meke damun ki ne"?

 Ta6e mashi lips dinta tayi alamar zata fashe mashi da kuka

Da sauri yace"ya isa ni bance kimin kuka ba, Yanzu fada min ya kikeso ayi da 6eran nan da kika kama"

 "Ka cire mashi hannuwa" gyada kai yayi tare da sanya hannu ya kar6i 6eran"ki jira ni yanzu zan dawo amsa mashi tayi da toh, fita yai daga dakin tana atsaye tana jiran shi, badajimawa ba ya dawo hannunsa babu 6eran

  "Yana ina"?

 "Na cire mashi hannuwa na yar" murmushi tasaki"mun hutu da masifa ko"? Ɗaga mata gira yai alamar eh

 "Muje na rakaki daki kiyi bacci" maƙe mashi kafada tayi"Ni yunwa nake ji, kaje kitchen ka dafa min abinci"

   Wahalallan kallo yabita dashi gaba ɗaya ta takurasa

  "Shikenan muje" Ya fada tare da yin gaba tabi bayan shi suka shiga falo, ta zauna saman sofa.

 Kitchen Ya shiga bawan Allah ga gajiyar bacci A haka Ya dafa mata indomie, Ya haɗo mata da water bottle, Ya shigo Da plate din Ya miƙa mata, gefen ta ya zauna don yasan koya koma daki indai batayi bacci ba to shima bazai runtsa ba.

 Yana kallonta Har ta cinye taliyar ta kora da ruwa, kwanciya tayi saman sofa din ta daura kafafuwanta saman laps dinshi bai tanka mata ba, yasan rigima take nema, Cikin sa'a bacci yai awon gaba da ita, A hankali Ya zame ƙafafuwanta ya miƙe tare da ɗaukarta ya nufi upstairs da ita, a kan gado ya kwantar da ita, yabi da bargo ya lullu6e mata jikinta, kafin ya fito ya datse kofar dakin nata, cikin sauri ya nufi dakinsa don ya kwanta ya karasa baccin dabai isheshi ba, bayan shigarshi daki har ya kwanta ya soma tunanin ko me ya hana jazz zuwa? Tun safe yake jaraba kiran layin shi baya picking, har ta 6angaren danish ba a kira shi ba wunin yau, fatan shi Allah yasa lafiya da wannan tunanin bacci 6arawo ya ɗauke shi.


*💋BENAZIR❤*


Kwance take a saman darduma, tun bayan data kammala sallar Isha bacci mai nauyi yayi awon gaba da ita, yayin da zeenatu take a can saman gado tana bacci.


      Tana a nannaɗe cikin dogon hijab dinta, tayi nisa acikin baccin ta, Ba zato ba tsammani hasken fitilar bedroom ɗinta ya ɗauke ɗuff, wani iko na Allah ba wutar gidan bace ta samu matsala, ɗakinta ne kadai hasken ya ɗauke, abun ka game bacci sam bata ji alamun hasken dakin ta ya ɗauke ba.


    Kwatsam! taji an damƙi wuyanta, tsabar zafin shaƙar da akayi mata ne yasa ta ware idanunta waje, bata iya ganin komai sai duhu baƙi wulik a idanunta 

 Wani irin mahaukacin bugun fargaba zuciyarta keyi mata, Hankalinta a matuƙar tashe ta soma kokarin kwace wuyanta daga hannun mutumin daya shaƙeta, wuyanta tuni ya soma yi mata zogin azaba, zufa ta ko'ina ta wanke fuskarta, duk yadda benazir taso ta kwace kanta sai dai kash takasa, ga zeenatu kwance saman gado sai dai babu halin da zata iya buɗe baki ta nemi agajin ta, koma wanene yayi mata muguwar shaƙar da ko yatsanta takasa ɗagawa, bakinta tamkar an ɗaure mata shi takasa buɗe shi, hakan yasa tafara kukan zuci tana ambaton sunan Daddy, mommy, yaya shurem, Zeenatu, A karshe ta kamo kalmar Innalillahi wa'inna ilaihirraji"un tacigaba da anbatonta acikin zuciyarta.


