Kurkukun Kaddara Takun Karshe Page 8


Health College

Kurkukun Kaddara Takun Karshe Page 8

 _ *~✊💋BOSSLADIESWRITERS💋✊~*_




سجن القدر💋✊🔥



~Takun Ƙarshe🔥~




قصة حب رومانسية غير عادية بين السجناء مع تطورات معقدة💋💘😘



An extraordinary romantic love story between prisoners with complex twists ❤💋💘




Daga alƙalamin Boss Bature💋✊




__________________________✍️






Tana ƙarasa fadar hakan ta sanya hannu ta ture ƙofar ta shiga ciki, A ƙalla Yafi karfin mintuna biyar a bakin kofar yana yanke shawara da zuciyarsa, haƙiƙa Yana matuƙar jin tsoron Allah, bayason zama daki ɗaya da macen da ba muharramarsa ba, hakanan ba tare da wata lalura ba, balle kuma faryat da ta kasance tantiriya, sai dai baya jin zai iya rasa wannan damar, Allah ya jarabce shi da tsananin ƙaunarta, Itace mace ta farko da ya fara jin tsantsar sonta tun lokacin daya mallaki hankalinsa, ya mutu akan kaunar faryat yana son yarinyar duk da kasancewarta mara jin magana.


Numfasawa yayi kafin ahankali ya tura kofar dakin nata ya shiga daga ciki, katafaren dakin kwana ne, kamar na ƴar sarki, tsabar haduwar furniture din dakin, Komai na cikinsa Launin black pink ne.


 Bayan shigarsa dakin, Sanyayyan sanyin A.c ne mai haɗe da daddaɗan kamshin turaren faryat ya ratsa hancinsa da fatar jikinsa, Lumshe idanunsa yayi slowly ya buɗe su akan faryat dake a tsaye gaban dressing mirror, ta juya baya kitson kalabar kanta ya sauko har mid back dinta, ta cikin madubin ta ke jifar shi da shu'umin kallo.


  Ganin yaƙi ƙarasowa gare ta, yasa ta juyo ta nufe shi, dab dashi ta ɗaya suka soma jefa wa junansu kallo.


      Ba zai iya jurar shaƙar ƙamshin turarenta ba da kallon surar jikinta hakan ba ƙaramin jefa shi yanayi ya ke yi ba, Muryarshi na rawa ya furta"Am.. umm.. tun da naganki zan tafi"


  ba zato ba tsammani yaji ta ɗaura hannayenta saman kirjinshi, muryarta da shagwa6a ta furta"Ni ban gaji da kallon ka ba, My honey, tsawon lokaci bansanya ka a idanuwana ba, nayi kewar komai naka jazz..  " kafin ta ƙare maganar, jazz ya tari numfashinta da cewa"Faryat tayaya zan yarda da kalamanki? Bayan ke da kanki kika faɗi cewa bazaki ta6a sona ba, kuma ba zaki iya aure na ba"


 Juya mashi baya tayi haɗi da goya hannayenta saman kirjinta kafin ta soma magana.


  "Jazz, I won't hide it from you. Nothing has changed. I love you, but I can't marry someone who has no origin", (Jazz bazan 6oye maka ba, Har yanzu babu abun da ya canza, Inasonka amma bazan Iya auran wanda bashi da asali ba,)" ta faɗa tana girgiza kanta, kafin ta ɗaura da cewa.


"kaima ka sani jazz mommyna da daddyna ba zasu ta6a yarda mukasance atare ba, jazz I come from a wealthy family. How can I love someone like you who has no origin? What is your family status?" ta jefa mashi tambaya ba tare da ta jira amsar shi ba taci gaba da magana 


"Ta ya ya zan auri ɗan tsohuwar mai aikin gidan mu" tun da ta fara magana sai yanzu ta juyo ta fuskance shi, Jikin shi yayi sanyi lakwas, hawaye tuni sun soma taruwa a cikin fararen idanuwansa, kalamanta sun kashe mashi kwarin gwiwarshi, sai yajima gaba ɗaya ya tsani kan shi, ta fahimci halin da ya shiga sai dai ko kaɗan bata ji tausayin shi ba.


  "Jazz Hamshaƙan masu kuɗi suna rububi akaina, waɗanda duniya tasan da zamansu, How can I choose a meaningless future for myself when I could have so much more?"  a tsiwace ta faɗa tana zare mashi kyawawan idanuwanta masu dauke da zira ziran eye lashes.


 Hawayen da suka cika idanunsa tuni sun wanke fuskarshi 


    Cikin karyayyar murya yace"Nasan ni bakowa bane faryat, bani da asali, amma inaso ki sani, ina son ki tsakani da Allah badan wani abu naki ba, ba lallai ki sami wanda zai so ki kamar yarda nike sonki ba, nayi maki alkawarin zan baki kyakkyawar kulawa idan har kika amince da soyayya ta, ba zaki ta6a danasani ba faryat"! 


 Shu'umin murmushin gefen fuska tasakar mashi, wani irin kyawuntane Ya kara bayyana.


     Matsawa tayi tare da shige mashi, Har takaiga mumfashinsu na kokawar fitowa, hannayenta biyu ta ɗaura saman waist dinsa, da sauri ya yi kokarin kwace kansa daga gareta sai dai taki bashi damar yin hakan, gaba ɗaya ta kashe mashi jikin shi.