 Tana acikin wannan mawuyacin Halin har tafara fidda rai da rayuwa kwatsam wayar zeenatu da ta ajiye kan gado ta soma ringing, taken karatun al'ƙur'ani mai girma ne, Kamar Walkiya taji alamun an sakar mata wuyanta, kuma nan take hasken ɗakinta ya kawo, a gigice ta zabura ta miƙe zaune tana faman zazzare idanunta, bin ko'ina na dakin tayi da kallo bata ga kowa ba, Lamarin ya daure mata kai, tagaza gane meke shirin faruwa da ita? Don wannan yafi karfin a kirashi da mafarki, tabbas akwai me son rabata da rayuwarta, lokaci ɗaya ta fashe da matsanancin kuka tamkar ƙaramar yarinya ita kadai tasan radaɗin da wuyan ta ke yi mata, zeenatu dake ta sharar baccin ta tuni ta soma mutsu mutsun farkawa saboda sautin kukan benazir daya fara addabar kunnuwanta, da sauri benazir ta tsagaita da yin kukan gudun kada zeenatu ta farka taga halin da take a ciki, cikin juriya ta miƙe ta zame hijab din jikinta, ta jefar da shi gefen gado, gaban madubi taje ta tsaya tana kallon wuyanta yayi jawur da shi hada sawun yatsun hannuwan mutun rudu rudu..


   Hakika Ta gigita ta kuma tsorata a yanzu ta ƙara tabbatarwa kanta cewa akwai me son ganin bayan ta? Wanene? Laifin me ta aikata da har ake son kashe ta? Zuciyarta ce ta raya mata cewa zai iya yiwuwa jinnu ne, tafi yarda da abun da zuciyan nata ta raya mata saboda babu wanda take zargin zai iya yi mata haka acikin mutanan da take rayuwa da su,ta dai yanke shawarar zata sanarwa yaya shureim ko dan su nemi mafita a tare.


  Miryarta na rawa ta furta"Ya Allah ban cutar da kowa ba, Kada ka bada damar da wani zai cutar dani" ta jima atsaye gaban mirror, zuciyarta cike da rudani, ta nufi toilet, tsawon mintuna kafin ta fito jikinta da alamun lemar ruwan da ta watsa ma kanta.


   Tunawa da kiran wayar da akai mata ne yasa ta nufi bakin gado ta ɗauko phone din ta soma daddanawa call logs ta shiga nan take taga missed call na bakuwar number din nan


   Sai da ta fara kallon agogo, karfe wani abu na dare kafin ta danna call tana faman zazzare idanunta, jikinta nata kerma kamar wadda aka kada ma mazari


Adai dai wannan lokacin Unaisah tana a zaune kan darduma ta zumbula hijabi a jikinta ta ɗaga hannayenta sama fuskarta sharkaf da hawaye bakomai take yi ba face yima danish addu'ar samun lafiya, Batul tana a kwance gefen ta, tun bayan da boss ya tashe su domin yin nafilfilin da za su yi kowannansu bai koma bacci ba, duk suna a dakunansu suna yin sallah, ita dama batul bata da jumurin yin sallah duka raka'a biyu ta samu tayi adaddafe kafin bacci yai awon gaba da ita, shigowar kiran wayar ta ne yasa takai hannu ta dauke ta, a inda ta ajiye ta gefen prayer mat din da suka akai


Ko da tayi tozali da layin da take ta dannawa kira taga da shi aka kirata Yatsun hannunta har kerma sukeyi wurin yin picking din kiran, hadi da kara wayar a kunnanta.

  Tamkar kurame sunyi shiru suna sauraran sautin fitar numfashin juna.


       Jira take taji wanene mamallakin layin nan daya kira, Haka zalika itama benazir jira take tafara jin wanda ya ɗaga kiran yayi mata magana.


  Jin shirun yayi yawane yasa unaisah tace"Assalamu Alaikum" sautin daddaɗan muryarta ne ya daki kunnan Benazir, batasan ya akai ta tsinci kanta da jin faɗuwar gaba ba.


  Muryarta babu nutsuwa ta amsa mata sallamar"Wa'alaikum Salam, barka da dare, dan Allah zan iya sanin dawa nake magana" ta fada cikin ƙagara.


Shiru Unaisah tayi tana tunanin wacece wannan matar mai muryar ƴan gayu? Daga ji dai wayayyiya ce.


  Jin shiru ba'a ƙara magana ba yasa banezir furta"nayi magana anyi shiru b'a bani amsa ba, in ansan baza'a tanka min ba meyasa za'a takurani da kira da tsakar dare"? Har zata katse kiran Unaisah tayi saurin cewa"Aunty kiyi haƙuri, bakisan wacece ni ba, nima bansan ki ba"


 Ajiyar zuciya Benezir ta sauke kafin tace"okey, amma meyasa kika kira layina bayan baki sanni ba"!


"Nayi kuskurene wurin rubuta number din da zan kira"


"Okey" shiru su ka yi, babu mai magana na tsawon mintuna kafin benazir tayi karfin hali cewa"meye sunan ki? Shekarun ki nawa"? ta tambaya ne jin muryar kamar ta ƙaramar yarinya


"sunana Unaisah, shekarata goma sha shida, ke fa"?


Murmushine ya bayyana akan fuskar benazir, batasan ya akai ta tsinci kanta da jin farin ciki ba.


  "Sunana Aunty pretty, Amma fa ni ba yarinya bace, na girme ki, Shekarata talatin da wani abu"


Murmushi unaisah tayi ita kanta dadi take ji, duk da halin damuwar da take aciki silar kiran nan ya haifar mata da kwanciyar hankali.


  "Kiyi hakuri na kiraki bisa kuskure, sannan na katse maki baccin ki"


"Kada ki damu, Naji dadin haduwa dake"


Shiru sukayi Kamar karsu Kashe kiran haka suke ji.


"Baki so na sake kiranki"? Unaisah ce ta jefa mata tambayar .


 Murmushi benazir tayi don ta fahinci yarinyar batason su daina magana.


"Ina so mana, tun da naji muryarki naji kin kwanta min araina, da ace babba ce ke da mun kulla kawance sai dai kin min ƙanƙanta"


Cike da zumuɗi Unaisah tace"zan dinga kiranki muna gaisawa a matsayin aunty na, Idan kuma kina da ɗiya kamar ni, ko ƙanwa to ki hadani da ita sai mu dinga zumunci"


"In sha Allah, yanzu ki kwanta ki yi bacci kada mommyn ki ta kama ki kina waya da dare, gobe zan kiraki mu ƙarasa gaisawa, Yanzu kinga dare yayi," 


Kamar karsu rabu, Haka sukayi sallama da junansu, fuskar kowannansu dauke da murmushi.


Karatun kur'ani benazir ta kunna a wayar, saboda ta fahimci Kiran wayar da akayi mata sautin karatun kur'ani ya fita shine silar da Aljanin daya shaƙeta ya gudu, Gefenta ta ajiye wayar, ta kwanta tare da jan bargon da zeenatu ta lullu6a da shi, itama  ta lullu6e kanta, zuciyarta acike fal da annurin farin ciki, Harta kosa gobe tayi, kodan ta kira Yarinyar su ƙara gaisawa, ita kadai take ta tufka da warwara har ta yanke shawarar zata haɗa yarinyar da zeenatu su dinga zumunci, in yaso ita sai ta kar6i layin maman yarinyar suna gaisawa da wannan tunanin wani baccin ya kuma daukarta.


Bayan Unaisah ta kashe Kiran, wani irin daɗi take ji, aranta ta ayyana meyasa nake farin ciki akan matar da bansan wacece ita ba, wata'kil ma maman Sajeed ce, dole gobe in fada mashi munyi waya da matar dake a ruƙe da layin wayarsa, bata koma bacci ba sai da ta kara zuwa dakin danish cikin daren ta leƙa don ganin koya farka, kamar yarda suka barshi haka ta same shi, addu'o'i ta ƙara tofe shi da su

ta ruƙo dogayen yatsun hannayensa ta sumbace su, tasha kuka a yayin da take agefen gadon shi ta roƙi Allah akan ya ba man dinta lafiya tamkar zatayi hauka ita kadai a dakin sa ko tsoro bata ji, raba dare tayi tana gadinsa har bacci yafara kokarin daukarta sai da aka fara kiran sallar Asubahi tukunna ta baro dakin tana sharar kwalla..............😥💋✍️