"Jazz ka daina wahalar da kanka akaina, cos I will never marry you. Owning me is not an easy thing, idan mommy taji zancen kana neman soyayyata kai kasan me zai biyo baya, shiyasa nake rufa maka asiri, saboda ina da buri akanka," lumshe idanunsa yayi cikin jin ƙunar rai, Allah ne kadai yasan Irin azabtuwar da zuciyarsa take yi mashi akan soyayyar faryat, zai iya jure komai amma bazai juri ya rasa ta ba.


  Jin motsin hannunta akan Trouser dinsa ne yasa shi yin saurin buɗe idanuwansa a hanzarce ya buge hannunta Yana faman fitar da huci... 


 Kashe mashi ido ɗaya tayi tare da zuro harshenta waje ta lashe pink lower lips dinta, cikin jin shaukin shi ta furta"jazz, har yanzu ban canza ra'ayina akanka ba, ka bani dama, in ɗebe maka kewa, kaga babu mai kallon mu daga ni sai kai, zan faranta maka rai, sannan inyi maka abun da zai zautar dakai ya gigita ka" ta faɗa cikin jin shauƙin shi tana kokarin tura mashi boobs ɗin ta da suke acike fam.


 Jikin shine ya soma kakarwa a ruɗe ya furta"bani da wannan ƙazamin tunanin araina, dan Allah ki daina fadamin kalaman nan, Hakan Yana karya min zuciyata, Ni tsakani da Allah nake sonki, Idan babu mai kallon mu Allah Yana kallon mu faryat, Bazan bari mu sa6a mashi ba, "


   Harara ta jefa mashi"matsalata dakai kenan, Har yanzu bakauyene kai, sai kace ba bature ba, sam baka da wayewar nan irin ta zamani, Daga anyi magana sai ka ambaci sunan Allah kamar kafi kowa tsoronsa, Ay Allah gafurirrahim ne, Idan mukayi sai mu roƙi rafiyarsa... " tunkafin taƙare maganar yace"Idan kuma muka mutu muna cikin aikatawa fa"? Murguɗa mashi baki tayi"nima bansani ba, tun da baka buƙatana ka tafi kawai, zan nemi wanda zamuyi da shi" ta fada tana ruƙe qugunta.

 Wani irin kishine ya ziyarce shi, tamkar Ya haɗiyi zuciya haka yake ji

   "Faryat ba ki jin kunyar fadin hakan agabana ba"? Ɗaga mashi gira tayi 


 "Yeah i can sleep with someone in front of you. tun da kai bazaka bani abun da nakeso ba, jazz bakason farin cikina, na jima ina sha'awar son kasancewa dakai amma kaƙi bani haɗin kai" cikin rauni na murya yace" idan kina son kasancewa dani ki aure ni mana, zan zama naki ke kadai, Mallakin ki, ko da yaushe kike bukatana zan kasance atare dake",


 Girgiza mashi kai tayi"A'a nidai kawai kayi min abun da nakeso, ay na fada maka bazan iya auranka ba, sai dai mu kwanta in baka kaina" Lamarin faryat ba karamin mamaki yake bashi ba, A shekaru bazata wuce 22 Years ba, Mace har mace sai dai babu kunya ko kadan.


  Ganin Ya tsareta da idanunsa ne yasa ta fara tunanin ko ya amince mata ne, ɗaura yatsun hannayenta tayi akan wandonsa da niyar ta zame masa shi, A hanzarce Ya buge hannunta, da sauri jiki na rawa ya nufi kofar dakin zai fuce, da gudu tabi bayanshi tayi hugging dinshi, ta soma raira mashi kukan shagwa6a, hakan baƙaramin yanayi ya jefa shi ba, baisan da wani yare zaiyi mata magana ta fahince shi ba, ya riga daya gane faryat tana sonshi, Rashin asalin shine yasa take gudin shi.


  Muryarta da shessheƙar kukan ƙarya take fadin"Jazz, kada ka tafi kabarni, Ina buƙatarka Jazz, Ina son kasancewa tare dakai, dan Allah ka amince min muyi nayi maka alkawarin bazan faɗama kowa ba, Idan ma kana fargaban wani ya gan mu, sai mu je  hotel in kama mana room, ko muyi a cikin motana" ta faɗa tana murza mashi mararshi da hannayenta, gaba ɗaya tagama susutar dashi wata irin zuface tasoma wanko fuskarshi

 Muryarshi da matsananciyar kalasa sautinta ke fita

  "Bazan iya sabama mahaliccina ba faryat, Ina jin tsoron Allah, kiyi haƙuri, Nima inajin abun da kike ji amma bazan iya ba, Kina bani wahala faryat, kema kuma kina cutar dakanki, saboda kina sona, Kina son kasancewa dani, amma kin haramta ma kanki aurena akan wani dalili naki mara ma'ana, Meyasa bazaki tausaya mana ba daga ni har ke? Faryat ki cika mana burinmu na ganin mun raya soyayyarmu, kada ki bari shaidan Yaci galaba akanki, ki fi karfin zuciyarki faryat, ki zauna kiyi tunani... " daƙyar ya ƙare maganar muryarshi na sarƙewa ya daddage ya 6an6are hannayenta daga ruƙon da tayi mashi, da sauri ya ruƙo handle din ƙofar ya fuce daga dakin


A jikin kofar Ya jingina kanshi hawaye masu ɗumi suka shiga zarya akan kuncinsa.


  Sautin shessheƙar kukan faryat ne ya cika kunnuwansa, baisan ya zaiyi da ita ba, yasan da irin mugun sha'awar dake gareta sai dai shi bazai amince mata su aikata sabo ba, saboda babu ɗa'a ga abokin halitta wurin sa6ama mahalicci Allah! Bazai juri sauraron kukanta ba, zuciyarshi karaya take yi, da sauri Ya sauko down stairs Cikin takun sauri Ya Nufi part din baba Obinna, zuciyarshi na cigaba da tafarfasa, Abakin kofar dakinsa Ya tsaya da yin tafiyar Ya zaro hanky, Ya goge kwallarsa, Kafin ya daidaita nutsuwarsa, sallama yayi mashi.