    *FRIDAY MORNING*


*Hajjaty the head maids*


Sautin ringing ɗin wayar pravin ne ya katse mata baccin ta, A hankali ta buɗe idanunta masu dauke da bacci ta kalli ceilling na tsawon mintuna kamar mai nazarin wani abu, sam ta manta da abun da ya farkar da ita daga bacci har saida aka ƙara kira tukunna ta miƙa hannu saman mattress ta janyo wayar ta karata a kunnanta ba tare da ta duba sunan mai kira ba.


    Bankaɗo kofar toilet da akayine ya firgitar da ita kafin tayi wani yunkuri taji ya fisge wayar daga hannunta, har sai da gabanta ya faɗi ganin kumfar sabulu a jikin shi, Ko sutura babu haka ya fito daga bathroom zindir haihuwar uwarsa, duk dan kada taɗaga mashi waya' juyawa yayi da sauri ya koma toilet, hajjaty dake kallon shi da tsantsar mamaki ta miƙe zaune tare da jingina bayanta jikin headboard tana jiran fitowarshi

  Badajimawa ba pravin ya fito daga toilet waist dinsa daure da towal, fuskarshi babu walwala tunkafin tayi mashi magana yai saurin tarar umfashinta da cewa"Karki kuskura kiƙara gigin ɗaga min waya idan an kira ni, babu ruwanki da wayata" lamarin ya ɗaure mata kai adabarbarce ta furta"laifine idan an kiraka na daga? Anya pravin kana da gaskiya kuwa saboda kawai na ɗaga wayarka shi ne ka fito tsirara daga toilet da ruwan kumfa a jikin ka"! 

 Harara ya galla mata"wannan bai shafe ki ba, Nidai ina ƙara jan kunnanki babu ruwanki da wayata, ban yi maki iyaka da komai nawa ba, amma banda wayata," Kallon tuhuma take jefa mashi, ba tun yau ba ya tsani yaga ta ta6a wayarshi kamar ta tsunkuli ranshi ne.

 "Kallon Ya isa haka, ki tashi kije ki yi wanka" ta6e baki tayi kafin tace"ba yanzu ba, sai zuwa anjima idan zamu je dinner din Hateem"


  Ɗaure fuska yayi babu annuri ya furta"ay na faɗa maki, bazan bari ki halarcin dinner ɗin nan ba"


  "Amma dai dawasa kake min ko"?

 "Na ta6a yi maki wasa irin wannan"?

 "Amma meyasa zaka hanani zuwa bayan na riga dana kwallafa raina"? fuskarta a yamutse ta jefa mashi tambayar

   Shiru yai bai tanka mata ba, taci gaba da cewa"bazaiyiwu ba pravin, matan family din nan gaba ɗaya zasu halarci taron sai ni kadai zaka hana zuwa"?

   Gaban mirror ya tsaya yana gyara jikin shi,

  "Dakai fa nake magana"?

Sai da ya mula yasha iska tukunna yace"abun da nakeso ki fahimta, zuwanki dinner din baida amfani! Saboda matan family din nan ba kaunarki su ke yi ba, iyakaci suci maki mutunci su zazzageki ni kuma abun da banaso kenan, sannan ni ina kishin kije wadannan dattawan masu gemu su kalle min ke"


 Kwantar da kanta tayi jikin pillow

  "Wannan ba hujja bace pravin, meya kawo maganar cin mutunci a taron bankwana da hateem kaima in banda abun ka, sannan kishi da kake ji ay bani kadai bace matar da zanje dinner din ba muna dayawa...." kafin takare magabar ya tari numfashinta da cewa"Amma ay ke kadai ce ba'asan da igiyar aure akanki ba, kowa kallon bazawara yake yi maki, uwa uba kuma surar jikin ki dake jan hankalin su"


 Saukowa tayi daga kan gadon ta nufe shi, ta tsaya daga bayanshi tare da ɗaura kanta saman bayanshi.