   Daga Ciki Ya jiyo muryar baba obie 


"Shigo daga ciki" Buɗe kofar yai tare da shiga Ciki, adai dai lokacin Baba Obie, Yana zaune saman darduma hannun shi ruƙe da cazbaha.


   Ba zato ba tsammani, Yaji saukar Jazz saman bayanshi, gaba ɗaya ya rungume shi tare da cusa fuskarshi saitin kafadarsa, Hakan ba ƙaramin ɗaga mashi hankali yayi ba, saboda a duk lokacin da jazz yayi mashi irin wannan rungumar to an 6ata masa raine," Yana Iya jiyo sautin fitar numfashinsa, dakatawa yayi da jan cazbahar, Ya ruƙo hannun Jazz Ya zagayo da shi ta gabanshi, tare da rungume shi ya kwantar da kansa saman kirjinsa tamkar ɗansa na cikinsa ko jikansa.


   Cikin sigar lallashi yake bubbuga bayansa batare daya furta masa ƙala ba, har saida Yaji alamun Ya fara samun nutsuwa tukunna Ya soma magana

  "Waya ta6a min shalelena"? Muryarshi adisashe Ya furta"Baba ka ta ya ni da addu'a, ita kadai nake bukata daga gare ka" ya fada batare daya raba jikin shi daga na Obie ba.


 "Jazz kasan bana son damuwarka, Ka fada min koma menene nayi maka alkawarin indai baifi karfina ba wallahi zanyi maka shi," babu wasa a kalamansa

Jazz yayi fatan ace zai iya fada mashi abunda ke damunshi amma bazai iyaba, Yasan muddin baba obie yaji zancen Yana son faryat sai ya aura mashi ita, koda kuwa Iyayenta basa so, shi kuma abunda yake gudu tada husuma, saboda ba lallai hajiya saratu da Pravin su amince mashi ya aureta ba, komai zai iya faru.


 Shafa bayanshi baba obie yaci gaba dayi yana fadin"Ina sauraronka, Fadamin meke damunka rabin raina"


  Ɗagowa yayi da fuskarshi wadda tuni ta jiƙe sharkar da hawaye, cikin rauni na murya yace"baba, Bana jin daɗin yadda wasu suke guduna saboda rashin asalina, meyasa sauran mutane ba kamar kai da daddy mubarak suke ba"? Zuciyar baba obie ba karamin karaya tayi ba, nan take ya gane gori akayi masa, bawan Allah tsantsar tausayinsa ne yakama shi.


  Cigaba da yin magana yayi"Na tsani kaina baba, Rashin asalina Yana neman Yaja min na rasa abunda nakeso, kowa ya buɗi baki sai yace ni ɗan mai aikine bani da asali, Har shege ake kirana baba" daƙyar ya kare maganar wani irin kukane Yaci karfinsa da sauri Baba obie Ya janyoshi zuwa jikinshi sosai Ya rungune shi, Yana lallashin shi.


 "Toh toh ya isa ka yi shiru, Bana son Kana sanya damuwa aranka, Kukan Ya isa haka, kowani ɗan adam da ka gani a duniyar nan da irin tashi ƙaddarar, babu wanda Allah baya jarabta, inaso ka rungumi wannan amatsayin ƙaddararka, Kada ka ta6a bari wani Yasa ka canza tunaninka, Allah Shi yake son ganin rayuwarka haka, Kuma shine zai nema maka mafita"  nasiha mai ratsa zuciya baba obie Yaci gaba dayi mashi har saida yaji ya daina kukan tukunna Ya raba shi daga jikinshi

Cikin kulawa yace dashi"Yanzu fada min wanene Ya tsokane ka"? 

 Shiru yayi batare dayace komai ba, baba obie ya fahimci bayason ya sanar da shi, hakan yasanshi cewa"Ko da yake basai ka fadamin ba, ni da kaina zan binciko wanene, kuma zan hukuntashi" ya fada yana daure fuskarshi alamar ranshi ya 6aci.


     "Baba," Kallon shi obie yayi ina sauraronka

 "Kamar yadda nasaba fadamaka,Yau ma zan maimaita maka, Ni dai inason family ɗinka, Ina alfahari daku, nayi fatan ace nima ina ɗaya daga cikin jikokin ka sai dai Allah bai nufa"


 Wani irin annurin farin cikine Ya bayyana akan fuskar baba obie.


  "Jazz baka ɗauke ni kamar yadda na dauke ka ba, ko da yake ba laifinka bane, laifin wadanda suke yi maka gorine, sune sukasa kake jin kanka bare afamily dina, amma inaso kasani, baba obie baya yi maka kallon bare, inasonka jazz kamar yadda nakeson jikokina, Kamar yadda kake fatan ka zama daya daga zuri'ata nima haka nake fatan ka kasance" yayin da baba obie ke yin maganar, wani irin sanyi da daɗi ne ke tsuma zuciyar jazz, har abada bazai ta6a mantawa da halaccinsu agare shi ba.


  Ganin Ya faranta masa raine yasa baba obie cewa"namanta ban tambayeka ba, Ya jikin naka"?