   "Hubbyna, dan Allah kada ka hanani zuwa, wallahi na ƙwallafa raina akan dinner din nan, ka taimaka min pls nayi maka alkawarin zan kare mutunci na, indai ka yarda dani pravin kabarni inje' da shagwa6a ta ƙare maganar tare da zagayo hannayenta kan waist dinsa tuni yafara jinshi a wata duniyar, ta san duk wata hanya da zata canza mashi ra'ayin shi.


 Lumshe idanunshi yayi, yayin da yake kallonta ta cikin mirror, tsantsar sonta da kaunarta yake ji,

  Ɗago dakanta tayi daga bayanshi ta daura kan kafadarsa ta hagu.


    Suka ci gaba da kallon juna.


 "Inaso ka faɗamin tsakanin ni da kai waya fi kama da ɗan mu" 


 Shiru yayi tamkar baison furta maganar ya ce "kin fi kama da shi"


 Murmushi tasaki har dimple dinta ya lotsa


 "Allah ya ji ƙan shi" ya amsa mata da ameen.


 Sumbatar wuyanshi tayi, hakan ba karamin dadi yayi mashi ba

  "Zaka barni inje babyna"?

 Baiyi niyar barinta taje ba, amma yanayin da tayi mashi maganar yasa shi amincewa batare daya shirya ba.

  Wani irin farin cikine ya lullu6eta shi kanshi ya shaida hakan

  "Atare dakai zamu je ne"? 

 "No,ni ba lallai naje ba,"

"Amma yakamata kaje kaima zaiji daɗi, kaga daga yau shikenan gobe ba lallai ka samu danar ganawa dashi ba may be tashin asuba jirginsu zai lula"

  Janyo hannunta yayi ya dawo da ita ta gabanshi, yadda zaiji dadin kallonta dakyau

    "Nima zanje in sha Allah"

  "Bari na taimaka maka ka idasa shiryawa, nasan hajiya Saratu tana can tana dakonka, daga zuwa sallar asuba ka gudo dakina"

  "Matar da bata damu dani ba, ni fa banda amfani awurinta... " bata bari ya karasa maganarba ta rufemashi baki, don bata son yana aibata hajiya saratu awurinta.


Shirye shiryen sun kankama, Don tun wuraren ƙarfe tara na safe Zungureriyar motar kamfanin su zahra mai ɗauke da tambarin Zahra World of beauty ta karaso estate din, kafin shigar motar sai da Security officers su ka yi mata wankan tsarki ciki da bai suka bincike komai da na'urorin tsaro, hatta Interior designers din dake a cikin ta ƴan matasa mata sai da Sojoji suka bincike su from head to toe, suka tabbatar ba su shigo da wani abun cutarwa ba, kafin suka bar motar ta shiga ciki, Hajiya saratu ce ta tsara lokacin da za'a fara aikin decoration din dakin taron saboda friday ne kurarran lokaci kwara ay komai da wuri acewar ta


 Masu aikin gidan kuwa tun asuba suka fara ɗaura girke girke, saboda uban aikin dake gare su, abinci ne za'a girka kala kala, Na ƙabilu daban daban, kafin kace me cikin ƙanƙanin lokaci ƙamshi ya gauraye ko'ina na gidan baba obie, don anan ake aikin girkin....


Hajiya zahra kuwa yau tsabar murna kamar wadda akaiwa albishiri da gidan Aljana, tun jiya akayi mata saloon da kunshi na jan lalle kamar amarya, taci buri akan dinner din nan kamar ranar auranta, Saboda son ta dau gayu na kece raini motar Aneelerh ta ara da yake tafi tata motar tsada da kyau, Tuni taba mahboob motar ta hada shi da ƴan canji ya tafi kai ta wurin da za'a wanke ta don ta ƙara kyau, kowa na gidan sai da yasan da zancen zuwan Zahra Obie estate saboda ta addabi kowa duk bayan ƴan mintuna sai ta kalli agogo burinta lokaci kawai lokaci ya ci ka....