 Fuskarshi dauke da murmushi Yace"naji sauki, nagode na kulawarka agareni"

Jinjina kai baba obie yai"gobe idan Allah yakaimu, Ina fata zaka halacci Dinner din Hateem"


 Jim ya ɗanyi harga Allah baison zuwa kodan gudun a ci mutuncinsa, amma saboda yana son ya faranta ma baba obie yasa shi cewa "In sha Allah tare dani za'a buɗe taro"


Murmushi baba obie yai masa"Naji dadin jin hakan rabin raina.


  Jan shi da fira baba obie yai, kamar wani abokinsa, tuni jazz ya saki jikin shi.



*💋 UMMIN AMERICA❤*



Duk Yinin Yau Bata fito daga ɗaki ba, ta killace kanta tun safe bata jin daɗin zuciyarta, duk ta ƙuntata kanta, tayi jiran zuwansu unaisah su shigo don su ɗe6e mata kewa sai dai shiru babu alamarsu, tuntana sa ran ganin su har ta fidda ranta, ta ƙundundune kanta cikin lallausar bargonta, Sallah ce kaɗai take tada ta daga saman gado

Har ta fara nutsawa cikin baccinta kwatsam wayarta dake ajiye kan nightstand ta soma yin ruri, da wata irin kasala ta ɗago da kanta, sumar kanta duk ta hargitse babu gyara, laluba Hannu tayi ta kamo wayar batare data duba sunan mai kiranta ba tayi picking tare da kara wayar a kunnanta.


   Sautin Muryar NATASHA ne ya Daki Dodon Kunnanta"nayi fushi Kin manta dani ko"?  ta faɗa cikin harshen turan ci.


Muryarta da kasala Ta furta"ba haka bane Natasha, Kina araina, dake nake kwana dake nake tashi"


 "Ban yarda da kalamanki ba Ummi, Idan Dagaske kinyi kewata meyasa baki kirani ba? Sai da na kira ki ni da na damu dake ko"?


  Shiru tayi na ɗan wani lokaci har sai da Natasha Ta furta Naji kinyi shiru tukunna taja numfashi tana faman sauke ajiyar zuciya tace"bansan yadda zanyi maki bayani ba NATASHA, ni kaɗai nasan halin da nake aciki, ina cikin damuwa, Ina cikin kaɗaici, Rayuwata a ƙuntace take natasha, bani da wani ƴan ci, ba wanda Ya damu dani, tun safe bana jin daɗin jikina babu wanda ya leƙo ɗaki na don Yaga awani hali nake aciki....   "Muryarta na rawa ta ƙare maganar, tamkar zata fashe da kuka, hakan Ba ƙaramin ɗaga Hankalin Natasha Yayi ba, Jin sautin miryar aminiyarta da alamun matsananciyar damuwa..

 Cikin saurin mirya ta furta"Ummi,  muyi magana ta video Call, Inason naganki ko hankalina Ya kwanta"


  "Toh, amma kafin nan zan shiga toilet,  Ƴan mintuna kaɗan Idan na fito zan kiraki" natasha ta amsa mata da toh, bayan ta yi rejecting Kiran, ta daura wayar kan drawer, kafin Ta sanya hannu ta yaye bargon data lullu6a da shi, Jallabiya ce a jikinta launin dark ash, saukowa tayi daga kan gadon ta nufi toilet, After Some minutes ta fito fuskarta da alamun lemar ruwa, Laptop dinta dake ajiye kan desk ta dauko ta koma kan gado ta zauna daga tsakiya ta ajiyeta agabanta, kafin ta buɗe ta soma sarrafata, Natasha ta kira video Call nan take ta ɗaga, kallon juna suka soma yi tamkar suna a wuri ɗaya, Natasha tana a kishingiɗe saman beach chair dake a ga6ar teku, babu suturar mutunci a jikinta, dama ita bata cika son sanya suturar da zata rufe mata tsiraicinta ba, tafi sha'awar ta sanya pant da bra.


cikin harshen turanci suke yin magana. 

"Yanayin fuskarki Ya tabbatarmin da bakyajin dadin Ummi, Ki faɗamin meke damunki? Waya ta6a min ke"?


Yamutsa fuska Ummi tayi tamkar batason furta maganar tace"kamar yadda na faɗa maki bana jin daɗin jikina, narasa gane meke damuna, amma ina da tabbacin hada kaɗaici, ban ta6a ƙuntataba Irin na Yau, Jin kaina nake tamkar Ina a prison"


 Cikin kulawa Natasha tace"meyasa ba zaki janye aikin da Commender Ya baki ba? Ummi dama ni nasan bazaki Iya jurewa ba, tuntuni naso In gargaɗeki saboda ba zaki Iya ba, mu da muka saba da yawo kullum sai mun fita wurin abokan harkar mu, taya zaki Iya jure rayuwar kulle"? Ta faɗa tana mai dubanta,

Dafe kai Ummi tayi da hannu ɗaya"Har yanzu banyi danasanin kar6ar aikin kula da yaran nan ba, Saboda Inaji araina akwai wani alkhairi atattare da zamana da su, shiyasa bana danasani, ni kawai abunda ke damuna rayuwar kullance ke banaso, Yana ƙuntata Rayuwana, hada ƙarin Yaran da suke ɗebe min kewa basu zo wurina ba yau, ni kuma nakasa tashi naje gare su" fuskarta a yamutse tayi maganar

 "Har Yanzu ba zaki fahimce ni ba Ummi, Ni inaso na kwatarmaki ƴan cinki ne, Inason farin cikin ki, Kina buƙatar abokan Harka, kefa ba irin matan da za'a ƙuntata ba ne...'  tunkan Natasha ta ƙare maganarta, ummi tayi saurin tarar numfashinta da cewa


  "Akwai labari mai daɗi, nasan idan na fada maki zakiyi mamaki"


  Ta faɗi hakan ne don batason Natasha taci gaba da yi mata zancen Ajiye aikin da take Yi.