Ƙarfe 9 na safe, Zeenatu tana a zaune kan mirror chair, tana ƴan shafe shafen ta, bata jima da fitowa daga wanka ba, jikin ta sanye da bathrobe mai kyan gaske, ta ɗaure gashin kanta

Fitowa benazir tayi daga toilet da alama itama wankan tayo, ta yi daurin gaba da towel, fuskarta babu walwala ta kumbura jawur da ita saboda kukan da tayi adaren jiya da abun nan ya faru

 Ganin zeenatu dake ta shafa powder yasa ta ɗan saki face din ta da zolaya tace"uhum su baby shuriem wa ake ma kwalliya" kunyar maganar Benazir yasa tayi kamar bata ji me tace ba

 Gyaran murya benazir tayi still bata ɗago ba, saima ta ɗauki jan baki tana shafawa

  "Wato kinyi imanin sai kin zautar min da yaya na"? Cak zeenatu ta tsaya da shafa jan baki, cike da jin kunyar benazir ta sunnar dakai ƙasa

 "Duk hasken da Allah yayi maki zeenatu har sai kin ƙara da powder in ban da asara, so kike ki koma zabayyana ne'? dariya ce ta kubce ma zeenatu har fararen hakoranta suka bayyana masu kyau da tsari

    Muryarta ƙasa ƙasa tamkar ta mai yin raɗa ta furta"aunty benazir mommy ma tana shafa powder in zata ma daddy kwalliya, shiyasa nima nake shafawa" dariya benazir tayi hadi da ɗan girgiza kanta..

     Wucewa wurin closet din dakin tayi domin shirya kanta, within minutes benazir ta fito asanye da riga da skirt sun ɗan kama jikin ta

     Gaban madubin ta tsaya daga gefen zeenatu tana fadin"naga abun naki bamai karewa bane, ki tashi ki je ki sanya kaya, kafin darling din naki ya farka daga bacci" cike da jin kunyar maganarta, zeenatu ta miƙe tana faman sakin murmushi sai da tafara daukar hijab dinta dake ajiye bisa gado kafin ta nufi hanyar fita dakin don taje nata dakin ta sanya kaya

  Fitarta ke da wuya suka yi kici6us da dr shureim wanda ke kokarin doka sallama, tun da ya sauke idonshi akanta ya kasa janye su, cikin jin kunyarsa ta sunnar da kanta kasa tana faman noƙe kai ta furta"yaya shurem ɗina ina kwana, fatan ka ta shi lafiya.. ' ta faɗa la66anta na dan kerma without looking at him

  Gogan naka ya kasa magana saboda kyanta da ya dauke ma shi hankali

 Muryar ta da shagwa6a ta furta ya shureim ina magana ka share ni...

 Lumshe idanunsa yai yayin da yake shakar kamshin turaren dake fesowa daga jikin ta

 Muryarshi can ƙasa makoshi ya furta" nabd alqalb (نبض القلب) kin yi min kyau ban yi tsammanin idanuwana za suyi min tozali da kyakkyawar fuskar ki ba..." arude ta maimaita kalmar nabd alqalb ta dago tana zare mashi blue eyes din ta, muryarta na ɗan rawa ta furta"ya shureim bansan me kake nufi ba"

Side smile ya sakar mata, tare da matsawa dab da ita, tamkar zaiyi mata raɗa a kunne ya furta"Bugun zuciyata" farfari tayi da idanunta wani irin farin ciki Ya lullu6eta

 Batai wanai aune ba taji ya manna mata sumbata saman soft cheek din ta' waro idanu tayi a ruɗe ta watsa da gudu ta nufi hanyar bedroom din ta

  Bin bayanta yayi da kallo tamkar yabi ta haka ya ke ji

   "Yaya Shureim kaine? Yaushe ka zo shine baka min sallama ba" kamar daga sama yaji muryar benazir firgigit yai tare da dubanta

   Yana kokarin bude baki yai mata magana karaf idanunsa suka sauka akan shatun yatsun hannun dake akan wuyanta ruɗu rudu fatar wurin tayi dabra dabra jawur, gabansa ne yayi wani irin mugun faɗuwa ji kake rass