  "Naƙosa naji labarin nan fadamin mana" ta fada tana sakin murmushin shaƙiyanci.

  

  "Mutumin Ya ziyarce ni Har cikin gidan da nake,"


 Waro idanu waje natasha tayi da mamaki ta furta kina nufin Big Boss? Ya ziyarce ki? Ɗaga mata gira ummi tayi alamar eh.


"Amma  ya akai ya iya shigowa gidan Jami'an Isod, bayan kin faɗamin acikin sharuddan da suka baki, babu shige babu fuce basu buƙatar wani naki yazo inda kike, har zuwa lokacin da kika kammala Yi masu aikin su" ta faɗa a kagare da son jin ƙarashen xancen.

 Dariyar shaƙiyancin Ummi tasaki tamkar babu damuwa aranta"kinsan mutumin na dabanne, ni kaina bansan tayaya akai ya shigo gidan ba, Har tambayarshi nayi sai yace min idan na yarda dashi indaina tambayarsa.... " dariya natasha tayi cike da nishaɗi tace"Namijin Duniya, Nayi kewarshi ummi, kullum cikin begen ganinsa nake yi, yayi min nisa yanzu, ba kamar lokacin da nake yi mashi rainon babynsa Pretty ba, tun da Ya kar6i Yarinyar sai nayi dagaske nake ganin shi, ko wayana baya picking...  " kafin Natasha ta ƙare maganar Ummi tayi hanzarin tarar numfashinta da cewa"wai ina yarinyar take ne? Na jima ina son na tambayeki ita, nayi missing dinta, tun ranar dana fara Yin tozali da ita naji kaunarta ta shiga raina, duk da bata jin magana amma tana da kyau"

 Natasha tace"hmmm, Ummi Ya raba ni da ita, tsawon watanni, duk idan na tambayeshi ina baby Pretty na sai yace min ya mayar da ita wurin mamanta, har alfarma na nema awurin shi akan ya amince min inbiyo shi nigeria saboda ina son ganinta amma Ya hanani....   "muryarta na rawa ta ƙare maganar idanunta sun cicciko tab da kwalla.


  "Ummi Inason yarinyar nan, Ina ƙaunarta, nayi fatan ace ni na haifeta ko dan saboda mu kasance atare har abada, mun shaƙu da juna, na saba da ita, Amma yayi min yankan ƙauna.... " tunda tafara magana ummi ta natsu tana kallon fuskar Natasha ta cikin screen din laptop tamkar suna awuri ɗaya.


 "Ummi nasan zaki Iya taimaka mani, tunda Yana kaunarki, Yasha fadamin ke kadaice kike Iya sarrafashi son ranki, please kiyi amfani da damar da kika da ita, Ki lalla6a shi Ya dawo min da baby pretty" cikin sanyin Murya ta ƙare maganar, Ummi dake kallonta tuni tausayinta Ya kamata, bata ta6a ganin Natasha tana zubar da kwallarta akan wani ɗan adam ba sai akan babyn da take mutuwar so, tasan da irin kaunar da take yima yarinyar a lokacin baya.


  Cikin kwantar da murya ummi  ta furta"Am sorry, Kinsan bana son ganin hawayenki, zan Iya yin komai akanki, saboda halaccin ki agare ni, Kin wuce ƙawa a wurina sai dai ƴar uwa, saboda kin kaunace ni a lokacin da kowa yake guduna, abun da nakeso dake ki kwantar da hankalin ki, zanyi kokarin ganin na shawo kanshi don ya dawo maki da babyn ki"

Murmushin farin ciki natasha tasaki tana fadin"thank u ummi, nasan zaki iya yin komai saboda farin cikina, shiyasa nake ƙara kaunarki, ina nan ina shirye shiryen zuwa Nigeria saboda ke"


  Martanin murmushin ummi ta mayar mata,

   "Ina handsome boy din nan, namanta ban tambaye ki shi ba"


   "Bashi da lafiya, Yana a kwance"

Yamutsa fuska Natasha tayi"najiye mashi ba dadi, Allah Ya bashi lafiya, har yau ban manta da fuskar shi ba"

 Murmushi Ummi tayi mata" dama ke ay bakya mantawa da abu mai kyau, naga kin kirani da layinki Na england, hakan na nufin kin koma gidanki"?

 Ɗaga mata gira tayi alamar eh. Jinjina kai ummi tayi, shiru sukayi na wani lokaci yayin da suke kallon juna batare da ƙyaftawa ba.

  "Kin tsareni da ido Kina kallona, Kamar akwai wani abu da kikeson fadamin" acewar natasha ta faɗa tana ɗage mata gira.

  Dariya Ummi tayi, Harta Buɗe baki da niyar furta magana, Sautin knocking ƙofar da akayine Yasa ta fasa yi mata maganar,

"Zan Kiraki Anjima Ki kula min da kan ki" 

 "Bangaji da jin muryarki ba ummi, amma shikenan zan jira zuwa anjiman inma kin manta baki kirani ba, Ni zan Kira ki, ki kula min da kanki and pls ki daina sanya damuwa aranki" a hankali ummi ta furta mata"toh, nagode da kulawarki agare ni" bayan sunyi sallama, Ta kashe video Call din, ta sauko tare da laptop din a hannunta, ta  nufi desk ta ɗaurata, kafin ta shiga wurin closet dinta, mayafi ta daura akanta.


    ɗaga Murya ta yi Wanene"?

Daga waje tajiyo Muryar Batool Tana fadin"aunty Ummi ni ce" wani irin sanyi ne ya ratsa zuciyarta jin muryar Batool.


   "Ki shigo daga ciki," turo ƙofar batool tayi tare da shigowa ciki, tana bin dakin da kallo kafin ta ɗaura idanunta akan fuskar Ummi, Murmushi suka sakarma juna

  "Nayi fushi Batool, sai yanzu zaki tuna dani? Nayi tsammanin kece mutun na farko da zaki zo gare ni idan kika ji shiru ban fito ba, amma sai naji shiru babu ke babu unaisah" tafaɗa tana haɗe mata fuska alamar ranta Ya 6aci.

  "Aunty ummi am sorry, Kina araina, tun ɗazu nake taso in shigo wurin ki'

Miƙa mata hannu Ummi tayi da sauri Batool ta ƙarasa gabanta tare da faɗawa kan chest dinta, sosai Ummi tai hugging dinta.


   "Nayi missing dinki My babe, kun barni a daki ni kaɗai inata kewarku, Ina unaisah ne"! Ta faɗa batare data raba jikinta daga na batool ba.


  "Nima bansan inda take ba, ɗazu muka rabu"

 "Okey,ina fata kina lafiya, " ɗago dakai Batool tayi"Lafiyata lou, amma ke kamar baki da lafiya"

 Shafa gefen fuskarta ummi tayi"bana jin dadi, amma kada hakan Ya dame ki, ganinki da nayi ya faranta raina" ta ƙare maganar tare da ruƙo mayafin Pakistan din batool"kayan sunyi maki kyau sai naga kinyi min kama da wata Old friend ɗina da muka rabu da dadaɗewa, kamar ita ta haifeki, Itama doguwace fara, Mom dinta balarabiya ce"

Murmushi batool tayi"amma ni da Unaisah nake kama"


Girgiza kai Ummi tayi"No, baki kama da Unaisah kun dai yi yanayi da ita"


Kwa6e fuska Batool tayi saboda ita tafison ace tana kama da Unaisah, ummi ta fahimci hakan sai tayi saurin cewa"wasa nake maki, dama don in ga reaction dinki ne, gaskiya kuna kama da ita sosaima kamar twins" jin hakan yasa batool sakin dariyar farin ciki, ummi dake kallonta batayi mamakin hakan ba ta riga data fahimci tsantsar ƙaunar da suke ma junansu.


  "Mu zauna ki tayani fira, Ko baki gaji da tsayuwa bane"


 "Aunty ummi, nasan kina jin yunwa, ki tafo muje falo zan sama maki abunda zaki ci" wani irin kallon ƙauna ummi keyi mata ba ƙaramin dadi take ji ba idan Batool ta nuna damuwa akanta.

  Ruƙo hannunta ummi tayi acikin nata atare suka fito daga dakin. 


Sautin Muryoyinsu Naufal ne Yajawo Hankalin Ummi Ga kallon su, tun Dazu suna a falo, Tare da Boss Man, Sun tasa shi gaba sai surutu suke zuba mashi.


 Jin takun Takalmansu Yasa su dagowa suka kalli su Ummi dake saukowa down stairs, Har suna haɗa baki wurin ambaton sunanta Aunty Ummi.

 Saukowa Jamimah da azeeza su ka yi daga kan sofan da suke zaune, da gudu suka nufe ta, Hannah da Parveen ma suke miƙe suka nufe, wani irin daɗi taji aranta,

Ɗaya bayan ɗaya ta soma rungumarsu a jikinta,

  "Aunty Ummi, Yanzu kika tashi daga bacci"? Azeeza ce tayi mata tambayar

Girgiza mata kai tayi alamar a'a

Parveen tace"Ko dai baki lafiya" Harara Ummi ta jefa ma Parveen tare da cewa"kun damu dani ne? Meyasa ba ku zo bedroom ɗina kun duba ni ba? Shiru sukayi sai jamimah ce tai kokarin cewa"mantawa mu ka yi" Jan kumatunta Ummi tayi da hannu"Aku sarkin ɗumi, Na riga da nage baku kaunata, Shiyasa baku damu dani ba" ta faɗa haɗi da marairaice masu fuska,

"Wallahi aunty Ummi Muna ƙaunarki, kuma mun damu dake" Hannah ce tayi maganar 

"Ni dai Inasonki aunty Ummi, kiyi hakuri  idan mun 6ata maki rai," murmushi ummi tasakar ma Azeeza da tayi maganar.

Ruƙo hannunta Jemimah Tayi"Aunty ummi nima ina sonki" 

"Naji na Yarda kuna sona, Yanzu mu shiga ciki," ta fada tare da Jan hannun Batool suka nufi ciki tare da su Hannah 

 Tunkafin Su ƙaraso, Boss man Yake Kallon Ummi, sam ya manta da ita.


"Barka da hutawa Yalla6ai, Fatan ka wuni Lafiya, Ya iyali" 

A hankali Ya furta"Lafiyalou Ummi, Ina fata kema haka"? Ɗaga mashi gira tai alamar eh, ta faɗa tare da samun wuri saman Sofa ta zauna, suma sauran duk suka zauna.


   hankalin Sajeed na akan screen din wayar Unaisah, Haris da javed suna zaune gefe da gefen shi tare da naufal sai kallon Game din da Yake bugawa suke yi, baijima da sauke shi akan wayar ba.


 Gyaran Murya Ummi tayi masu atare suka dago suna kallon ta.