  Benazir bata lura da abun da yake kallo ba, gaba ɗaya ta faɗa kirjinshi ta rungume shi haɗi da manna mashi peck kan kuncinsa, irin gaisuwarsu ta larabawa

 Idanunsa a zare yake kallon fatar wuyanta, kafin ya daddage ya ɗaura tafukan hannayensa kan kafaɗunta ya ɗago da ita

"Benazir! " da karfi Ya ambaci sunanta

 "Me nake gani akan wuyan ki"? Ya jefa mata tambayar

Farat ɗaya ta gane me yake magana akai, da sauri taja hannun shi suka shiga dakin gudun kada wani yajiyo su

   "Tambayarki nake yi kinyi shiru baki ce komai ba!" adan tsawace ya furta maganar

Batasan sa'adda ta fashe mashi da kuka ba, cikin shessheƙar murya ta labarta mashi abun da ke faruwa tun daga rana ta farko da aka fara kawo mata hari

Ranshi yayi mugun 6aci na kin fada mashin da batayi ba, 

In a breaking voice ya furta"shi ne baki faɗa min ba"?

  "Yaya shureim bansan wanene yake son rabani da rayuwana ba, bansan meke shirin faruwa dani ba, na 6oye maku ne saboda ban dauki abun serious ba, da farko nayi tsammanin mafarki ne, ashe ba haka bane so ake akashe ni yaya shureim bansan zunubin dana aikata ba.... ' ta ƙarasa maganar tana faman shessheƙar kukan, Hankalin shi idan yayi dubu toh ya tashi, ya gaza yarda da abun da idanuwanshi suke gane mashi

 Ɗaura yatsun hannayenshi yai akan wuyan nata ya shafa shi a hankali, runtse idanunta tayi saboda raɗaɗin da taji, ganin hakan yasa shi janye yatsun sa

  Yama rasa tunanin da zanyi dangane da bakon al'amarin nan

    Ruko hannayensa tai acikin nashi tana cigaba da kuka take fadin"yaya shureim ka tayani da addu'a, bana son in mutu ban hadu da mijina da ƴata ba, yaya shureim ka taimaka min idan ba haka ba wata rana za'a iya farkawa ataras da gawata, jiya ba don kiran da akayi min ba har sautin karatun al'kurni ya fita da tuni na jima da mutuwa... Bai bari ta ƙare maganar ba, Ya toshe mata bakinta da tafin hannunsa

 Kwantar da kanta yayi kan chest dinsa muryarsa kasa kasa yake ambaton Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un yayin da zuciyarsa ke dakan uku uku!!!

  "Yaya shureim ko dai aljanune suke son kashe ni? Idan ba su ba to waye zaiyi min hakan a gidan nan? Babu wani bare a cikin mu, sai house maids  da security officers, babu abun da ya ta6a haɗani da wani daga cikin su, bansan su ba, balle har ace na aikata  wani abu ne da zaisa a nemi rabani da rayuwana...... ' cikin jin kunar rai ta furta maganar.

  "Yaya shureim dan Allah mubar gidan nan, dama saboda mu haɗu da aneeleerh ne yasa na ƙwallafa raina akan zuwa, tun da ban samu hanyar da zan hadu da ita ba, mu koma gida zai fi min kwanciyar hankali na...."

Tuni idanun dr shureim sun cicciko da hawaye, yai matuƙar girgiza da jin abun da ke faruwa da yar uwarsa tabbas yana ji aranshi wani abu ne ke shirin faruwa da ita, dole ya miƙe tsaye don ganin ya ceci rayuwarta


*(Mu haɗu Jibi Alhamis Idan Allah Ya kai mu da rai da Lafiya, Don jin Yadda zata kaya)*



*Daga Alƙalamin Boss Bature💋✊✍️*



 *Littafin kurkukun ƙaddara 500 ne, dukanshi Book One two and 3 Idan kin shirya biya ga Details da zaki tura*


3196407426


First bank 


Bature Hafsat Muhammad,


 *bayan kin tura zaki bada transaction reciept ko screenshot na debit alert a matsayin shaida ta wannan layin 08169856268*

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post