 "Sannunku, ba hello ba Hi kun samu Waya kunata danna waya baku ita ne"

"Ta Unaisah ce," Acewar Sajeed

 Da mamaki Ummi tace"Unaisah ke da waya iphone15pro? Amma ban ta6a ganinta ba"

"Dr Laurace ta bata Kyautarta, ɗaya daga cikin Likitocin da suka yi jinyarsu a america"

Boss man ne Ya bata amsa, Jinjina kai tayi.

"Ina ita Unaisah dinne"? Tayi tambayar tana kallon su

 Boss Yace"Bansan meya tsayar da ita ba, tunɗazu da muka shigo tare da big guy Ya tafi da ita zai nuna mata kitchen din gidan nan ban ƙara ganin ta ba, ba mamaki ta tsaya taya masu aiki girkin dinner"


"Dan Allah ka nuna min kitchen din, Inaso In kar6o ma aunty Ummi abinci, Yunwa take ji"  acewar Batool.

Murmushi boss man Yayi yana dubanta yace"kin damun da auntyn nan naki da alama, kada ki damu, bari na kira big guy awaya, idan suna a kitchen din zansa akawo mata abincin.... " kafin Ya ƙare maganar, Parveen tayi saurin cewa"Dan Allah Nima zanci" dariya sukayi gaba dayansu.

Ummi tace"foodie, Baki Gajiya da cin abinci, shiyasa kika fi sauran ƴan uwanki jiki"

Kwa6e fuska tai"ay bani kadai bace me cin abincin ba, Ki kalli kumatun jamimah sunyi manya manya da su" maganarta ta basu dariya.

Harara jemimah ta watsa mata"ay dai ban kaiki Cin abinci dayawa ba, Ni madara da bonbita nake sha, Sai dafaffan kwai da Fika fikin Kaza," boss dake kallonsu murmushine dauke akan fuskarshi, Firarsu ba karamin nishadi take sanya shi ba

Wayarshi Ya zaro daga aljihu Ya danna ma Big guy kira, Bugu uku Yayi Picking


  Miƙewa yai da sauri Ya nufi cikin falon nesa da su ya tsaya saboda hayaniyarsu.


 "Malam Ina ka shiga ne? Ka tafin mun da rabin raina"


 On the other hand sautin dariyar Big guy ta karaɗe Kunnuwansa,


 "Nifa Yanzu Haka Ina daki kwance saman gadona"


"Bana son Iya shege, To ita ina kabarta?

  

 "Ka riga da kasan Halin Jarin naka, yarinyarce da kiriniya, Tunfa dazu dana nuna mata kitchen din nace mata ta dawo cikin yan uwanta, bayan na fada mata hakan na wuce room dina, yanzu haka bata wuce kitchen din, Cikin kattai" ya karasa maganar Yana dariya.


 Daure fuska boss yayi tamkar Yana agabanshi, 

 "Zamu hadu dakai ne, Allah idan wani abu Yasamu Yarinyar nan jikinka ne zai gaya maka dan rainin wayau" ya fada tare da yin rejecting kiran,

Cikin takun sauri Ya nufi hanyar zuwa kitchen din, ba laifi akwai tazara tsakanin kitchen din da main falo,


Lokacin da Ya Isa katafaren kitchen din gidan tamkar a restaurant tsabar haɗuwarshi, kai kace ba wurin Girka abinci bane saboda girman shi da ƙawatuwarshi, An zuba kayan aiki masu tsada da inganci, gaba ɗaya masu girka abincin Gidan Jami'an Isod ne cikin chef'uniform, matasan samari masu jini a jika, daga ganin Yadda suke aiki zaka shaida kwarewarsu a 6angaren catering, ko mace bazata nuna masu Iya sarrafa abinci ba, A ƙalla sunkai su Bakwai, Babu wanda Ya lura da shigowar Taj acikinsu, Gaba ɗaya Hankalinsu na akan Unaisah, dake agaban kitchen island tana Yanka masu kayan Lambu, abun da ya ɗaure ma taj kai, ganin Yadda sukayi mata rumfa kamar zasu haɗiyeta tsabar yadda suke binta da mayataccen Kallo, Ta saki baki sai Labari take basu su kuwa sun Kasa kunne suna sauraron daddaɗar muryarta, Tunda suka kafe ta da idanunsu ko kyaftawa basa yi kamar zasu haɗiyeta.


 Gyaran Muryar da Taj yayi masu ne Yaja Hankulansu ga dubanshi, kamar sunga wani mugun abu, A gaggauce su kayi saurin barin Inda Take, kusan atare suka buga ƙafa Haɗi da sara mashi.

Kallon Harara Ya watsa masu, Cikin harshen turanci Ya furta"wannan wani irin gangancine zaku bar Yarinya tana amfani da wuƙa? Kun wani tsareta da idanunku kamar zaku lashe ta" Sunnar dakai su kayi Suna faman sosa keya suka hada baki wurin furta"sorry Sir, ba laifin mu bane, Itace ta buƙaci damu koya mata girki, munyi kokarin Hanata amma saita sanya mana rigima"

Wurga eye balls dinsa Yayi akan Unaisah dake Kallon shi, Har ta ajiye wuƙar hannunta, nufo shi tayi fuskarta da murmushin Yaƙe tace"ay ni nace su bani In tayasu aiki, Kuma dama Na iya ba yar koya bace" ta fada tana ruƙe qugunta da hannu.

 Wani kallo Ya jefa mata me kama da harara, bakomai Yake tunawa ba face lokacin da tana yar ƙaramarta, ranar daya tafi aiki yabarta a gida tana jin yunwa taje ta  kunna cooker gass da sunan zata yi girki, wuta ta kama a gidan, wai yau itace take mashi kurin ta Iya girki ba yar koyo bace? Girgiza kai Yayi haɗi da yin murmushi tacikin face mask dinshi

 "Daughter, ƴan uwanki sunata nemanki, Yakamata Kizo Mu koma falo" maƙe mashi kafaɗa tayi"ay bamu gama girkin ba"

 "Bana son gaddama, zo ki wuce mu tafi"

 Marairaice mashi fuska tai"dan Allah kabarni wallahi inason In Iya girki kala kala,"

"Kada Ki damu, zansa a koya maki amma ba yanzu ba, dokar Aikin mu ce mace bata shiga hurumin mu, baki ga maza bane a kitchen din"? Cikin lallashi yayi mata maganar Yana nuna mata chefs din dake tsaitsaye cirko cirko suna kallon su

"Yalla6ai, da dai anbarta ta koya tun da ta nuna tana so, kuma ni aganina maca ce ita, wata rana zataso tayi ma mijinta.... "Tunkafin chef din daya dauko Maganar Ya karasa boss Yayi mashi wani kallo mai nuni da kashedi, Hakan yasa shi yin saurin Katse maganar, 

Janyo hannun Unaisah Yayi dakarfi Ya fito da ita daga kitchen din, Chefs din basu ji dadin zuwan Shi ba, Ya raba su da Yarinyar data ɗe6e masu kewa yau, zuwanta Ya faranta masu rai, sunji dadin surutun da tadinga yi masu, komai nata burgesu Yake yi.


Ranta Ya 6aci, Ganin yadda ya janyota daga kitchen din, da sauri ta fusge hannunta tana fadin"Ni ka ƙyale ni, in tafi da kaina" Ta faɗa tana daure mashi fuska, Sam Yakasa ce mata komai sai dai kallonta da yake yi.


"Bansan meyasa ka takura rayuwata ba, girki fa kawai na roƙa kabarni In tayasu amma ka hanani, dan Allah menene alaƙata dakai ne? Na lura so kake kana Yin iko dani, Idan don saboda taimakon da kukayi mana ne ay dan Allah ku ka yi ko"? A fadace ta faɗa tana zare mashi gray eyes dinta tamkar zata rufe shi da bugu,

Har saida Yaji gabanshi Yaɗan fadi, sauƙinta ma yasan halinta,

 "Meyasa ni kadai kake ma haka? 

"Saboda ke jini na ce" a zuciyarshi Ya furta maganar

  "Kiyi haƙuri Idan na 6ata maki rai, bana son 6acin ranki, Ƴan uwanki ne suke ta nemanki, bayan haka kamar yarda na fada maki dokar aikin mu ce mace bata shiga hurumin mu, waɗannan chefs din da kike gani dukansu a lokacin baya ba mutanan kirki bane, Dayawansu Ƴan shaye shaye ne da masu bin matan banza, wasun su mugayen ƴan ta'adda ne wadanda suka gagari Iyayensu da hukuma, Ire iren su chief Yake kamowa Ya koya masu hankali, Idan suka shiryu sai ya maida su Jami'an Isod..."


  Waro ido waje tayi jin Ya ambaci mugayen ƴan ta'adda.


  "Ba Zanso abun da zai cutar min dake ba, Haƙƙina ne kula da rayuwarki Unaisah dan Allah kada ki hanani Yin aikin lada... " in cool voice ya faɗa...


 Wani irin kallo yaga tana bin shi da shi, kamar akwai wani abu da take son ganowa

 Muryarta na rawa ta furta"dan Allah ka cire min face mask din fuskarka inason ganinka"

 Girgiza mata kai yayi"zaki ganni amma ba yanzu ba, amma meyasa kike son ganin fuskata"?

 "Saboda muryarka, tayi min kama da ta daddyna wallah sai nake ji kamar daddyna ne kai, duk da nasan ma ba shi bane, ina ji araina baya araye ma"  idanunta har sun ciko da kwalla.

  "Kina ji aranki ni daddyn ki ne" ɗaga mashi kai tayi alamar eh"

 "Ki ƙaddara aranki cewa Ni ne" ya faɗa tare da ruƙo arm dinta, Ya janyota jikin shi, haɗi da kwantar mata da kanta saman kirjinsa, wani irin sanyine taji ya ratsa zuciyarta, lumshe idanunsa yai a hankali ya sanya hannu tare da zame face mask dinsa, Sumbatar head dinta yai, kafin da sauri ya maida mask din fuskarsa.

  Tsawon mintuna biyar cuf suna manne da juna, sai daga bisani ya raba ta da jikin shi, baiwar Allah jikinta yayi sanyi tamkar an watsa mata ruwan sanyi,

 Shafa gefen fuskarta yayi da tafin hannunsa"Ina sonki my daughter" murmushi tayi mashi"Nima ina sonka daddy na"



*Daga Alƙalamin Boss Bature💋✊✍️*


*(Kaɗan daga cikin na sati mai zuwa idan Allah yakaimu da rai da lafiya,  unaisah zatayi waya da Benazir😍  Garkuwa zaiyi tashin bazata, kada ku bari abaku labarin walimar hateem😂🤣 Ni kaina zumuɗin ta nake yi🔥🔥🔥)* 


 *Littafin kurkukun ƙaddara 500 ne, dukanshi Book One two and 3 Idan kin shirya biya ga Details da zaki tura*


3196407426


First bank 


Bature Hafsat Muhammad,


 *bayan kin tura zaki bada transaction reciept ko screenshot na debit alert a matsayin shaida ta wannan layin 08169856268*

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post